Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   6 / 80

15K to 18K   out of 237.2K words

dunƙule masa a kahon zuciya a fusace ya baro jikin window ɗin ya ɗauki wayarsa ya yi dialling numbern abokin ci mushe sa "Alhaji Umar kaga abinda naga ni kuwa??
"Me ka gani Alhajin Allah?
Alhaji Umar ya faɗa har yana haɗawa da wata 'yar bazawarar dariya.
"Alh Umar wannan shegen yaro tsintatce yanzu nan naga ya fita daga kamfani tare da 'yar gidan Bello madawaki?"
"What??
"Wallahi nake gayamaka ai na zaci ka ga fitar su hankalina ya yi mugun tashi Alh Umar kada waɗannan shegun yara su mayar mana da aiki baya.
"in-sha-Allah hakan ba za ta taɓa faruwa ba bari nayi gaggawar kiran Alh Bello madawaki na ƙara rura wutar al'amari.
"Haka nake so mutumina.
Alh Sanusi ya faɗa tare da hanging up yana saki murmushin mugunta, alƙawari ne ya ɗaukar wa kansa ba zai taɓa bari Alhaji Bashir da shegen ɗansa AB su sake farin ciki a rayuwarsa, shekaru 15 da kafa wannan kamfani shine silar hasassa shi duk wani cigaban kamfani shine ya kawo shi burinsa a ce yafi kowa damawa a wannan kamfani a matsayin sa na ƙani Alhaji Bashir da suke uwa ɗaya amma abin takaici sai da ya gama shan wahala kamfani ya haɓaka ya zama lamba ɗaya, Alhaji Bashir ya ɗauki babban matsayin da yake hari ya ba wa ɗansa AB duk da haka ya danne zuciyarsa ya cigaba da aiki a kamfani daga hawan AB kujerar CEO (Chief Executive officer) shegen yaro nan ya dinga bincike da bin diddigi shige da fice kuɗaɗen Kamfani har yai nasarar gano irin almudahana da suka dinga yi shi da financial director, AB bai bar su ba har sai da suka dawowa da kamfani kuɗaɗen da suka sata wannan abin da yai musu shine silar da yasa account ɗinsu yai ƙasa har yau basu farfaɗo ba. Sannan kuma ya bi ya tare gaba ya tare musu baya duk wani motsinsu akan idanuwanshi. Wannan shine silar da ya haifar da zazzafar ƙiyayya tsakanin AB dasu Alh Sanusi daga wannan lokaci suka shiga bincike hanyar da za su kawo ƙarshen AB a kamfani. Alh Sanusi ya yi nisa da tunani ƙarar buɗe ƙofa da Alh Umar ya yi ya dawo dashi natsuwarsa ba tare da ya ƙarasa tunano irin gada zare da suka ɗannawa AB da mahaifinsa.
*GUSTO RESTAURANT*
AB da Rumaisa suna fita kai tsaye
Gusto restaurant suka nufa AB yana gaba tana bin sa a baya AB ya zaɓi Gusto restaurant a dalili ya yaba da daɗin abincinsu ga kuma wurin babu haniya, bayan an kawo musu menu kowanne su ya zaɓi abunda yake so yaci koda suka kammala ci abinci ƙarfe 3:00pm AB yana duba wristwatch ɗinsa sai da gabansa ya faɗi kasancewa da Rumaisa ya manta da Aydah da ya yiwa alƙawari zai je ya yi picking ɗinta a school agaggauce ya sha ruwa ko ta kai juice ɗin da aka kawo masa bai bi ba ya miƙe tare da kallon Rumaisa yana faɗin "Habibty I have to go bansan cewa lokaci ya tafi sosai har haka ba.
Cike da zallan mamaki ta dire spoon ɗin hannunta ta ɗago "Habibi ina za ka tafi kake wannan saurin??
"Zan je nayi picking Aydah a school kinga lokaci ya tafi sosai sai mu yi waya.
Yana ƙarashe magana bai jira jin ta bakinta ba ya nufar entrance ɗin fita da sauri ta bishi da kallo wannan hali na AB dangane da irin wannan kulawar da yake ba wa ƙannansa yana bala'in ƙona mata rai duk wani abu da ya shafe su sai ya dinga wani rawar ƙafa more especially wannan brat girl Aydah, yanzu da tasan babu alaƙa ta jini a tsakanin shi da Aydah sai ta wani irin mugun kishi ya lulluɓe ciki da wajen zuciyarta, tsabar takaici sai ture abinci tayi ba don ta ƙoshi ba ta ɗauki handbag ɗinta a fusace ta bar restaurant ɗin.
*CRESCENT INTERNATIONAL SCHOOL*
Tun kafin AB ya yi parking ya hango Aydah tana ta faman kumbure fuska murmushi ya yi yasan yau sai sun yi daru da ita Aydah ba dai rigima ba har ta siyarwa tana dashi. Sai da ya yi mata horn kusan sau uku kafin ta nufo wurinsa duk da yasan ta ganshi tun ma kafin ya yi parking ita a dole fushi tayi fushi, tana zuwa buɗe backseat ta jefa backpack ɗinta kana ta zagaya ta buɗe front seat ta zauna, lulu eyes ɗinsa ya watsa mata yana sakar mata da tsadadden murmushinsa. Turo baki tayi gami da kauda fuska tana ci-gaba da kumbure-kumburenta cike da tsokana ya fara yi mata waƙar da yake mata sanda tana yarinya muddin yana so saka ta kuka a wancan lokaci ita yake mata "Aididi, Aididin ya Abba mai majina a hanci tayi k....
"Ya Abbaaaaa! Please stop that horrible song of yours na tsani wannan waƙa bana sonta.
Aydah ta faɗa tamkar cikin muryar kuka, yadda ta kwabe fuska yai masifar ba wa AB dariya sosai ya dinga yi mata dariya ita kuma ta ƙara hasale wa sai kawai ta kwaɓar da seat ta kwanta tare da lumshe idanuwanta "okay I'm sorry my little baby gayamin me kike so na siya miki kafin mu isa gida?"
Taƙi ta tanka masa sai rarrashinta yake tai biris dashi "Shikenan tun da ba za ki kula ni ba nima nayi fushi daga yau mun bata karki sake yi min magana.
Ya yi magana shima yana turo baki kaman ita. Aydah tana ji abunda ya faɗa tai sauri tashi daga kwance da take ta mayar da seat ɗin daidai fuskarta ya bayyanar da irin razanarwa da tayi na ji furuncinsa zuciyarta har wani kalar bugawa yake yi ba abunda ke sauri tayar mata da hankali irin Ya Abba ya ce ya yi fushi da ita "Ya Abba dan Allah karka yi fushi dani.
Tayi magana yayin da idanuwanta suka cicciko da ƙwalla, a natse AB ya juyo ya kalleta yaga yadda take danne hawayenta murmushi ya sakar mata yana faɗin "who touch my Baby??
"Ya Abba ne.
Ya faɗa sounding so childishness har wani kalar turo ƙaramin bakinta take yi wanda hakan ya daɗa ƙarawa fuskarta kyau, a daidai wani super store ya tsaya ya siya mata tarkace chocolate da biscuits, a bakin gate ya ajiye ta bai shiga gida ba yana kara jaddada mata ta tabbata taje islamiyya idan ya bincika bata je ba zai yi fushi da ita. Hakan yasa tana shiga gida ta wuce bathroom tayi wanka ta shirya cikin uniform ɗinta na islamiyya da yake Siyama bata dawo daga school ba dole ita kaɗai za ta tafi ko abinci bata tsaya ci ba ta fice direban dake kai su school ya kaita.




#Love Story 2023)2024
#Jiddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#team tagwaye Novels
#Kurman Allo








Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[11/27/2023, 10:24 AM] Jiddarh Aliyu 2: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU




#Love Story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye novels












*RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU.*
*TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA*




PAID BOOK
008.


(FLASH BACK)
Alhaji Bashir Shamaki shi kaɗai mahaifiyarsa ta haifa tare da mahaifinsa tun yana da ƙaranci shekaru Allah ya yiwa mahaifinsa rasuwa sai dai yana da 'yan uwan su uku da suka haɗa uba ɗaya biyu mata namiji guda. Bayan rasuwar mahaifinsa, mahaifiyarsa ta sake aure idan ta haifi yara biyu Sanusi da Jamila. Matar Alhaji Bashir ta fari maryam ta rasu wacce duniya ta shaida ita ce ta haifi AB bayan rasuwarta ne ya auro Mariya ita kuma ta haifa masa yara uku Sadiya ita ce babba mai shekaru 25 a duniya Sadiya kyakkyawa ce sai dai ba irin matsananci kyau ɗinan ba tana da matsakaici tsayi, ga ta da jiki sosai 'yar lukuta ce kiwon parlor. Sai Siyama ita kuma tana shekara 22 Siyama da Sadiya tsayin su zai iya zuwa ɗaya sai dai Siyama bata yi jikin Sadiya ba, kuma kusan kamanunsu ɗaya sai dai Sadiya tafi Siyama hasken fata, dukkansu suna karatu ne a skyline university Sadiya tana shekarar ƙarshe yayin da Siyama yanzu ne farkon shigarta, sai auta kuma shalelen Ya Abba Aydah tana da shekaru 15 saura watanni uku ta cika shekara 16 tana SS two a crescent International school. Aydah duk ta fi su Sadiya kyawo nesa ba kusa ba, sai dai su nuna mata hasken fata saboda ita fatar jikinta chocolate color ce, bata jiki ko kaɗan gata gajera 'yar firitt da ita har yanzu da ta kai SS two ƙirjinta da kaɗan ya wuce na mai kirge dangi, su kan hips a bar ma maganar su, Aydah tana da wata irin baiwa ta ƙwaƙwalwa bala'in gifted ce komai aka faɗa mata ya zauna akanta, gata da bala'in shiga rai da wuya Aydah ta zauna a wurin ba ka ji kana sonta ba saboda talktive ce ta ƙarshen lissafi bata da saurin fushi sai dai akwai saurin kuka da shagwaɓa wannan kuma ya samu asali ne daga raino da Ya Abba ya yi mata. Duk girman laifi idan Aydah tayi indai Ya Abba yana nan ba a isa a dake ta ba.
Muhammad Bashir shamaki shi ne cikakken sunansa amma an fi saninsa da Abba schoolmate ɗinsa suna kiransa da AB saboda su saukakawa kansu fadar Abba Bashir ɗin. Abba matashi ne mai jini a jiki shekarun sa na haihuwa ba za su wuce 37 ba zuwa dai 38 Abba dogo ne sosai tsawonsa yasa har wani ɗan rankwafa ya yi yana da girman jiki don ba za a kira shi da ramamen ba. Yana da round face mai ɗauke da dogon hanci, Abba yana da wasu irin idanuwa masu masifar ɗaukar hankali gasu manya ne sosai eyes ball ɗinsa gray color ne, laɓɓansa pink kamar yana shafa lipstick sumar kansa baƙa wulik da ita, sajensa da ya bari mai haɗe da gejeren gemin ya ƙara ƙawata fuskarsa, Abba kyakkyawa ne ajin farko fatar jikinsa fara ce mai silke da ja, ja, tun kafin yasan cewa ba Daddy bane ya haife shi ya sha tambayar Daddy shi da wa ya yi kama domin Kwata-kwata ba abinda ya ɗebo daga kamanu Daddy ɓalle kuma Maryam saboda yana da hotunata sometime har saka hotonta gaba yake yi yana kallo ko zai ga idan ya ɗebo kamaninta. mutane sun sha tambayarsa ko shi half-caste ne(ruwa biyu) wannan tambayar har gobe ana masa ita Abba Yayi karatunsa tun daga primary har izuwa secondary school anan gida kano bayan ya kammala sakandare ne Daddy ya samar masa da gurɓin karatu a Kyiv national economic university ukraine ya karanci fannin ilimin kasuwanci da tattalin arziki anan ya yi degree sa har zuwa masters kana ya dawo gida Nigeria idan Daddy ya bashi matsayin CEO (Chief Executive officer) na kamfaninsa. Abba yana farko-farko dawowarsa Nigeria ya haɗu da Rumaisa Bello madawaki suka ƙula alaƙa ta soyayya wacce har takai su matakin aure wanda a ranar ɗaurin aurensu ne ɓoyayyen sirri da Daddy ya ɓoye akan Abba ya bayyana wanda shi ne silar da yasa mahaifin Rumaisa ya ce ba zai haɗa zuri'a da shege marar asali ba. Shi kuma Daddy saboda baƙin ciki da fushin zuciya anan take a wuri ya aurawa AB Sadiya.
(FLASH BACK END)
Koda AB ya dawo gida dare ya yi sosai ya tarar da abincinsa Aydah ta kawo masa da ya yi arba da warmers ɗin sai da ya yi murmushi saboda cikinsa a cike yake, ya kuma san gobe akwai rigima tsakaninsa da ita. A gajiye ya wuce bedroom ɗinsa ya yi wanka boxer kaɗai ya saka ya bi lafiyar gado.
*MASAURATAR KUDU*
Wata kyakkyawar mota ce kirar Mercedes Benz GLS 2023 fara tass da ita, ta shigo zuwa cikin masauratar daidai wurin da aka tanada domin parking mamallaki motar ya nufa ya yi parking da sauri murfin gefen direba ya buɗe wani matashin saurayi ya fito wanda da ganinsa kasan direba ne, ya buɗe backseat ƙafarsa ɗaya da ke sanye cikin takalmin sarauta halfcover ya fara sauke ta kan interlock, sai da ya kusan share 60 seconds kana ya zuro guda ɗaya nan ma sai da ya ɓata lokaci kafin ya fito da gangar jikinsa ya subhanalillah! Tsalki ya tabbata ga Ubangiji da ya halicci wannan kyakkyawar sura duk da shekarunsa sun tafi amma hakan bai ɓoye komai ba na daga kyau halittar da Ubangiji yai masa at least shekarunsa na haihuwa za su kai 52 l swear za ka zaci bai wuce 40yrs ba wani irin kyau gare shi mai fizgar hankali, gashi fari tass kaman ka taɓa skin ɗinsa jini ya fita. Jikinsa sanye da shadda milk in color dinkin babbar riga kansa ɗauke da rawani wanda ya yi matching da shaddar jikinsa. Alhaji Aliyu Mustapha na uku kenan ƙani ga Sarkin Kudu Alhaji Mahmood Mustapha na uku. Cike da izza mai ɗauke da zallan ƙasaita ya shiga takawa zuwa ainihin cikin faɗar ta mai martaba sarkin kudu faɗawa na hango shi suka fara zuba masa kirari yayin da bayi sai zubewa ƙasa suke yi suna kwasar gaisuwa ko kallo basu isheshi ba ballantana su saka ran zai amsa musu, fuskar nan tashi a maturƙe as usual. Faɗar a cike take da 'yan majalisar Sarki, irin su waziri, ciroma, wambai Galadima, jakadan Sarki da dai sauransu yana zuwa ya isa gaban sarki dake zaune akan kujerar sa ta mulki yasha naɗi da alkibba sai da ya zube ya kwashi gaisuwa kana ya nemi wurin ya zauna. Kallo ɗaya za ka yiwa mai martaba ka gano tsanani kamanin shi da Alhaji Aliyu. Sai da sarki ya ƙare masa kallo kana ya yi gyaran murya cikin izza irin ta sarakuna da suka amsa sunansu mai martaba ya ce "Aliyu mun aika maka saƙo muna so ganinka tun kwana biyu da suka gabata amma ba ka amsa kiran mu ba sai yau da ka ga dama, shin ko za mu iya sani dalilinka na yin hakan?"
Shima Alh Aliyu sai da ya gama shan ƙamshinsa irin na wanda jini sarauta ya gama ratsa shi kafin ya amsa wa mai martaba da cewa "Allah ya taimaki mai martaba Amma kasan da cewa tun inada ƙanunun shekaru bana da ra'ayin mulki, saurata kwata-kwata bata gabana.
A fusace mai martaba ke faɗin."wannan karon ba zan saurari uzurin da kake kawomin ba Aliyu nacewa baka son sarauta, kamanta sauratar gadonka ce jininka na zagaye da ita, wannan karon na rantse bazan saurari uzurinka ba kaje kawai ka fara shiri domin na saka sunanka a cikin jerin mutane goma da masaurata za ta yi bikin naɗin sauratarsu. Tashi ka tafi nagama magana.
Aliyu ya sadda kansa ƙasa yana bai wa yayansa haƙuri "Allah ya jada ranka ya ƙara ma lafiya da nisan kwana Allah ya huci zuciyarka."
Daga haka Aliyu ya miƙe tsaye ya fito daga cikin fadar wanda fadawa sai zuba masa kirarin da suka saba yi masa suke ko kallonsu bai yi ba shi wannan kirarin ma ciwon kai yake sakasa to ina ga ranar da yake mulki yasan sai ya kwanta gadon asibiti. Daga nan ɓangaren mahaifiyarsa ya wuce kai tsaye bayi mata tun daga kofar da zata sadaka da babban ɓangaren mai babban ɗaki bayi mata birjik ne ke kai da komawa kowa yana hidima bayyanar Aliyu a wajen yasa suka shiga zubewa gabansa suna miƙa gaisuwa ko kallo basu ishesa ba kai tsaye parlorn da mahaifiyarsa ke ganawa da 'ya'yanta ya nufa, wannan karon bai sameta zaune a Parlon ba kamar yadda ta saba zama ya kalli amintacciyar baiwarta ya faɗa mata tayi masa magana da mahaifiyarsa, ko minti goma bata yi ba ta dawo ta faɗa masa tana zuwa anan ta shiga hidima dashi ta cika gabansa da 'ya'yan itatuwa cima dai mai rai da lafiya irinta gidan sarauta kusan mintina goma sha biyar da zamansa sai ga mahaifiyarsa ta fito cikin babbar shigar alfarma wuyanta da hannayenta sun sha ado da gold tun kafin ta bayyana cikin parlorn ƙamshi ya gama cika ko'ina gami da zagaye ko'ina acikin Parlon,wannan ƙamshin mahaifiyarsa ce kawai mamallakiyyarsa, bayi biyu ne a bayanta tana shiga suka rufo mata ƙofar suka juya suka koma ganin bayyanar mahaifiyarsa cikin Parlon yasa ya miƙe tsaye har ta ƙaraso ta zauna bai zauna ba sai da ta zauna ya durƙusa gafda kafafunta yana gaisheta ta amsa cike da kulawa tana nazarta yanayin yaron nata. Kusan shekaru talatin harda doriyya haka yaron nata yake tun kafin ma yayi aure idan zata iya tunawa tun da ya dawo daga karatu, a haka kullum fuskarsa take babu kalar tambayar da bata yiwa Aliyu ba a lokacin sai dai yace mata babu komai idan tace rashin walwala yaron nata bai hanata sukuni za tayi karya. Jin mahaifiyarsa tayi shiru yasa ya ɗago ya kalleta cikin natsuwa yadda ta haɗe rai yasa gabansa yayi mummuna faɗuwa cikin wani irin yanayi yace "ummah.!"
"Mai sabon birnin.
ta kira sa da sunan da take kiransa dashi yana jin yadda muryarta ke shaking
A razane yake kallon fuskar mahaifiyar tasa yadda ta koma lokaci ɗaya "ba zan gaji da tambayarka ba meke faruwa da rayuwarka? Nasan akwai abunda kake boyemin tsawon shekaru talatin ko ka kashe wani rai ne da ka hana kanka walwala da farin ciki kamar yadda sauran al'umma keyi?"
Girgiza kai ya shiga yi ba tare da ya kalli mahaifiyar tasa ba ,cike da karfin hali ya furta "Dama wajen mai martaba na fito akan maganar naɗin sauratana ta Sarkin sabon birnin kudu.
Ki saka baki ummah,da gaske bazan iya daukar wannan nauyin ba duk yadda zan yi masa bayani ya kasa fahimta ta.
Aliyu ya ƙarasa maganar da respect a muryarsa, yana kallon yadda mahaifiyarsa ke karkaɗa ƙafa sunfi minti biyar a haka ba tare da kowa ya sake faɗar wata kalma ba.
Cike da izza mai babban ɗaki ke faɗin."tashi ka tafi naka gidan Allah ya bamu alkhairi. Jin haka yasa ya ɗan kalli mahaifiyarsa bai ƙara cewa komai ba ya miƙe tsaye yai mata sai da safe dama acikin gidan nasu aka yanki wani fili akayi masa gini irin na sarauta acewar mahaifin su mai martaba Sarki Mustapha na uku

6 / 80