Author : EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category : KDP NOVELS
su
Idan na tashi nayi nawa.
Da mamaki Huwaila ke faɗin
"ki rufamin asiri Auta kome ya miki karki ƙi zuwa kuyi break fast karki bata ransa bakya ganin kishiya gareki ai sai tayi maki dariya.
Shiru kawai Aydah tayi tana jin ranta na ɗan tafasa dakyar dai Huwaila ta lallabata ta sauko kasa kallo ɗaya ta yiwa AB da Rumaisah ta wani dauke kai ganin yadda Rumaisah ɗin ke feeding ɗinsa shi kuma ya wani hangame baki sai kace ɗan yaye.
Zama tayi batareda ta kula kowa acikinsu ba ta ɗauki plate ta shiga sarving ɗin kanta shi dai mamaki kusan kashesa yayi ganin Aydah bata gaishesa ba wannan shine karo na farko da ta nuna masa halin ko in kula,yaga lafiya lau jiya suka rabu suna cikin farin ciki to mai ya canja ta haka lokaci ɗaya?
"Baby Aydah kin tashi lafiya babu gaisuwa yau?"
Rumaisah ta faɗa tana kallonta wearing a big smile kwance akan fuskarta nan ma Aydah ta yiwa Rumaisah banza tamkar babu ita a wurin take magana abun da ya kara fusata AB kenan Aydah har nawa take zata gansa a wuri ta wulakantasa tayi kamar bata gansa ba wata irin zuciya ce ta kwashi Abba a mugun fusace ya fisgo Aydah yana kallonta da idanunsa da suka gama rikidewa saboda ɓacin rai.
"me kika dauki kanki haaa?"kin wulakanta ni jiya yau ma haka ko don na fara haɗa gado dake kike ko fara raina ni ko me?"
Banda kyarma babu abun da jikin Aydah yake hawaye sai rolling suke akan fuskarta bata taɓa ganin yayanta so upset ba irin na wannan lokaci cikin kuka da majina take faɗin."ban raina ka ba yayanmu Amman ko mai z akayi ka rika yin adalci jiya ka siyawa matarka gifts na budurcinta da ta ka kawo maka ni me nai maka da baka bani nawa ba. Ko don saboda ba ka sona dan biyan buƙatar ka da sauke sha'awarka kawai ka......!
Saukar mari taji akan fuskarta yasata haɗiye raguwar kalamanta yana nunata da yatsa jikinsa banda rawa babu abunda yake ba'a taba tozarta sa ba irin wannan lokacin wai kamar Aydah ke faɗa masa irin wa'yannan maganganun dole raini ya shiga tsakaninsu tunda taga makwancinsa.
Meyesa bai haɗe duk wani abu da yake ji ba ya danne sha'awarsa bai tun kari Aydah da bukatarsa ba, daman abun da yake ta gudu kenan raini tun kafin aje ko'ina raini ya fara giftawa a tsakaninsu da sauri Rumaisah ta shiga tsakaninsu tana rike hannayensa,cikin tattausan lafazin take faɗin
"Haba Habibi idan rai ya bata hankali ake sawa ya nemo sa ai ko ba komai ka fita hankali meyesa zaka biye mata ita ɗin yarinya ce ƙarama ba hankali fahimtar abubuwa cikin sauki take da ba kamata ya yi ka lallaɓa ta.
Wani irin mummunan tsaki Aydah ta saukewa Rumaisah cike da jaraba da tsiwa da rashin kunya ce "Duk abin da ya faru ba munafucin ki bane ya haɗasa shi ba baƙar munafuka kawai.
Ganin AB ya juya kanta da gudu tabar cikin dinning ɗin tana jin wani mahaukacin kuka mai cike da kishi da bacin rai na kwace mata lokaci ɗaya, zama AB yayi yana dafe kansa da ya ɗauki zafi sosai jin yake tamkar ya amayar da zuciyarsa duka saboda takaici wani irin daɗi ne ya cika zuciyar Rumaisah idan zasu riƙa samun matsala haka a tsakaninsu ai ita ta kwanta kawai tayi ta bacci hadda kyakkyawan minshari.
"Habeebi!"
Ta wani kira sunansa da kwatacciyar murya, har da wani langwaɓar da kai take yi da wata irin zuciya AB ya ɗaga mata hannu miƙewa yayi cikin sassarfa yabar cikin dinning area din, tamkar zai tashi sama saboda zuciya dan tabe bakinta Rumaisah tayi zuciyarta fesss!
Juyawa tayi ta shiga break fast ɗinta a natse dan ita bata ga tashin hankalin da zai saka taƙi cika cikinta ba. AB ko sallama bai yi mata ba ya wuce office duk ransa a ɓace yana mamakin Aydah yana ƙara regretting fara taɓa jikinta, Huwaila tayi tagumi tana kallon yadda Aydah ke shesshekar kuka.
"Yanzu da kika faɗa masa magana haka cikin zafin rai kina gani shi zai sa ya fahimci ya yi maki laifi?"ita fa da kissar mu ta mata tayi amfani da ita ta haɗaki faɗa da mijinki mai sonki da kaunarki, ashe duk karatun litattafai da kike ya tashi a banza tun da baki san yadda za ki kama mijinki a hannunki ba nan gaba idan bakiyi hankali ba za ki zama yar kallo a gidanan ina faɗa maki gaskiya idan baki buɗe idonki ba kika bar wannan sakarcin ba kina ji kina gani Yayanmu zai fi ƙarfin ki tsakaninki dashi sai gani daga nesa.
Cikin murya kuka Aydah tace "shi bakya ganin laifinsa sai ni ko Aunty Huwaila.?"
Baki Huwaila ta buɗe tana kallon Aydah dashi da gaske wawancin Aydah ba zai daina bata mamaki ba dan takaici bar mata ɗakin tayi idan ta natsu zuwa anjima suyi magana.
#JEEDDAH ALIYU
#ASMY B ALIYU
#KURMAN ALLO.
[1/26, 2:29 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels
084.
Huwaila tana kammala share-share da 'yan goge-goge da take yi a kullum wanda kamar hakan ya zame mata jiki idan bata yi ba bata ji daɗi, ta nufo ɗakin Aydah babban abin takaici har yanzu Aydah tana nan kwance da rigar bacci a jikinta, haushinta kamar zai kashe Huwaila amma da tuno da irin tarbiyyar da Aydah ta samu ta ba kyara balle tsangwama sai ta haɗiye abin da take ji ta nemi gefen ta, ta zauna sai ta ƙare mata kallo da kyau kamin ta furta "Auta tashi ki zauna mu yi magana.
Aydah ta ya mutsa fuska da gaske bata so duk wata magana idan dai ta shafi yayanta ne, gaba ɗaya haushinsa take ji ahalin yanzu tana masa kallon azzalumi mutum marar adalci don haka bata so duk wani da ya shafe sa.
"Auta dake nake magana fa ki tashi wannan kwanciyar da kike yi kamar ruwa ba zai fishe ki ba.
"Aunty Huwaila idan maganar Yayanmu ce banaso Dan Allah ki yi tafiyarki.
"Mtss! Ni kam na tsani naga nama ya ja kare shin za ki tashi ne ko a'ah?"
Aydah ta miƙe zaune tare da jingina bayanta ga allon gado tana ta faman ya mutsa fuska.
"Auta ki natsu ki saurare abun da zan gayamiki muddin ba ki yi da gaske ba shakka babu zaman gidanan zai gaggare ki, wannan kodaddiyar mata da kike gani bala'in makira ce ba boka ba malam za ta raba ki da Yayanmu zallan kissa da makircinta za ta kashe miki aure dasu, ke kuma da yake kanki baya kawo wuta kin ƙi ki gane idan ta dosa sai uban shirme kike bugawa.
"Aunty Huwaila ai akan idonki fa jiya ta shigo da tulin kayayyakin da ya siya mata, a matsayin kyautar ta musamman na budurcinta da ta kawo masa, amma ni ko me bai bani ba tun dani daman can ba ƙaunata yake yi ba kuma nayi magana cibi ya zama ƙari to ba zai yu ba matuƙar yana so zaman lafiya a gidanan dole nima ya bani nawa gift.
"Aydah ki aro natsuwa ki yafawa kanki ina miki gudun kwabarki ta yi ruwa tsululu ki ɓata goma biyar bata samu ba. Ai shi yaƙi ɗan zamba ne kuma kowa ya iya allonsa ya wanke. Rumaisa a shirye take tsaf don gani ta kuntata miki ta kowace fuska, kuruciya da watau ne suka hana miki fahimtar manufarta akanki. Idan kika kwantar da hankalinki ni nan zan ɗora ki a hanyar da kema sai Yayanmu ya ba ki kyatuttuka wata kila ma naki su fi nata.
Jin abin da Huwaila ta faɗa yasa Aydah gyara zama har tana haɗawa da sauke ajiyar zuciya, matuƙar Yayanmu zai siya mata nata gift to kuwa a shirye take da ta yi duk abun da Huwaila ta umarce ta.
"Ina jin ki aunty Huwaila.
Aydah ta faɗa cike da zumudi cikin sigar da ƙwaƙwalwar Aydah za ta fahimta nan take Huwaila take ɗora mata karatu "yanzu kalli kanki tun safe kike kwance da kayan bacci ba ki yi wanka ba amman ita ai kin ga kalar shigar da tayi to da wannan shigar za ta iya sace zuciyar Yayanmu dukka, yau da kanta ta shiga kitchen ta yi masa breakfast ke kuma bayan indomie sai ruwan tea su ne kaɗai abun da kika iya sarrafawa. Idan har kina so kema ki zama tamkar ita dole ki koyi abubuwa da ba ki iya ba. Sannan ki tashi ki yi wanka ki ci abinci idan Yayanmu ya dawo ki je ki basa hakuri idan ya haƙura zan gayamiki hanyar da za ki bi kema ya siya miki kyaututtuka.
Ba ko musu balle gardama Aydah ta tashi ta shiga bathroom kamin ta fito Huwaila ta gyara mata ɗaki ta turare shi da hadaddun turaruka wuta masu bala'in ƙamshi. Tana kammalawa ta fice zuwa downstairs parlor Rumaisa dake kitchen ta fito fuskarta a gimtse ta kalli Huwaila.
"Ke mai aiki zo nan.
Sai da gaban Huwaila ya faɗi tsakani da Allah ta fara jin tsoron shu'umancin Rumaisa jikin a sabule ta ƙaraso gaban Rumaisa ta tsaya tare da sadda kanta ƙasa.
"Gani Hajiya.
"Ai na ganki munafuka kin san dai ni ba makauniya bace balle ki yi min tuni, daga ina kike sau biyu ina lekawa ɗakinki ba ki ciki?"
"Ina bangaren Auta.
"Kina dai can kina kimtsa mata munafuci da kinibibi to bari ki ji wallahi kina dab da bari gidanan munafuka wuce ki je ki gyara min kayan miya.
Batareda da Huwaila ta tanka ba ta wuce cikin kitchen Rumaisa ta bi ta da mugun kallo tana kissima dole ta kore Huwaila daga gidanan.
*LAGOS NIGERIA*
(The George hotel)
Aliyu na Uku ya kalli Maysun cikin natsuwarsa yana faɗin "Ki kula da kanki oum Azhar in shaa Allah ba zan daɗe ba da zarar an kammala naɗin sarautar zan dawo domin wanda na ba wa aikin bincike akan ɓata ɗan mu ina da tabbacin zan zo da min da kyakkyawan sakamako.
Dauriya sosai Maysun ta ya fawa kanta tana jin ba dadi dangane da wannan tafiya da Aliyu zai yi zuwa masarautar kudu wanda dukka saura kwanaki ƙalilan an yi bikin naɗin sarautar sa shi da Ciroma, har parking lot ta rasa shi sai da taga tafiyarsa sannan ta koma ɗakin hotel ɗin da yanzu ya zama kamar nata.
Daga hotel ɗin ya wuce gidansa inda ya tarar da Anaal da twins sun shirya har sun saka luggage ɗinsu a mota shi ƙarasowar sa kaɗai suke jira, dan haka yana zuwa batare da bata lokaci ba suka wuce airport, tun kamin
su iso cikin masaurata har labarin zuwan Aliyu na Uku ya je kunne su Ciroma wanda har yau bai sami wata makama da zai rusa Aliyu na Uku da ita ba gashi Galadima ya sako shi a gaba shi fa lallai-lallai so yake ayi ta, ta ƙare ya cika masa alƙawari da ya ɗauka masa ga baki ɗaya Galadima ya hana masa sakatt, da dukkan alama Galadima yana so ya zame masa ƙarfen ƙafa.
Tun zuwan su Anaal masarauta ta ƙunshe kanta a ɗaki Safiya ta lura da yadda 'yarta ta dawo mata cikin damuwa don ba haka ta saba dawowa mata ba sai dai bata sami cikakken lokaci ta zauna da ita ba saboda, tana fama da kula da Aliyu tun sanda ya dawo tana ɓangaren sa duk da babu wata hira da ke shiga tsakanin su, hatta da abinci da ta ɓata dogon lokaci ta girka masa kaɗan ya tsukura yace ya koshi, sai dai a wannan karon taga canji na saki fuska a wurinsa sabani yadda ya saba haɗe mata fuska. Sai wuraren bayan la'asar Aliyu na Uku ya fita zuwa bangaren mai babban ɗaki sai a lokacin Safiya ta sami damar shiga ɗakin Anaal a lokacin Anaal tana zaune a gefen gado da laptop akan lap ɗinta, tana wani binciken sirri da tasa kanta tsawon kwanaki kenan da ta fara wannan bincike, sai yau ta kawo karshen sa kuma abun da take zargi ne yake neman tabbata,shiru tayi tana kallon hoton da ke kan screen ɗin laptop ɗin bata yi mamaki ba ko kadan da sakamakon bincike nata domin ta daɗe tana zargin hakan amman domin tabbatar wa tare da cire kokwanto dole tayi wata tafiyar sirri. Turo kofar ɗakinta da ummie tayi yasa ta sauri rufe laptop ɗin, ta kakkalo murmushin dole ta yafawa fuskarta. Kusa da ita ummie ta nema ta zauna "Barka da warhaka ummie!
"Barka Anaal halan bakya ji daɗi ne?"
"Me kika gani ne ummie?
"Naga tun da ku ka iso kike ƙunshe a ɗaki ga kuma damuwa akan fuskarki ko akwai wata matsala ne tsakaninki da Abbun ki?"
"Gajiya ce kurum ummie sai migraine headache da nake ji sama-sama na kuma sha magani in shaa Allah zuwa anjima zan wartsake.
"Anaal ki dinga sassautawa kanki wannan aikin wahala da kika daukawa kanki kina mace amma ace kullum ba ki da hutu, Allah ya sanar min Anaal na gaji da ganinki haka ya kamata ki yi wa kanki faɗa ki fara tunani gina rayuwarki ke fa ta mace ce rayuwarki gajeriya ce, gara ki yi aurenki tun kina da taguwar kuruciyarki. Ki daina biyewa mahaifinki domin na fahimci rashin aurenki ba damun sa ya yi ba.
Wani gwaron numfashi Anaal ta sauke,tana jin tausayin kanta da na mahaifiyarta yana kamata domin tasan da zarar Abbu yaga ɗansa gwamnatinta zai rushe ne a wurinsa zai tattara duk wasu harkokinsa ya ɗora ɗansa akai daman can rashinsa ne yasa ya dora ta a harkokin kasuwancin sa, don haka za ta bi kowacce irin hanya ce domin ta hana sa ganinsa ko....
"Anaalll!!!
Ummie ta kira sunanta da ɗan ƙarfi tana girgiza kafaɗarta firgigit Anaal tayi tare da dawowa dukkan natsuwarta yadda ummie ta tsare ta da idanuwanta yasa duk tabi ta ruɗe ta shiga kame-kame "Anaal kina da wata uwa ce da tafi ni da ba za ki gaya damuwarki ba?"
"Ba haka bane ummie akwai wasu documents na yarjejeniyar kulla kasuwanci da Abbu ya bani na ajiye masa tun muna lagos nemi su na rasa kwata-kwata na manta da inda na ajiye su to shi ne jiya ya tambaya ni kuma na rasa amsar da zan basa banaso yaga sakacina ummie shi ne nake so ki bani dama batare da yasani ba gobe na tafi Kano na gana da CEO na kamfanin mu sake rubutu wasu.
Ajiyar zuciya ummie ta sauke tare da dafa kafaɗar Anaal cikin sanyayyar muryata ta ce "Idan wannan ne babu matsala Anaal sai ki shirya ɗin gobe ki tafi amman in yaso sai ki sauka a gidan yaya Zeenah, banaso ki sauka a hotel tun da kina da gun da za ki zauna.
Wani irin farin ciki ne mai cike da natsuwa ya saukarwa da Anaal rungume ummie tana hamdallah aranta yadda plan ɗinta yake tafiya yadda ta tsara.
Hankali tashe Ciroma ya nufi gidan gonarsa inda Galadima yake zaman jiransa har ga Allah ya fara gajiya da halin nacin Galadima mutum sai kace ya haɗe tsatso da mayyu, tun daga sanda ya ji labarin isowar Aliyu na Uku masarauta ya bi ya tashi hankalinsa ya kuma tashe na Ciroma, sai buge-buge waya yake masa "ko uban me zan masa a yanzu da yai kirana izuwa nan, kwata-kwata Galadima bashi da haƙuri gashi da shegiyar zalama da gaggawar tsiya mtss! Me za a yi da mutum mai hali irin na Galadima.
Ciroma ya faɗa cike da mita da zallan takaicin taso shi da Galadima ya yi adaidai lokaci da yake ganiyar hutawa. A fusace Ciroma ya isa wurin da suka sabawa haduwa da Galadima tun kamin ya ƙarasa ya hango Galadima sai safa da marwa yake yi da hannayensa naɗe a bayansa ya kasa zaune ya kasa tsaye wuri ɗaya shi fa da son samu ne kada jibi a naɗa Aliyu na Uku sarkin sabon birnin kudu, burinsa ace shi ne za a naɗa don haka ya bi ya tashe hankalinsa gani yake yi da zarar an naɗa Aliyu na Uku shi kenan ganyensa ya kaɗe da babu sauran wani abu da Ciroma zai masa. Har Ciroma ya zauna Galadima yana kai da komu wani mugun kallo Ciroma ya wurga masa yana faɗin "To ai sai ka nemi wuri ka zauna don kuwa wannan shawagi da kake yi ba zai rage ka da komai ba.
A fusace Galadima ya fincike kujera ya zauna yana wani irin huci "Tura ta kai bango Ciroma haƙurina yana dab da ƙarewa ya kamata kasan yarda za ka yi dani domin idan haƙurin nawa ya je ƙarshe daga ni har kai za mu ji jiki.
"Mtss! Kana bani mamaki Galadima kai a rayuwarka kwata-kwata bada haƙuri.
"Ban san shi ba kalma ɗaya nake fahimta a halin yanzu ka bani tabbacin a bisa faruwar muradina.
Wani malalacin kallo Ciroma yake wa Galadima kamin ya fito da goro daga gaban alhun babbar rigarsa ya kai bakinsa ya gutsara kana ya miƙe tsaye yana faɗin.
"Na fahimci so kake yi mu ɓata goma biyar bata gyaru ba to kasani wannan kasassabar bada ni ba idan lokacin cikar muradina ya yi ni kaina zan zantar da haka, ina kuma gargadinka da babbar murya kada ka aiwatar da komai sai tare da izinina.
Ciroma yana ƙarashe magana ya yi tafiyarsa yabar Galadima yana cizan yatsa shi da ya gaji da gafara sa bai ga ƙaho ba.
*WASHEGARI*
Gaba ɗaya masarauta ta kacame da shirye-shirye nadin sarakuna biyu, an painting ciki da wajen masarauta yayin da wasu abubuwa sababbin aka saka. Mutane da dama kansu ya daure matuka a dalilin yadda suka ga Aliyu na Uku yana farin ciki, sannan kuma tare dashi ake shirya yarda bikin nadin nasu zai ƙayatar. Da misalin ƙarfe goma daidai Anaal ta fito cikin shirinta na tafiya Kano, ummie ce kaɗai tasan da tafiyar ta, ta yayin da ummie ta dinga gargadinta da kada ta wuce gobe saboda jibi ne nadin sarautar Abbu. Da gwarin gwiwa cikar muradinta ta ja motarta ta baro masarauta ta daukin hanyar Kano zuciyarta cike da buruka kala daban-daban.
Kilishi zaune a ɗakinta tare da amintacciyar jakadiyarta cikin lokaci kaɗan Kilishi ta zabge tayi wata mummunan rama, babban kuskure da za ta tafka a rayuwarta ta bar Ciroma ya hau karagar mulkin kudu idan har hakan ya tabbata, abubuwa da dama za su faru ba kuma masu daɗi ba dole tayi bi kowacce irin hanya