Author : EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category : KDP NOVELS
tayi ta nufi toilet batareda ta kara kula AB ba. Shima ficewa yayi daga ɗakin kai tsaye bangarensa ya nufa ya shafa mayukansa ya saka riga da wando na English wears ajikinsa wanda suka yi bala'in karbarsa kai tsaye ɗakin Aydah ya wuce kwance ya sameta tamkar haɗin baki ita ma da English wears ajikinta riga da wando, wando same color da nashi rigar ce kowane su da color ɗinsa. Kallonta kawai yake tana riƙe da wayar hannunta ko mai take kalla aciki oho.
Ta amsa sallamarsa ciki-ciki ta tashi zaune kana ganin idanunta kasan taci kuka haka kuma babu wadataccen bacci acikinsu "Baby yau ba gaisuwa?" Nan turo baki sa'annan ta gaishesa ya harareta yana faɗin."Sai da na roƙa, kin yi break fast?"
Ita fa yayan nata yanzu haushi yake bata Allah kaɗai yasan abun da suka yi jiya shi da Rumaisa zai zo yabi ya dameta. Wata kwallah taji tana taruwa cikin idanunta,lokaci zai zo da zata rama duk irin abubuwan da yayanta yayi mata yaje can ya haɗe Rumaisa idan yana iyawa.
"Aydaah!"
AB ya faɗa da sauri dan kusan sau biyu na kiran sunanta tayi nisa a tunanin da take a firgice ta dago tana kallonsa.
"Tunanin me kike haka?"kin ma yi break fast kuwa?"
Ranta haɗe tace.
"Ban yi ba.
Ya gyada kai yana faɗin "Tau tashi kije kasa ki kwaso mana kayan break fast ɗin sai muyi a parlorna har Rumaisa.
Jin ya ambaci sunan Rumaisa taji wani abu ya tsaya mata daidai wuyanta miƙewa tayi tsaye ta nufi kofa a kitchen ta samu Huwaila tana markada kayan miya na abincin rana,ta gaisheta tana mata sannu da aiki ganin yanayin Aydah ita ma Huwaila bata wani dame Aydah da surutu ba ,ta faɗa mata kayan karin kumallo su suna can dinning area. Ficewa kawai daga kitchen din Aydah tayi ta dauki breakfast ɗin ta wuce dashi falon AB babu kowa a cikinsa sai karar AC aje kayan karin kumallon tayi akan rug ta nufi ɗakin baccinsa,sai da tayi knocking ta tura kofar ɗakin nasa AB ne tsaye agaban mirror dressing shi da Rumaisa ya rungumeta ta baya ya sakalo kansa cikin kafaɗarta karar buɗe kofa yasa suka kalli kofar da sauri fuskarsu kan Aydah da ta haɗe rai tamkar ba'a taba halittar dariya akan fuskarta ba ta juya tabar kofar ɗakin haka ta kasa jamasu kofar. Da sauri AB ya saki Rumaisa ta ƙarasa ta gyara masa gadonsa,rai abace take faɗin."ita wannan ƙanwar taka bata da hankali ne da za ta dinga shigowa mutane ɗaki anyhow idan da a wani yanayi ta same mu fa?"
Rumaisa ta faɗa duk ranta a ɓace,tun farko bata so AB ya ajesu gida ɗaya da Aydah ba tana bukatar Kebantacciyyar rayuwa ita da mijin aurenta. Shi kansa AB ransa ya ɗan ɓaci ganin Aydah ta shigo ba tayi sallama ba,ya juya yana faɗin."Rumaisa idan kin gama ki sami ni a falo muyi break fast.
Da haka ya fice daga ɗakin,dan ƙaramin tsaki Rumaisa ta saki.
AB yabi kayan karin kumallon da Aydah ta aje sai dai babu ita a parlor kai tsaye ɗakinta ya nufa samunta yayi tana kuka tsaye yayi a bakin kofa. Da mamaki yake tambayarta wani abu akayi mata?"lokaci ɗaya ya haɗe fuska da sauri ta girgiza kanta ganin yadda ya koma lokaci ɗaya tamkar ba'a taɓa halittar dariya cikin fuskarsa ba.
"Tashi mu je kiyi break fast.
Ya faɗa babu alamar wasa a muryarsa cikin rawar murya take faɗin "Na koshi yayanmu.
Kallon da ya shiga yimata yasa ta miƙe ta nufi kofa parlor sa
Rumaisa na zaune tana jiransu ganin sun shigo tare ta wani dauke kai
Dakyar Aydah ta gaisheta tuno faɗan da AB yayi mata na rashin gaisar da Rumaisa da tayi jiya ita ma Rumaisa bata kalli gefen da Aydah take ba ta amsa. Ta dauki cup ta shiga haɗawa AB tea ta dibi dankali da farfesun naman kai ta tura a gabansa sai da ya saki murmushi sa'annan yace "Na gode. Ita ma murmushin ta saki tea kawai ta haɗa acikin plate ɗin AB tayi joining ɗinsa dakyar Aydah ta haɗa tea ta dibi dankalin ta koma gefe ta soma ci badan tasan daɗin sa a bakinta ba ita dai turawa kawai take sai AB yaji duk babu daɗi a haka dai aka gama breakfast ɗin, Aydah ta kwashi kayan ta kai kitchen,AB yace idan taje ta wanke komai karta bai wa Huwaila idan ta gama ta zo yana jiranta zaiyi magana da dukansu, tamkar guguwa haka Aydah ta fice daga falon ta sauka kasa wani marayan kuka na taho mata
tana jin kamar ta cakawa Rumaisa wuƙa ta mutu kowa ma ya huta ji wani shigewa yayanta da take tana fari da idanu tamkar wata karuwa. Ganin tana shirin sakin tray Huwaila ta karba da sauri anan kasan kitchen din Aydah ta durkushe tana kuka hankalin Huwaila idan yayi dubu ya tashi,a rude ta shiga tambayarta menene?"kasa cewa komai Aydah tayi sai kukan da ta cigaba dayi. Hakan ba ƙaramin haushi ya bai wa Huwaila ba. Yanzu idan da agaban Rumaisa ne fa?"ai sai ta rainata da abun da ya isa da wanda bai isa ba duk na kuka ne a wurin Aydah wannan sakarcin dame yayi kama."To bari naje na tambayi yayanmu dalilin kukan ki tun da naga daga wurinsa kika fito.
Da sauri Aydah ta miyke tsaye cikin shesshekar kuka take faɗin "Ni wallahi na gaji wurin Mamina zan koma amma ba zan zauna a gidanan ba.
Huwaila ta ware ido tana kallon Aydah cike da mamaki cikin jin haushi Huwaila tace."shi kwana ɗaya da Rumaisa tayi cikin gidan nan har ta saka gidan ya fice miki arai Auta?"
Cikin kuka Aydah ta bata amsa."Ba ki ga yadda take shisshige masa bane gara nabar masu gidan kar zuciyata ta buga Aunty Huwaila. Tana gama faɗin haka ta karasa wurin sink ta shiga wanke kayan da suka bata kamar yadda yayanta yayi mata umarnin sai da ta wanke komai ta mayar a inda yake
Ta juya ta koma sama sai da tayi sallama tayi knocking sa'annan ta shiga.
#JEEDDAH ALIYU
#ASMY B ALIYU
#KURMAN ALLO.
Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[1/17, 4:40 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels.
071.
Kallo ɗaya tai musu ta kauda fuska tana taɓe baki zaune suke akan kujera guda ƙugunta manne da nasa, sai wani banza murmushi da take ta faman dokawa ita a dole sai ta nunawa Aydah ita ke da miji. Zuciyar Aydah tamkar za ta tsaga ƙirjinta ta fito ta nemi kujera dake nesa dasu ta zauna tare da sadda kanta ƙasa tana lankwasa yatsunta sai sautinsu kake ji ƙass!ƙass! AB ya kalle side ɗin da Aydah take ya fito ta da hannunsa "Baby zo nan ki zauna.
Ya ƙarashe magana tare da nuna bangaren hagunsa da yake Rumaisa tana zaune ne a bangaren damansa, Aydah ta ɗago a natse ta kalle shi sau daya ta maida kanta ƙasa tana girgiza kanta "Ka bar shi kawai Yayanmu nan ya isa.
Yadda tai magana cikin dushewar murya tai bala'in basa tausayi ya sake cewa "Magana mai muhimmanci zan yi daku baby idan kina nesa dani taya za ki ji abun da nake faɗa?"
Batareda ta ce komai ba ta taso kanta yana ƙasa ta zauna kusa dashi sai da ta bada tazara a tsakaninsu ta sake sadda kanta ƙasa AB ya kalle rata da ta bayar a tsakaninsu ya yi murmushi ya juya ya kalle Rumaisa wacce tayi kici-kici da fuska, nan ma ya sake murmusawa kana ya ɗora da yi basmallah nasiha sosai ya yi musu ta su haɗa kansu su zauna lafiya "Rumaisa duk da a shekaru kin girme Baby Aydah nesa ba kusa ba amma a gidanan ita ce babba domin ita ce na fara aure saboda haka ki kama girmanki ki ja ƙanwarki a jiki ku idan tayi kuskure a matsayin ki na babba mai hankali ki lurar da ita. Iya sani da na yiwa baby Aydah batada matsala za ki ji daɗin zama da ita. Sai dangane da kwana ya kuke gani za a tsara duk a yanzu sai na sake maida kwanaki shidda a ɗakin Rumaisa kamar yadda addini ya tsara amman yana da kyau a wannan zaman da muka yi ku raba girki ko me ku ka ce?"
Rumaisa wacce ta cika tayi bam! Jira take a taɓa ta fashe ba ta kalle AB a ɗage ta watsar sai wani yatsine fuska take yi ba ƙaramin haifar mata da mamaki AB ya yi ba wato ya mayar da ita shashasha ai kamin ta shigo gidansa ya sha faɗa mata ba abunda zai tsinta a jikin Aydah ashe duk zuƙi ta malle ce yake mata kai maza munafukai ne gane gaskiyarsu sai Allah. Tabo ƙafarta da ya yi da ƙafarsa yasa ta dawo da ganinta kansa "Habibty ba ki ce komai ba?"
"Duk abun da kace Habibi ya yi.
"Amman ya kamata na ji ra'ayinku dangane da kwanaki da ku ka tsara na girki?"
"Ka tambaye uwargida duk yadda ta tsara ni banida matsala.
Yadda Rumaisa tayi magana kai da ji kasa da walaki goro a miya sai lokacin Aydah ta ɗago ta kalle su ta sake maida kanta ƙasa "Yayanmu ni ba sai an raba girki dani ba na bar mata duka daman can kasan ban iya girki ba.
Unexpected ya ji wannan maganar tana fita daga bakin Aydah ya zuba mata manyan idanunsa yana kallonta yayin da Rumaisa ta saki murmushi mai sautin gaske don ita kan ba ƙaramin daɗi furuncin Aydah ya yi mata ba.
"Baby bani na tsara raba girki a tsakaninku ba addini ne ya tsara kuma ni ba zan so na danne haqqin ko ɗaya daga cikinku ba, banaso gobe kiyama Allah ya tuhume ni da cutar guda daga cikinku saboda haka na raba muku girki kwana bibbiyu idan da akwai wacce hakan bai mata ba tayi magana ko ta faɗi ra'ayinta.
Dukkansu shiru suka yi ita daman Aydaah batada abun faɗa ita kuma Rumaisa duk haushinsa ya gama cikata saboda haka ta miƙe zubur tana faɗin "Habibi zan je na ƙarasa kimtsa ɗakina kada nayi baƙi su zo ɗaki a ya mutse.
Kamin ya bata amsa har ta nufi ƙofar fita, daga shi har Aydah da ido suka bi ta Aydah ta taɓe baki ita ma ta tashi tana faɗin "nima zan je na kwanta Yayanmu bacci nake ji.
Kamar dai yarda Rumaisa tai masa ita ma haka tayi bata jira jin ta bakinsa ba ta fice abinta, kaitsaye ɗakinta ta wuce ta haye gado ta kwanta hawayen da tun ɗazu take rikewa suka dinga bi gefen idanunta suna sauka a wuyanta.
*HAMBURG GERMANY*
Tun saukar Aliyu na Uku hamburg bai samun kansa ba sai yau shi ma shi ne last day na seminar ɗin da suke yi na gamayyar kamfanoni wannan seminar ɗin suna yinsa ne a duk ƙarshen shekara a wannan karo a mercure hotel suka gudanar dashi a katafaren conference hall dake cikin hotel ɗin. Yanzu ma sun tashi ne domin kowa ya je ya yi lunch su dawo a karasa tun daga wannan zaman shi kenan sun kammala seminar ɗin, yayin da kowa ya nufi gun ci abinci shi kuma Aliyu na uku ya nufi harabar hotel ɗin domin ya sha fresh air jikinsa sanya da Italian suit blue-black in color daidai yana kawowa entrance ɗin fita daga receptionist hankalinsa yana ga wayar da yake yi da Anaal shiyasa hankalinsa ya tafi sosai sai kawai ya ji yaci karo da mutum kusan a tare wayarsa ta zame daga hannunsa ta fadi kusan a tare suka sunkunya domin dauko wayar kafin ya kai hannunsa har ta riga shi ɗaukar wayar ta miƙa masa tana faɗin
"I'm sorry sir, I didn't hit you on purpose, I was in a hurry.
Ya ɗago tare da miƙewa tsaye ita ma ta miƙe tana ƙara miƙa masa wayarsa sai lokacin idanunsa suka sauka akan fuskarta cikin shock yake kallon kyakkyawar fusrkarta jikinta sanye da baƙar Abaya tayi rolling da kanta da mayafin rigar cikin kaɗuwa ya furta "Maysun!Maysun are you the one I am seeing in reality or it is a dream that I used to have?"
Kamar ba za ta amsa mishi ba sai faman kallonsa take yi tana tunano irin rayuwar da suka yi a shekarun baya, yau shi ne a tsaye a gabanta duk da shekarunsa sun tafi amman kyawunsa da kwarjininsa yana nan sai ma taga kamar ya daɗa ƙaruwa ko kaɗan bataso ta kula shi ba saboda ganinsa da tayi yanzu nan ya tayar mata da tsohon miki da ya tafi ya barta dashi a tsawon shekaru da tayi basa tare sai dai zuciyarta tana cike da kwadayin so sani lafiyar yaronta wanda kullum da tunaninsa a dankare a zuciyarta, cikin nauyin harshe ta ce "It's not a dream, I'm the Maysun you knew years ago, the one you ran away and left her.
"Kada ki ce haka Maysun ni ban gudu ba kawai dai tafiya ce ta gaggawa ta kamani kuma na dawo na tarar da bakya nan kum...
"Ali where's is my son yanzu ya girma ko?"
Tayi sauri katse shi da tambayar da ta gigita masa ƙwaƙwalwarsa har jikinsa ya dau rawa cikin kaɗuwa ya ce "Me kike nufi da wannan tambaya Maysun?
"Ali banaso wata doguwar magana a tsakanin mu kawai ka faɗamin lafiyar yarona idan da hali ka taimaka ka haɗani dashi.
"Maysun idan wasa kike yi dan Allah ki daina nima na damu da na ji labarin Azhar daga wurinki.
Wani irin ja da baya Maysun ta shiga yi idanunta sun firfito da sauri Aliyu ya riƙo hannunta, zuciyarta tana wani kalan bugawa kaitsaye ɗakinsa dake hotel ɗin ya nufa da ita kafanɗunta biyu ya riƙe ya girgiza ta da dukkan ƙarfinsa "Maysun where's our son idan baya tare dake Maysun yana ina kisan dai tare na tafi na barku a lokacin yana bacci akan gado ke kuma kina bathroom do you remember?
Maysun ji tayi wani abu ya tsaya mata a wuya sai girgiza kai take yi numfashinta ya shiga sarkewa ta durƙushe ƙasa tana dafe ƙirjinta da sauri Aliyu ya zube a gabanta yadda yaga tana fizgar numfashi ya tashi hankalinsa idan bai manta ba tana da Asthma cikin fitar hayyaci ya fizge jakkar hannunta ya zuge zip ya zazzage kayan dake ciki kamin idonsa ya kai kan inheler ɗinta ya ɗauka ya danna mata a baki, dakyar take shaƙar iheler ɗin ta ɗauki lokaci tana shaƙar iskar inheler kamin numfashinta ya daidaita sai kuma ta fashe da kuka tana faɗin أين ابني علي؟(where's my son Ali) "لا أعرف ميسون(I don't know Maysun) shi ma ya faɗa hawaye na bin fuskarsa "Ki faɗamin hakikanin gaskiyar abun da ya faru bayan tafiyata?"
"Bayan na fito daga bathroom sai na tarar da short note ɗinka kana gayamin tafiyar gaggawa ta kama ka ba za ka wuce three ɗays za ka dawo har tsawon wata ɗaya ba ka dawo ba ni kuma aka kira ni daga gida na zo Abbie ɗina bashi da lafiya, sai na kai Azhar gidan cousin ɗinka na ce su ajiye ma shi koda Allah zai sa ka dawo saboda nima ina jin tsoron na tafi dashi Qatar iyayena su tuhume inda na samu shi ina jin tsoron asirina ya tono sun gano nayi aure batareda da sani su ba.
"Innalillahi wa'inna illahim raji'um! Maysun kin kashe ni waya gayamiki ina da alaƙa da waɗannan mutane?" Makwabtaka kawai ta haɗa ni dasu sai kuma kasantuwar mun fito ƙasa ɗaya amma daga wannan babu wata alaƙa a tsakanin mu.
Ai kuwa Maysun ta karawa kukanta kaimi kusan larabawa da mugun so 'ya'ya tun Aliyu na Uku yana rarrashinta har ya zuba mata ido shi ma ya ji da kansa.
*NIGERIA*
Bugun kofar ɗakin Sadiya Mami ke yi tare da kiran sunanta amman Sadiya tana ji tai banza da ita, hali yanzu kowa haushinsa take ji Mami bata fasa buga mata ƙofa ba sai da ta kai da yi mata rantsuwa sannan ta taso da kumburarrin idanunta tana zuburo baki fuskar nan ta, ta a haɗe "Mami ba fa mutuwa nayi ba da za a dame ni da bugun ƙofa.
Ta faɗa sa'ili da ta buɗe kofar wawan duka Mami ta kai mata tai sauri kaucewa cikin ɓacin rai Mami ta shiga zazzaga mata masifa "Ka ji min 'yar banza yarinya har ni za ki faɗa wa maganar banza da ki mutu ɗin ja'irar yarinya mai taurin kan tsiya to da kika ƙunshe kanki ɗaki tun jiya nufinki kika kashe kanko ko me?"
"Ba za ki taɓa gane halin da nake ciki ba Mami.
"Dallah rufe min baki shashasha banza Abba ne kaɗai namiji da ya rage a duniya da har za ki nemi ki illatar da rayuwarki domin sa?"
"Mami ni fa duk abunda za ki faɗa jin ki kawai nake yi amman zuciyata ta riga tayi nisa akan Yayanmu shi ne namiji tilo dake sarrafa zuciyata.
Duk mugun kallo da Mami ke yiwa Sadiya bai sa tayi shiru da sai da kai aya, hakan kuwa ba ƙaramin linkawa Mami ɓacin ranta ya yi ba,dan haka ta cigaba da zazzaga mata faɗa "To bari ki ji idan ma kwayoyi da kike sha ne ke ƙara tunzira ki kina wannan shashanci a banza don kuwa Abban da kike hauka akansa yana can gidansa da matansa har gudu biyu hankalinsa kwace zuciyarsa zaune,ke kuma kina nan kina haukar banza.
Sosai kalaman Mami suka taɓawa Sadiya zuciya don kuwa jin su take yi tamkar tafasasshen ruwa zafi ne Mami ta watsa mata a sassan jikinta, ta juya a fusace ta nufi bathroom Mami ta bi ta da kallon takaici, tana kissima dole ta ɗauki tsatsauran mataki akanta.
*ABBA BASHIR MANSION*
Rumaisa tana komawa ɗaki kiran Aunty Raliya yana shigowa wayarta da hanzari tayi picking daman tana buƙatar abokin da za ta fesarwa da abun da ke cinta a zuciya, ko gaisawa bata bari suka yi da kyau ba ta shiga fadar "Aunty kin ga