Author : EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category : KDP NOVELS
b Aliyu
#team tagwaye Novels
#kurman Allo.
Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/15/2023, 10:35 AM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye Novels
024.
*AREWA BOOK:*
Jeddah3256
*MASARAUTAR KUDU*
Tun daga ranar da Kilishi ta bayyanar wa Ciroma da ainihin buri da muradinta ta ya ye masa natsuwa da kwanciyar hankali. Kullum burinsa da fafutukarsa, haɗe da faɗin tashinsa sun ta'allaka ne a nema da lallube mafita wacce yake kyautata zaton za ta kaishi ga cimma muradin sa. To amma wani babban abin takaici har yau ɗinan da ya tashi tsakiyar yana shawagi daga bangon gabas zuwa na yamma bacci ya kauracewa ganinsa duk da wannan ba shi bane karo na farko da ya tsinci kansa a cikin irin wannan yanayi ba. Kusan duk daren Allah sai ya tashi tare da matsanta wa ƙwaƙwalwarsa da ta nemo masa saukaƙkiyar hanya da zai bi ba tare da wani ko wata ya farga da takunsa. Burinsa ya sami mafitar da za ta sada shi da daɗe muradinsa. Matuƙar zai sami biyan bukata bai damu da ko mutane nawa za su cutu ba.
Matarsa kuma amaryarsa Hajiya Umaima ce ta juya domin gyara kwanciyar ta sai kawai ta yi tozali da mijinta dake sarƙe da hannaye a ƙirji yadda yake safa da marwa yafi kama da mace mai naƙuda.
"Allah ya taimake Ciroma kuma sarki gobe a masarautar birnin kudu wacce damuwa ce ta saukar maka haka wacce ta hana ka more dare wanda Allah subhanahu wata'ala ya sanya don ya zamo wa bayinsa mahuta (hutu)?"
Hajiya Umaima ta ƙarasa magana tare da sakkowa daga kan gado ta nufa wurin Ciroma wanda yake gani ga baki ɗaya duniya ta yi masa juyi ɗan mangwaro wani kyakkyawan numfashi Ciroma ya fesar kafin ya juya ya fuskanci Umaima cikin wata rikitatciya murya ya ce "Umaima dole kin ganni a haka domin abubuwa suna neman kwace min duk wani buri nawa yana neman subuce min, wani abin takaici ina ji ina gani Umaima zan rasa cikar burina.
Sai da umaima ta fesar da wata kalar iska daga bakinta kafin ta ce "Allah ya ƙara wa Ciroma lafiya tun farko na zo maka da shawarwari masu kyau da inganci amma sai wannan munafukar matar taka wacce ba ka taɓa gani laifinta sai ta hana ka bin shawarar tawa to wallahi kasani Ciroma matuƙar ba za ka bi hanyar da nake so ɗora ka ba har abada burinka ba zai taɓa cika ba. Hatta da wannan sarautar ta Ciroma da ka gama rainawa wata rana kana ji kana gani za ta gaggare ka, Allah ya ri ga ya haɗa ka da uwar da bata so cigaban ka, ka duba ka gani kaine babba a wurinta amma a koda yaushe ƙannanka take ɗorawa akan komai, kai ta mayar da kai saniyar ware kai da banza da babu duk ɗaya. Amma ka gafarce ni idan na faɗi maganar da ba daidai ba. Raina mugun ɓaci yake a duk sanda na tuna da irin abunda Hajiya Kilishi take maka.
Wani zazzafan iskar Ciroma ya fara furzar wa tare da dunƙule hannunsa na dama ya naushin tafin hannunsa na hagu, wani irin takaici da baƙin ciki yake ji yana taso masa tun daga yarinta yake fuskantar nuna bambanci da mahaifiyarsa Hajiya Kilishi ke nuna wa a tsakaninsa da 'yan uwansa, sau dama ya sha tambayar ta idan akwai laifin da yai mata wanda shi baisan dashi ba ta yi haƙuri ta yafe masa. A duk lokaci da ya yi mata magana kwatankwacin wannan da zarar ta buɗe bakinta sai dai ka ji ta ce dashi "Ciroma wasu abubuwa da muke gani suna jingine ne a matsayin Kurman allo domin ba kowa ke da basirar iya fahimtar su cikin saukaƙkiyar hausa ba balle har ya fassara su zuwa ga harshe mafi sauƙin fahimta.
Wadannan kalaman nata masu cike da murɗaɗdiyar ma'ana da ƙwaƙwalwarsa ta kasa fahimtar ma'anar su.
"Umaima ba wai naƙi shawararki bane kawai dai ina duba da gobena ne kada garin gyaran gira aransa ido.
"Ranka ya dade wannan al'amari fa za a iya aikatawa daga baya sai a nemi yafiyar ubangiji ai Allah gafuru raheem ne. Amma wallahi ina tabbatar maka idan ka ci-gaba da biye wa tsohuwar matarka za ci kasuwa a watse a bar ka da kuturun jaki.
Ba tare da Ciroma ya yi magana ba ya nufi gadonsa ya zauna ya deep breath kana ya yafito umaima da hannunsa "Zo ki zauna Umaima ki yi min ƙarin haske domin a shirye nake tsaf da na bi kowacce irin hanya za a ɗora ni matuƙar dai zan sami biyan buƙatata.
Da sassarfa Umaima ta zo ta zauna kusa dashi ta dinga warware masa zare da abawa.
"Amma Umaima kina gani shigo da jakadiyar Umma a wannan tafiyar zai haifar mana da ɗa marar ido ba?
"Ranka ya dade kafin na shigo da ita cikin wannan al'amari sai da na toshe duk wata kafa da za ta iya zama barazana a gare ka sannan kuma komai na duniya yana da sanadi ka sa aranka jakadiya ita ce mattakalar nasarar ka ta farko.
"Na yarda dake Umaima na kuma damƙa miki wuka da nama idan har muka yi nasara a wannan tafiya Allah ne kaɗai yasan adadin kyaututtukan da za ki mallaka daga gareni.
"Godiya nake Ciroma Allah yabar min kai.
"Amin! Amaryata. Yanzu daga ina za mu fara?"
"Ka bani ɗan lokaci ƙanƙani zan yi magana da jakadiya duk yadda muka yi da ita za ka ji daga gare ni.
"Shi kenan!
Ciroma ya faɗa zuciyarsa cike da muradin mallakar masauratar kudu.
*Washegari*
(Part ɗin mai Babban ɗaki)
Mai babban ɗaki tana zaune a cikin ɗakin baccinta ranta a ɓace yake al'amari Aliyu ya fara kaita bango jakadiya ce ta buɗe ƙofa ta shigo bakinta ɗauke da sallama tana zuba ta zube a gaban mai babban ɗaki "Ranki ya dade gani na amsa kira.
Shiru mai babban ɗaki ta yi na ɗan takaitaccen lokaci kafin cikin izza ta yada ganinta akan jakadiya wacce ke durƙushe tana jiran umarni "Jakadiya na kira ki ne dangane da naɗin sarautar Aliyu gashi lokaci sai daɗa karatowa yake amma babu wani shiri da Aliyu ya yi kuma ko na nemi shi a waya bana samun shi. Shin kin aikatar da aikin da na saka ki?"
"Ranki ya dade ɗazu cikin hukuncin Ubangiji cikin dabara na dinga bugun cikin Magaji ƙarami ya tabbatar min da Sarkin sabon birni yana ikko (Lagos) babu wata kasar turawa da ya je a lokaci da muke tattauna wannan maganar da Magaji ƙarami zuciyata har wani zafi take min miyasa Sarkin sabon birni yake so ya watsa miki ƙasa a ido? Bayan yasan 'yan baƙin ciki da masu son gani bayansa burinsu kenan yabar sarauta da masarauta.
Ajiyar zuciya mai babban ɗaki ta sauke wani irin nauyi take ji ƙirjinta ya yi mata har sai yaushe Aliyu zai san muhimmanci da sauratar nan take da a wurinsa bata taɓa gani jinin sarauta dake gudun sarauta irin Aliyu ba.
"Jakadiya dauko ɗaya daga cikin wayoyina ki kira Anaal.
"An gama! Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana mai amfani.
Jakadiya ta yi magana tare da miƙewa ta dauko wayar, ta yi dialling numbern Anaal har ta tsinke Anaal ba ta ɗaga ba. "Allah ya ƙarawa uwar magajin masaurata nan Lafia na kira Anaal amma cikin rashin dace ba ta ɗaga ba.
"Ki aika ɗaya daga cikin bayi su kira min sarkin fada akwai tattaunawa da za mu yi dashi. Sannan ki faɗawa Rahane ta tabbata magaji ƙarami ya ci karin kumallon sa.
"An gama Ranki ya dade faɗa taki cikawa ta mu makiyanki fadawanki balbela ba ki yi farin banza ba, ki yi naki ki yi na wasu baya goya marayu Allahu ya haskaka kabarin Sarki Usman na Uku.
"Amin jakadiya!
Mai babban ɗaki ta faɗa cikin wata irin izza da taƙama kafin ta kishigiɗa tare da lulawa duniyar tunani.
*ALH BASHIR MANSION*
"Ya aka yi Sadiya ba ki tafi school ba ko yau ba ki da lectures ne?"
Mami ta yi magana tana kallon Sadiya ta shigo mata ɗakin bacci.
Sai da Sadiya ta gaida Mami kafin ta nemi gefen gado kusa da ƙafafuwan Mami ta zauna cikin sanyi murya ta ce "Bana jin daɗi jikina shiyasa ban je ba.
Cike da kulawa Mami ta tashi zaune ta kai hannunta gefen wuyan Sadiya ta tattaba "Subhanalillah! Gashi nan jikin ki har ya yi zafi kin sha magani kuwa?"
"Eh! Na sha. Mami dama zuwa na yi na tambaya ko kin yi maganar komawa ta gidan yayanmu da Daddy?"
Mami ta yi ajiyar zuciya yayin da damuwar da take ƙoƙarin ɓoyewa ta bayyana akan fuskarta "Sadiya Daddynku bai amince ba.
"Innalillahi wa'inna illahim raji'um! Mami saboda me?
Sadiya ta yi maganar a ruɗe ga wani irin bugawa da zuciyarta ke mata da ƙarfin gaske tuni har idanuwanta sun cicciko da ƙwalla.
"Saboda Aydah yake so ya haɗa da shi nan da one week za a ɗaura aure har ya buga invitation card kuma wannan maganar banaso ta fita ta tsaya iya tsakanina dake.
Duk yadda Sadiya taso ta hanawa kanta kuka kasa wa ta yi domin kukan zuwa maka yake ba tare da ka shirya wa zuwan nasa ba, da sauri Mami ta jawo ta zuwa cikin jikinta tana shafa gadon bayanta "Sadiya dama kina so Abba ko kuma daga baya ne kika fara son nasa?"
"Nima bansan yaushe ne ba Mami zan iya cewa dake kawai wayuwar gari nayi na tsince kaina dumu-dumu a cikin matsananciyar soyayyarsa. Mami ki taimake ni ki yi wani abu akai ki hana faruwar aure nan da Aydah dukka Aydah guda nawa ce da za a yi mata aure. Wallahi ko kaɗan bata dace da yayanmu ba.
"Sadiya ba irin maganar da ban gayawa Daddynku ba amma kwata-kwata yaƙi ya saurare ni me ƙato kaman Abba zai tsinta a jikin 'yar mitsiyaya yarinya irin Aydah fisabillahi me ya hau kan Daddynku ya yi wannan bahagon tunani.
Mami ta ƙarashe magana cike da wani irin takaici. Sadiya ta karawa kukanta sauti bata taɓa sanin soyayyar da take yiwa Abba Bashir ta yi girman haka ba sai da ta ji Mami ta furta aurensa da Aydah wannan wacce irin ƙaddara ce take so ta yiwa rayuwarta shigar kutsu jiya-jiya nan ta gama ganin hotunan auren Hafiz Sale suna trending a social media, duk da bata da sauran feelings akansa amma sai da ta ji haushi sai ta ji burinta na son komawa gidan Abba ya karu ko ba komai za ta nuna wa Hafiz Sale ita ma fa ta daina sonshi ko shi kansa Hafiz ɗin yasan Yaya Abba yafi shi nesa ba kusa ba. Ba ma za a hadu su ba. Rarrashin duniya nan Mami ta yiwa Sadiya amma ta kasa daina kuka daga ƙarshe ma tashi ta yi ta fice daga ɗakin na Mami ta koma nata, ta rufe ƙofa da key ta zube anan bakin ƙofar ta cigaba da rusa kuka, ta dauki lokaci yashe a bakin ƙofa kafin ta koma kan gado. Sai yau tasan zafi da ciwo idan ka rasa abinda kake so ashe duk son da take yiwa Hafiz Sale na karya ne ashe yaya Abba shi ne ainihin wanda zuciyarta ta daɗe da ginawa fada. Sannu a hankali take jin tsanar Aydah yana darsuwa a zuciyata yadda take ji raɗaɗi a cikin zuciyarta komai za ta iya aikatawa matuƙar Abba zai zama mallakinta.
AB yana zaune a parlorn sa hannunsa riƙe da mug ɗin coffee saboda yanayi jikinsa yasa yau ya haƙura da zuwa kamfani duk da yasan akwai tarin ayyukan dake jiraye dashi, ba ya jin ƙarfin jikinsa ko kaɗan, tun jiya zuwa yau coffee kawai yake ta durawa cikinsa. A dalilin rasa appetite da ya yi bakinsa har wani ɗaci-ɗaci yake masa coffee kaɗai yake iya sha shima ba don wai yana ji daɗinsa ba. Sai da aka yi kiran sallar azhar sannan ya tashi daga parlorn ya wuce master bedroom ɗinsa ya sako jallabiya ya tafi masallaci, bayan ya dawo daga masallaci ya tsaya bakin gate yana magana da maigadi daidai direban da ya ɗauko Aydah daga school ya yi horn maigadi ya buɗe masa gate Aydah tana fitowa daga mota ta hango AB tsaye, ta ɗaga masa hannu tana dariya shima hannu ya ɗaga mata har ta juya da zimmar ta shiga gida sai kuma ta fasa tana mamaki me ya dawo da yayanta gida yanzu ko kuma dai yau bai je office bane. Sai ta nufi gate wurinsa yana gani ta nufo wurinsa ya yi mata alama da hannu ta wuce ciki gida maƙe kafaɗa ta yi tare da bubbuga ƙafafunta akan interlock girgiza kansa ya yi zuciyarsa tana kisimamai yanzu wannan yarinya da ba a gama raino ba ita ce nan da sati mai zuwa za ta zama matarsa. Wani irin ɓacin rai ya ji yana kanainaye masa zuciya sai da ya ja deep breath kafin ya cira ƙafafuwansa ya fara tafiya ita tana tunkuro shi tana dariya shi kuma yana mata murmushi yaƙe don bai ga laifin da Aydah tai mishi ba da zai sauya mata ko ya tsane ta da alamar bata ma san waina da ake toyawa ba. Da yadda take da ɗan banza surutu nan da tuni ta tambaye shi akan gaskiyar al'amarin.
Sadiya tana kwance kamar wacce aka mintsina ta tashi ta nufi window ɗakinta dake facing compound ta buɗe idanuwanta suka sauka akan AB da Aydah yadda taga AB yana yiwa Aydah murmushi ya haddasa wa zuciyarta mugun bugawa har bata san sanda ta dafe ƙirjinta da dukkan hannayenta, idanunta suka firfito wani irin kishi taji ya lulluɓe ta.
#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.
Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/15/2023, 10:35 AM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
*AREWA BOOK*:Jeddah3256
#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye novels
025.
A hankali ta sulale ta zauna dabas akan marbles tana jin yadda take fitar da numfashi da wani irin sauri da sauri tamkar numfashin nata zai tsaya ga baki ɗaya. Dunkule hannayenta tayi duka ta shiga gogasu akan marbales ɗin "noo no way!" ta shiga furtawa da dukkan karfinta tamkar mai cutar jinnu haka ta koma cikin ɗakin,watsi ta shiga yi da kayan ɗakin tana sakin wani irin razanannen ihu. Daidai lokacin da AB da Aydah suka shigo cikin parlor dukansu suka kalli junansu kowanne da fuskar mamakin ta ina ihun ke fitowa daidai ita ma lokaci Mami, ta fito daga nata ɗakin jin kamar ihun Sadiya ganin yadda mami ta fito a hargitse yasa AB ya nufi stairs da sassarfa Aydah na biye a bayansa
Da dukkan karfinta Mami ta shiga kiran sunan Sadiya tana buga kofar hankali a mugun tashe. Abba ya ƙaraso yana tambayar mami "me ya samu Sadiyar.?" Ita dai Mami duk a ruɗe take, Aydah ma tazo ta tsaya jikin kofar tana kwalawa Sadiya kira
da damuwa Mami,ta kalli AB dake tsaye a wurin tana faɗin."Abba ko za ka gwada kiranta?" da haka mami ta bashi wuri yazo ya tsaya gaban kofar
yana buga ƙofar Sadiya jin muryarsa yasa ta kalli kofar da sauri."zo ki buɗemin kofa.
Abba ya faɗa da sanyin muryarsa da sauri Sadiya ta nufi ƙofa ta cire key.
A hankali suke bin ɗakin nata da kallo yadda ta hargitsa shi kayanta dake jere a gaban mirror dressing duk ta farfasa su.
Hankali tashe Abba ya kai dubansa kan hannunta dake fitar da jini sosai da sauri ya ƙaraso cikin ɗakin yana riƙe hannun sosai a rikice yake faɗin."kin fara shaye-shaye ne?"You are bleeding for god sake sadiya.!"
Rudewar da yayi lokaci ɗaya yasa Sadiya ta rungumesa sosai cikin jikinta yadda ta rikesa sosai yasa yaji yanayinsa ya fara canjawa dan ba irin wannan kalar rungumar suka saba yi masa ba duka kannen nasa yau sai ya jita is different akan wacce suka saba yi masa duk kokarinsa na son fisge Sadiya daga jikinsa ya kasa tamkar ma ta mance da Mami da Aydah a wajen a fusace yace "meye haka sadiya?" Ta kwantar da kanta cikin ƙirjinsa tana shaƙar sanyayye ƙamshin turarensa da take bala'in so tun ba yanzu ba tun yana matsayin yayanta uba ɗaya, murya a harɗe take faɗin."Dan Allah Yayanmu ka yafe min ko zanga daidai a rayuwata tun da wannan abun ya faru tsakani na da kai nayi bankwana da duk wani farin ciki da walwalata. Daddy har yanzun bai sakarmin fuska hakama
kai nagane kuskure na wallahi a shirye nake da na koma gidanka muyi zaman aure na har abada.
Ɗagota ya yi cikin jikinsa arikice yake faɗin."In dai nine na yafe maki Sadiya. Aydah ta miƙo masa ɗan ƙaramin first aid box shi ya yi mata dressing hannun, Aydah itakuma ta fara tattara ɗakin da Sadiya tagama hargitsa shi har lokacin Sadiya taki barin Abba yabar ɗakin nata
dama Mami tun lokacin da taga Sadiya ta rungume Abba, tabar masu ɗakin ganin dai Sadiya ta dawo natsuwarta AB yabar room ɗin ga baki ɗaya ya fice daga part ɗin yana mamakin sudden change ɗinta.
Wuraren ƙarfe 3 na rana Mami ta fito da shirin fita da car key a hannunta haka ma Sadiya Aydah kawai ce a parlor tana kallo tana cin abincinta a har yanzu uniform ne ajikinta
Ta kalli Sadiya da Mami, lokaci ɗaya ganin kamar fita za su yi da sauri ta cewa Mami "zan bi ku dan Allah. Tun kafin Mamin tayi magana da sauri Sadiya tace "A'ah ki yi zamanki ke da za ki je islamiyya. Lokaci ɗaya Aydah ta haɗe rai tana kallon Mami take faɗin."Yau fa Mami babu abunda zan yi a islamiyya hardar ma sai