Author : EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category : KDP NOVELS
musulmi ka kasa yi min sallama baya kuma kasan irin tarin albarkar dake cikin sallama.
"Ko zan yi sallama Ciroma ba ka cikin jerin mutane da zan iya yiwa ita saboda haka ka yi gaggawa zuwa ga gundarin dalili da yasa ka nemi ganina a wuri irin wannan.
"Galadima alkhairai nake nemanka ba da sharri ba kai kasan wanene ni da ina nemanka da mummunan abu ba zan nemi ganinka a wurin da ya kasance mallaki na.
"Mtss! Ni fa Ciroma idan za ka kwana dubu kana faɗa min magana indai daga bakinka ta fito ba zan taɓa aminta da ita ba, muradina ka faɗa min meyasa kake nema na?"
"Da fari ka nemi wuri ka zauna domin muhimmancin maganar da zan yi da kai ta wuce a yi ta a tsaye.
Wani kallo kama raina min da wayau Galadima ya watsawa Ciroma, kafin kuma ya ja kujera ya zauna rai ɓace ya yi haka ne domin ya kai Ciroma ƙarshe.
"Galadima na zauna nayi nazari kuma na zurfafa bincike kafin Allah yasa nayi gamdakatar da saukaƙkiyar hanya da za mu bi domin cikar burukan mu. Daga ni har kai Galadima baƙin jinin mu ɗaya Allah ya jarabce mu da son mulki amma tsabar baƙin jini da muke dashi har yau mun kasa cimma burukan mu...
"Dan Allah Ciroma ka tafi kaitsaye ga gundarin manufarka kai kasani banaso nuku-nuku duk abinda za a yi na fi so a tafi straight to the point.
"Dadina da kai Galadima gaggawa kuma ka sani aikin shaiɗan ce kuma idan ba ka iya kama barowa ba sai barowa ya kama ka, ka tsaya na yi maka bayani daki-daki kafin na zarce zuwa ga ainihin manufa ta.
Kyakkyawar ajiyar zuciya Galadima ya sauke kana ya tattaro hankali da natsuwarsa zuwa kan Ciroma, nan take Ciroma ya kwararo masa manufar sa "idan Allah yasa sarki Mahmood ya mutu ni kuma zan sami damar ɗane karagar mulkin kudu, daga nan zan tsige Aliyu daga sarautar sa kai kuma na naɗa ka a matsayin sabon sarkin sabon birnin kudu, ina fatar za ka bani haɗin kai mu haɗa karfe da ƙarfi mu kwace abinda ya kasance mallakin mu dukka su biyu babu wanda ya cancanta da sauratar da aka basa, to gara ma Mahmood yana da sha'awar mulki ba kaman Aliyu ba ka ga shi Aliyu tsige sa ba zai min wahala ba. Amma ya ka ga wannan dabarar tawa sannan kuma ka amince mu yi wannan tafiyar a tare ko kuwa har yanzu kana da sauran wani kokwanto akaina.
A karo na biyu da Galadima ya sake sauke ajiyar zuciya ya gyara zaman babbar rigarsa kana ya ce "Ban ji ka faɗi ta inda zan iya ba da tawa gudummawa acikin wannan tafiyar ba?"
Ciroma ya saki ja'irin murmushi cike da farin ciki yadda ya yi nasarar shawo kan Galadima duk tun farko yana da yakini ba zai sha wahala wajen saka shi ya aminta da manufar sa. "Galadima na duba na hango kai kaɗai ne mutumin da zai iya aiwatar da aikin boka batare da an sami kuskure ko wata matsala ba.
Murmushin kaima raina min da hankali Galadima ya yi tare da kallon Ciroma a shaƙeƙe kafin ya furta "lallai Ciroma kai ɗin cikakken marar lissafi ne in banda kana mahaukaci ta ya har kake tunani ni Galadima zan amince da wannan mummunan manufa ta ka watau nufinka kura da shan bugu gardi da kwace kuɗi.
"Haba Galadima miyasa kake da gaggawa ka tsaya na buga maka lissafi da nayi domin ban taɓa haɗa lissafi batare da ya tafi daidai ba.
"Sai kuma gashi a wannan karo bai tafi a daidai ba asalima ka faɗi a lissafin naka.
Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo
Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/19/2023, 11:14 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
*AREWABOOK*:3256
Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye
031.
Sai da Ciroma ya yi kyakkyawan murmushi kafin ya zarce da faɗin "Duk wanda ke cikin masarautar kudu kama daga manya har zuwa yara kowa ya shaida irin matsananciyar ƙauna dake tsakaninka da Fulani Ƙarama ƙauna ce wacce ku ka gina ta a bisa yarda da aminci amma kwatsam! Mahaifinta ya datse wannan zazzafar ƙaunar taku ya aurar da ita ga sarki Mahmood a cewarsa bai kamata sarki irin Mahmood ya zauna da mata ɗaya ba. Duk da a wancan lokaci sarki Mahmood baya ƙaunar Hafsatu amma saboda irin girman Wambai da yake gani yasa aminta da aure Hafsatu ba don yana sonta ba. A dalilin wannan babban rashi da ka yi sai ya haifar maka da matsananciyar damuwa wanda har sai da ka bar masaurata daga baya ne ka dawo daga nan sai kuka kula haramtacciyar alaka wacce ba kowa ne yasan da ita ba sai ire-iren mu masu bacci da ido ɗaya.
"Ka ga Ciroma nagaji da saurare abinda na daɗe da saninsa ka faɗamin sabon abu ko kuma na tashi na ƙara gaba Idan kai ba ka da abin yi ni ina dashi.
"Galadima da wannan damar za mu yi amfani ka ɗorawa Fulani Ƙarama alhakin aiwatar mana da wannan aiki kasancewar ta matar sarki Mahmood, na kuma tabbata za ta bi kowacce Irin hanya ce domin mu cimma burin mu saboda irin ƙaunar da take maka.
Shiru Galadima ya yi tare da zurfafa nazari da tunanin sa take ya aminta da wannan shawara bai baro gidan gonar Ciroma ba sai da ya basa assurance akan tabbatuwa kudirin su.
Bayan kwana biyu Galadima ya haɗu da Fulani Ƙarama inda ya bijiro mata da bukatarsa haɗe da kwaɗaita mata abubuwa da dama. Daman can bata so sarki Mahmood shiyasa bai wani sha wahala wurin shawo kanta ba.
*ALH BASHIR MANSION*
Sanin da AB ya yi Mami tana jiraye dashi sai ya ƙirkira 'yar boya a tsakaninsu da sassafe zai fice zuwa kamfani ba kuma zai dawo ba sai karfe goma dare, kusan kwanaki uku kenan da ya daina shiga part ɗinta, hakan da ya yi ba ƙaramin tunzira ta ya yi ba Sadiya kuma duk sanda ta fita school tana kammala lectures za ta wuce hostel wurin Sarah ta dirka mata kayan maye tayi tatul sannan ta kwanta tasha bacci abinta da zarar ta falka sai ta ji kanta wasai bata da wata damuwa sai dai a can ƙasan zuciyarta soyayyar AB ce a danƙare sai daɗa hauhawa take, ba za ta dawo gida ba sai magarib dama AB ne mai tsawata musu shi kuma yanzu damuwarsa kaɗai ta isheshi, wannan ya kara bata cikakken freedom da yake shi Daddy ba zama yake yi ba a wasu lokuta yana kai har karfe goma kafin ya dawo gida Mami ce kuma ko kaɗan bata so abinda zai ɓata wa Sadiya rai duk acikin su uku da ta haifa Sadiya ita ce mafi soyuwa a zuciyarta.
Yau kam Mami tasha alwashi koda AB zai kai ɗayan dare sai ta yi magana dashi domin ta ji a ina zance su ya kwana shiyasa ta zo ta zauna a main parlor ta kasa ta tsare ƙarfe 10:08pm daidai AB ya tsayar da motarsa a parking lot, ya fito tare da rufe murfin motar ransa a ɓace yake a dalili yadda cikin ƙanƙani lokaci Rumaisa take so ta susuta shi yanzu akan hanyar sa ta zuwa gida ya kira ta sai da ya jerenta mata 7 miscall kafin ta yi picking daga ƙarshe ma baram-baram suka rabu kusan kwana uku kenan tana wahalar da ruhi da gangar jikinsa ko ya yi niyar ya haƙura da ita sai zuciyarsa ta ƙi ba shi haɗin kai yana matuƙar ƙaunar Rumaisa shiyasa yake ta haƙuri yana bibbiyarta. Balmo maigadi yana gani dawowar sa ya kira Mami a waya da kanta ta zura hijab ta nufi bangaren AB a lokacin yana zaune a parlornsa yana waya da Abdulkarim yana faɗa masa irin abubuwan dake faruwa tsakaninsa da Rumaisa sai dai ya boya bai faɗa masa hakikanin gaskiya abunda Rumaisa ɗin ke so ya yi mata, ya ji an turo ƙofa gami da shigowa kaitsaye da fari ya yi tunani ko Aydah ce shiyasa ya yi saurin waigawa sai kawai ya tozali da fuskar Mami wacce babu annuri ko kaɗan akanta "ina so magana da kai ka zo ka same ni a ɓangarena karka ɓata min lokaci ka ji ko?"
Mami ta faɗa cikin muryar dake nuna tana cikin fushi, da sauri AB ya yi sallama da Abdulkarim ta hanyar bashi uzurinsa.
A zaune ya tarar da Mami a main parlor sai wani girgiza ƙafa take tare da yin ƙwafa.
"Mami gani.
AB ya faɗa ya nemi kujera ya zauna ya wani sadda kai ƙasa.
"Abba yaushe raini ya shiga tsakanina da kai?"
Da sauri AB ya ɗago ya kalleta sai kuma ya sake maida kansa ƙasa "Ki yi haƙuri Mami.
"Rufe min baki karka sake ka ƙara furta min kalmar haƙuri.
"Wallahi Mami na yiwa Daddy magana kamar yadda kika umarce ni amma sai ya fatattake ni tare da ƙin amincewa. A halin yanzu bansan ya zan yi ba Mami.
Wani mugun kallo Mami ta wulga masa gani take yi ya ma zo mata da raini hankali shi fa ke aure nan ba Daddy zai yi masa zaman aure ba idan ya kafe lallai-lallai Sadiya yake so ba Aydah ba duk taurin kan Daddy dole ya janye kudirin sa, saboda haka a mugun hassale ta daka masa razananniyar tsawa "dallah dakata Abba! Daman duk yadda aka yi da jaki sai ya ci kara kuma tsintatciyar magge har abada bata magge ɗan tsintuwa ba zai taɓa zama ɗa ba idan ba ka yi min butulci ba Abba ai ba ka cika tsintaccen ba.
Wani irin zabura AB ya yi tare da miƙewa tsaye idanunsa suka firfito jikinsa ya dauki rawa tsigar jikinsa ta mimmiƙe, a rikice yake ambaton Allah, gumi ya karyo masa a sassan jikinsa sai kallo fuskar Mami yake yi ya kasa yarda waɗannan zafafan maganganu daga bakinta suke fitowa, yayin da Mami idanuwanta suka rufe ruff cikin ɗaga murya ta cigaba da faɗin "Ka duba irin wahala da na dinga yi da kai tun kafin na haihu a duniya na fara rainonka naci kashi da fitsarinka ga ka da ɗan banza kukan tsiya sai dare ya raba tsakiya kake tashi ka dinga tsala fitinanne kukanka, haka zan tashi idanuwana cike da bacci na saɓa ka a baya na dinga safa da marwa bana bango gabas bana na yamma hankali da natsuwa ta ba za su dawo jikina ba har ka yi bacci. Hatta da uwar da ta haife ni a wancan lokaci sai da ta nuna min kuskuren ƙauna da soyayyar da nake maka ashe tun a wancan lokaci ta hango min zuwan wannan rana. To bari ka ji daga Sadiyar da kake gudu kana nuna mata zallan ƙiyayya da Aydar da kake ƙauna ni ce nan na haife su kuma su duka biyu na haramta maka su. Kai ba ma abin alfaharin ka bane yarinya mai cikakken asali irin Sadiya 'yar halak gaba da baya ta nuna tana son irinka marar asali wanda babu tabbacin ta tsalkakkiyar hanya aka same ka, amma tsabar butulci irin na ɗan adam za ka nuna ba ka sonta.
Yadda Mami take magana tare da ɗaga murya ga baki ɗaya muryata, ta cika gidan hakan yasa su Sadiya firfitowa daga dakunan su. Kowanne da kalar mamakinsa yayin da AB ya zube guiwayoyinsa a gabanta ya idonsa suka Kada suka canja kala lokaci ɗaya, yayin da Mami ta cigaba da kare masa tanadi da gudu Siyama ta zo ta rungume shi ta fashe da kuka gani haka yasa ita ma Aydah ta zo ta haɗe su duka shi da Siyama ta ƙamƙame tasa kukan da ya fi na Siyama. Tsaye Sadiya ta yi tare da harɗe hannunta akan kirjinta tana kallonsu ita kuma Mami baki buɗe take kallonsu wata irin tsawa Mami ta yi masu "baza ku tashi ko koma ɗakin ku ba sai ranku ya ɓaci"
Tamkar tunzurasu take musamman Aydah da take jin haushin Mami a fusace Mami ta yo kansu Siyama ta fara fisgowa kafin ta yi kan Aydah kara manne masa Aydah ta yi kamar zata koma jikinsa cikin kuka Aydah ke faɗin."Mami yayanmu ne fa?"a hasale Mami ta fisgota ta kaiwa fuskarta mari. Marin AB ya ji yana tabasa wurare da dama dake cikin zuciyarsa idan ya ci-gaba da zama anan zuciyarsa za ta iya bugawa nan take da kyar ya miƙe tsaye yana jin yadda kafafunsa suka yi masa wani irin nauyi harma da nauyin da yake ji acikin zuciyarsa.
A nan Tsakiyar Parlorn Aydah ta zube ta haɗe kai da gwiwa ta shiga raira kuka mai ban tausayi, a hankali Siyama ta miƙe tsaye tana ta goge hawayen da suka kasa tsayawa acikin idanuwanta kallon mami da Sadiya take ta kasa gasgata duk maganganun da ta ji suna fitowa daga bakin Mami, watau shiyasa Mami da Sadiya suka canja lokaci ɗaya kenan Daddynsu aure zai haɗa yaya Abba da Aydah samun kanta ta yi da tsintar kanta cikin farin ciki sosai ta taya uwarta murna samun miji irin yaya Abba a wannan lokacin ba ƙaramar sa'a bane a rayuwa."Mami duk abunda yaya Sadiya ta yiwa yaya Abba baki gani ba ta tashi kashesa a daren aurensu saboda irin ƙiyayyar da take masa
yanzu a karo na biyu bayan sun rabu kuma kikeso ya kara aurenta?"da gaske kece kuwa Mami.!"me naji kina faɗawa yaya Abba dan tsintuwa kike kiransa marar asali marar gata haba mami yaushe zuciyarki ta zama haka?" ke yafi dacewa ki bada goyon bayan auren nan shine kike bin bayan yaya Sadiya da sai yanzu ne take da tasani nakin amincewa da auren yaya Abba, nasàni mami koda can baya soyayyar yaya Sadiya daban ne a zuciyarki."
Sai ta kalli gefen Sadiya dake mata wani shegen kallo jin take kamar ta karaso ta rufeta da duka "baki ji kunya ba yaya Sadiya? Duk wanda ya furta maka Kalmar ƙi da safe sai kuma ya dawo yamma ya furta ma ta so karya yake sai har da wata manufa shimfiɗe a ƙasan zuciyarsa, ke ɗinan har abada ba za ki taɓa zama cikin mutanen kirki ba. Ke kanki kin san yaya Abba yafi karfin ajinki wallahi kuma insha-Allahu Aydah ce matar aurensa uwar 'ya'yansa sai dai ki haɗe zuciya ki mutu.!"
"Siyama! Mami ta kirata a hargitse tana wani daka mata tsawa Siyama ko kallon Mami bata yi ba ta ƙarasa wajen Aydah da har yanzu kanta yana cikin cinyoyinta maganganunsu ta ji suna ƙoƙarin fasa mata kai ta rasa me maganganunsu ke nufi. Ta daga Aydah ta rikata suka nufi stairs daga Mami har Sadiya bin su suka yi da kallo."Mami kina jin yaran nan fa idan ba ki yi da gaske ba su za su bamu matsala wallahi."ji yadda suka je cikin jikinsa tamkar wani ubansu Mami ki yi wani abu akai jibi ne ɗaurin Aure wallahi-tallahi idan ban auri yayanmu ba zuciyata za ta iya tarwatsewa ina sonsa ina sonsa Mami."!
Sadiya ta faɗa da wani yanayi a muryarta Mami ko fahimtar ta bata yi ga baki ɗaya hankalinta a tashe yake dole zuwa gobe ta yi wani abu kara Abba yabar rayuwarsu na har abada ya koma wani wurin ya cigaba da rayuwa da ta barsa ya auri Aydah.
#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye Novels
#Kurman Allo.
Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/20/2023, 10:56 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
*AREWABOOK*: Jeddah 3256
#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels
032.
Tana jikin Siyama har lokacin kuma kukan take ta kasa gasgata Mami ce take fadawa yaya Abba waya'annan baƙaƙen kalaman wanda ko a cikin mafarki bata taɓa hasaso Mami zata iya fadarsu ba. Cikin rawar murya Aydah ke faɗin."Da gaske ne yaya Siyam Daddy zai haɗa aurena da yaya Abba?"cikin fita hayyacinta take yin maganar. Siyama dai banda tafasa babu abunda zuciyarta ke yi shafa kan Aydah take a hankali cikin kwantar da murya ta ce "ki yi shiru Aydah babu abunda zai faru da wasa Mami ke yi maki.
Shiru Aydah tayi Amman acan ƙasan ranta tsoro da fargaba ga kuma damuwa su suka taru suka yi mata yawa, jin take kamar ta je yanzu ta samu yayan nasu taga wane hali yake ciki. ita ma a bangaren Siyama tunanin da take ta yi kenan jawo wayarta ta yi ta shiga dialling lambarsa har ta katse bai ɗaga ba kara kira tayi nan ma bai daga ba sai da ta jera masa kira kusan goma a na ma ƙarshen da ta kira aka faɗa mata a kashe wayar take a wannan daren AB kasa bacci ya yi duk inda ya juya kalaman Mami ke yi masa ihu cikin kunne da gaske rashin asali bala'i ne gaskiyar Mami ne da tace me Sadiya zata yi dashi. Wani irin ciwo ne kwance can a ƙasan zuciyarsa wanda ba zai faɗuwa ba, tun a daren ranar yaso barin rayuwar gidan Daddy Bashir na har abada da zarar ya tuna Daddy da aydah sai jikinsa ya yi wani kalar sanyi na ban mamaki. Aydah za ta fi kowa shiga tashin hankalin rashinsa a kusa da ita, bai san meyasa zuciyarsa bata son abunda zai taɓa Aydah ba komai kankantarsa. washegari suna gama sallar Asuba, Siyama ta koma ta kwanta dan sai 2 zata fita lecture saɓanin Aydah da ta ɗora kanta akan bed ɗin ta yi nisa cikin tunani, dan jiya tare da Siyama suka kwana ɗaki ɗaya, lokaci ɗaya idanunta suka cicciko da ƙwalla ga kanta da take jin yana mata wani irin ciwo kamar zai fashe. Yaya Abba kawai take tunani