Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   14 / 80

39K to 42K   out of 237.2K words

ruwan lipton ɗinta da Sadiyar ta haɗa mata, Sadiya ta dawo gabansa tana ƙoƙarin ɗaukar cup ta haɗa masa tea ya yi saurin daukar wani ya shiga haɗawa, tuni idanu Sadiya suka cika da hawaye juyawa kawai tayi tabar cikin dinning area ɗin. Mintuna goma sha biyar kacal ya yi cikin dining area ɗin ya yiwa Mami sallama ta bisa da addu'ar Allah ya tsare hanya. Mami tana tsaye da 'yar aiki tana yi mata list ɗin abubuwan da zata siyo mata a kasuwa tana gama rubuta mata tabar kitchen ɗin tana ƙara jaddada mata da ta yi sauri rana ta yi sosai. Kai tsaye ɗakin Sadiya ta nufa kwance ta sameta kan doguwar sofa ta yi ruf da ciki ganin mami a ɗakinta yasa ta yi saurin goge hawayen da har lokacin basu daina zuba mata ba ta tashi zaune haka sai kawai ta tsince kanta da kasa kallon mami. "meke damunki?"kukan me kika zauna kina yiwa mutane haka?" Wasu hawaye suka kara zubowa akan kumatun Sadiya.
Cikin shesshekar kuka ta shiga faɗin."Mami bakya ganin yadda yaya Abba ke avoiding ɗina acikin gidan nan yana kula kowa banda ni duk ya bi ya tsaneni shi bai san tsautsayi bane? Ko Allah ana yiwa laifi ya yafe balle mutum ɗan adam. Ban san Me yake so nayi da zai fahimci nayi kuskure ba na kuma yi nadama biye wa ruɗin zuciyata da nayi, jiya akan Aydah tayi min rashin kunya na mareta sau biyu Mami ya mareni abunda bai taɓa yi ba sakawa wani hannu a cikinmu duk girman laifin da za muyi masa iyakacinsa ya ɗauki fushi damu."
Sadiya ta ƙarasa maganar tana rufe fuskarta da tafukkan hannayenta kana ta ci-gaba da rera kukanta a hankali.
"Duk bake kika jefa kanki cikin wannan masifar ba saboda taurin kai irin naki da yanzu ba kina zaune can gidanki lafiya lau ba. Kika mannewa wannan gantalalle yaro gashi kin kashe aurenki saboda shi har kuma yanzu ya kasa fitowa ayi maganar aurenku. Shawarata na karshe dake ki daina shiga sabgar Aydah a gidan nan musamman idan kin san yayan naku yana gida.
"Mami ko ita keda laifi bamu ba baya gani rufe idonsa yake da anyi magana sai yace yarinya ce 'yar ss 2 ɗin ce?" Yarinya saboda ya daure mata shiyasa ta rainamu wallahi ko gobe ta sake yi min rashin kunya ba raga mata zan yi ba.
Mami dai tayi ƙwafa tabar mata room ɗin kawai saboda duk abinda zata ta faɗa ba fahimta za ya yi ba. Da yamma Mami ta ce 'yanmatan nata su shirya a fita shopping dasu kaman yadda ta sabar musu duk ƙarshen wata tana fita dasu shopping su siye abubuwan da suke bukata. Siyama ta kalli Mami a natse ta ce "mami dan Allah dan Annabi yau ki bar Aydah ta dauko bra ta fara sakawa nawa fa take dauka mami ko sun mata yawa sai ta saka."
Aydah ta wani zaro ido lokaci ɗaya kuma ta haɗe rai tana faɗin."Yaushe na daukar maki bra na saka yaya Siyam saboda sharri ni yaushe ma bra ɗinki zata tsaya ajikina saboda gir..... kafin ta karasa mami ta kaiwa bakin bugu da sauri Aydah ta riƙe bakinta tana jin tamkar ba bakin nata bane saboda mugun azabar da taji
"Bana hanaki yi musu rashin kunya ba?" karyama tai miki kenan? Mami ta faɗa a fusace, da sauri Aydah ta miƙe tsaye still tana riƙe da bakinta hawayen azaba na feso mata bata kara koda minti ɗaya ba a wajen tabar cikin parlorn tana fashewa da kukan tabara
Sosai Sadiya da Siyama suka ji daɗin abunda Mami tayi mata. Kowa ya fito cikin shirin sa a parlor har lokacin Aydah bata fito ba Mami ta nufi ɗakinta a kwance ta sameta tana shesshekar kuka har lokaci sai kace wacce aka kwakulewa idanuwa. Jin muryar Mami yasa ta miƙe a razane Mami na bin ta da kallo ta ce "ubanwa kika mayar sa'arki da zai tsaya jiranki?" Cikin sautin kuka Aydah ta ce."Tare da yayanmu zan je.
Ganin Mami tayo kanta a mugun fusace yasa ta saukowa daga kan bed ɗin ta ɗauki hijab ta nufi ƙofa
Ko kallon su Sadiya ba tayi ba ta nufi hanyar barin parlorn Siyama ce ta karbarwa Mami,tukin daman sun iya Driving kuma suna da motocinsu sai dai anyi wata biyu da yaya Abba,ya yi seizing ɗin keys ɗinsu kafin aurensa da Sadiya suke masa magiya ya mayar musu da key ɗin amma yaƙi. Duka kuma saboda Aydah ta faɗa masa yadda suke mata wulakanci musamman idan suka tashi fita sai wannan yace bazai dauketa ba wannan ma haka.
Shima saboda tafiya school aka basu motocin akwai ranar da suka je biki babu wanda ya dawo da Ayda acikinsu bikin na familyn Mami ne wai acewarsu ta yi masu rashin kunya shine suka saka ta shiga adaidaita shi kuma ya ji haushi ya kwace. Har magana Mami tayi masa yace zai basu amma ba yanzu ba sai ya gama hora su ta yadda next time ba za su ƙi ɗaukar Aydah ba, dama kuma shi Daddy babu ruwansa bai shiga sabgarsu duk irin hukuncin da zai yi masu bai cewa uffan. Dama Aydah bata yadda ta zauna baya wajen Mami ba frontseat ta buɗe ta shiga sai dai fuskar nan a ɗaure kuma babu wanda ya kulata acikinsu har suka tsaya cikin parking lot na kantin da suke yin shopping ɗinsu, dama Siyama na gama parking Aydah ta balle marfin motar ta nufi entrance ɗin shiga wajen babu wanda ta jira acikinsu tana zuwa ta ɗauki shopping cart tayi shigewarta cikin mall ɗin.


#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.








Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/11/2023, 10:22 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU






#Love Story
#gwagwarmaya
#Team tagwaye novels




019..


*RUBUTUN YA'N TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU.*
*TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA*


*KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?*
*INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?”*
*KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.*
Mun gwada mun gani 💯
Mun gani mun shaida 💯
Anyi mun gani 💯
MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
GYARAN MAIJEGO
MALLAKAR MIJI KO MATA
SUBULU DA SCRUB
MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
MAGANIN TSUMI
INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯


08142800199
07068558096








Aydah ta dinga jido kayan kwalliya kamar wacce za ta buɗe shagon makeup alhali ko powder bata damu da ta shafa ba, da Aydah ta yi wanka iyakanci ta shafa turare amma ko mai bata shafawa, idan ka ga tasha mai to ga bazara (hunturu) ne shima don kada skin ɗinta ya bushe amma ba don haka ba, ba abinda zai haɗa ta dashi. Siyama ce ta iso kusa da ita ta leƙa kayan dake ciki cart ɗin Siyama batasan sanda ta zare idanuwa gami da faɗin "Aydah me za ki yi da wannan tulin kayan kwalliya ke da ba makeup kike yi ba?"
Tura cart ɗin ta Aydah ta yi ta wuce Siyama ba tare da ta kula ta ba, saurin bin bayanta Siyama ta yi "Magana nake dake Aydah ki faɗamin me za ki yi da kayan kwalliya ko don salon almubabzaranci? A shawarce ki ɗauke abinda kika saba dauka a kowanne wata amma wannan powder lipstick, mascara da sauransu ba amfani da za su yi miki asalima Mami ba za ta biya kuɗi wannan tarkace da kika ɗiba ba, don tasan ba amfani za ki yi dasu ba.
"Yaya Siyam kowa yana da 'yanci zabar abinda yake so nima a wannan karo kayan kwalliya nake so.
Siyama ta fashe da dariya tasan saboda Mami ta bugewa Aydah baki shine ta sauke fushinta ta hanyar daukar abubuwan da za su mata amfani ba. "Aydah ke fa ba baƙuwa ta bace nasanki sarai fushi kike yi doke miki bakin da Mami ta yi shine kika kwashe waɗannan kayan...
"Yaya Siyam ki kyaleni dan Allah kar nayi magana kuma ace na yi miki rashin kunya.
"Shi kenan naga ta yadda Mami za ta biya kudaden wannan tarkacen.
Siyama ta ƙarashe magana tare da nuna cart ɗin da bakinta ta wuce abinta, ta bar Aydah tana gunguni kowanne su ya zo da kayayyaki da ya ɗiba da aka zo kan na Aydah da mamaki Mami take kallon ta, tai sauri kauda fuska tamkar bata lura da kallon da Mami take mata ba. Mami ta haɗiye mamakinta ta ciro ATM ɗin ta ta miƙa aka cire kuɗin. Akan hanyar su na zuwa gida Siyama da Sadiya suka dinga korafi dangane da ɓannata kuɗi da Mami ta yi akan abubuwan da Aydah ta dauka ita dai Mami ta na jin su ta yi biris dasu kaman yadda Aydah ta yi musu. Tun kafin Siyama ta iso parking lot suka hango ya Abba tsaye ya jingina bayansa ga jikin motarsa ya wani harɗe ƙafafuwansa yana amsa waya. Sadiya tana kallonsa sau ɗaya sai da ta ji matsananci faɗuwar gaba, tai sauri janye idanunta akansa ganinsu da ya yi ya saka shi ƙarashe maganar da yake yi agaggauce kowacce su ta fito tare da ɗaukar ledar shopping ɗinta. Walking majestically ya nufo su "Sannu da hanya Mami!
"Yawwa Abbati ina fatar da ka dawo ka ci abinci?
Mami ta yi magana gami da kallon cikin idanunsa, yai sauri sadda kai ƙasa yana sosa ƙeya "Na dai sha fresh milk Mami.
"Abba ka daina wasa da abinci kwana biyu nan bana gane kanka kwata-kwata ba ka son cin abinci, idan ba ka gyara ba za mu sami matsala dakai.
Mami ta ƙarashe maganar tare da nufar entrance ba tare da ta tsaya jin ban haƙuri da AB yake yi ba. Kusan su dukka uku suka gaida shi ya amsawa Siyama, Sadiya kuma kaman dai koda yaushe bai amsa ba ya yada idanuwansa akan baby face ɗin Aydah yana faɗin "Baby miƙawa Siyama kayan hannunki ki zo mu tafi yamma ta yi banaso mu yi dare sosai.
"Ya Abba bari na shiga na canza kayan jikina.
Sanin halinta da ya yi da saka fingilallu riguna yasa shi cewa "Oya ki yi sauri karki ɓata min lokaci.
Da gudunta ta wuce cikin gida Siyama kuma ta karasa rurrufe kofofin mota ta bi bayan Aydah, aka bar Abba da Sadiya kallo guda yai mata ya kauda fuska sai ma fito da wayarsa ya yi daga gaban aljihun black in colour shadda dake jikinsa wacce ta ƙara fito da farar fatarsa da kuma kyawonsa kansa ba hula sumar kansa ta kwanta lub-lub kaman ta jariri sabuwar haihuwa. Sadiya ta sauke wani lafiyayyen numfashi tai wani kalan langwaɓar da kai tare da marairaice murya tamkar za ta sa kuka ta ce
"I'm sorry, Ya Abba, please forgive me, you know I'm not happy at all the way you're treating me kowanne ɗan adam yana kuskure idan kuma ya tuba ya gane kuskurensa afuwa ake masa ba nuna masa tsana da tsangwama ba.
Cike da ƙosawa da zancenta ya ja guntun tsaki ya bi ta gefenta ya buɗe motarsa ya shiga, cikin rauni zuciya Sadiya ta bi shi da kallo tana ji wani irin kuka yana zuwa mata duk iya ƙokarinta na hanawa hawayen ta zuba hakan bai samu ba domin kuwa kuka mai ƙarfi ya subuce mata tasaki ledar hannunta kayan ciki suka tarwatse ita kuma ta zube guiwayoyinta kan interlock ta fashe da raunatatce kuka. Abba ya fesar da wata zazzafar iska daga bakinsa har yau yana mamaki irin ƙiyayyar da Sadiya ta nuna masa wacce har ta kaita da yunkuri ɗaukar ransa, duba da irin shaƙuwa da kyautatawa da ya dinga mata tun daga yarinta har zuwa girmanta, bai zaci cewa ko bakin bindiga aka ɗora mata aka aka ce ta caka masa wuƙa ko aɗauki ranta za ta zaɓi ta sadaukar da rayuwarta akansa sai dai kashh! Hasashen sa ne yake bashi hakan. A duk lokaci da ya tuna wancan daren sai ya ji wani irin ƙunci da takaici Sadiya don ba zai ce tsana ba domin kuwa har yanzu yana ji ƙaunarta a matsayin ƙanwarsa. Sai dai zuciyarsa ta kasa yi mata afuwa ta kasa goge hoton abunda ta aikata masa a zuciya da idanuwansa.
Aydah ta wuce ɗakinta da gudunta tana zuwa ta jefa ledar shopping ɗinta akan bed, jikinta har wani kalan rawa yake yi duk da bata so kitso da Ya Abba yake ikirarin za ai mata amma tana mararin fita dashi duk wani abu da ya shafi yaya Abba ko ya dangance shi tana daukarsa da matuƙar muhimmanci. Fitted gown ta ciro na wani black and gold ɗin lace ta cire kayan jikinta ta maye gurbin su da gown ɗin. Kayan da shigo dasu ta ciro powder haɗe da man lebe ta shafa powder akan kyakkyawar fuskarta lips ɗinta sai ƙyali suke a a dalilin man lebe da ta shafe su dashi. Turare kusan kala uku ta fesa, ta zari ƙaramin veil ɗinta gold in colour takalmin ƙafarta ma gold ne ya subhanalillah! Ba ƙaramin fitinanne kyau ta yi ba cike da farin ciki ta fice tana fitowa ta hango Sadiya tsugunne tana rusar kuka tun daga gun da Aydah take ta ji sautin kukan nata, taɓe baki ta yi a zuciyarta kissima watakila wani mari Ya Abba ya sake zuzzuba mata. Aydah ta so ta wuce ta ba tare da ta kula ta ba amma abinka da jini ɗaya ba wasa bane, sai ta tsaya musamman yadda taga Sadiyar take shasshekar kuka, ta jikin mirror mota yaya Abba ya hangon ta tsaye kusa da Sadiya tun kafin ta kai da yi mata magana ya danna mata mahaukacin horn dole ta haɗiye kalamanta ta nufi wurinsa da sauri, ta buɗe front seat ta zauna ƙamshin turarenta ya mamaye ƙofufin hancinsa sai da suka fice daga gidan kana ya dawo ganinsa akan fuskarta sosai ta yi masa kyau "Babyn yaya Abba yau kwalliya aka yi?"
Murmushi ta yi tana ƙara jefa idanunta acikin nasa tana mai gyaɗa kanta "To amma miyasa ba ki shafa ƙwalli ba?
Wani kalan cunno baki ta yi muryarta cike da shagwaɓa take faɗin "Banso kwalli Ya Abba zafi yake min ya dinga sakani hawaye dole.
Ɗan ƙaramin murmushi ya yi "Ki ɗaure ki dinga sakawa yana miki kyau sosai.
"Ni dai banaso.
"To ni inaso ko ba za ki saka saboda yaya Abbanki ba?"
Sosai ta washe fararen ƙanana haƙoranta masu ɗauke da siririyar wushirya dimple ɗinta na kunce ɗaya ya lotsa ta ƙara narke masa "Zan saka amma ba koda yaushe ba.
Ta yi magana cike da zallan shagwaɓa.
"Gaskiya Aydah ki rage ƙazanta kina mace amma ace bakyso kitso, kwali, kwalliya na rasa asalin ƙiyayyar ki da triple k ɗinan.
Dariya Aydah ta yi tana bubbuga ƙafafunta akan carpet ɗin da ke wurin ajiye ƙafafuwa a mota "Ni wallahi ba ƙazama bace ina wanka sau uku a yini idan da akwai zafi har sau huɗu nake yi.
Ta yi magana tana ɗaga yatsunta huɗu.
Taɓe baki ya yi yana faɗin "Miye amfani wankan da babu kwalliya.
"Yaya Abba saboda wannan korafin naka yau dai na runtse ido da muka je shopping na dauko kayan kwalliya ba ga gansu ba masu yawa.
"Iyeee! 'yanmata yaya Abba dai kwana nan za a ƙaro wulaƙanci.
Kusan a tare suka sa dariya sai hira suke abinsu har suka iso Aj beauty palace and spa da sauri Aydah ta kalle shi "yaya Abba ina ne nan?
"Saloon ne haɗe da wurin gyaran jiki anan yake yiwa Rumaisa kitso da gyaran jiki na yaba da kwarewarsu fiye da wancan da muke zuwa.
Turo baki ta yi ba tare da ta yi magana ba ta ɓalle murfin mota ta fito da kanshi ya yi musu bayani abubuwan da yake buƙata ai mata daga ciki har da pedicure da manicure sannan ya baro shagon ya nufi wuri da suka saba haɗuwa da Rumaisa sai dai su haɗu a keɓaɓɓen wuri ba dai a gidan su Rumaisa ɗin ba duk da irin kakkausar gargaɗin da mahaifin nata ya yi mata akan ta rabu da AB ɗin. Sai dai gargaɗin nasa ya kasa tasiri akanta kamar ma ya ce ta ƙara linƙaya a kogin soyayyar Abba ne. Duk wayewar gari sai sonsa da ƙaunarsa sun daɗa ƙaruwa a farfajiyar zuciyarta.
Wuri ne can a ƙarshen gari a wani gidan gona Daddy wuri ne da ake kiwon kaji, kifi, dabbobin mu na gida da na kasashen ketare ga itatuwan fruits sosai wuri ke da wata irin ni'ima wacce ke haifar da natsuwa da kwanciyar hankali. Kusa da motarta ya yi Parking motarsa tuni ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan gonar ya kai musu red plastic chairs a gidin bishiyar mangwaro wanda dama anan suka saba zama. Abba ya fito daga motarsa gami da maida ƙofa ya rufe, ya taka a hankali cikin natsuwa ya kai hannunsa ya buɗe side ɗin da Rumaisa take suna haɗa idanuwa suka sakar wa junansu da ƙayatattce murmushi "Ka ɓata almost 15 minutes a bisa lokaci da muka saba haɗuwa halan ka haɗu da traffic jams??
Sai da ya rufe mata murfin motarta ya juya tare da nufar wurin zamansu sai da zauna kana ya bata amsar tambayarta "Baby Aydah na kai Aj beauty palace and spa za a yi mata gyaran gashi.
"Baby Aydah!
she repeated the name with so much of jealous all over her face. Yayin da shi kuma ko kaɗan bai lura da yanayi da take ciki ba. "Habibi na fara kokwanto akanka da wannan yarinyar ka faɗamin gaskiyar abinda yake a tsakanin ka da ita?
Da shock yake kallon fuskar Rumaisa wacce sai cika da

14 / 80