Author : EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category : KDP NOVELS
ce domin gani ta hana faruwar naɗin sa da za a yi jibi amman ta yaya?"
Tambayar da ta kasa nemo amsar ta shi ne ta nemi amintacciyar jakadiyarta ko za ta iya lallaɓo mata mafita.
Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.
[1/29, 1:07 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye
085.
AB yana fitowa daga meeting da board members kiran Anaal Aliyu na Uku ya shigo wayarsa bai yi picking ba sai da ya isa ofishin sa ya zauna akan ɗaya daga cikin kujera da suka ƙawata ofishin nasa, yana mamakin kira me CEO Kim's Automobile ke masa yasan babu wani dalili da zai sa ta nemi shi a daidai wannan lokaci. Kamin ya kirata, ta sake kiransa ya yi picking tare da sallama a ɓangaren Anaal a natse ta amsa masa tamkar babu wata damuwa a tattare da ita.
"Barka da warhaka mr Abba Bashir.
"Barka mss Anaal.
"Na kira ne domin mu warware wata 'yar matsala da ta kunno kai dangane da partnership ɗinmu.
"Subhanalillah! Matsala kuma? Wacce irin matsala mss Anaal iya sanina mu riga da kowanne bangarori ya amince da tsarin da kowanne mu ya kawo, to wacce matsala ce za ta biyo baya?"
"Ka kwantar da hankalinka mr Abba domin mu warware wannan matsala yanzu haka ina kan hanyar Kano ka yi min addu'a isowa lafiya.
"Whats! Kina kan hanyar Kano fa?" Amman ya kamata mu fara tattaunawa wannan matsalar a waya kamin mu hadu da fari ma sai kin nemi amincewata kafin mu yi zama irin wannan.
"Ka yi haƙuri mr Abba banida lokaci ne gani irin muhimmanci da tattaunawar ta mu take da yasa ban tsaya neman izinika ka ba na taho.
"Shi kenan Allah ya kawo ki lafiya idan kin iso ki kira ni.
Daga haka ya yi hanging up, secretary ɗinsa Skyler ce ta shigo hannunta ɗauke da wasu files ta ajiye akan desk ɗinsa "sir ga files ɗin da ka buƙaci na kawo maka daga cikinsu akwai file ɗin kamfanin three stars automobile suna buƙatar sa hannunka.
"Shi kenan zan duba.
Ya faɗa a takaice secretary Skyler ta juya ta fice bata daɗe da fita ba sai ga Abdulkarim ya shigo hannunsa riƙe da waɗansu files,sallamarsa ya saka Ab buɗe idanunsa saboda tun fitowarsa gida yake fama da ɓacin rai akan abun da Aydah tai masa a duk sanda ya tuna sai ya ji wani sabon samfurin haushinta ya kama shi.
"Ango na Rumaisa da baby Aydah ya naganka sukuku da kai ko duk gajiya ce?"Gashi kuwa zuwa nan da nayi fita za mu yi akan wancan issue ɗin gara ayi komai a yau ɗinan mu karbi kuɗin mu a wuce wuri.
Abdulkarim ya ƙarashe magana yana miƙawa AB hannu suka yi musabaha kamin ya nemi kusa dashi ya zauna kana ya jefa files ɗin hannunsa akan mini center table da ke kusa dashi. AB ya sauke numfashi tare da kallon Abdulkarim "Bari kawai Abdulkarim yau baby Aydah ta charger min battery ɗina, tun safe nake fama da ɓacin ranta.
"Subhanalillah! Me ta yi maka?" Dan Allah ka dinga haƙuri kasan akwai ɗanyar kuruciyar a tare da ita.
"Uhm!
AB ya faɗa tare da furzar da iska daga bakinsa kamin ya rattabo wa Abdulkarim labarin abun da ya faru.
"Gaskiya abokina ba ka kyauta ba yanzu ɗan wannan abun har ya kai matsayin ayi mari akansa?"Miyasa sanda Rumaisa ta dinga dura maka men power miyasa ita ba ka dake ta ba ka ce kuskure ne ko don ita baby Aydah ba ka sonta auren dole aka yi maka da ita?"
"Ka ga Ak kada ka yi min mummunan fassara da Aydah da Rumaisa duk ɗaya suke a wurina....
"Ƙarya ka ke yi Abba Bashir da duk ɗaya suke a wurinka da ba za ka dauki Rumaisa ka kaita shopping ka kashe mata makudan kudade ita kaɗai dole ka haɗa da baby Aydah domin ita ma matarka ce ta sunnah yadda Rumaisa ta kawo maka virginity ɗinta haka zalika ita ma baby Aydah ta kawo ma wannan nuna bambanci ne da rashin adalci murara kuma sai Allah ya tambaye ka.
"Ya salam! Abdulkarim please ka fahimci zancena da idon basira mana na gayamaka ba a bisa radin kaina na kai Rumaisah shopping ba ita ce ta buƙaci hakan, da ita ma baby ta buƙaci hakan ba abun da zai hanani kaita amman sai ta hau ni da rashin kunya sai kace wani sa'anta.
"Ba rashin kunya bane Ab ta ji kishin yadda ka bambanta ta Rumaisa ne ko kaine a matsayinta za ka ji ba daɗi, dan Allah ka dinga bin Aydah a hankali ka fi kowa sani har yanzu ita ɗin yarinya ce ƙarama da ba za ta iya tantance waɗansu abubuwa ba.
AB ya yi ajiyar zuciya shi kanshi daga baya ya ji babu daɗin marinta da ya yi yarinyar da zai saɓawa da kowa akanta, amman yau shi da kansa ya mare fuskarta.
"Shi kenan na ji nayi kuskure in shaa Allah zan kiyaye gaba ita ma zan ɗauke ta na kaita shopping ɗin.
"To ko kai fa.
Abdulkarim ya faɗa yana dariya kana ya dauko zance da ya kawo sa da yake suna business ɗinsu a gefe shi da AB suna saye da sayarwa na filaye kana suna gina gidaje da plaza sai su sayar kuma su bada haya yanzu ma wani plaza ne da suka kammala gininsa a kwananan wani ke so siya shi ne ya zo su je a ƙarasa magana. AB ya ɗauki wayoyinsa da car key ɗinsa suka fice.
Rumaisah ta shirya wa AB lunch mai rai da lafiya, tana kammala arranging table ta wuce ɗakinta lokacin da ta je wanka taga yadda jini ya sake dawowa bayan da ɗazu da taga ya ɗauke har tana murna yanzu za ta yi wanka tsarki sai gashi kuma yanzu ya dawo cikin tsanani tashin hankali ta zube guiwayoyinta akan tiles ɗin bathroom ta fashe da matsanancin kuka, wani irin baƙin ciki take ji yana ratsa mata zuciya don tasan da matuƙar wahala Ab bai je wa Aydah ba saboda tasan halinsa da rashin haƙuri wannan wacce irin masifa ce ta saukar mata a daidai lokacin da take ganiyar cin amarcinta. Adaddafe tayi wanka ta fito koda ta shiga bathroom taci burin idan ta fito za ta tsala kwalliya da za ta gigita AB amman dawowa bleeding ɗin duk sai ta ji komai ya fice mata arai, tana fitowa turare kaɗai ta shafa ta zura plain gown material ta ɗauki wayarta, ta kira Ammie cikin muryar kuka ta zayyana wa Ammie halin da take ciki.
Shiru Ammie ta yi na ɗan wani takaitaccen lokaci kamin ta ce ta jira za ta kira ta.
After thirty minutes sai ga Ammie ta kira ta, ta ce ta kira Ab ta faɗa masa za ta zo gida akwai likita da zai dubata. Rumaisa ta kira Ab ta faɗa masa da fari sai da ya rufe ta da faɗa yana faɗar ba sun je taga Dr Sameer matawalle ba ya kuma rubuta mata magani tun bata kammala shan maganin da ya rubuta mata ba, za ta je ganin wani likita shi fa bayaso haka. Da kyar ta rarrashe shi ya amince ta ce ya dawo gida ya yi lunch tayi masa girki na musamman, agaggauce ta canza kayan jikinta ta ɗauki car key da wayoyinta ta fice, Huwaila tana ganin fitar ta ta nufi ɗakin Aydah, kamar tasan AB zai dawo gida ta cilasta wa Aydah yi wanka ta shirya ta cikin wani tsadadden lace coffee color style ɗin skirt and blouse. Suka fito downstairs parlor Huwaila ta kunna musu kayan kallo, suna cikin kallo suka jiyo horn ɗin AB da sauri Huwaila ta kalli Aydah tana faɗin "Auta ki saurare ni da kyau tun da wannan kodaddiyar ta fita ga kuma Yayanmu ya dawo wannan shi ne lokaci mafi dacewa da za ki daidaita tsakaninki da mijinki, ki basa hakuri ki nuna masa kin yi kuskure ba za ki ƙara ba kin jin ni da kyau?"
Aydah ta ɓata fuska tana cuno baki gaba "Aunty Huwaila mari na fa ya yi.
"To don ya mare ki ba za ki iya yafe masa ba? Wai ni kam Aydah ko kin daina son Yayanmu ne?"
"Ina sonsa sosai amman ba zan taɓa lamunta ya dinga danne min haqqena.
"Kai Auta Ni kam yaushe kika koyi mita ne?"
Kamin Aydah ta bata amsa Ab ya tura kofar main parlor ya shigo da sallama Huwaila ce ta amsa masa tare da yi masa barka da dawowa kallo guda Aydah tai masa ta kauda fuska, shi kuma ga baki ɗaya hankalinsa yana kanta don ba ƙaramin kyau tai masa ba, ji yadda yaga tana cin magani yasa shi saki murmushin gefen baki.
Huwaila ta juya ta nufi ɗakinta, ta bar musu parlon.
"Barka da dawowa!
Aydah ta faɗa adakile kamar mai ciwon hakori.
"Yawwa sarkin fushi da dai kin saki fuskar don wannan ɗaure fuska da kike yi ko kaɗan baya miki kyau asalima ya ɓata miki kwalliya da kin saki fuskar da wata kila mu je shopping.
Murmushi Aydah ta yi tare da nufar wurinsa cikin sigar shagwaɓa ta ce "Na saki fuska Yayanmu har dariya ma zan maka.
"Saboda kin ji zance shopping ko? To na fasa tun da dariya bata Allah da Annabi bace.
Batasan sanda ta riƙe masa hannu ta marairaice murya tana faɗin "Ka yi haƙuri dan Allah ba zan sake ɓata maka rai ba.
"Shi kenan mu je ki bani abinci idan nayi wanka na huta sai mu fita ɗin saboda nasan halin nacinki muddin ba shopping ɗinan na kai ki ba, ba zan sake gane kanki ba.
Zuciyar Aydah tayi fari tass suka jera zuwa dinning room yana faɗin "kin yi matuƙar kyau cikin lace ɗinan baby ki dinga saka color ɗin ya karɓi jikinki sosai.
Cikin shagwaɓaɓbiyar muryarta ta furta.
"Thank you mi amor!
Ta kama kujera ta ja masa ya zauna sai da ya zauna kana ya kalleta yana faɗin "me na ji kin ce?"
"Cewa nayi nagode!
"No bayan kalmar godiya ɗin na ji kin ambaci wani suna.
Dariya Aydah ta yi tare da ajiye masa plate ɗin sa ta yi masa serving a gabansa.
"Oh! Wai mi amor?"
"Eh! Shi ɗin me hakan ke nufi?"
Da sauri ya rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana dariya ƙasa-ƙasa ta bar cikin dinning ɗin da kallo ya bita yana murmushi yayin da yake maimata sunan acikin zuciyarsa, yana so yasan me kalmar ke nufi, Aydah tana gani ya wuce ɗakinsa ta nufi parlornsa dake sama ta kasa ta tsare tun kamin ya ƙaraso cikin parlor ta fara shaƙar ƙamshin turarensa, ya fito sanye cikin filtex material milk colour ya saka hula zanna bukar da ta dace da kayan jikin nasa ƙafafunsa sanye cikin sandal shi ma milk in colour, ya kalli Aydah yana murmushi "Wannan tsarewa duk ta mene ne?"
Ya yi magana yana daidaita zaman hular kansa.
"Yayanmu ba ka ce za mu je shopping ba?"
"Cewa nayi sai na huta.
Ya yi magana yana zaunawa kusa da ita ya mutsa fuska ta yi tamkar za ta rushe masa da kuka "Dan Allah yayanmu.
Ta karasa magana tana haɗe hannayenta.
"Okay! Tashi mu tafi
Ya yi maganar yana dugure mata goshi already ta dauko veil ɗinta, da takalminta a ƙafafunta sai wayarta dake riƙe da hannunta, tare suka sauko ƙasa "Yayanmu bara na leƙa ɗakin aunty Huwaila na faɗa mata mun fita ta kula da gida.
"Shi kenan ki yi sauri ina jiranki a mota.
Aydah tana zuwa ta rungume Huwaila tana tsalle murna dariya Huwaila ta yi tare da ciro ta daga jikinta tana faɗin "wannan farin cikin fa?"
"Aunty Huwaila shopping za mu je ni da Yayanmu nima zan rama wulaƙanci da aunty Rumaisa tayi min.
Aydah ta faɗa cike da zallan wauta da kuruciya tura ta waje Huwaila ta yi tana faɗin "je ki in kin dawo za mu yi celebration.
Da dan gudun ta ta fice, har ta buɗe mota ta zauna Ab yana waya da ta baza kunne sai ta fahimci da mace ne yake magana musamman da ta ji ya kama suna.
"Mss Anaal ashe har kin iso.
Sai ya yi jim yana sauraren abun da Anaal ɗin take faɗa.
"Okay! A bon hotel kika sauka? To meyasa kika kama masauki batareda da kin jira ni ba kika sani ko na tanadar miki da masaukinki ko kin manta lokacin da na je Lagos kin ce min accommodation ɗina yana kanku?
Ya yi shiru kafin kuma ya yi dariya
"Yanzu dai gani tare da madam za mu fita unguwa idan na dawo koda zuwa bayan ishaa ne zan zo mu tattauna ɗin.
Yana ƙarasa magana tare da ajiye wayar akan dashboard kana ya maida ganinsa akan Aydah wacce ta yi kici-kici kishi ya bayyana ƙarara akan fuskarta.
"Business partner ɗina ce ba budurwa ta ba.
AB ya faɗa yana yiwa mota key.
Turo baki Aydah ta yi tare da furta
"To ai ban yi ƙorafi ba.
"Nima ban ce kin yi korafi ba amman kin ɓata fuska.
"To meye don na ɓata fuska naga dai fuskar ma marinta kake yi.
"Baby kodai na tsaya a gefen titi ki rama marenki?"
Zaro idanuwa ta yi tana kama bakinta.
"Ai gara ki rama marenki baby kamar zai fi min sauki da ki dinga tuna min dashi.
"Na rama fa ka ce?"
"En mana!
"Uhm! Wato Yayanmu so kake a saka ni wutar jahannama ko?"
Dariya Ab ya yi sai da ya yi mai isarsa kamin ya ce "Ashe Babyn yaya Abba ta fara hankali.
"Daman can da hankalina.
Da haka suka iso ado bayero mall Aydah sai murna take yi ta dinga jidar kaya kamar za ta buɗe ɗan ƙaramin shop shi dai AB sai Kallonta yake yi yana murmushi, sai da ta gaji don kanta sannan ta ce iya abubuwan da take buƙata kenan. Suka je ya biya kuɗi aka zuba musu kayan a mota, kallonta ya ce "Yanzu sai mu wuce shagon waya ko?
Girgiza kai Aydah ta yi tana turo baki "Ni banaso waya.
"To me kike so?"
"Mota nake so Yayanmu ka tuna ka yi min alƙawari since yanzu ne right time da za ka cika.
"Baby cewa nayi sai kin kammala secondary school idan kika fara zuwa high school sannan zan ba ki mota.
"Dan Allah Yayanmu ka bani yanzu ko ba zan fara driving ba zan so na dinga ganinta a parking lot a matsayin tawa.
"Na ce ba yanzu ba.
Ya faɗa yana tamƙe fuska cigaba da yi masa magiya ta yi har sai da ta haɗa da kuka kamin ya amince.
"Shi kenan na ji zan ba ki ɗin sai ki shafa min lafiya. Amman ba yau ba sai dai gobe saboda yau.
Ihun farin ciki Aydah tasa tare da rungume Ab ta da sauri ya saka signal ya gangara gefen titi ya yi parking.
"Ke kin yi hauka ne da za ki yi min wannan wawan runguma salon na ɓarar da damu.
Sumbatar kumatunsa ta yi "ina sonka ina sonka Yayanmu!
Aydah ta faɗa very excited, tura mata bakinsa ya yi "anan za ki nuna farin cikinki ba a kumatuna ba.
Ga mamakinsa sai gani ya yi ta zagaye hannayenta a wuyansa ta yi connecting lips ɗinsu wani kalar sucking lips ɗinsa take yi ga baki ɗaya AB ya gigice yana neman fita daga hayyacinsa ƙara shigar da ita jikinsa ya yi.
Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.
[1/29, 1:07 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye
086.
Sun ɗauki lokaci suna ya mutsa junansu da kyar ya iya kyaleta ya koma jikin kujerar mota ya lafe sai wani wahalalle numfashi yake saukewa yayin da Aydah take kici-kici maida zip ɗin rigarta da zugesa ya janye hannayenta ya maida zip ɗin ya rufe mata sai da ya sakar mata kiss a wuya kamin ya tada mota "Baby na tambaye ki mana?"
"Uhm!
Aydah ta faɗa batareda da ta kallesa ba batasan meyasa a duk sanda irin haka ta faru a tsakaninta da yayanta take jin kunyar haɗa ido dashi.
"Dinkin da aka yi miki ya warke ko?"
Girgiza kai ta yi cikin sarƙewar lafazi ta furta "Da saura Yayanmu doctor ma ta ce idan na cika One week na koma za ta duba dinkin idan ya yi healing.
Numfashi ya sauke tare da jin tausayinsa kansa ga shi da mata har guda biyu sai dai babu wacce daren yau zai more ta.
Yana sauke Aydah ƙofar gida ya wuce masallaci ya yi sallah magarib da ishaa sannan ya nufi hotel ɗin da Anaal na uku ta sauka, restaurant ɗin da ke cikin hotel ɗin ya nufa a bangaren vip ya nemi wuri ya zauna sannan ya kira Anaal ya faɗa mata inda za ta same shi.
Anaal ta tashi da sauri jikinta har rawa yake yi a can kasan zuciyata tana jin tsoro haɗe da shakku akan abun da take shirin aikatawa, har ta ji kamar ta fasa sai kuma tuna da girman al'amari da yake shirin tunkaro ta. Da sauri ta ɗauki wayoyinta tare da wani brown envelope cike da kuzari da kwarin gwiwa ta fice,har ta isa vip ɗin tana jin wasi-wasi a zuciyata. A hankali AB ya sauke idanunsa akanta tana sanye da Abaya dark green ta yi rolling da mayafin rigar abin ka da farar fata cikin green colour sai tayi bala'in kyau, gabansa ne ya yi wani irin bugawa wani abu yake ji mai wahalar fassara wa yana bin jini da ɓargon jikinsa, kasa ɗauke idonsa akanta ya yi har ta zo ta zauna ta sakar masa murmushi shi ma ya mayar mata da martanin murmushin nata. Murmushinsa yai masifar faɗar mata da gaba ta zauna a kujerar dake facing ɗinsa yayin da gabanta ke cigaba da dokawa, a kasan zuciyata tana ji rashin dacewar abun da take niyar aikatawa to amman wani sashe na zuciyata yana daɗa karfafa mata gwiwa da ta yi ɗin matsoraci baya taɓa zama gwani da wannan kwarin gwiwa da ta samu daga daga dayan bangare zuciyarta ta saita natsuwarta wuri ɗaya ta fuskance shi da kyau cike da jarumta ta gaishesa tare da tambayarsa iyalinsa duk yana amsa mata da alhamdullah!
"Mr Abba na zo ne domin dangane da partnership ɗin dake tsakanin kamfanonin mu, a kwanaki huɗu da suka gabata mahaifina ya kira ni ya nuna min ayi cancel ɗin wannan yarjejeniya. Na nemi nasan dalilinsa na so yi hakan amman sai ya nuna min nayi abun da ya umarci ni shiyasa na zo da kaina na kawo maka waɗannan takardun ka sanya hannu.
"Amman dai wasa kike yi ko?"
AB ya