Author : EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category : KDP NOVELS
saboda kamar daga sama ya ji muryata a dodon kunnensa, da sauri ya juyar da hoton ya ɓoye fuskar wacce ke jikin hoton cike da rashin gaskiya ya kalleta sai kuma ya ɗaure fuska ba tare da ya ce da ita uffan ba ya miƙe ya shige bathroom ta bishi da kallo still tana dafe da ƙirjinta dake barazanar rabewa gida biyu. Tasan miskilanci irin na mijinta ba zai taɓa faɗa mata wacece ta jikin hoton da yake kallo ko da kuwa za ta mutu ne. Wani irin zazzafan kishi ya rufe ta har wani ɗaci-ɗaci take ji a maƙoshinta Hajiya Safiya mace ce mai ɗan bala'in zafin kishi. Tana masifar son mijinta duk da shi a wurinsa sunan sun yi aure ne kawai amma babu wata kyakkyawar fahimtar juna a tsakaninsu kullum yana busy bashi da lokacin ta ko kaɗan.
#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.
Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/25/2023, 12:47 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
*AREWABOOK*Jedddah3256
#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels
036.
Shiru-shiru Hajiya Safiya tana jiran Aliyu na uku ya fito daga bathroom ya bata gamsasshiyar amsa akan baturiya da yake kallon hotonta, da taga shiru nasa yana neman ya yi yawa sai ta tashi ta nufi ƙofar bathroom ɗin ta shiga knocking tana kiran sunansa "Abbu! Lafiya kake kuwa?"
Saurin kunna shower ya yi ya nuna mata wanka yake yi tuni ta fahimci manufarsa baya so magana da ita don haka sai ta juya ta fice daga ɗakin nasa, zuciyarta tana kisimamata abubuwa da dama. Duk tsawon shekaru nan da suka yi aure take fuskantar rashin kulawarsa a gareta babu wata shaƙuwa irin ta miji da mata a tsakaninsu, duk da a fannin shimfiɗarsu yana ƙoƙarin gani ya sauke hakkinta dake wuyansa. Bangare dukiyarsa ma yana hidima da ita da yaranta duk abinda suka nuna so suna bukata komai tsadarsa take yake fitar da kuɗi ya siya musu wannan abin, sai duk wadannan abubuwan da Aliyu na uku yaga ya wadata matarsa dasu a wurinta aikin banza ne domin ta rasa wani bangare na mijinta.
*CIROMA DA GALADIMA*
"Kwatar da hankalinka Ciroma ai abin nema ne ya samu wai mata ɗan sanda ta haifi barawo, don kawai mai martaba bai mutu lokaci guda ba hakan baya nufi da aikin mu warware ba. Ko yanzu za mu iya ƙarasa shi amma kafin sannan me zai hana ka sake komawa wajen wannan malamin naka ka faɗa masa yadda aikin naka ya kasance idan da wani taimako sai ya taimaka mana.
Shiru Ciroma ya yi yana kara nazarta maganganun Galadima kafin ya nisa tare da sauke naunnayar ajiyar zuciya "maganarka abar dubawa ce Galadima gobe da sassafe mu haɗu anan sai mu dunguma ga baki ɗaya mu je wurin mai Gundulelliya ɗin gara ayi komai akan idanunka saboda mun zama partners.
"Haka ne gaskiya gara mu tafi ɗin ai mai nema na tare da samu kada ma wannan ya sanyaya maka gwiwa Allah na tuba Ciroma yadda mai martaba yake kwance nan ai da matuƙar wahala ya ƙara tashi da ƙafafuwansa.
"Gaskiya kam da wahala ya tashi faratt ɗaya domin kuwa mai Gundulelliya ya tabbatar min idan har bai mutu ba zai kwanta matsananciyar jinya.
Ciroma ya faɗa da wani murmushin zallan mugunta akan fuskarsa.
"Ai kuwa gashi nan ya kwanta domin banbancinsa da mataccen kaɗan ne.
Kafin ma yasan inda yake tuni mun gama cimma burin mu.
"Ni fa Galadima na kasa bari mamakin Fulani karama wannan matar cikakkiyar 'yar wasan kwaikwayo ce ka ga yadda ta bi ta birkice, sai ka ce ba da hannunta ta zubawa mijin nata guba ba.
Sai kawai suka sheƙe da dariya, takon tafiya suka ji akan dry grass na tarin bishiyoyi dake zube a cikin lambu suke kusan a tare suka miƙe tsaye cikin kaɗuwa suke kallon juna kafin da sauri suka nufi gun da suka ji sautin ya ƙaru saboda wanda ya yi musu laɓe ya ɗiba da gudu ne. Hankali tashe Ciroma ya shiga kwallawa bayi dake cikin gidan gona kira ya umarce su da su bi bayan mutumin kada su bari ya sha kodai su kawo shi a raye kuma su kawo masa gawarsa. Tun mutumin yana iya gudu da dukan ƙarfin sa har ya zo ya fara jigata, kasancewar tsufa ya fara riskarsa fahimtar ya yi ba zai sha daga hannun waɗannan azzalumai ba sai ya ciro wayarsa da ya nade zantukan Galadima da Ciroma ya kira wata number ya yi magana wacce bata wuce ta mintuna uku ba ya kashe wayar, ya ƙarawa gudun nasa ya shiga wata duhuwa mai sarƙaƙƙiya ya boya a ciki yana ji maganganu bayi amma bai motsa daga inda yake ba yana kallonsu suka ƙara kwasa wa da gudu suka nusa cikin jeji, shi kuma ya fito daga maɓoyarsa ya nufi gindin wata bishiya ya haƙa rami tare da ciro wata baƙar leda cikin aljihunsa ya kashe wayarsa ya naɗe ta ciki ya binne ta cikin ramin.
*ALH BASHIR MANSION*
Acikin kunnensa aka kira sallar asuba, idan yace ga baki ɗaya wannan daren ya samu bacci mai daɗi ya yi karya. gaba ɗaya wannan daren yazo masa a birkice har addu'a yake Allah yasa daren ya yi ta tsayi kar gari ya waye, har lokacin da ake kokarin tada sallah acikin kunnuwansa amma sai ya tsinci kansa da kasa tashi jikinsa tamkar an ɗaɗɗaure masa shi da sassari da kyar ya yi karfin hali miƙewa tsaye yana jin yadda kansa ya yi masa wani irin nauyi saboda baccin da bai samu ya yi ba. Hakanan ya daure ya yi wanka ya dauro alwallah a gurguje ya saka jallabiya a jikinsa ya wuce zuwa masallaci lokacin har an tada sallah. kusan karfe bakwai suka fito daga masallaci shi da Daddy ya gaishe da Daddy, kallan idanunsa Daddy kurum yake wanda babu wadataccen bacci acikin su, "Bayan saukowa daga masallaci ne daurin auren kana da lokaci har na awa bakwai ka je ka samu kayi bacci ,zan jira ka zuwa karfe goma ka fito muyi break fast. Da mamaki yake kallon Daddy tun kafin ya furta Daddyn ya katsesa yana faɗin."na sani zan jiraka ka je kayi baccinka.
Daddy ya faɗa yana nufar part ɗinsu shima AB ya juya zuwa nasa,kamar yadda Daddy ya umurce sa ya hau gado ya kwanta kuma cikin sa'a baccin yazo masa. ƙarfe bakwai da rabi Mami ta turo kofar ɗakin nata, kwance take cikin kyakkyawan gadonta daga ita sai towel ajikinta tayi rufda ciki tana baccinta cikin natsuwa, kallonta kawai Mami take cike da takaici ta tabbata wanka tayi niyar shiga ta buge da komawa ta kwanta dan tun jiya da Daddy ya yi mata maganar kar Aydah ta fita makaranta a yau bata faɗawa Aydah ba. Mami dai ta tsaya tanata bin Aydah da kallo tamkar mai son ta gano wani abu a jikinta wani abu taji yana tsaya mata a wuya idan kuma ta tuna wai nan da wasu awanni Aydah ɗin za a daura aurenta da Abba sai zuciyarta ta kara dagulewa ta rasa meyasa har ranta take jin bata son wannan auren ta rasa meyasa take jin babu daɗi har acan kasan zuciyarta har ga Allah akwai mugun kwaruwa acikin auren Aydah da AB to duka -duka Aydah nawa take me ma ta sani acikin rayuwar Auren saboda kawai daukar hakki da zalunci irin na mahaifinta zai ɗaura mata nauyin da shekarunta ba su isa dauka ba.
Juyawa kawai Mami ta yi ta rufowa Aydah ƙofar yau ko kitchen bata leƙa ba domin ganin me Huwaila take shiryawa na break fast saboda takaicin Daddy. Kusan karfe 8 na safe ta farko a wani gigice da sauri ta zuro kafafunta daga kan bed , ɗin tamkar zata yi kuka ta nufi toilet babu wanda ya tasheta gashi har ta makara zuwa school agurguje ta watsa ruwa cikin mintuna goma kacal har uniform ta saka babu kowa a parlor lokacin da ta sauko , ɗakin Mami ta nufa kai tsaye knocking ta yi jin shiru yasa ta tura ƙofar kanta tsaye ta shiga ga mamakinta Mami na kwance akan bed sai dai ba bacci take ba, yanayin da ta samu Mami ya ɗan daga hankalinta dan ganin damuwa kwance acikin fusrkarta.
"mami!"Aydah ta kira sunanta da sanyin murya "Karki dameni dan Allah ki fita ki bani waje Zulaiha!"Mami ta kira sunanta baro-baro daman kuma sunan mahaifiyar Daddy ne musamman idan tana cikin fushi haka take kiran sunan nata babu ruwanta ko a gaban Daddy ne. Ganin taki tafiya Mami ta daga kai tana kallonta ta wani daure fuska tana wani daka mata tsawa "ki je ki cire uniform tunda zaman gidan kike so karfe nawa kika sani yanzu?har zata buɗe baki ta yiwa Mami magana ganin tana shirin tasowa yasa Aydah ta fice da gudu tabar cikin ɗakin tamkar zata yi kuka
Kai tsaye part din mahaifinsu ta nufa
ganin bata gansa a parlor ba tasan yana master bedroom ɗinsa ya koma
Bacci TV parlorn kawai ta kunna tayi kwanciyarta anan, ita ma bata daɗe ba wani baccin ya kara daukarta batare da ta yi tunanin cire uniform ba.
Da mamaki sosai Alhaji Sanusi ke kallon matar tasa jin abunda take faɗa, "kin san bana son kalar wannan wasar wannan wane irin aure ne auren ma da Aydah?" wata dariya Alhaji Sanusi ya saki yana kallon matar tasa cike da takaicinsa take faɗin. "Na taɓa yimaka irin wannan wasar jiya Hajiya mariya da muka yi waya take sanar dani ta tabbatar min dacewa yau ne daurin auren Abba da Aydah.
Wata irin zufa Alhaji Sanusi ya fara haɗawa ga baki ɗaya abubuwa ya ji suna neman kwabe masa duk abunda yake shiryawa baya tafiyar masa adaidai lallai wannan karon yayan nasa yayi masa ba zata kuma ya shayar dashi mamaki. meyasa ko a Company bai ji ana maganar ba.?" Wannan karon bai san kuma me yayan nasa ya shirya ba, acan kuma ɓangaren Alhaji Bashir shi kaɗai ya zauna ya yi tunani bai raba card ɗin daurin aure ga kowa ba. Musamman cikin Companyn su gudun matsala da kuma kare martabar Abba Bashir
hasalima Abba kawai ya baiwa card ɗin ya rabawa friends ɗinsa, shima yasan a bangaren Abban ba wasu friends ne garesa ba sosai. miƙewa tsaye Alhaji Sanusi ya yi ya shiga kai da kawo tsakiyar parlor ɗinsa ga baki ɗaya hannayensa sargafe a bayansa. break fast ɗin da ya gama yi yanzu ya ji yana ya mutsa cikinsa da wani irin yanayi cikin fuskarsa yake kallon matar tasa dake ta kallon sa. Wani numfashi mai zafi ya fitar rai a ɓace yake faɗin."meyasa da na dawo jiya baki sanar dani ba?"kin san ko awa nawa ya rage a daura aure taya zan iya dakatar da wannan auren?" ta buɗe idanunta tana kallon mijin nata cike da takaici take faɗin."ƙarfe ɗaya na dare zan zauna parlor ina zaman jiran dawowarka tunda ni na aike ka zaman majalisa har karfe ɗayan dare aini lokacin ban ma san inda kaina yake ba. Kawai ka dauki haƙuri a daura auren. Da yanayin yadda mariya ke yimin magana kamar bata son auren nan na Abba da Aydah yanayin muryarta ya nuna kamar akwai tsanar Abba Bashir a kasan zuciyarta.
Shiyasa ma nake ta sauri na gama abubuwan da zan yi na tafi gidan na sha kallo, shi dai Alhaji Sanusi car key ɗinsa kurum ya dauka ya fice daga Parlor yana kuma neman hanyar da zai dakatar da wannan auren.
Fitowar Daddy kenan daga dakin baccinsa kusan karfe 9 har da mintuna goma a sama da mamaki yake kallon TV dake aiki cikin parlor kafin ya mayarda kallonsa kan Aydah dake kwance tana bacci da uniform ajikinta murmushi kurum Daddy ya yi ya karaso cikin parlor ya ɗan rage volume, zama ya yi yana canja channel zuwa channel ɗin (TVC NEWS)bai jima da zama ba Mami ta karaso cikin parlor cikin shigar alfarma bayanta Siyama ce da dan ƙaramin tray a hannunta ta ɗorasa akan side table dake cikin parlor ta gaishe da Abba,ya amsa cike da fara'a ita da Mami har lokacin idanunta na kan Aydah hannu Mami tasa da niyar ta tasheta Daddy, ya yi saurin dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu. kallonsa Mami take tana jiran karin bayani "ki kyaleta tunda bata tashi ba. cikin ƙunar rai Mami kamar jira take Daddy, ya yi magana ta sauke masa kwadon masifa "A haka kake tunanin aurar da wannan yarinyar Alhaji?" idan taje gidan auren me ma zata iya da kanta za ta ji ko da responsibilities ɗin dake kanta a matsayinta Na matar aure. shi dai Daddy kallonta kawai yake harta gama faɗanta ta zauna tana kokarin jawo ruwan dake cikin flask wanda ta dafawa Daddy ruwan lipton da suka ji citta ,da kanumfari daman a ka'idar Daddy kafin ya yi break fast sune farkon abunda yake sha. Siyama na ganin mami ta fara faɗa daman ta sulale tabar parlorn har yau tana mamakin meyasa Mami bata son auren yaya Abba, da Aydah mutane nawa ne a kauye suka yi aure batare da ma sun kai shekarun Aydah ba. harga Allah tana son Yaya Abba,ya auri autar tasu ko taga haukan da Sadiya zata yi kuma sai yanzu tasan Yaya Abban yafi dacewa da Aydah akan Sadiya, Mami ta zuba masa lipton ɗin acikin tea cup ta miƙa masa ya karba da murmushi kwance a fuskarsa yake faɗin."thank you wife.
ƙara haɗe rai ta yi hayaniyar su ya tayar da Aydah ta miƙe zaune tana saukar da kanta akan iyayen nata,
"Mamana kin sha bacci tana murza ido take gaisheda Daddy, ya amsa yana tamabayarta meyasa ta saka uniform banci yace ba zata je school ba yau."da sauri Mami ta karɓe zancen da faɗin "Sai kace baka san halin rigimarta ba.
"Daddy yau koda na tashi asuba, bana jin daɗin jikina na rasa meke damuna ga yawan faɗuwar gaba.
Murmushi kurum Daddy ya yi dole duk maccen da igiyoyin aure zasu hau kanta sai ta tsinci kanta a irin wannan yanayi. jeki ki cire uniform ki wanke baki zuwa 10 zan fito mu yi break fast kafin nan yayanku ya karaso. Nasan shima yana can yana baccin.
Ɗagawa Daddy kai kurum ta yi tabar masu Parlorn da gaske bata jin Daddyn jikinta tun daga wayewar safiyar yau take jin jikinta wani irin tamkar wacce aka yiwa shegen duka. Har Daddy ya gama shan ruwan lipton Mami na zaune jin shiru har na minti biyar bai da alamar tashi ayi break fast, Mami tace "yara fa sunata jira."kuje kuyi ke da yaranki Mariya idan Abba,ya tashi zamu yi tare.
Da mugun shock Mami ke kallonsa ranta banda tafasa babu Abunda yake, lallai akwai aiki babba a gabanta tun farko meyasa ta baiwa Daddy dama irin wannan?"yanzu ma Abba zai jira suyi break fast a tare kenan ma yafi 'ya'yan da ya haifa acikinsa muhimmanci Mami saboda bakin ciki kasa cewa komai tayi ta fice daga Parlor acan kasan ranta wata irin tsanar Abba ce ta fara sauka a kasan zuciyarta.
#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.
Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/25/2023, 12:56 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
*AREWABOOK*:Jeddah3256
Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye
037.
Mami tana shiga main parlor ta tarar da Sadiya zaune akan kujera da kayan baccin a jikinta, ta yi tagumi idanuwanta sun yi luhu-luhu alamar tasha kuka ga kuma rashin bacci yadda idanunta suka yi jajir ya ƙara ɗagawa Mami hankali, cikin sanyi jiki ta nemi gefen Sadiyar ta zauna "Sadiya!
Mami ta kira sunanta cikin mutuwar jiki da sanyi murya.
"Na'am!
Sadiya ta amsa da dusasshiyar muryata.
"Ki yi haƙuri ki cire Abba daga zuciyarki domin na yi iya ƙoƙarina na gani ya maida ke ɗakinki amma abin ya ci tura, ga baki ɗaya na rasa kowacce irin dama.
Wani naunnayar numfashi Sadiya ta sauke yayin da har hawaye sun fara bin kumatunta "Duk duniya babu wata kalma da na tsana a furta min Mami irin ace na haƙura da yaya Abba ko na cire shi daga zuciyata wannan kalmar tana kona min rai Mami anan nake ji tururin zafinta.
Sadiya ta ƙarasa magana da shouting tana pointing ƙirjinta.
Ko kaɗan Mami ba ta ji mamakin fitar waɗannan maganganu daga bakin Sadiya ba domin ko makaho ya kalleta zai fahimci she's depressing "Dole ki yi haƙuri Sadiya ki rungume ƙaddara ki roki Allah ya cire miki soyayyarsa nan da 'yan awannin ƙalilan Abba zai zama mijin Aydah kin kuma san ko a garin jahilai ya da ƙanwa ba za su aure namiji ɗaya ba.
Wani kalan miƙewa tsaye Sadiya ta yi jikinta ko'ina rawa yake ƙwaƙwalwarta sai kimtsa mata abubuwa da dama take yi "Ƙaddara fa kika ce Mami? Wallahil-azim ba zan taɓa karɓa wannan ƙaddarar ba duk ƙaddarar da za ta ja katanga tsakanina da abin ƙaunata, ban yarda da ita ba. Ke kin yi iya naki Mami babu nasara ni ki zuba min ido ki ga ta yarda zan dawo da yaya Abba gareni.
Tana ƙarasa magana ta juya a mugun fusace ta haura upstairs idanunta ga baki ɗaya sun gama rufewa, a yadda take ji zazzafar soyayyar AB kowa ma za ta iya kashewa matuƙar zai zama nata ita kaɗai.
Tana zuwa ta murza kofar ɗakinta key bedside drawer ta nufa ta buɗe ta a fusace ta ciro wata bakar leda ta yi zaune darshan akan marbles ta zazzage abunda ke ciki bottle ɗin tortulin with codeine syrup ne aciki sai waɗansu tablets, ta ɓalle two tablet ta afka a bakinta kana tanata korawa da