Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   68 / 80

201K to 204K   out of 237.2K words

Aydah take ta ji a rufe ta kwakwasa haɗe da kiran sunan Aydah "Aydah idan kina ji na ki taso ki buɗe ƙofa Sadiya ta tafi.
Adaddafe Aydah ta taso ta buɗe ƙofar wuyanta jin sa take yi tamkar an ɗaɗɗaure mata shi ga maƙoshinta sai raɗaɗi yake mata.
Karo na farko a rayuwar Rumaisah da ta ji tausayin Aydah ya kamata da sauri ta kama kafaɗarta suka sakko ƙasa Huwaila tana gani halin da Aydah take ciki ta kara rudewa gaba ɗaya fuskar Aydah ta kumbure Rumaisah ta zaunar da ita akan kujera ta ce Huwaila ta je ɗakinta ta dauko mata wayarta, da sauri Huwaila ta je ta dauko ta kawo mata ta kira Ab ta faɗa masa abun da ya faru "Da bacci nake yi Habibi sai da ka dawo ka tarar da gawar Aydah dan kuwa sheƙe mata wuya ta yi bayan ta yi mata ɗankaran duka, nima ba ka ga yadda ta yi min raunuka a jikina ba. Ya dai kamata ka ɗauki mataki akan Sadiya wannan abu da take yi mana ya yi yawa duk sanda ta sha kayan mayenta ta zo ta sauke haukarta akan iyalinka.
Tun sanda Rumaisah ta fara magana zuciyar AB ke bugawa bai ce mata komai ba ya kashe wayar ransa ɓace ya kalli Abdulkarim dake zaune kusa dashi a mota daman suna kan hanyar zuwa gidan su Abdul ɗin zai sauke shi, shi kuma ya nufo gida kiran Rumaisah ya shigo wayarsa ya kwashe labari abun da ya faru ya fadawa Abdulkarim.
"Gaskiya a wannan karo nima ina goyon bayanka da ka ɗauki mataki akan Sadiya hauka take yi da za ta dinga zuwa har cikin gidanka tana dukan matanka, kanta aka fara shaye-shaye ne ko me?"
Sai da AB ya yi ƙwafa kafin ya ce "Ka barni da ita wallahi sai na nunawa Sadiya ita ɗin ƙaramar 'yar iska ce sai na yi mata abun da ko sunana ta ji sai gabanta ya faɗi ƙarya iskanci take yi.
Ya ƙarashe magana ransa na ƙuna.
"Da dai yafi gara ka nuna mata kuskurenta.
Ak ya faɗa daidai suna isowa ƙofar gidansu suka yi sallama da ab kaitsaye Ab gida ya nufo yadda yaga fuskar matansa duk zane faratan Sadiya ne ya yi bala'in harzuƙa shi musamman fuskar Aydah da ta kumbure sutum! Dukkansu sai ya kwashe su zuwa asibiti aka duba su tare da rubuto masu magani.
Sai bayan ishaa Ab ya sami zuwa gidan Mami, koda ya shiga babban parlon Sadiya da Siyama suna zaune suna kallon India series. Ya yi sallama fuskarsa a haɗe sallamarsa kaɗai da Sadiya ta ji sai da hanji cikinta ya hartsune, ta ji gudawa tana so kamata.
"Barka da dare Yayanmu.
Siyama ta faɗa da murmushi akan fuskarta.
Yadda ran AB yake a ɓace baya tunani zai iya amsawa Siyama, kan Sadiya ya yi yana zuwa ya ɓalla mata mari, har sai da ta fado daga kan kujera, daidai Mami tana sakkowa daga bene "Kai Abba kanka ɗaya kuwa me ta yi ma da za ka mare ta?"
Mami ta faɗa a fusace Ab ya ɗaga kai ya kalleta kamin ya dawo da ganinsa kan Sadiya ya kama hannunta ya ja ta da ƙarfi dole ta miƙe tsaye ya nufi ƙofar fita janye da ita cikin sauri Mami take tattaka mattakalar bene tana faɗin "Kai don ubanka ina za ka kai min yarinya Abba dawo min da 'yata na rantse idan wani abu ya same ta sai na yi shari'a da kai shegen yaro watsatse.
A daidai ƙofar fita Ab ya tsaya a juya yana kallon Mami da fusatattun idanuwansa "Ga watsatsiya nan kin haifa Mami wannan da kike gani wata rana sai ta dauko miki bala'in da masifan da sai kin yi Allah wadarai haifar ta da kika yi. Daga ke har ita a sannu za ku girbi abubuwan da kuka shuka.
AB yana gama faɗar haka ya juya ya buga ƙofar da ƙarfi yana cigaba da jan Sadiya kamar tinkiya, maganganu da AB ya gayawa Mami yasa ta yi mutuwar tsaye ta kasa bin sa, Siyama ta tashi ta bar cikin parlor ta wuce ɗakinta. Ta bar Mami tsaye cikin jimami.
Da ƙarfi AB ya jifa Sadiya cikin mota ya shiga ya ja Balmo maigadi ya buɗe masa gate, yadda yake sharara gudu akan titi kaɗai ya isa ya jefa wa Sadiya tsoro, amman ita ko a jikinta sai ma kwantawa da ta yi jikin seat hakan da ta yi ya kara linkawa Ab ɓacin ransa ji yake yi zai iya kakkarya kasusuwan jikinta. Kaitsaye office ɗinsa ya nufa ya yi parking ya fito tare da fizgota ta fito kanta daga ita sai riga da wando na bacci kanta dauke da hula bata da takalmi a haka ya ja ta zuwa office ɗinsa securities ne kaɗai a cikin company.
Yana buɗe kofar office ɗin ya tura ta da ƙarfi har sai da ta faɗi ƙasa ya maida kofar ya rufe, Sadiya ta miƙe tsaye tana kallonsa yana warware belt ɗin jikinsa ta sakar masa murmushi nan da nan ya ƙara harzuƙa ya zare belt ɗin a mugun fusace ya yi kanta ya dinga zuba mata duk duka da yake mata tsaye kawai take ta runtse idanuwanta gam! Da Ab ya gaji da dukanta da belt ya kama wuyanta kaita jikin bango ya shaƙe ta sosai tsabar taurin kai irin na Sadiya ko gizau bata yi ba sai ma ta kalle cikin idanunsa da shaƙaƙƙiyar muryarta ta ce "Zan yi farin ciki da zan mutu a hannun masoyina.
AB ya ƙara hasalewa da jin furuncinta ya shiga wanke mata fuska da maruka duka sosai ya yi mata bana wasa ba duk ya farfasa mata jiki fuskarta ta kumbura saboda mari bakinta da hancinta yana zubda jini, amman ita ko a jikinta, sai ma maganganu banza da take faɗa masa.
"Ka sani Yayanmu wannan duka da ka yi min babu abun da ya rage na daga dimbin son da nake maka asalima ƙara min sonka ya yi yanzu na daura damarar yaƙi da shegun matanka sai na yi ajalinsu dukkan su ba wacce zan bari a raye.
Wani irin zuba mata ido Ab ya yi anya kuwa Sadiya bata samu matsala a ƙwaƙwalwarta ba. Ya dubi irin mugun dukan da ya yi mata amman bakinta bai mutu ba a duniya nan me zai yi mata da zai sa ta tsane shi ta fita daga rayuwarsa dukka. Ya tuna da wuƙa da ya dauko daga gida wacce ya yi kudirin ya tsorata ta da ita, a fusace ya zaro ta daga aljihun wandonsa ya fizgo ta, ta miƙe tsaye ya ɗora wuƙar a wuyanta cikin zare idanuwa cikin kakkausar murya ya ce "wannan shi ne kashedi na, na ƙarshe dake idan har kika kuskura hannunki ya sake sauka a jikin matana sai na shayar dake zallar mamaki. Kin ga wannan wuƙar da ita zan daddatsa naman jikinki na yi gunduwa-gunduwa da sassan jikinki ina tabbatar miki ko sallah ba za ki samu ba. Ba dai taƙamar ki taurin kai ba to nine Babanki a taurin kai.
Jin abun da ya faɗa yasa Sadiya ta sheƙe da dariya tana kallonsa tana dariya abinta kai da gani wannan dariya da take yi kasan babu lafiya Ab ya rasa yadda zai yi da ita wani tunani ne ya fado masa shi ne kadai hanyar da zai bi ya kawo ƙarshen iskancin Sadiya. A fusace ya sake kama hannunta ya ja ta suka fito daga office ɗin suna tafe Sadiya take faɗin "Wai kana nufi Yayanmu har ka gama hora ni kenan? Dan Allah mu koma ciki ka cigaba da dukana har sai garin Allah ya waye hucin kaɗai yana haifar min da natsuwa a duk sanda hannunka ya sauka a jikina da sunan duka sai na ji wani irin daɗi yana lulluɓe ni. Ina sonka Yayanmu wallahi ina bala'in sonka Dan girman Allah ka saki shegun matanka ka aure ni ni kaɗai na isheka rayuwa.
Tsabar takaicinta da ya gama cika Ab bai sake kula ta ba har suka iso ƙofar gidan Mami ya buɗe kofar mota ya fito ya zagaya wurinta ya ɓalle ƙofa ya daka mata tsawa "fito!
Sadiya ta fito tana cigaba da tsoki burutsunta wanda Ab ya ma daina fahimtar me take cewa ya ja motarsa ya yi gaba Sadiya tana shiga main parlor ta tarar da Mami ta kai gwaro ta kai mari.


#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.
[2/1, 12:51 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels


092.


Shiru Hajiya Zeenah tayi tana kallon Mami,dake mata bayani with shock har lokacin kuma taki tace komai.
"Zeenatu kina jin ina maki bayani bakice komai ba.
Mami ta faɗa cikin rawar murya,Hajiya Zeenah ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin."to me kikeso nace Hajiya mariya bakya jin magana bakya bin shawara duk yadda mutum ya kawo maki shawara bakya dauka sai kinga dama. Ya kikeso nayi mun fi wata ɗaya da zuwa wurin mutumin nan da sunan zaki haɗa kudi ayi maki aiki shiru akeji, na tabbata bazaki rasa miliyan guda ba sai idan baki da dama bayarwa ba.
"Wallahi-tallahi Zeenah tun lokacin na faɗa maki kudin dake cikin account ɗina bai kai miliyan ɗaya ba.
"To wai ba kina da kaddarori ba? Mariya ki daga sarkarki ta zinari ki saida ayi aikin nan kema wallahi wata rana kin fiye son abun duniya.
Shiru Mami tayi kafin ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin.
"In sha Allahu yanzun nan zan je na daga ɗaya daga cikin sarqoqina na sayar idan ma bamu samu tafiya yau ba sai gobe ki yi sammako mu tafi wallahi jiya banyi barci ba akan dukan mutuwar da Abba ya yiwa Sadiya ya tsaya min arai kuma babu damar na yiwa mahaifinsu bayani zai fara tambayar ina Sadiya ta haɗu da Abba laifi me tai masa kinsan dai halinsa da tambayar kwakwafi.
Dole sai ya ji dalilin da yasa yayi mata wannan ta'asar ke yanzu ta kai ta kawo fa ko amsa gaisuwar Sadiya baya yi kiri-kiri ya cire hannunsa akan lamarinta duk akan shegen yaro nan.
Alhaji Sanusi dake labe tun ɗazu yana jinsu ya saki wani murmushi kafin ya turo kofar ɗakin batareda an basa izinin shigowa ba,daga matarsa har Mami kallonsa suke ya zauna kan Soofa yana murmushi mami ta gaishesa da respect ya amsa yana tambayarta gida da yara ta amsa masa da duk suna lafiya. Sai kuma yayi fuskar tausayi yana kallon mami "ai wallahi Hajiya mariya ina gayama maki in har yaron nan bai bar cikin rayuwar yaya na har abada ba ba za ki taɓa farin ciki ke da alhalin ki ba. Baki ga nima yanzu komai na yayan ba sani nayi ba ai idan kin lura ko gidanku na rage zuwa.
Mami ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin."hakane Alhaji Sanusi ka kam rage zuwa,wannan karon ko na dauki alwashin idan komai da na tara zai kare sai Abba Bashir yabar rayuwar mu na har abada.
"Hakan shi ne daidai kuma babbar mafita agareki, ba za ki raina kanki ba sai yaya ya faɗi ya mutu duk dukiyarsa tana hannun Abba ga kuma Aydah ya aure shi kadai zai mallake komai ke da yaranki za ku koma 'yan kallo.
"In shaa Allahu hakan ba za ta taɓa faruwa ba inda karfina ya ƙare.
Har mota Alhaji Sanusi da matarsa Hajiya Zeenah,suka raka Mami suna kara cusa mata kiyayyar Abba Bashir muraran. Koda Mami ta koma gida ta samu kanwarta Safeena ta je daman sunyi waya da safe ta faɗawa Safeena idan tana da lokaci tazo zasu yi magana mai muhimmanci,lokaci ɗaya Mami ta saki fuska ta karasa cikin parlor tana gaisawa da kanwarta, "hope baki dade da zuwa ba.?
"A'ah! banji ma ba kam dan na kira wayarki a kashe.
"A gida ma nabar wayar tunda nasan ba dadewa zan yi ba na saka caji.l sai kawai na kashe kar ayita kira bana nan.
Da haka Mami taja kanwarta suka wuce cikin master bedroom ɗinta,bayan sun zauna Safeena ta kalli yayarta dauke da damuwa a fuskarta take faɗin."Na shiga ɗakin Sadiya ita kadai ce a gida mai aiki ta faɗa min Siyama ta tafi school. Yaya anya Sadiya akwai zuciya a kirjinta kuwa kan wani ɗa namiji take kokarin ta lalata rayuwarta a banza a wofi menene ribarta ?"ita ko Aydah akace ta mutu ace Abba ,ya aureta zai yarda ya aureta, ni na dauka tabar halin nata ashe sai abun da ya cigaba
harda ke dake daure mata ki bani ita na sati ɗaya na gyara mata zama dan ni kam ba zan dauki wannan Kananun Iskanci na sadiya ba. Ita ko karatun taki tsayawa tayi samarin ma ta daina kulasu gaba baki ɗaya ta lalata rayuwarta.
Lokaci ɗaya Mami ta ɗan haɗe fuska dan ita bata kaunar taji ana aibanta Sadiya agabanta nan take za taji ranta ya ɓaci "kin manta shi wanda kike zance akansa duk shi ya sakata cikin wannan ƙaddara.
"Amman yaya har da son ran Sadiya akan ɗa namiji marar tabbas za ta dinga shan kayan maye akan me sai kace....
"Kin ga dan Allah muyi abun da ya kawoki malama karki batamin rai.
Shiru Safeena tayi tana kallon yayar tata kawai.
Fuskar Mami a tanke ta ce "Daman iyayen yaron dake neman auren
Siyama suke so a saka masu rana
Jibi zasu zo da kayan lefe da kuɗin saka rana. Ni bama wannan ba babban damuwa na shirun da Daddynsu yayi ya sakawa Sadiya ido ina tsoron ya je ya samo mata wanda bata so tunda ita taurin kaine da ita taki tsayawa ta kwantar da hankalinta tama kula samarin dake nemanta.
Ke kin san da an sakawa siyama,rana babu makawa har da na Sadiya. Aunty Safeena da ta gama sauran Mami ta sauke numfashi tana kallon Mami kafin tace "to ke yanzu menene mafita?"da gaske yaya ya kamata ace Sadiya na gidan aurenta tuntuni Amman da yake taurin kaine da ita sai gashi wanda taso kashewa ta dawo kuma Allah ya jarbceta da mugun sonsa.
"Ni ina da wata shawara.
Da sauri Aunty Safeena tace "wace irin shawara kenan?
"Me zai hana mu haɗa Sadiya da Jamal aure?" tunda Aydah Allah bai yi zai sameta ba. Kin ga asirin mu a rufe daga Jamal har Sadiyar babu wanda ba zai ƙi bin umarninmu ba.
baki buɗe Aunty Safeena,ke kallonta tamkar bata fahimci me Mami ke faɗa ba.
"Ban fahimci zancenki ba yaya mariya kina nufin a haɗa Jamal da Sadiya aure?
"ehhhh haka nake nufi Safeena,ko bai yi maki bane.?"naga duk kin birkice ne lokaci ɗaya,wani ja'irin murmushi kurum Aunty Safeena tayi tana faɗin."kina ganin wannan auren zai yiwu tsakanin Jamal da Sadiya shi zuciya ita zuciya suna ganin ai sha'anin juna ne ya za'ayi suyi aure tsakaninsu kuma ma Jamal bai gama makaranta ba akwai shekara ɗaya a gaba kin manta ne?"kuma kin san mahaifinsa ba zai yarda yayi masa aure yanzu ba.
Tun sanda Aunty Safeena ta buɗe baki tana magana Mami,ke kallonta har ta kai karshe.
"Aure yana hana karatu ne Safeena?"ina jin ko anyi auren zai ci gaba da karatunsa ni banga wani abun daga hankali ba.
"To yaya Allah yasa mahaifin Jamal da shi kansa Jamal ɗin su amince.
"Jamal nasan bai da matsala mahaifinsa ma na tabbata idan yaji Sadiya ce ba zai ƙi amincewa ba sai dai kawai idan akwai wani nufi a zuciyarki Safeena.!
Da sauri Aunty Safeena ta girgiza kai tana kallon Mami take faɗin "Ni babu komai a zuciya ta duk yadda muka yi zan kiraki.
Da haka Aunty Safeena ,ta dauki jakkarta ta yiwa Mami,sallama Mami ta bin kanwartata da kallo kurum
Har ta fice daga dakin. Sai da Aunty Safeena tabar gidan ta saki wani dariyar rainin hankali lallai yayarta ta ta samu tabin hankali da alama, idan ba tabin hankali ba taya zata haɗa Jamal da Sadiya?"ae Sadiya ba sa'ar aurensa bace yarinyar dake shaye-shaye take da tabin ƙwaƙwalwa haka kawai zata wani zo da zancen da hankali ba zai dauka ba. Tana komawa gida ta dauki waya ta kira Jamal,cikin basa umarni take faɗin duk inda yake yazo yanzu ya sameta jin yanayin muryar mahaifiyarsa kamar ba daidai ba yace "lafiya mum?"a fusace Aunty Safeena ke faɗin."Dan Allah ka zauna karka zo tun da har sai na faɗa maka dalilin kiran ka.
Ta faɗa so pissed up a muryarta tana sauke wayar Jamal bai fi minti talatin ba ya ƙaraso gidan nasu duk hankalinsa a tashe ya zata wani mummunan abu ya samu mum,har ɗaki ya sameta ya zauna yana kallonta ita ma zaunawa tayi fuska babu walwala take faɗin "kana jina Jamal.?
"Eh! Ina jinki mum.
"sauran kwana nawa hutun naku ya ƙare?"
"Akwai kusan sati biyu fa lafiya wani abu ya faru?"
"Daman so nake yanzu ka dauki waya ka fara booking ɗin flight ka tattara ka koma makaranta ka karasa hutunka acan.
Da mamaki yake kallon mum, ɗin tasa kamin ya furta "mum wani abune ya faru ?" Ai na faɗa maki fa akwai sauran sati biyu a gaba.
A mugun fusace Aunty Safeena ta katsesa tana wani zare masa ido tana faɗin "kawai kayi abun da nace.
shi dai kallon mum ɗin tasa kawai yake yi yana mamakin ta.
"To mum,me zan faɗawa Abba kuma.?"kai kasan yadda za kayi dashi. Magana ta biyu ko bayan ka tafi yaya mariya ta kira wayarka tayi ma magana kana da sha'awar auren Sadiya kace kana da wacce kakeso acan familyn babanka.
Da sauri Jamal ya kalli mum da mamaki yake faɗin."mum naji kamar kin ce Sadiya, faɗamaku aka yi dama akwai wani abu tsakani na da ita ne ko me?"
Nan mahaifiyarsa tayi masa bayanin kudurin Mami wani dariya Jamal ya fashe dashi yana faɗin."lallai ni za'a haɗa da yar shaye-shaye da kurciyarta.?"ko na rasa matar aure Sadiya ba sa'ar aurena bace bata cikin zubin kalar matan da nakeso ,ko ita Aydah na haƙura da ita ina da kishi ba zan iya auren ƙaramar bazawara ba ragin wani ba.
murmushi mum tayi daman tasan halin Jamal ba yadda za a yi ya yi na'am da wannan zancen na Mami. "Banda dai son kai irin na yayarta ina Jamal ina Sadiya.
Sai da yamma Mami,ta dauki ɗaya daga cikin sarqoqinta na zinari ta tafi shago aka auna aka bata kusan dubu dari biyar,ta account ma aka tura mata kuɗin gobe idan zasu je wurin Malam sai ta ciro su je dasu. Bayan sallah ishaai sun kammala cin abincin dare Daddy

68 / 80