Author : EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category : KDP NOVELS
mu koma gida.
"Shi kenan Yayanmu Allah tsare ya kaiku lafiya lil sis sai mun yi waya ko? Tun da yanzu kina da naki waya ba sai mun dame yaya Abba da kira ba.
Aydah ta gyada mata kai AB ya yi reverse ya fi ce daga parking lot kamin ya nufi gate Balmo maigadi ya buɗe masa, sai da suka dau hanya kamin ya tuna da wayar da yake yi da Rumaisa a firgice ya dauko wayar still Rumaisa ba ta kashe ba dukka abunda ya wakana tsakaninsu akan kunnenta, sai kawai ya kashe kiran ya yi concentrate tukinsa. A maimakon ya nufi gida sai ya wuce da ita Aj beauty palace and spa yana buƙatar ayi mata kitso ya gaji da gani kanta a ya mutse yau kan har gyara jikin aka yi mata, Aydah har da su kuka sa'ili da ake tirza fatar jikinta ana cire datti. After four hours har kitso an kammala mata a lokaci har an kammala sallar isha kamin ta kira AB sai gashi ya zo tun acikin ya shagon ya kama cheeks ɗinta ya goga tsini hancinsa akan nata yana yaba yadda ta yi kyau ita kuma sai daɗi take ji tana washe haƙora, yana riƙe da hannunta suka fito daga shagon shi ya buɗe mata murfin mota ta shiga sannan ya shiga ya tashi mota, sai da ya tsaya ya yi musu takeaway ya kuma siya musu tsire yasan Aydah da son tsire, sai da dukkan su biyu suka yo wanka shi ya shirya cikin fararen kayan baccinsa sai dai bai rufe bottoms ɗin rigar ba, ita kuma ta saka riga da wando light pink wando iya cinyarta rigar kuma ta kaɗan ta wuce cibiyarta, ta saki kitsonta da aka yi mata two step mai zigzag ya sauka gefen wuyanta jikinta ta ko'ina fidda ƙamshi turare yake. Ta sauko parlorn ƙasa ta nemi cushion ta zauna ta miƙar da ƙafafuwanta akan kujerar ta jingina bayanta a hannun kujerar, ta dukufa dannar wayata yau farin tass! Take ji ranta yaya Abba ya wanke mata duk wani takaicinta na duniya. Burinta ta mallaki wayata kanta sai gashi yau yayanta ya cika mata wannan burin nata. Abba yana ƙoƙarin saukowa ƙasa Rumaisa ta kira sa kaman ba zai yi picking ba saboda yasan karshenta za ta yi masa ƙorafi abunda ya faru ɗazu gudun korafi da mita yasa bai kira ta ba. Ya yi picking cikin taushin murya ya kira sunanta a dalili ya ji ta ya shiru sai ta ja wani kalan numfashi wanda ke bayyanar da ɓacin ranta a fili, kamin ta zarce zuwa ga gundarin maganarta "Nagode Habibi nagode sosai da wulaƙanci ba sai ka yi min hakan ba zan fahimci muhimmancin da Aydah take dashi a wurinka. Abba ni na kira ka fa amman tsabar wulaƙanci ka ajiye waya kana rarrashi 'yar gold, kamata ya yi ka bani uzurinka mu yi sallama in yaso ka dinga rarrashinta har a busa ƙaho sai ka ajiye min waya ina ji duk abunda kake yi, tsakani da Allah Abba na gaji da kalolin wulaƙanci da kake min.
Sai da ya murza fatar goshinsa yana sauke numfashi kafin ya ƙara yi ƙasa da murya ya shiga rarrashinta shi mutum ne da baya so tashin hankali ko kaɗan shiyasa duk yadda Rumaisa ta kai da so su yi rigama baya biye mata sai ya kwatar da kansa yana rarrashinta, yana daɗewa kafin ya yi fushi sai dai fa duk ranar da ya yi fushi abin ba kyau, kamin ya sauko wani jan aiki ne. Ya cigaba da rarrashin Rumaisa dakyar ya samu ta sauko ya faɗa mata zai ci abinci idan ya kammala before ya kwanta bacci zai kira ta da haka suka yi sallama zuciyar Rumaisa wasai ita gani take yi tana juya AB son ranta.
Har ya iso cikin parlor ya yi kusa da kanta batasani ba saboda ta yi nisa sosai akan wayarta, ya kai hannunsa ya wafce waya sai da Aydah ta diro ƙasa tana haɗawa da ihu don ta tsorata, tana gani yayanta ne ya yi mata wannan danye aiki sai kawai ta fara kukan nata na zallan shagwaɓa, kukan da babu hawaye ya ajiye wayata ta, a centre table ya kama hannunta ya miƙar da ita tsaye ya maida ta kan kujera ya zaunar da ita yana faɗin ta bari ta ci abinci zai bata wayar kansa ya je kitchen ya dauko plates ya juye musu abinci tare suka ci sai dai dukkan su ba su ci sosai ba shi ya haɗa coffee ita kuma ta ci tsirenta da ya siya mata bayan sun kammala still shine ya tattare wuri hatta da ledar tsire shi ya ɗauke, ba abunda ta yi cikin natsuwarsa wacce ta zama mishi jiki ya faɗa mata gobe monday za ta koma school ita kanta Aydah ta yi farin ciki ji za ta koma school saboda ta nunawa ƙawaye ita fa ta faso gari ta yi waya ta kece raini.
Washegari gari tun da asuba da AB ya tashe ta yi sallah ya hanata komawa bacci suka yi tilawa Alqur'ani mai girma sai 6:30am suka gama ya umarce ta da ta je tayi wanka, ta shirya cikin clean uniform ɗinta. 7:30am daidai ya yi dropping ɗinta a school ya kawo three thousand ya bata duk da yana da tabbaci ba abinda za ta yi dasu. Ya dawo gida ya kwanta ƙarfe 10:22am ya kammala shirinsa na tafiya office ya haɗa coffee ya sha ya hau motarsa sai da ya fara biyawa gida ya gaida Daddy da Mami gani Daddy yana nan yasa dole Mami ta amsar gaisuwar tasa har da karin tambayarsa Aydah ya ce tana school. Yana fitowa ya tarar da Sadiya tsaye jikin motarsa ko kaɗan bai yi mamaki ganinta ba saboda, yasan za ta aikata fiye da hakan nan take ya murtuƙe fuska, ya yi tamkar bai gannta ba ya buɗe mota ya shiga kamin ya tashe motar sai kawai Sadiya ta ɓalle murfin front seat ta shiga ta zauna a natse ya kalleta sai lokaci ya lura da kayan bacci ne sanye da jikinta riga da wando irin masu tsatsin nan ya kauda fuska.
"Sadiya dan Allah ki fita sauri nake yi idan magana kike so yi dani ki yi hakuri har na dawo daga office zan biyo ta nan.
Tun sanda ya fara magana cikin zallan natsuwa da taushin murya Sadiya ta yi mishi kur da idanunta, tana kallon yadda tattausan laɓɓansa ke motsi ji take kamar ta kai mishi sumbata akansu, a halin yanzu komai AB ke yi bala'in burge ta yake yi sai da ta ja deep breath kamin ta furta "Shikenan zan jira ka Yayanmu nasan za ka zo saboda ba ka saba faɗar karya ko saɓa alƙawari ba. Amman kafin na fita inaso na faɗa maka Yayanmu ina sonka kwatakwacin yadda nake so rai da numfashina na yarda na kuma amince soyayyarka jabranta ce gare ni da zan iya yaƙi da zuciyata Yaya Abba da na yi yaƙi da ita ta dangana da kai kasantuwar a yanzu kana matsayin mijin ƙanwata ne, sai dai zuciyata ba za ta iya ba domin ta yi nitso acikin kogin sonka da ƙaunarka. shiyasa na yanke wa kaina shawara zan nemi soyayyarka ko ta ƙarfin tsiya wata kila za ka, kalle ni a matsayin mai sonka kai wata kila kuma za ka ce ina da matsala a ƙwaƙwalwata amman a zahirin gaskiya sonka ne kawai ya yi min yawa idan akanka ne yaya Abba bana ji bana gani na kuma shirya wa fuskantar kowanne irin kalubalen.
Na yi zurfin a sonka har bana iya banbance me nafi so a tare da kai ba, zai iya zama muryarka ko kuma kyawunka, amma in mun hadu sai na ji gaba ɗayanka nake so tinda zuciya ta bataso nayi son kai. Dan haka na shirya tsaf domin cikar muradin zuciyata, ni ban damu da ka soni ko karka soni ni dai kawai naga na mallake ka a matsayin nawa ni kaɗai anan ne zan tantance tsakanin me nake so a tare da kai na kuma share kokwanto na.
Batareda AB ya ce uffan ba sai jujjuya key ɗin mota yake yi tana dasa aya ya ce "To naji duk abunda kika faɗa Sadiya ba kuma zan hana ki abunda shaɗaniyar zuciyarki take kisimamiki akaina ba. Kawai alfarma guda za ki yi min ki fita min daga mota kada ki sa nayi latti akwai masu jira na a company.
Yadda ya yi magana cikin tattausan kalami yasa ta buɗe motar ta fita amman duk da haka sai da ta sake tuna mishi da tana jiransa kar ya saɓa alƙawari bai ce da ita komai ba ya ja motarsa ya wuce office, ya tarar da ayyuka da dama yana cikin duba wasu cars design kira ya shigo wayarsa na wata baƙuwar number ta truecaller yaga sunan Anaal Aliyu na Uku sai lokacin ya tuna da kulla yarjejeniyar kasuwanci da kamfanin KIM'S Automobile ya yi requesting za su yi a can Lagos. Cikin sanyi muryarsa ya ya picking wani abin mamaki muryar Anaal na Uku tana sauka a dodon kunnensa ya ji wani irin bugawa zuciya ita ma Anaal ana ta bangaren haka ta ji ita har da wani sanyi-sanyi ke ratsa kasusuwan jikinta, tun sanda kamfanin whitepaper Automotive Germany ya nemi su kulla yarjejeniyar kasuwanci da kamfani su AB bata taɓa magana dashi a waya ba iyakanci su chat shima sau biyu ne suka taɓa magana, gaba ɗayansu jikinsu ya dau rawa sakamakon jin muryoyin junansu.
#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.
Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[1/2, 9:38 AM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
#Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye.
048.
Da kyar Abba ya haɗa natsuwarsa guri ɗaya ya amsa sallama da gaishesa da Anaal ta yi, ba ƙaramin namijin kokari Anaal ta yi ba da ta iya tattara kalaman bakinta har ta tuna masa da makasudin kira shi da ta yi sun dauki mintuna biyar shiru kafin AB ya iya bata amsa da cewa zai zo on Wednesday daga nan suka yi sallama. Ya maida ganinsa akan secretary Skyler wacce ta shigo ofishin nasa lokacin da yake waya da Anaal.
"What is happening Skyler?
"Sir, there is a girl who wants to see you. I told her to wait. I will let you know if you want to see her because her name is not in the list of people who have an appointment with you.
Shiru AB ya yi tare da nazarin wacce yarinya ce za ta zo neman sa ƙosai wannan mahaukaciya ce Sadiya yasan Skyler tasan Rumaisa da ita ce bama za ta tsaya jiran permission ɗinsa ba za ta bankaɗo ƙofa ta shigo.
"She told you her name?"
"Yes sir she said her name is Mufeeda Habib Bichi sir she's beautiful.tsayawar da fuskarsa yayi cikin ta Skyler yana son ya tuna inda ya taɓa jin sunan kafin kwakwalwarsa ta tariyo masa komai
Wannan karon bai san meya kawota ba.Ya rabbi !"kasa wannan karon abubuwa suzo masa da sauki ya faɗa murya can ciki har lokacin Skyler na tsaye tana jiran umurnin maigidan nata,ya juya kan Skyler ya faɗa mata tace ta shigo.kamshin turarenta ne ya fara ziyartarsa kafin ya daga kai ya kalleta , gaskiyyar Skyler ne mufeeda ta cika macce a duk inda namiji yake neman macce cikakkiyya mufeeda ta kai ,zama tayi akan doguwar soofar dake girke a katafaren office din nasa ta dauki kafa daya akan ɗaya ta cigaba da bin AB din da wani asiritaccen kallo wanda ya kasa fassara sa."mufeeda ya kike!"Ya faɗa yana kallon gefen da take murmushi ta ɗan saki cike da kunya tana sauke murya take faɗin."ina kwana.!"dan har lokacin safiya ne,lafiya lau ya guda ya kwana biyu."muryarsa kawai da takeji tana sata cikin wani irin yanayin kaunarsa mai dulmiyar daita.cikin rawar murya take faɗin."gida lafiya lau Alhmdullahi,ta faɗa cikin rawar murya idonta na taruwa da hawaye lokaci ɗaya,duk girmanta duk kyawonta duk ajinta durkusawa tayi agaban Abba Bashir tana wani irin kuka na ban mamaki mai taɓa zuciya da ruhin mai saurare lumshe ido yayi a hankali ko kaɗan bayason kukan macce har cikin kansa yakejin kukanta yana wani hargitsa
Ba shiri ya taso daga kan kujerar da yake zaune ya tsaya a gabanta.da sanyin muryarsa ya kira sunanta ta dago kanta fuskarta da hawaye har lokacin da suka kasa tsayawa."mufeeda tashi ki zauna muyi magana."Ya faɗa yana bata umurni kanta take girgiza masa cikin raunin murya take faɗin bazan tashi anan ba har sai ka amince da zaka aureni Abba,nayi kokarin na cireka araina nabi umurnin mahaifina hakan bai yuyuba.idan ka amince zaka aureni zan kaika wurin baffana a daura aurenmu baffana yana da jinkai ba kamar mahaifina ba da yake da zafi."ina sonka ina sonka Abba tun ranar da na fara ɗora idanuna akanka!"wani irin bugawa zuciyarsa keyi da sauri da sauri wannan wace irin rayuwace?"daga wannan sai wannan."shiru ya ratsa a tsakaninsu na kusan minti biyar Abba ya faɗa cikin duniyar tunani ta yadda zai bullowa Al'amarin mufeeda batareda ta kara jefa kanta cikin rikici ba ko taji haushinsa.mufeeda tashi zauna muyi magana,yadda yayi mata magana cikin sauke kai ta zata zaiji tausayinta yace zai aureta sai tayi yadda yace ta tashi ta koma kan soofa ta zauna ta shiga share hawayenta da mayafin kayanta.zaki yimin wata alfarma mufeeda."daga kai tayi tana kallonsa sai ya daga mata kai ya cigaba da faɗin."ki dauka kaddarar haɗuwarmu bazai sa muyi aure ba mufeeda ki dauki haka a matsayin ƙaddara Acikin salloli biyar ki rika addu'a Allah ya cire maki soyayyata aranki ya kawo maki Alkhairi acikin Rayuwarki."mufeeda aurenmu bazai yuyuba bazan boye maki ba mahaifina ya riga yayi min aure tun lokacin da Mahaifinka yaki yadda da zancen aurenmu ko sati ɗaya baayi ba.kallonsa take cikin tashin hankali da kidemewa cikin rawar murya take faɗin "na amince zan zo a matsayin matarka ta biyu na yadda zanbi matarka yadda kakeso zan tafi da duk yadda ka tsara gidanka.ba karamin karya masa zuciya Nabeela tayi ba.bai taɓa sonta ba,yaji mugun tausayinta sosai,sai ya zauna ya soma rarrashinta cikin kalamai masu tausasa zuciya kuma babu laifi ta fahimcesa har bakin mota ya taka mata sai da yaga motarta ta fice daga harabar companyn ya shiga sauke numfashin da yake rike dashi addu'a ya shigayi aransa Allah yasa karshen wannan matsalar kenan Allah yasa bazai kara haduwa da mufeeda ba a rayuwarsa inhar akan wannan matsalar ne.yana mata fatan Alkhairi a duk inda rayuwa zata kaita.karfe biyu ya dauko Aidah school ganin sun nufi hanyar restaurant ta kallesa yana tuki take faɗin."Yayanmu ni na gaji da cin abincin Restaurant snacks kawai za'a karbo ,shi kaɗai yayi oder abincin da zai ci ita kuma aka haɗota da snacks, gida suka wuce daman shi yayi sallarsa a office.sai da ta fara yin wanka tayi sallah sa'annan ta sauko kasa taci samosarta ,AB dake zaune cikin parlor da laptop yana aiki akanta dan shi har lokacin ya dade da kammala cin abincinsa.Aidah ta kalli gefensa tana faɗin."Yayanmu kai bazakaci snacks din ba.?"girgiza mata kai yaqi batareda ya kalli gegenta ba
Kwanciyarta ta gyara cikin kujera da wayarta a hannunta da lokacin har ta buɗe kafafen sada zumunta ,tun daga kan facebook, twitter,IG, TikTok wahtsapp,wani Hausa book da Farhaa Kabir ta tura mata takeso ta fara karantawa ,taji anata zuzuta haduwar littafin mai suna (fathiyya)rike Wayarta tayi ta soma karatu cike da nishadi da walwala daman tafi son haka ba irin gidan Mami ba ayita takurawa mutum ana sakasa aiki a kitchen,jin shirun yayiwa yasa AB ya daga kai ya kalleta karfa kiyi bacci zuwa 4 zan kaiki islamiyya baby."wani kalar turnuke fuska tayi tana tura masa baki cikin Shagwaba take faɗin."Yayanmu yanzu fa inada aure ya kamata ace na aje islamiyyar nan na sauki Alkur'ani harda haddar wani bangare acikinsa ga kuma sauran littafan addini Nidai kawai nabar zuwa."ta faɗa sounding so very free a muryarta,wannan karon bude baki yayi yana kallonta yaji ransa ya ɓaci jin wai har Tasan tanada aure.
"Dawa kike AUREN?"ya faɗa cikin kakkausar murya ,sai ta tura masa baki a tsawace ya kara yimata tambayar,cikin rawar murya tace kayi hakuri juyawa kawai yayi ya cigaba da abunda yake bai san meyasa maganarta ta bata masa rai ba.karfe huɗu kamar yadda yace ya sauketa a school ya shige cikin gari sai da suka tashi yaje ya dauketa direct gida suka wuce dan ana gafda kiran sallar magarib har lokacin kuma Fuskar AB a tamke take dan hakama Aidah ta shiga hankalinta ,ita yanzu tunda tana da Wayarta bata wani damu da fushin da yayan nata yayi ba daman suna shigowa kowane ya nufi bangarensa.har bayan sallar magarib sadiya na zaune a parlor Gabaki ɗaya ranta a ɓace yake ganin har lokacin babu alamar Abba zaizo kasa daurewa tayi daman kowa na daki ita kaɗaice a parlor ,sama ta koma ta dauki hijab har kasa ta dauki car key ta fice daga gidan batareda ta sanarwa Mami ba sai da ta duddurawa maigadin gidan AB ashar kafin ya bude mata get shi dai da kallon mamaki ya rika Binta ,AB na zaune a parlor ya rikajin karar door bell daman aidah tunda ta taso islamiyya bata sauko kasa ba ,da mamaki yaje ya buɗe kofar ,sai da gabansa ya fadi ganin wacce ke tsaye a bakin kofa da sauri sadiya ta nufesa babu kunya barantana tsoron Allah ta wani shige cikin jikinsa ta rikesa sosai ta kwantar da kanta cikin jikinsa da sauri AB ya hankadata a tsawace yake faɗin."sadiya daga ina kike cikin wannan daren,ta shagwabe fuska tana fadin."nata jiranka baka zoba na kasa daurewa ne yayanmu.!"da gaske sadiya bata da hankali !"ya faɗa can kasan ransa shigewa tayi acikin parlor da kallo ya bita ya rufe kofar ya