Author : EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category : KDP NOVELS
hankali zubewa ya yi a gabanta cikin muryar kuka yake faɗa mata abun da ya faru wani irin bugawa zuciyarta ta yi sai ga mai babban ɗaki ta zube a sume, tashin hankali goma da ashirin aka kwashe ta zuwa asibiti kamin ka ce kwabo, video Aliyu na Uku tare da karuwarsa kamar yadda suka ce ya fara trending a social media wanda aka rasa waye ya saki video.
Yaya Gimbiya ce ta ɗaga waya ta kira Aliyu tana kuka tana tsine masa, tare da faɗin idan ya zama silar mutuwar mahaifiyarsu ba za su taɓa yafe masa ba. Cike da tashin hankali ya shigo jirgin yamma shi da twins suka nufo birnin kudu, twins ke kwatar masa da hankali.
*KANO NIGERIA*
Cikin hukunci Ubangiji su Aydah suka kammala zana jarabawa yanzu tana zaman jiran fitowar result ne. Rumaisa har ta wuce EDD ta wanda hakan ya ɗaga mata hankali ga ciki har ya shiga watanni goma amma babu alamar haihuwarsa, yau da ta je awo sai riƙe ta suka yi aka yi inducing ɗinta Rumaisah tasha bakar wahala domin haihuwa taki zuwa sai azaba take sha daga ƙarshe jini ya ɓalle mata ga baki ɗaya ta fita hayyancinta, dole sai cs aka yi mata aka fito da baby girl wani abun tashin hankali idan ana ƙara mata jini tana bleeding likitocin sun kasa gane idan matsalar take. Aunty Raliya ce ta kira Aydah ta sanar da ita halin da Rumaisah take ciki a haukace Aydah ta iso asibitin, bayan kuka babu abin da Aydah, Ammi da Aunty Raliya wata nurse ce ta fito ta kira Ammi tazo a ruɗe Ammi ta shiga ɗakin tun daga yadda taga numfashin Rumaisah na hawa da sauka ta tsinke, hannunta Ammi ta kama ta jinke cikin nata, idanunta na ambaliyar hawaye "Ammi ki yafe min ki roƙa min gafara wurin Abba da aunty Raliya da yaya Safwan har ma Aydah. Ammi mutuwa zan yi.
"Ba za ki mutu ba Rumaisah in shaa Allahu Allah zai tashi kafaɗarki, ki raini 'yarki da hannunki ki bata ingantacciyar tarbiyya.
Murmushi kurum Rumaisah ta yi tare da girgiza kai "Ammi ko bayan na mutu don Allah ki cika min alkawarin da na daukar wa Aydah ki bata abun da na haifa nasan za ta kula da ita za ta bata tarbiyyar da kike hasashen zan bata dan Allah Ammi ki cika min wannan alƙawari.
Kasa magana Ammi ta yi a dalilin kukan da ya ci karfin ta nurse ɗin da ta shigo da ita ta ja ta zuwa waje, hannun Rumaisa dake cikin nata tasaki har ta isa bakin ƙofa tana waiwayen Rumaisah. Bayan fitar Ammi aka sakawa Rumaisah oxygen, babu jimawa numfashinta ya tsaya cak! Hatta da likitocin dake kanta sai da mutuwarta ta girgiza su, sai dai babu yanda suka iya duk mai rai sai ya dandani mutuwa. Farin mayafi suka ja tare da lulluɓeta kana babba daga cikinsu ya fito yana goge zufa dake ta tsatsafo masa a goshi cikin rauni murya ya faɗa musu rasuwar ta. Daga Ammi har su Aydah rushewa da matsanancin kuka har aka wuce da gawar Rumaisah zuwa gida Aydah ta kasa daina kuka da kyar ta iya kiran Mami da Daddy ta faɗa musu hatta da Sadiya da bata jituwa da Rumaisah mutuwarta ta girgiza ta.
Misali karfe 4:30pm aka yi jana'izar Rumaisah aka kaita gidanta na gaskiya, duk wanda ya zo ta'azziyya zai tarar da Aydah rungume da baby a jikinta, ta yi kuka har idanunta sun kumbure mutuwar Ab ta dawo mata sabuwa ji take kamar yanzu ne ta rasa shi, idan kuma ta tuno da irin zaman da suka yi da Rumaisa shi kenan sun tafi sun barta sai ta sake fashewa da kuka.
#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.
[2/6, 1:54 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye.
097.
Har aka yi sadakar bakwai Aydah bata daina kukan mutuwar Rumaisah ba. Yadda ta yi kukan mutuwar Rumaisah bata yi ta Ab haka ba saboda duk sanda ta kalli Babyn Rumaisah sai tausayin yarinyar ya kamata sai ta ji mutuwar mamarta ya dawo mata sabuwa. Ammi bata hana wa Aydah tafiya da little Rumaisah wacce suke yi wa lakabi da Baby Noor sai dai Mami ce ta nuna ƙin amincewarta a cewarta yaushe aka gama rainon Aydah ballantana ta raini wani ko ma wanin jinjira sabuwar haihuwa.Haka Mami,ta murje ido
renon baby Noor ya koma hannun Ammi,Amman kullum Aydah na hanyar zuwa gidansu Rumaisa ganin Baby Noor,idan Mami tace abun baya daga mata hankali tayi karya.har shawara Hajiya Zeenah ta kawo mata
akan ayiwa Aydah asirin da Baby Noor za ta fice mata arai ta ji ta tsani yarinyar Ga baki ɗaya Mami taki yadda da haka. Tun da ta yi wa Daddy asiri ya kori AB bata kara ganin kwanciyar hankali cikin gidan aurenta ba ga Daddy ya zama wani iri tun faruwar al'amarin iyakasa ya riqa bin kowa da kallo bai cika magana ya dawo mata miskilin ƙarfi da ya ji, shi kan murmushinsa ba ma za ta iya tuna sanda ya yi mata shi ba. Ga kamfaninsa da ya sakarwa su Alhaji Sanusi da Alh Umaru,sunayin yadda suka ga dama abun duniya duk ya yiwa Mami,yawa karo na farko
da ta tsani laifukanta karo na farko da ta yi da danasanin raba Abba Bashir dasu,da tasani da tabarsa, gashi nan dukiyar da take hange tana dab da subuce musu ga bangaren auren Sadiya da Alh samanni kullum cikin tashin hankali suke uwargidanta Hajiya Saratu ta hana Sadiya walwala acikin gidan,tun da ta shigo gidan basu taɓa haɗa shimfida da Alh sammani ba duk lokacin da yazo kusantar Sadiyar sai yaji an mayar dashi kamar ba namiji ba sannan duk lokacin da yake tare da Sadiya,sai yaji tana wani irin mummunan warin jaba har ta kai ta kawo baya kwana a gidan Sadiya,iyakarsa su yi waya idan tana bukatar wani abu ya tura mata kudi ta account ta siya. ba ƙaramin damuwa Sadiya ta shiga ba. wata rana Siyama,ta kai wa Sadiya ziyara ganin halin da Sadiyar take ciki yayi mugun ɗagawa Siyama,hankali dakyar Sadiya ta buɗe baki ta yi wa Siyama bayanin matsalarta da Alh.samanni tun lokacin da ta tako kafarta acikin gidansa bata kara samun farin ciki ba,haka take fadawa Siyama wata rana jin take kamar ta kashe kanta saboda bakin ciki har wurin malamin dake mata aiki ta koma ta tarar ya mutu.
Dan tasan ba haka Hajiya Saratu tabarta ba. Siyama ,ta girgiza kai tana faɗin."Yaya Sadiya har yanzu duniya bata koya maki hankali ba?"baki tuna irin hakkokin mutane dake kanki ba keda Mami,nasan duk irin biyar malamman da kuke yi yaya Sadiya ki godewa Allah tun da Allah ya fara nuna maki ishara tun anan duniya.
Da shock Sadiya ke kallon Siyama,bata taɓa tunanin duk tasan irin abubuwan da suka aikata ta karkashin ƙasa ita da Mami ba, Siyama ta gyada kai tana faɗin."nasan komai yaya Sadiya,ko asirin da kika je kika saka gidan yaya Abba ni da kaina naje na cire,yaya Sadiya tun kafin lokaci ya kure maki ki tuba ki komawa Allah.
Wata irin nasiha Siyama, keyi wa Sadiya mai shiga jiki har dare suna tare da Sadiyar haka Sadiya ta dauki alkawarin duk irin shawarwarin da Siyama ta bata za ta yi amfani dasu tun daga lokacin Sadiya,bata barcin dare ita ce azumi Litinin da Alhamis,ita ce zuwa makarantun islamiyya a boye tana bada sadaka cikin watanni ukku Sadiya ta yi wani irin sanyi na ban mamaki, haka zalika taga canji sosai a al'amurranta musamman yanzu Alhaji sammani da yake zuwa gidanta yana kwana,shima tana masa addu'a sosai dan ta lura ba haka nan kawai matarsa tabarsa ba,itama tana sa yayi sallolin dare da yawan azkar da azumi,shi kansa yaga canji sosai ajikinsa duk wannan tsoron matar tasa Saratu da yake yi ya ragu sosai a zuciyarsa har takai ta kawo wani dare ya nemi Sadiya da karfin addu'oin da suke yi daga shi har ita a ranar yasan Sadiya a matsayin 'ya macce.
Hawaye ta rika sharewa afakaice tana godiya ga Allah da yaganar da ita kuskurenta tun anan duniya. Ita ma Mami,sosai tayi murnar yadda Sadiya hankalinta ya kwanta.
Yau tun karfe bakwai Siyama ta kira sadiya a waya suka gaisa,cikin sanyi murya Siyama ke faɗin."yaya Sadiya ko mu je mu lallashi Mami,tayi hakuri tabar Aydah ta karbi Baby Noor. Naga yadda Aydah take cikin damuwa hanata karɓar ta da ta yi,kina ganin yadda Aydah ta zabge tayi wata irin rama lokaci ɗaya, don kawai Mami ta hanata daukar Baby Noor ina tsoron wani ciwo ya je ya shige ta, ga Daddy yaki yace komai a maganar.
Siyama ta karasa maganar da karaya a muryarta Sadiya
ta sauke numfashi tana faɗin."ki fito da wuri sai ki biyo tana nan ki daukeni da mota,ni kaina damuwar Daddy tana damuna.
Da haka suka yiwa junansu sallama,kusan karfe goma na safe sai ga Sadiya da Siyama,sun zo gida bangaren mahaifinsu suka nufa kai tsaye Aydah suka samu wurin Daddy, Daddy ya daga kai ya kallesu har suka karaso cikin falon cike da girmamawa suka nufi mahaifinsu suka durkusa a kasa suka gaishesa da respect ,ya amsa yana tambayarsu mazajensu,acan kasan ran Daddy ,yaji dadi yadda yaga ya'yan nasa sun natsu lokaci ɗaya,musamman Sadiya bai taɓa kawowa ransa zata canja haka cikin sauki ba.
"Auta yau baki fita school ba?"Aydah ta mairairai ce masu tana faɗin."bata da lecture sai zuwa karfe biyu, murmushi dukansu suka yi mata.
Shiru ya ratsa a tsakaninsu na kusan sakan biyar,kafin Siyama ta daga kai ta kalli Daddy,da yayi nisa a tunaninsa kallon wani gefe daban yake zuciyar Siyama taji tana wani irin bugawa.
Cikin sanyin murya Siyama,ke faɗin."Nasan damuwarka Daddy,
Kai musulmine ya kamata ka karbi ƙaddara mai kyau ko marar kyau a duk sanda tazo maka. Daddy yaya Abba addu'ar ka yake bukata koda yaushe. Wanda ya mutu ba zai dawo ba har abada Daddy,ka yadda da wannan komai ya canja saboda rasuwar yaya Abba, Daddy ya kamata ka buɗe ido ka fuskanci harkokin kasuwanci ka kamfaninka ga baki ɗaya ka saki.
"Yaya kake so muyi ne Daddy,muna son ganin walwala a fuskarka.
Sadiya ta karɓe itama tana masa nata kalar nasihar kafin suyi magana akan abunda ya kawosu.
"Daddy kayi wa Mami magana dan Allah tabar Aydah ta riƙe Baby Noor tun da aka fara wannan maganar har yau kaki kace komai.
"munafukai dama shiya kawoku kuka dokomin samakko a gida.?"
Mami ta faɗa so pissed up a muryarta "ku saboda kuna wawaye ba ku san inda ke maku ciwo ba kamar Aydah ita za tayi rainon jaririyar yarinya?"da karatun da ta fara za taji koda rainon jinjira?"
Yadda ta haukace tana faɗa yasa Daddy,ya daga kai yana kallonta "mariya!"ki zauna.
Yadda daddy ya kira sunanta cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa yasa ta nemi wuri ta zauna
Amman ga baki ɗaya ranta a ɓace yake."idan cikin zamana dake na taba cutarki ko na rana ɗaya ne Allah ya saka maki tun anan duniya nima idan kin cuceni acikin zamanmu Allah ya sakamin.
kalaman Daddy ba ƙaramin razana Mami,suka yi ba ya dubi Aydah yace Mamana da yaushe zaki dawo makaranta?"yaushe lectures ɗinki zai kare.?"cikin rawar murya ta faɗa masa zuwa 6 na yamma ya gyada kai ya kalli Siyama da Sadiya yace ku jira har ta dawo zuwa bayan magarib za muje mu karbo Noor ɗin.
Da wani irin farin ciki suke kallon mahaifinsu
Aydah ce ta fara matsawa kusa dashi ta Rungumesa haka Siyama kafin Sadiya tabi bayansu. Baki buɗe Mami ta saki tana kallonsu,wani irin mugun sanyi jikinta yayi lokaci ɗaya,kalaman Daddy,ba ƙaramin ruguzata suka yi ba.
Tana jin yadda Daddy ke sakawa 'ya'yan nasa albarka. Tun rasuwar AB bata kara ganin Daddy,yana farin ciki ba sai a wannan lokacin.
*MASARAUTAR KUDU*
Hankali tashe ya iso masarauta kansa tsaye ya wuce kingdom hospital inda mai babban ɗaki take kwace magashiyam! Batasan wanda yake kanta ba. Jininta ne ya yi mummunan hawa Aliyu yana isa ɗakin da take yaya Gimbiya ta taso ta wanke sa da mugun mari cikin tsanani fushi da fusata ta soma zazzaga masa masifa babu kalar zagin da bata yi masa ba. Duk iya ƙoƙarinsa na gani ya fahimtar da ita ya warware mata kurman allo da suke ciki amman taƙi basa haɗin kai, daga ƙarshe ma cewa ta yi ya fice bata son ganinsa. Duk abun da ke faruwa Safiya tana gefen a zaune ko a bisa kuskure bata kalli gefen da Aliyu yake ba.
"Yaya Gimbiya Dan Allah ki tsaya ki saurareni koda na mintuna biyar ne.
"Bakada sauran abun da za ka faɗa har ni ɗin nan na saurare ka Aliyu, ka ci mutuncin mu ka tozarta mu a idon duniya ka wulakanta martaba ta wannan gidan, amma kasani kanka ka yi wa.
Dafe goshinsa ya yi ga baki ɗaya ji yake duniya ta yi masa zafi tare da yi masa juyin ɗan mangwaro.
"Yaya Gimbiya wannan video da ake yawo dashi ta cikin video mata ta ce da muka yi aure tsawon shekaru talatin da biyu..
"What??
In shock yaya Gimbiya ta furta tare da zaro idanuwanta waje tana kallon Aliyu, wani irin juyowa Safiya ta yi tare da miƙewa tsaye har kujera da take zaune akai ta fadi jikinta ne ya ɗauki rawa sai kakkarwa take yi tamkar mai jin sanyi, tsabar kaɗuwar da ta yi har dishi-dishi take gani kallon Aliyu take ta faman yi babu ko kyaftawa ta kasa yarda da abun da kunnuwanta suka ji. Lallai namiji munafuki ne sai yau da asirinsa ya gama tonuwa sunansa ya ɓaci a idon duniya kowa yana masa kallon fasiki mazinaci sannan zai gayamusu wannan daɗadden sirri wato da asirinsa bai tonu ba yana nufi kenan zai yi ta boye musu ne. Nan da nan ƙwaƙwalwarta ta soma tunano mata irin kalar ƙunci da ta dinga shiga tun aurenta dashi, da irin halin ko in kula da yake nuna mata. Yes! Tasan ta yi haƙuri yayin zamanta dashi ta yi juriya haɗe da haɗiye tulin baƙin ciki da yake jefa ta ciki, daidai da rana ɗaya bata taɓa tuhumarsa ba ko ta ji haushinsa kullum burinta ta kyautata masa kuma tana masa uzuri ga zamantakewar su. Sanadin baƙin cikinsa yasa depression ya kamata, kuma har kawo yau ɗinan da yake tsaye a gabanta bata taɓa kai karar sa wurin kowa ba. Ashe duk wannan baƙin wulaƙanci da yake mata saboda wata macce ne duk da bata ganta ba tana da yakini ba za ta fi ta nagarta ba. Akanta ne ta ɗauki tsawon shekaru ashirin da bakwai bata gane kan mijin da take aure ba sai nuƙurƙusar baƙin ciki da zaman haƙuri take yi, iyakacinta tana amsa sunan matar aure ne ba don tasan daɗi dake cikinsa ba. Cikin wani yanayi ta tako ta iso gaban Aliyu na uku ta tsaya tana ƙare masa kallo from head to toe kamin ta girgiza kai hawaye masu masifar zafi suka wanke mata kumatu, cikin sarƙewar lafazi ta furta "ina so ka sake maimaita abun da ka faɗa yanzu nan Aliyu.
A rikice Aliyu na uku ya jefa ƙwayar idonsa cikin nata zuciyarsa tana wani irin bugawa domin ba zai iya tuna sanda Safiya ta kira ainihin sunansa ba tun kafin ta haifi Anaal take kiransa da Yallaɓai bayan haihuwar Anaal ne ta sauya masa suna zuwa Abbu amma a yau gata tsaye a gabansa tana kallonsa ido cikin ido ta kira sunansa na yanka lallai wannan al'amari babba ne ya zarce yadda yake tunani.
"Mata ta ce Safiya sunanta ma....
"Bana so jin sunanta bana kuma buƙatar sake ji komai akanta.
Safiya ta faɗa tare da juyawa a fusace ta nufi ƙofar fita da sauri Aliyu na uku ya cimmata ya riƙo hannunta "Kafin ki tafi Safiya ki tsaya na ba ku labarin yadda al'amarin ya wakana.
"Don girman Allah ka cika min hannuna Aliyu a halin yanzu ina cikin yanayi da ni kaina tsanar kaina nake to balle kai da ka kasance makasudin da yasa nake ji wannan tsanar.
Sannu a hankali ya sakar mata hannu ta juya tare da barin asibitin, komawa ya yi gaban yaya Gimbiya ya mugun kallon da take masa kaɗai ya isa ya gamsar dashi ita ma ba za ta saurare shi, saboda haka ya bar asibitin ya nufo gida ba. Tun kafin ya shiga gidansa ya tarar da ɗan aike fada tana nemansa, ko kadan bai tsorata da kiran da ake masa ba duk tsiyarsu bai wuce su ce sun sauke shi daga sarautar sa ba. Daman can ba damuwa da sarautar ya yi ba damuwarsa ɗaya ce mai Babban ɗaki ya za ta ji idan ta farfaɗo ta tarar da baya matsayin sarki Allah kaɗai yasan irin halin da za ta sake shiga.
Fada ta cika ta yi makil duk wani mai faɗa a ji acikin masauratar kudu yana cikin fada, malam Liman ya buɗe taro da addu'a kana magatakarda ya karanto laifin Aliyu, daga nan waziri ya ɗaga hannu alamar yana so abashi dama zai yi magana. Sarki Hashim Ciroma ya ɓata fuska domin ya kwana da sani Waziri baya tsagin zalunci kuma tun da ya nemi abashi dama ya yi magana tabbas akwai wani abu a ƙasa, cikin daurarriyar fuska Ciroma ya gyaɗa kansa don bai isa ya hana sa magana ba a fada ba hakan zai iya kawo kananun maganganu. Waziri ya kalli Aliyu yana faɗin "Kafin zantar da kowanne irin hukunci yana da kyau mu tsaya mu saurare bangarori biyu, Aliyu fada tana tuhumar ka da zubar mata kima da daraja ta hanyar ajiye wata macce kana fasikanci da ita, ka kuma san irin hukunci da aka tanadarwa duk wanda aka sama da aikata zunubi irin wanda kai ɗinan ka aikata.
Karo na farko da Ciroma ya ji waziri ya burge sa ko kaɗan bai yi tsammaci irin wadannan maganganu ne za su fito daga bakinsa ya zaci ko zai nemi ya kare Aliyu. Kafin Ciroma ya gama tunani ya tsikayi muryar Waziri yana cigaba da faɗin "inaso ka faɗa mana hakikanin gaskiya abun da ya faru shin da gaske ne ka aikata abun da fada ke tuhumarka dashi?"
Aliyu ya yi shiru batareda ko ɗaga kansa ya kalli duk wanda ke cikin fada ba waziri da yaga shiru na Aliyu yana neman ya yi