Author : EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category : KDP NOVELS
da take yiwa ɗanta ƙafar ungulu ba sai akanki Kilishi.
Wani irin zabura Kilishi ta yi a firgice ta zubawa Ciroma idanunta, ba ƙaramin kaduwa ta yi ba na ji yadda ya kira sunanta cikin gatsali, wani irin mugun tsoro ne ya lulluɓeta hanta cikinta ya kaɗa zufa tana ta faman keto mata, kafin ta samu ta lallaɓo kalmar da za ta furta Ciroma har ya tashi sai da ya kare mata kallo a sheƙeƙe kamin ya kade babbar rigarsa ya juya yana faɗin "Allah ya ba mu wuni lafiya Kilishi uwar Ahmadu.
Sake jefa ta cikin zurfin tunani ya yi cikin mugun yanayi ta bishi da kallo baki sake ta ja dogon numfashi tana mai dafe saitin da zuciyarta yake. Wannan shi ake kira da ana zaton wuta a makera aka iske ta masaka an yanka ta tashi lallai tsugunne bata kare ba, wani shuɗadden al'amari wanda take kallo a matsayin kurman allo shi ne yake shiri fallasawa wannan ne kuma ba za ta taɓa bari ya faru ba dole ta yi gaggawar yiwa tufka hanci tun kamin kwabarta ta yi ruwa tsululu.
*BANGAREN MAI BABBAN ƊAKI*
A yau Aliyu na uku ya yanke shawarar komawa Lagos saboda tarin muhimman ayyukansa da ya baro gashi tare da Anaal yake daman ita ce idonsa idan baya Lagos, yanzu kuma gasu anan tare kuma mai babban ɗaki ta ce ba za a fitar da mai martaba waje ba don haka bai ga amfani da zaman da yake ba. Yanzu ma da ya nufo ɓangaren na mai babban ɗaki ya zo ne da zimmar yi mata sallama yau zai koma Lagos bakin aikinsa. As usual tana kishingiɗe hidimai biyu suna mata gyaran farce. Suna ganinsa suka kwashe gaisuwa ya ɗaga musu hannu kana suka fice.
"Barka da hutawa Ummi!
"Yawwa mai sabon birnin.
"Na zo ne nayi miki sallama yau in-sha-Allah zan koma Lagos saboda irin tarin ayyukan da na baro gashi dukka da yara nan na zo daman su ne ke taimaka min idan bana nan su jagoranci ayyukan da nake yi.
Shiru mai babban ɗaki ta yi na ɗan wani takaitaccen lokaci kamin ta yi gyaran murya.
#love story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Team kurman Allo.
Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/29/2023, 2:22 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
*AREWABOOK*:Jeddah3256
Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye
045.
Yadda ta yi gyaran murya yasa Aliyu na Uku ya tattara hankalinsa kacokan! Akanta duk lokaci da ta yi irin wannan gyaran murya za ta yi magana mai muhimmanci ko kuma ba da umarni.
"Mai sabon birnin ina so ka natsu kasan me kake ciki lokaci yana ta tafiya shekarunka sun ja amman har yanzu bansan takamaiman inda ka sa gaba ba. Ni ce mahaifiyarka a tunanina nice mutum ta farko da na dace na san damuwarka idan kuma ni ban isa nasani ita fa iyalin naka? Mai sabon birnin kai ba yaro bane da ace Allah yasa ka yi aure da wuri da yanzu kana da ɗa ko 'ya da za ka sha mamaki yawan shekarunsa.
Furuncin mai babban ɗaki na ƙarshe ya haifar masa da shiga mugun yanayi goshinsa ya tsatsafo da zufa jikinsa ya yi sanyi ya ciro handkerchief ya ciro daga aljihunsa, ya goge fuskarsa kamin ya furta "Umma na sha faɗa miki bani ciki kowacce irin damuwa ya kamata ki yarda dani da akwai da tuntuni na faɗa miki duk duniya nan banida kamarki saboda haka banga dalili da zai sa na ɓoye miki idan ina cikin wata damuwa.
Kyakkyawar ajiyar zuciya mai babban ɗaki ta sauke.
"Sai magana ta biyu Aliyu dangane da Fatimah (Anaal) yarinya nan girma ya kamata takai muzali aure, ka yiwa kanka faɗa ka aurar da ita tun da sauran ƙuruciyarta.
"Allah ya ƙara miki lafiya har yanzu Anaal bata da ko saurayi ni kaina ina yawan tuntuɓarta amman sai ta ce min bata sami wanda ya kwanta mata arai ba. Kuma kinga bai kamata mu yi mata dole ba.
"Mai sabon birnin ban ce ka yiwa 'yarka auren dole ba amman idan kana nuna mata darajar ta shine aure sai ka ga ta fito da wanda take so ba zai yiwu ace kaman Anaal bata da tsayayyen saurayi ba.
"Shi kenan Ranki shi dade zan yi yadda kika ce. Ni zan wuce ki yi min addu'a.
Sosai ta dinga kwararo masa addu'o'in su ka yi sallama ya fice yana fita koma ya koma ɓangarensa ya yi sallama da Hajiya Safiya, a parking lot ya tarar da Anaal da twins suna jiransa batareda da ɓata lokaci ba ya shiga mota direba ya ja ya yi dropping ɗinsu airport.
Rai ɓace Ciroma yake korawa mai ɗakinsa Hajiya Umaima labari yadda suka yi da Kilishi ita ma Umaima fusata ta yi cikin masifa ta ce "Wallahi ranka shi daɗe idan har ba ka tashi tsaye tsayin daka ba kana kallo za a ci kasuwa abarka da kuturun jaki. Kaini tun da Allah ya halicci ni ban taɓa gani uwar da take yiwa ɗanta ƙafar ungulu irin taka mahaifiya, duk wani cigaban ka ba sonshi take yi ba. Ta fiffita ƙannanka akanka. To bari ka ji karka sake ka yi sanyi a wannan tafiya jikina yana bani za ka yi nasara musamman sabon aiki nan da boka mai Gundulelliya ya yi maka, mun aiwatar da duk abunda ya umarce mu cikin nasara batareda da kuskure ko ƙanƙani ba. Saboda haka ka kwantar da hankalinka washin wuƙa baya faɗar da gaban doki, ba gudu ba ja da baya in Allah ya yardar kaine sabon sarkin kudu.
"Koda kuwa za a rasa rayukka masu dimbin yawa.
Ciroma ya yi magana yana sakin murmushin mugunta.
Fulani karama tana gani Fulani babba ta fito daga ɗakin da mai martaba yake ta fara addu'ar Allah yasa Fulani babba gida za ta tafi tun jiya take dakon ta fita, ta samu ta aiwatar da aikin da boka ya bayar ko ɗazu Galadima ya kira ta yana ƙara jaddada mata muhimmanci da mutuwar mai martaba a daidai wannan gabba, idan har suka yi sake da wannan damar to kuwa da matuƙar wahala kafin su sake samun irinta. Sai gashi Fulani babba tana so kawo musu cikass ta kasa ta tsare bata da wani aiki sai karantawa mai martaba Alqur'ani wannan ya sanya Fulani karama shiga firgici sai da Galadima ya kwantar mata da hankali, ya ce ta dai yi kokari ko ta hali yaya ta yi aikin da suka saka ta. Yanzu tana gani Fulani babba ta fito sai da ta sauke ɓoyayyiyar ajiyar zuciya.
"Yaya fita za ki yi ne?"
"Eh! Amman sai Yarima babba ya ƙaraso zai kula da mai martaba kamin na dawo.
Da wani irin mamaki Fulani karama take kallon Fulani babba gashi sai wani irin bugawa zuciyarta ke yi amman duk da haka da ta yi kokari ɓoye firgicinta ta hanyar furta.
"To ni miye amfanina yaya idan har ba zan iya kula da mijina ba? Ki tuna alhakin kula da mai martaba ba akan wuyanki kaɗai ya rataya ba nima ina da hakki, kwana biyu nan naga kin kasa kin tsare, ke kaɗai ke zama kusa dashi sai kace ke kaɗai ce matarsa.
Cikin isa da zallan iko Fulani babba ta buɗe bakiinta ta ce "Ba dole na nayi kane-kane akan mai martaba ba saboda na fahimci magauta nasa na kusa dashi ne ke kokarin cutar dashi ni sai in da ƙarfina ya ƙare.
Kafin Fulani karama ta kai da mayar mata da martani yarima babba ya ƙaraso ya gaishe su cikin girmamawa, Fulani babba ta yi masa umarni da ya zauna a ɗakin da mai martaba yake kada ya kuskura ya fita daga ɗakin har sai ta je ta dawo. Har Fulani babba ta ɓacewa Fulani karama da gani bata dauke idanunta daga bi ta da kallo da ta yi ba, ba ƙaramin mamaki furuncin Fulani babba ya haifar mata dashi ba yayin da tasha alwashi ko ana ha maza ha mata sai ta aiwatar da manufofin su akan mai martaba.
*ABBA BASHIR MANSION*
Tun bayan sallar asuba da AB ya tashe Aydah ta yi sallah ta koma bacci abinta, daman can ita masoyiyar bacci ce Mami ce ke tsawata mata akan lalaci da yawan bacci yau kuma an waye gari basu guri ɗaya saboda haka wata dama ce ta samu taci karenta babu babbaka daman shi AB ba so abunda zai takura ta yake yi ba. Har ten o'clock ya yi tana kwance cikin duvet tana sharar bacci, AB ya tashi tun eight da yake shi ba shi da ɗabi'ar baccin safe ya fita jogging ya dawo ya yi wanka ya shirya cikin ƙanana kayan ya kira Gusto restaurant ya yi musu order break fast kamin break fast ɗin ya iso ya wuce ɗakin Aydah ya tura kofa ya iso dab da fuskarta ya zauna ya kasa tashin ta ya yi sai kawai ya tsare ta da idanunsa yana kallon baby innocent face ɗinta, sai kurum ya tsince kansa da sakin tattausan murmushi kafin ya janye duvet ɗin zuwa cikin ta ya kama hannunta ya haɗe tafin hannunsa da nata ɗayan hannunsa ya ɗora shi akan kitson kanta a zuciyarsa yake yaba lazineess irin na Aydah daidai da kitson kanta idan ba shi ya matsa mata ta tsife ba sai tabar sa har sai tsaga ya ɓata wannan ma na kanta idan bai manta da lissafi ba almost three weeks ago da yinsa amma batada niyar tsife shi. A hankali yake shasshafa kitso ɗin cikin kwatacciyar murya yake kiran sunanta.
"Baby! Baby! Please wake up almost past ten kina bacci ki tashi ki yi wanka ki ci break fast sai idan bacci bai isheki ba ki koma kin ji?"
Yadda yake tashe ta za ka rantse da Allah yarinya mai shekaru biyu yake tayarwa, yatsine fuska tayi ta ƙara gyara kwanciyar ta, cikin wani turo baki ta yi kamin cikin shagwaɓaɓbiyar muryarta ta ce "Ni ka kyaleni ban gaji da bacci ba.
"Kin ga Baby Allah dole ki tashi koda ba za ki yi wanka ba at least have a breakfast sai ki cigaba da baccinki daman can kin saba da lalaci ki ba hana ki zan yi ba.
Ya karashe magana yana sakin hannunta ya kama shoulder ta sai kawai ta mirgina ta shige jikinsa, ta zagaye hannayenta akan ƙugunsa ta sunne kanta akan mararsa, tana wani kalan kukan tabara tare da shaƙar ƙamshin jikinsa nan take AB ya ji yanayinsa yana canzawa tsigar jikinsa tana mimmiƙe wa, yayin da mazantakarsa ta halba, bai san sanda ya ja deep breath ba cikin sarƙewar lafazi ya ce "Ke miye haka?
Aydah ta ɗago kanta a maimakon ta bar jikin nasa sai ta ja jikinta ta manne ƙirjinta akan nasa tana kallon cikin idanunsa ta cuno baki, rigar bacci da take sanye da ita irin mai tsantse nan ce shiyasa ta jaye har yana iya gani pink lace color pant ɗinta, ga baki ɗaya Baby Aydah tana neman ta rikita dan bawa Allah, musamman yadda take kallon cikin idanunsa tana zuba shagwaɓa abinta da sauri AB ya ture ta ya miƙe tsaye jikinsa yana rawa, ya haɗe fuska cike da bada umarni haɗe da kakkausar murya ya ce "Tashi ki je ki yi wanka ki same ni a parlor.
Yadda taga yayi maganar babu alamar wasa ga fuskarsa a murtuƙe yasa tayi saurin sauka daga gado, ta wuce bathroom kafin ta fito ya gyara mata bed ɗinta, murmushi Aydah tayi tana ji son yayan nata a cikin zuciyarta. Ranta farise sol ta shirya cikin party gown mai siririn hannu rigare bata wuce guiwayoyinta ba. Daga mai sai turare su kaɗai ta shafa ta fi ce, AB yana zaune akan cushion ɗin downstairs parlor yana waya da Rumaisa da gudu Aydah take tattaka mattakalar bene wanda hakan ya jawo hankali AB kanta, yadda take gudu da kuma rigar dake jikinta yasa ta dawo kamar wata 'yar tsana, kusa da ƙugunsa ta yiwa kanta masauki kallonta yake yi yana cigaba da magana da Rumaisa "Habibty na fi ki shiga damuwa babban burina mu kasance a inuwar aure, Rumaisa ke kaɗai ce mace da nake ji zan iya rayuwa irin ta aure dake ki ƙara hakuri ki bani koda two months ne kamin na yiwa Daddy maganar aurenmu a hali da ake ciki yanzu na yi gaggawa da sake bijiro da zance aure duba da dukka yaushe na yi aure.
"Habibi na ba ka one month domin nima inaso na ji ɗumin mijina a kusa dani kuma Allah ne kadai yasan hali da nake shiga a duk sanda na tuna kana kwana gida ɗaya da wannan brat girl ɗin.
AB ya ji zafin kalmar brat da ta kira Aydah dashi amman saboda gujewa fitinarta ya yi shiru, Rumaisa ta cigaba da jaddada masa da gaske wata ɗaya ta bashi. Tana gama magana ta kashe wayarta.
Aydah da ta fahimci da Rumaisa yake waya duk tasha jini jikinta "I hate that Rumaisa, I don't love her even a little.
AB ya jiyo ta tana faɗa ƙasa-ƙasa ya yi murmushi tare da mitsine mata cinya "maimata abunda kika ce ko na cire miki fatar cinya.
"Ouuchhh! Ka bari yayanmu Allah da zafi zan, faɗa zan faɗa yayanmu dan Allah ka daina Allah da zafi har cikin zuciyata nake jinsa.
Door bell da aka danna yasa shi miƙewa yana zuwa ya buɗe ƙofa a zaton shi delivery ne sai kawai ya yi arba da Abdulkarim riƙe da leda mai tambarin Gusto restaurant ga wani munafiki murmushi shimfiɗe akan fuskarsa "Amma gaskiya abokina kai ɗin tsohon ɗan iska ne me kake yiwa ɗiyar taka na ji tana ihun neman taimako?" Kar dai ka ce min haikewa 'yar jinjira yarinya nan ka yi.
Sosai AB ya ji ransa ya ɓaci da jin abunda Abdulkarim ya faɗa sai kawai ya haɗe fuska "Me ka zo yi min a gida da sassafe nan?"
"Zuwa nayi naga lafiyarka sai kuma gashi na ci karo kana lallube Babynka ashe cika bakinka na banza ne.
"Bana so kuturun iskanci Ak idan za ka shigo Bismillah ga hanya in kuma za ka tsaya munafuci da shiga abunda bai shafe ka ba sai ka yi ta tsayuwa.
Abdulkarim ya sheƙe da dariyar shakiyanci, AB ya ja guntun tsaki ya juya biyo shi Abdulkarim ya yi yana cigaba da dariya har da faɗin "abokina tsaya na goge maka jan baki a gefen wuyanka.
AB bai saurarensa ya nufi three seater ya zauna, Aydah tana gani Abdulkarim ta washe haƙora ta gaishe dashi ya miƙa mata ledar hannunsa yana faɗin "Babyn yaya Abba ga breakfast na kawo miki.
Aydah ta karbi ledar da hannu bibbiyu tana masa godiya.
AB ya kalleta da daurarriyar fuska ya ce ta tashi ta je ɗakinta ta yi break fast ɗin. Yadda taga ya haɗe rai yasa bata yi gardama ta tashi ta haura sama. Hakan yasa Abdulkarim ya buɗe shafin tsokanar AB tun AB yana jin haushi har ya sake yana mayar masa da martani. Aydah har ta shiga ɗakinta sai ta tuna da bata dauko plate da spoon ba duk abinci yana cikin takeaway container amma ita tafi jin daɗi ta juye a plate sai ta ajiye ledar ta juyo sai ta tsikayi muryar AB yana faɗin "za ka gaji da iskanci ka ne ka kyale ni Ak ni da nake da ƙosasshiyar budurwa irin Rumaisa madawaki me zan tsita a jikin Baby Aydah , kana gani yarinya ba nono ba duwawu.
Sai kawai suka fashe da dariya har suna tafawa cak Aydah ta tsaya duk da tana da karancin shekaru ita ɗin ba shashasha bace tabarar ta bata hana mata sani me ake nufi da aure ba, wani irin bugawa zuciyarta ta yi nan take ji ranta ya yi mugun ɓaci da sauri ta juya ta koma ɗaki ta faɗa kan gado tasa kuka ba ƙaramin zafin maganganu AB suka yi mata ba. Wato shi ya raina halittar da Allah ya yi mata kamar yarda Mami take gani ba za ta iya zaman aure dashi ba ashe shima kallo da yake mata kenan. An gayamasa girman nono da duwawu shine kadai cikakkiyar halittar mace.
Abdulkarim bai tafi ba sai kusan 11:30am daman wasu takardun ne ya zo karɓa wurin AB. Bayan ya wuce AB ya nufo ɗakin Aydah, yana tura ƙofa ya ji shasshekar kukanta.
"Subhanalillah!
Ya faɗa cikin zaro idanu ya ƙarasa kusa da ita ya zauna ya kai hannunsa da nufi ya tashe ta zaune ta buge mishi hannu tana gunji kuka take faɗin "Karka taɓa ni bana sonka yaya Abba ka tashi ka fice min daga ɗaki. Na ji ni ba ƙosasshiyar budurwa bace bani da manya-manyan nonuwa da duwawu amman ina so ka sani ba ni na halicci kaina a haka ba, Allah da ya halicci Rumaisa da manyan abubuwa da kake so da marari a jikinta shine ya halicce ni da kananuwa kuma na gode masa da irin halittar da ya yi min, ban kuma raina ba.
#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.
Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/31/2023, 10:21 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
*AREWABOOK*:jeddah3256
#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels
046.
Kanta ta saka cikin pillow ta cigaba da raira kukanta ,with shock AB ke kallonta maganganunta yake juyawa acikin kansa. Bai taɓa tunanin ƙanwar tasa zata rike wannan maganganun acikin kanta ba, har bakinta ya furta hakan. Bai taɓa tunanin wayonta har ya kai haka ba duk da kananun shekarunta. Kenan duk maganganun da yayi da Abdulkarim acikin kunnenta tsoro da fargaba da kuma wata irin kunyar Aydah suka lullube masa shi. "Ya rabbi kasa bata ji dukkan maganganun da muka tattauna da Abdulkarim