Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   26 / 80

75K to 78K   out of 237.2K words

doguwar casbahar hannunsa ta rike shima ya rike gefe runtse ido ya yi yana karanto wasu kalamai na tsafi. Hakan ma sai da ya dauki wani tsawon minti goma kafin ya bude idanunsa wanda aka saka masu bakin kwalli acikin har kwallin yaso yayi masu yawa, ya zuba cikin fuskar Ammi a hankali ya shiga karantowa Ammi matsalarta da mamaki Ammi ke kallonsa ganin yadda ya karanto lokaci ɗaya batare da ta buɗe baki ta yi masa bayani ba. Ko a zuwan farko Zulai ta aiko wannan shine karo na farko da ta haɗu dashi da sauri ta daga masa kai."yanzu ya kike so ayi?" Da sauri Ammi tace "maigidana yana da kafiya sosai idan yace abu babu wanda ya isa ya canja ra'ayinsa akan abun nan ina so a saka masa son auren yaron da yarinyar mu ke so aransa ya ji duk duniya baya da natsuwa har sai yaga wannan auren ya tabbata a tsakaninsu.
"bukatarki ta biya.
Cikin kankanin lokaci ya buga kasa sai ga bakar laya ta bayyana ya daga layar ya miƙa mata da hannu biyu ta karba acan kasan katifa daidai wurin da yake dora kansa "har abada za ya dinga yin abunda kikeso kuma yarinyar ki za ta auri wannan yaron."
Godiya Zulai da Ammi suka rika yi masa, kafin Zulai tace "To malam nawa kuɗin aiki?"
"Za ku aje dubu ɗariari idan aiki ya yi za ku dawo ku bada ragowar Ammi ta balle zip diyn handbag ɗinta ta ciro rafar kuɗi na naira dubu ta aje agabansa ,da haka suka kara yi masa godiya suka fito Ammi bata samu natsuwar da take buƙata ba sai da ta shiga mota da murmushi cikin fuskar Zulai take faɗin."Kinga riba biyu kenan ga auren auta ga kuma za ki cigaba da juya mahaifinsu yadda kike so daman can juyasa kike sai dai wannan malamin yafi malamin da kika sani karfi.
"Kin san har na matsu ma ya dawo saboda ga baki ɗaya a kwanakin nan Rumaisa ta firgice bata da wata natsuwa a tattare da ita har gida Ammi ta kai Zulai ta ciro dubu goma ta bata.
Ta rika yiwa Ammi godiya.
"Gobe wara haka angon baby kake fa?"Abdulkarim ya faɗa da muryar tsokana wani shegen kallo Ab ke yiwa Abdulkarim tun bayan la'asar yana tare da Abdulkarim idan kuma ya tuna gobe za a daura aurensa da Aydah sai ya ji komai dake zagaye dashi yana birkicewa cikin duniyarsa
miƙewa tsaye ya yi yana yiwa Abdulkarim wani malalaci kallo, kafin yace "Ni na kawo kaina shiyasa za ka rika fadaymun duk wata magana da za ta fito daga bakin ka ba laifinka bane.
da haka ya fice daga ɗakin na Abdulkarim yayin da Abdukarim ya bisa yana masa dariya cikin compound ɗin gidansu Abdulkarim ya dauki motarsa, a hanya ya tsaya ya yi sallar magarib batare da ya yi tunanin komai ba ya dauke kan motarsa zuwa gidansu Rumaisa wata irin kewarta ce ke zagaye dashi karfin hali kawai yake kwana biyu da bata daukar wayarsa shi kaɗai yasan irin azabar da ruhinsa ke sha, sai da ya yi parking adaidai kofar gate ɗin gidansu sa'annan ya samu kwarin gwiwar kiranta yanata addu'a wannan karon Allah yasa ta dauka. Har ta gama ring bata daga ba haka ya jera mata kira biyar bata dauki wayarsa ba. ƙarshe ya tura mata sako mai dauke da faɗin."ina kofar gidanku Rumaisa ba zan tafi ba koda zan kwana anan Dan Allah ki fito naga fuskarki koda so ɗaya ne koda daga nesa ne ki bani wannan damar. Lokacin da ya turo mata sakon tana kwance a Tsakiyar gadonta tana kallon wani American film acikin laptop ɗinta dakyar ta danne zuciyarta da duk wani abu da take ji akan AB ɗin kafin ta samu kwarin gwiwar kin daga wayarsa har na tsayin kwanaki biyu. Ganin sako yasa ta dauki wayar ta tsayar da idanunta tana ta juya sakon aranta tasan halinsa baya magana biyu da gaske zai iya kwana acikin mota har lokacin da za ta fito tana sonsa tana tsoron duk wani abu da zai taɓa lafiyarsa. ta san idan wani abu ya samesa ba zata taɓa yafewa kanta ba. Tafi minti goma tana shawara da zuciyarta akan taje ko kar taje ƙarshe dai ta mike tsaye riga da wando ne ajikinta wanda wando three quarter ne iyakarsa daidai gwiwarta doguwar bakar riga ta ɗora gamida yin rolling kanta da veill ɗin rigar ta saka flat shoe ,Ammi bata a parlor hakan yasa ta nufi kofa har zuwa wurin maigadi wanda ganinta yasa ya mike da sauri yana gaisheta bata damu da gaisuwar da yake mata ba ta nufi ƙaramar kofa ta buɗe, ganin motarsa kurum yaso ya tsayar da bugun zuciyarta tun kafin ta gansa jin take tamkar ta juya ta koma haushin kanta take ji meyesa zuciyarta keda rauni akan soyayyar Abba Bashir?"meyesa bata da juriya ne ko kaɗan hangota ya yi ta cikin madubin motar tasa ,da sauri ya buɗe marfin motar yana kallonta daga nesa ko kaɗan bai yi mamakin zata zo ba shiya ƙarasa har zuwa inda take da takunsu da Rumaisa ke ji har can kasan zuciyarta tsayawa ya yi agabanta hannayensa zube cikin kaftan ɗin dake jikinsa."bakya cin abinci ko habibty?"
Ya faɗa murya can kasa bai damu da rashin amsawarta ba ya sake faɗin."kin rame sosai.
Runtse idonta ta yi tana jin kalamansa na kara tafasa mata zuciya, fuska a haɗe murya a shaƙe take faɗin."mu karasa cikin gida da haka ta juya ta koma cikin gidansu yana biye da ita a bayanta har aransa yaji daɗin ganinta damuwar da yake ji ta gefenta yaji tana rage masa a hanakali, har cikin parlor da suke zama duk lokacin da yazo gidan ta jasa, sai da ta tabbatar ya zauna ta juya ta koma cikin gida da ido kurum yake bin ta yana jin wata mahaukaciyar soyayyarta na lulluɓe ruhi da duka gangar jikinsa sai yanzu yake ji idan bai auri Rumaisa ba yasan ba zai taɓa samun natsuwa ba. Jin kayrar wayarsa yasa ya fito daga ita cikin aljihun wandonsa yana bin sunan dake yawo acikin screen ɗin wayar da kallo...


#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo






Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/22/2023, 11:31 AM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU




*AREWABOOK*:Jeedah3256




Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye


035.


Sunan Sadiya da yaga ni yasa shi taɓe baki ya maida wayar cikin aljihunsa ba wai ba zai dauki kiranta bane kawai dai bayaso ya sake yi abinda zai ɓatawa Rumaisa rai, shiyasa ya bari sai yabar gidan ya kira ta. Mai aikin su Rumaisa ce ta shigo ta ajiye wa AB drinks da ruwa mai sanyi kana ta gaida shi ya amsa batare da ya kalle ta ba. Bata daɗe da fita ba sai ga Rumaisa ta shigo ta sauya kayan jikinta zuwa plain material gown pink in colour jikinta na fidda ƙamshin turarenta mai sanyayya zuciya, bata yi makeup ba amma ta shafa powder sai ɗan man lebe da ta shafa wanda ya ƙara haskaka mata laɓɓanta. Bata ɗaura ɗan ƙwali ba sai ta rolling da ƙaramin veil da ya yi matching da rigar jikinta. Kyakkyawar ajiyar zuciya AB ya sauke ta iso ta zauna kusa da kujarar dake facing ɗinsa cikin sanyi murya ta furta "Habibi ba ka sha ruwa ba ko na zuba maka da kaina ne?"
Murmushin farin ciki ne ya subuce masa ya tsare ta da rikitattun idanunsa da ke saurin narkar da da zuciyar 'ya mace "thanks love ni wannan kwalliya ma da aka yi min ta wadatar dani ya kamata na biya wannan kwalliya da tukuici mafi tsada.
Wani irin daɗi ne ya yiwa Rumaisa dirar makiya ta wani langwaɓar da kai tana ji masifaffiyar soyayyarsa tana ƙara mamaye mata zuciya "Ka ji da neman maganarka Habibi domin nasan ba za ka iya bayarda kalar tukuici da nake so ba.
"Habibty akwai wani tukuici sama da kyautar zuciyata ga baki ɗaya da na yi miki. Rumaisa
I love you so much, Rumaisa, you are the only woman in my heart. I can't live without you soyayyarki halitta ce acikin jinina idan har na rasaki bansan ya rayuwarta za ta kasance ba. Dan Allah ki janye zance rantsuwa da Alqur'ani da kike so na yi saboda babu wata 'ya mace a zuciyata sama dake.
Duk wata kalma dake fitowa daga bakinsa farin ciki take sanya Rumaisa ta adana su acan ƙasan zuciyata tare da killace su ita kanta tasan ba za ta iya rayuwa idan babu Ab acikin duniyar ta soyayya da take masa ta zarce wacce shi ɗin yake mata kawai dai shi mutum ne da bashi da juriya ta wannan fannin. Sun dauki lokaci a tare duk wani fushi da take dashi sai da ya tabbatar da ta goge shi a zuciyarta kafin ya yi mata sallama ya nufo gida. Wanka ya yi ya shirya cikin three quarter blue in colour tare da armless shirt white colour ya fito zuwa parlor sai lokacin ya tuna da kira da Sadiya ta yi masa ya dauki wayarsa ya yi dialling number ɗinta, ringing ɗaya zuwa biyu ta yi picking cikin dassashiyar murya ta furta "Yaya Abba zan mutu wallahi mutuwa zan yi dan Allah karka bari sanadin ciwon sonka na rasa rayuwata. Wallahi-tallahi idan ka aure Aydah ba zan iya cigaba da numfashi ba mutuwa zan yi domin ba zan iya jure ganinka kana amsa sunan mijin Aydah ba. Ka taimake ni yaya Abba ka ceto rayuwar ƙanwarka daga hallaka.
Dafe forhead ɗinsa ya yi wani irin takaici da bakin ciki ya mamaye zuciya da sassan jikinsa ya rasa ina zai saka kansa ya sami sassauci ƙunci, baƙin ciki, damuwa sune ababe da a yanzu suka zama abokan rayuwarsa. Duk wanda ya kalle shi zai san baya ciki hayyacinsa.
Sautin kukan Sadiya ne ya dawo dashi natsuwarsa ya ja numfashi yafi a kirga "Daman nasani ba za ka iya yi komai ba saboda ka tsaneni amma inaso ka sani yanzu haka akwai kwalba maganin kwari a hannuna muddin ba ka fasa auren Aydah ba, zan buɗe ne na tuttulawa cikina na gwammace na mutu na bar duniya da naga ranar daurin aurenka da ƙanwata.
Da wani kalan sabon tashin hankali ya mike tsaye tun daga yarinta yasan hali Sadiya da kafiya da daurin kai duk abinda ta faɗa za ta iya aikatawa, duk cikin ƙannansa ita ce mai zafin kai. Cikin rawar murya ya ce "Sadiya kina ina ne?"
Cikin shasshekar kuka ta bashi amsa da faɗin "Babu ruwanka da inda nake kawai ka zuba ido daga yanzu zuwa kowanne lokaci labarin mutuwata zai riske ka.
"Sadiya please don't do this to me ya kuke so na yi da rayuwa ta ne huh?"
AB ya faɗa kamar zai sa kuka.
"Yaya Abba ina sonka wallahi ina bala'in masifar sonka tun da ba zan sami ka ba banga amfani rayuwata ba.
"Sadiya ina gani kamar bakya cikin natsuwa da hankalinki kawai ki faɗamin inda kike yanzu nan zan zo na same ki mu magance matsala dake tsakanin mu.
"Idan na faɗa maka za ka fasa auren Aydah ne?"
"Duk abinda kike so shi zan yi miki Sadiya kawai ki faɗamin.
Ya ƙarashe magana a tsawace.
"Ina cikin balcony.
Sadiya ta faɗa cikin muryar kuka.
Da sauri AB ya fice direct ya wuce balcony tun kafin ya karasa cikin balcony ɗin ya hango Sadiya kwance akan grass carpet ɗin da ke lulluɓe a kasan balcony ɗin, da sauri ya isa kusa da ita ya durƙusa daidai fuskarta.
"Sadiya da ikon aurena a hannuna yake da daga ke har Aydah da ba ku shigo cikin rayuwata ba, da wannan kalmar ta aure ba za ta taɓa shiga a tsakanina daku. Sadiya da kashe kai shine magani dake warware matsala da ni ne ya dace na kashe kaina ba ke ba.
AB ya yi magana cikin raunin murya Sadiya ta tashi zaune idanunta sun yi jajir kaman an zuba mata barkono acikinsu, Ab ya yi mata kur da idanunsa cikin abinda bai fi 20 seconds ba ya zare idanuwa cikin kaɗuwa ya ce "me kika sha ne Sadiya?"
Sadiya ta yi saurin kauda fuskarta tana mai goge zafafan hawaye dake ambaliya akan kumatunta.
"Ba za ki buɗe baki ki yi min magana ba Sadiya?"
Sadiya ta tashi zaune AB yaga bottle ɗin magani kwari riƙe da tafin hannunta, ya yi sauri riƙo hannunta suka shiga kokawa da kyar ya yi nasarar cire bottle ɗin daga hannunta.
"Ka bani abina shine kadai hanyar da ya rage min da zan bi na huta da azabtar da ruhi da gangar jikina da soyayyarka ke yi.
Ba tare da ya sake magana ba ya nufi hanyar fita daga balcony, cikin ɗaga murya Sadiya ta furta "Kaine bugun numfashina yaya Abba ba zan iya rayuwa daidai da na second ɗaya ne idan babu kai, ka ji tausai na yaya Abba ka aureni idan ka aure Aydah na rantse da Allah sai na kashe kaina.
Sadiya ta ƙarasa magana tana wani irin gunji kuka mai matukar taɓa zuciya.
Cak ya tsaya ya juyo gami da kallonta sai kuma ya kada kai ya fice, yana dab da isa entrance ɗin shiga bangaren sa ya tsikayi muryar Aydah tana kwalla masa kira "yayanmu!
Sautin muryarta kadai da ya ji sai da gabansa ya yi wani irin bugawa tamkar wanda ke ji tsoron ta ya juya idanunsa suka sauka akanta.taji dawowarsa da mota tana tsaye a kitchen ta window ta hango dawowarsa ko yanzu ta faki idon Mami ne kawai ta fito da nufi shiga part dinsa sai ta hango shi shine ta ƙwalla masa wannan kiran, da ɗan gudunta ta iso wurinsa "yaya Abba tun safe da ka sauke school Bamu kara haɗu ba koda na dawo school har zuwa 5 na dauka ma zaka dawo kayi lunch har magarib."
Ta karawa maganar tana kallonsa.na dawo baby Aydah kara fita dai nayi."
Duk maganar da suke yi bai bari suka haɗa idanuwa ba sosai yake ji kunya kallonta musamman idan ya tuna da gobe warhaka ta zama matarsa. Ya tsikayi muryarta a dodon kunnensa tana faɗin "My heart tells me that there is something wrong with you. tell me Yaya Abba menene shi?"
Dole ba don zuciyarsa taso ba ya haɗa ido da ita yanda ta tsare shi da kallo mai cike da tuhuma, yasa shi ɗaure fuska ya wani haɗe rai "Babu abinda yake damuna baby ki shiga gida gashi nan an fara kiran sallar ishai karki sa na rasa jam'i.
Yana ƙarasa magana ya yi sauri shigewa bangarensa ta bishi da kallo har sai da ya ɓacewa ganinta sannan ta juya ta shiga cikin gidan, ashe duk abinda yake faruwa a tsakaninsu Sadiya tana laɓe jikin pillar tana kallonsu tana gani Aydah ta shiga gida, ita ma ta shiga amma sai ta wuce ɗakin Mami tana wani irin gunji kuka ta tura ƙofa, Mami tana zaune a gefen gado tana waya da Hajiya Zeena Sadiya ta shigo tana zuwa ta faɗa jikin Mami ta kara rushewa da matsanancin kuka "Mami mutuwa zan yi zuciyata za ta buga ki taimake ni ki yi gaggawar yi wani abu wanda zai dakatar da auren yaya Abba da Aydah wallahi Mami yaya Abba shine farin cikin rayuwata, ba zan iya jure rashinsa ba.
"Innalillahi wa'inna illahim raji'um! Kin ji ko Hajiya Zeena? Kin ji abinda nake kan faɗa miki sai gashi kin ji da kunnenki ko?"
Ajiyar zuciya Hajiya Zeena ta sauke ta cikin wayar yayin da zuciyarta ta cika da wani irin farin ciki, ta ƙudurta aranta tana gama waya da Mami za ta kira mijinta Alhaji Sanusi ƙanin Daddy ta fesa masa wannan daddaɗan labari burinsa na dab da cika.
"Na ji Hajiya Mariya amma tun farko laifinki ne da kika ɓoye min irin wannan murɗaɗɗen al'amari, koda ba ki sanar dani a matsayina na ƙawarki ba, ai kya faɗamin a matsayin matar ƙanin mijinki. Da tuni mun shawo kan wannan matsala da bata girmama har haka ba.
"Ki yi haƙuri Zeena ni kaina ban zaci al'amarin zai yi ƙamari har haka ba.
"To dama ɗan hakki da ka raina shi ke tsone maka ido gashi nan wankin hula yana neman ya kaiki dare.
"Wallahi haka ne Zeena karki so kika yanda gidana ya dawo tamkar gidan makoki, ga baki ɗaya farin cikin iyalina ya rikiɗe zuwa bakin ciki.
Sadiya dake ta faman rusar kuka Mami ta dakawa rikitacciyar tsawa "ke dallah rufe min baki na yi waya duk ba ke ce kika janyo ba, sanda aka aura miki shi a bagassss! Da kin kwatar da hankalinki da yanzu kina gidansa hankalinki kwance. Tsabar daƙiƙancin ki, kika daba masa wuƙa koma waye dole ya tsane ki. Tashi daga jikina na samu nayi magana cikin natsuwa.
Dole Sadiya ta tashi daga jikin Mami ta kwanta akan gado tana cigaba da kukanta, yayin da Mami ta cigaba da magana da Hajiya Zeena.
"Ki kwantar da hankalinki Mariya koda Alh Bashir ya yi nasarar aurawa Abba Aydah za mu shiga mu fita mu hana masa kwanciyar hankali har sai ya sakar miki 'ya. Ai ɗaura aure ba shi bane zaman aure ba, ki sa aranki muddin kina tare dani matsalolin ki sun zo ƙarshe.
Hajiya Zeena ta cigaba da kwantar wa da Mami hankali tare da ɗora ta akan mugaye shawarwari kafin suka yi sallama da zimmar gobe Hajiya Zeena za ta zo su ƙarasa magana. Mami ta koma kan Sadiya ta dinga rarrashinta da daddaɗan maganganu.
*MASARAUTAR KUDU*
Alh Aliyu ne zaune a dakinsa yana kallon hoton da ya zama masa jini da ɓargon jikinsa ya yi nisa sosai har bai ji ƙarar buɗe ƙofa da Hajiya Safiya ta yi ba har ta iso dab dashi bai sani ba idanunta suka sauka akan hoton kyakkyawar baturiya, wani irin bugawa ƙirjinta ya yi babu shiri ta dafe ƙirjin nata da duka hannayenta, cikin sarƙewa murya ta furta "Abbu wacece wannan da kake kallon hotonta miye alaƙar ka da ita?"
Firgigit ya yi

26 / 80