Author : EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category : KDP NOVELS
batsewa take yi ita kaɗai tasan irin mugun tsanar da ta yiwa shaƙuwar Abba da Aydah tun kafin ma tasan babu alaƙa ta jini a tsakanin su balle yanzu da tasan igiyar aure za ta iya shiga tsakaninsu. Sai abinda tsanar ta ƙara linkawa a zuciyarta, zazzafan kishin yarinya nan take ji marar misaltuwa balle har a faɗin adadin sa. Domin Abba ya kore zargi haɗin da hasashen fassarar kalamin Rumaisa sai ya furta "Ban fahimcin idan wannan tambayar taki ta dosa ba Rumaisa ki daina nuku-nuku ki fito fili ki faɗamin manufar ki.
#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo
Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/12/2023, 10:20 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
#Love Story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye novels
020..
*RUNBUTUN ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU.*
*TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA*
*KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?*
*INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?”*
*KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.*
Mun gwada mun gani 💯
Mun gani mun shaida 💯
Anyi mun gani 💯
MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
GYARAN MAIJEGO
MALLAKAR MIJI KO MATA
SUBULU DA SCRUB
MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
MAGANIN TSUMI
INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯
08142800199
07068558096
Wani jahilin kallo ta wulga masa shi kansa a yanzu haushinsa take ji ankai stage ɗin da ba za ta iya cigaba da sarrafa tsananin kishin Aydah da take ji. Ba ƙaramin takaici ke kamata ba a duk sanda ya kira Aydah da suna Baby ga bakinsa ya kware da iya kiran Baby Aydah, har wani lankwasa harafin Baby yake yi cike da salon jan hankali wanda shi kam baisan dashi ba watakila kunnen Rumaisa ne yake ji mata hakan.
"Abba karka ka raina min da hankali mana idan da can babu soyayya a tsakaninka da ita a yanzu fa?
Nan take ran Abba ya yi mugun ɓacin da duk duniya idan da akwai abinda yake saurin haifar masa da matsanancin fushi shi ne a danganta shi da kalmar aure ko soyayya da Aydah yanzu nan sai ka ga ya fusata irin fushin da baya misaltuwa.
"Wannan wacce irin maganar banza ce Rumaisa? Don kawai kina sha'awar ki ɓata min rai shine kika bijiro min da wannan zance.
"A'ah! Abba duk mai cikakken hankali zai fahimci yadda kake nuna tattali da kulawarka akan yarinya nan ya zarce ƙa'ida ta wa da ƙanwa. Haba sai kace ita kaɗai ce ƙanwarka naga dai su uku ne har ma da wacce aka yi maka auren huce haushi wannan nake nufi wacce taso ta datse numfashinka, ban da ma rashin zuciya irin naka Abba me za ka yi da zuri'ar da suka yi yunkuri kawo ƙarsh.....
Abba bai bari Rumaisa ta kai ƙarshen zancenta ba ya wanke mata kumatunta da kyakkyawan mari wanda sai da jinta da ganinta suka ɓace na wani lokaci. "How dare you Rumaisa! Ke har kin isa ki zagi family da suka inganta min rayuwa suka mayar dani ɗa kaman kowa, na zama abin sha'awa har ke ɗinan kika yi kwaɗayi haɗa zuri'a dani. Rumaisa ni ba butulu bane mai manta alkhairi duk da ba su kasance biological parents ɗina ba hakan ba zai sa na zuba ido ina kallo a furta mummunan kalma akansu. Har gobe su ɗin nake kallo a matsayin iyayena banida kamar su a duk faɗin duniya nan, inason su ina ƙaunarsu, sune komai nawa idan har bakinki zai ci-gaba da faɗar kwatankwacin irin wadannan zafafan maganganu akansu, dan Allah kowa ya kama gabansa dama can ke ce kika nacewa alaƙarmu.
Cike da wani kalan tashin hankali Rumaisa take dafe da kuncin ta tana kallon AB ba kalmar da ta fi ƙona mata rai irin cewar da ya yi ita ce ta nacewa alaƙarsu, ta ji zafin kalmar nan fiye da marin da ya yi mata.
"Wannan shine kashedi na dake na ƙarshe karki kuskure ki sake danganta aure ko soyayya a tsakanina da Aydah domin har gaba da abada babu wannan alaƙar a tsakanin mu.
Daga haka ya juya ransa a ɓace ya shiga motarsa ya ja ta da ƙarfi ta bishi da kallo har zuwa lokaci hannunta yana kan fuskarta gun da ya mara, bata taɓa sani Abba yana da zafin rai har haka ba iya sani da tai mishi mutum ne mai sanyi hali da haƙuri ba kasafai ake gane fushinsa ko ɓacin ransa ba. Ita kanta tasan ta kaishi bango ne shiyasa har ya ɗauki hukunci makamanci wannan akanta. Jiki a sabule ta shiga motarta ta nufi gida, zuciyarta a cukude ta wuce ɗakinta ta faɗa kan gado idan Allah ya taimake ta ammi bata cikin main parlor ɗin, balle taga yadda idanunta suka yi jajir ga kuma shatin kyawawan zara-zaran yatsun Abba biyar shimfiɗe akan tattausan farin kumatunta, sai lokaci tasami damar sakin ɗan marayan kuka.
Sai da Abba ya yi tafiya mai nisa kafin ya gangara gefen titi ya yi parking ya kifa kansa akan steering wheel, wani irin zafi haɗe da raɗaɗi can ƙasan zuciyarsa ke masa at least ya share 20 minutes wuri da taimakon addu'ar da yake furtawa acikin zuciyarsa ya sami sassauci abunda yake ji har ya iya ɗaukar water bottle ɗin da ke cikin motar duk da basu da sanyi a haka ya ɓalle murfin ya kafa a bakinsa a bottle ɗin sai da ya sha fiye da rabin ruwan kafin ya maida murfin ya rufe tare da mayar da su gun da ya ɗauko su. Ya ja dogon numfashi ya sauke ya sake ja wani ya sauke sai da ya yi hakan kusan sau huɗu sannan ya ji natsuwarsa tana dawo masa a hankali a jikinsa tuni duhun magariba ya yi wanda ke nuni da an kammala sallar magarib ya yiwa motar key cikin tuki natsuwa ya haura kan titi a wani masallaci ya tsaya ya yi sallar magariba da isha sannan ya nufo Aj beauty palace and spa ya ɗauki Aydah wacce yake tunani tun-tuni an kammala mata shi kaɗai take jira, ai kuwa hasashen ya tabbatar gaskiya domin kuwa a taƙure ya iskota zaune sai faman rarraba idanuwa take yi tana neman gun da zai ɓullo, tana arba dashi ta taso da sauri ta nufe shi tana ɓaɓɓata fuska kaman za ta yi kuka "You took long time Yaya Abba da ba ka zo yanzu ba Allah har zan fara musu kuka.
Ta ƙarashe magana cikin zallan tabarar nan da ta saba masa. "I'm sorry Baby na tsaya nayi sallah ne.
Ya yi magana yana mai shafa kumatunta ya je ya biya su kuɗin aikinsu kana suka wuce wurin mota tun yana reverse ta fara cewa "Ya Abba duba kitso na( shuku) aka yi min ya yi kyau sai dai yaya Abba akwai zafi Allah kaman kaina zai cire?
Ta faɗa tana wani kalan matso ƙwallan shagwaɓa. Bai kula ta ba har sai da ya daidaita motar akan titi ya dawo da ganinsa akan kitson kanta da bata maida ɗan ƙwalinta da ta cire ba "Wow! Kitso nan ya yi kyau sosai kin ga ma kuwa uhm! Uhm?
Sai kawai ya dinga uhm! Me ma zai ce can kuma cike da zolaya ya ke faɗin "Aididin yaya Abba mai majina a hanci ta yi kashi a wando.
Aydah ta fashe da kukan da babu hawaye tana faɗin."Yaya Abba! Yaya Abba! Ni ka daina banaso na girma bana kashi a wando kalli hancina ka gani babu majina!
Yadda ta dinga zuba mishi rigima kala daban-daban hakan ya mantar dashi damuwar da Rumaisa ta haifar mishi da ita kafin su iso gida ya tsaya ya siya mata tsire ita da Siyama yasan suna sonshi sosai ƙarfe 9:00pm daidai suka iso gida shi ya wuce a ɓangaren sa ita kuma ta shigo da ledar tsirenta a hannu da wani irin fara'a shimfiɗe akan fuskarta gashi kitso da aka yi mata ya ƙara haskaka fuskar nata goshinta sai ƙyali yake, sanin batayi magarib ba yasa ta wuce ɗakinta direct wanka tayi dan duk ƙanunun gashi sun manne mata cikin wuya, harda alwala ta haɗo ta a lokaci ɗaya ta gabatar da sallar magarib da ishai, tana gamawa ta dauko doguwar rigar bacci ta saka ajikinta
Kai tsaye parlor ta wuce,ta miƙawa Siyama ledar tsirenta har kusan ƙarfe goma sha ɗaya ta kai a parlor tana zaune tana taya su yaya Sadiya dake kallon wani movie a tashar (African magic epic )duka hankalinsu yana kan movie ɗin daidai lokacin da AB ya shigo cikin parlor dan bai ci abincin dare ba ya shigo yasha coffee kafin ya kwanta dan har jin yake cikinsa na wani kalar nadewa, daidai lokacin da idonsa ya hasko masa macce da namiji kwance akan gado suna romance ɗin juna hankali tashe yake kallon ƙannen nasa ganin duka hankalinsu ya tattara ga akwatin talabijin musamman Aydah wani kalar faɗuwa gabansa ya yi da sauri ya je ya kashe kayan kallon duka sai lokacin suka bisa da kallo dukkansu su uku. Siyama ta mike tsaye tana zaro idanuwa hakama Sadiya da Aydah kowacce ta yi wuƙi-wuƙi mugun kallon da Abba, ke jefa masu yasa Siyama ta fara kame-kame
sai ita Sadiya ta wani kalan daure fuska "Yaushe ku ka fara kallan tashar nan a gidan nan?" Abba ya faɗa rai ɓace tuni ita dai Aydah idanunta suka fara cika da kwallah cike da ƙarfin hali Siyama ta ce."Dan Allah yayanmu ka yi haƙuri wallahi koda na shigo Parlor nan na tarar da yaya Sadiya da Aydah suna kalla. Rasa ma abun faɗa ya yi duk yafi ji takaicin yadda Aydah ta tattara hankalinta akan Tv. Su yasan shekarunsu ya kai su kalla ita fa?" jin yaki cewa komai dukansu suka juya suka nufi stairs ita ma Aydah tana kallonsa ta juya tabi bayansu ganin yadda fuskarsa ta zama lokaci ɗaya tsoron yi masa magana take kar yayi mata ihu. Kitchen ya nufa ya haɗa coffee ɗinsa ya dawo cikin parlorn yana sha still kallon da ya sami ƙannen nasa nayi yana gilma masa cikin idanuwansa gobe zai yi waya da office ɗin Dstv acire masa duk wata tashar da ake haska ire-iren wa'yannan movies ɗin. Aydah har ta yi shirin kwanciya taji an turo ƙofar ɗakin nata da sauri ta kara danna kanta cikin pillow dan duk a tunaninta yaya Abba ne ya biyo ta yayi mata faɗa sai ta ji muryar Sadiya akanta buɗe idanu ta yi tana kallon yayarta ta, fuska a haɗe Sadiya ke faɗin."Daga yau idan kinga muna kallar irin wannan movie ɗin a parlor karki ƙara zuwa ki zauna a ɗakinki ko ranki ya ɓaci kema gulmace ta kawoki nasan saboda ke yaya Abba ya wani kashe kayan kallo. Bancin yasan mun isa muda muke zuwa jami'a danke yayi karki kara zuwa gashi nan kin ja mana a banza a wofi ba za mu sami damar ƙarasa kallan movie ɗin ba. Sadiya ta ƙarasa magana sounding so pissed up tana bar wa Aydah ɗakin. Sai mita take ita kaɗai yaya Abba, ya shiga hakkinsu kuma yayi ne saboda Aydah ita da take ƙarama a daren Sadiya bata kwanta ba sai da tai downloading movie ɗin akan laptop ɗinta ta kalli abunta hankali a kwance acan kasan ranta tana mamakin yayan nasu gashi dai yana da class yana da wayewa sai ya yi ta wasu abubuwan yan ƙauye kenan da har yanzu tana da aurensa akanta haka zai riƙa kallonta ya wuce bancin da ranta da lafiyarta.
Ranar Saturday misalin ƙarfe goma na safe Daddy ya ɗauki wayarsa ya kira layin Abba ,bata jima tana ringing ba Abba ya ɗauki wayar
Daddy ya faɗa masa ya samesa a parlor yanzu. Ya amsawa da Daddy da to gashi nan zuwa daga shi sai boxer ajikinsa ya nemi jallabiyya ya saka ya nufi part ɗin iyayen nasa da sallama ya shigo Parlor Mami ta amsa tana kallonsa ya samu wuri ya zauna kasan rug Daddy ya buɗe wata envelope ya ciro card ɗaya aciki ya kalli Mami ya mika mata da murmushi cikin fuskarsa gaban Mami banda faɗuwa babu abunda yake tun kafin tasan mene ne aciki taji iskar parlor nayi mata kaɗan wani irin tashin hankali ta ji yana zagaye zuciyarta still Mami taki kallon card ɗin dake hannunta da mamaki Daddy ki faɗin."ki duba mana Mariya.
AB ya ɗago yana kallon Mami ganin yanayinta ya canja sai da zuciyarsa tayi wani tsalle daga cikin ƙirjinsa a hankali Mami ta ɗora fuskarta saman rubutun dake cikin card ɗin.
#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#kurman Allo.
Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/12/2023, 10:43 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye novels
021.
Wani irin expression ne kwance a acikin fuskar Mami ta karanta rubutun ya kai sau goma tama kasa fahimtar komai sakin card ɗin kawai ta yi a ƙasa daga Daddy, har Abba bin card ɗin suka yi da kallo. Daddy bai damu da shock ɗin dake cikin fuskar Mami ba, a hankali ya dauki card ɗin ya miƙawa Abba tun kafin ya karɓi card ɗin daga hannun Daddy, ya ji wani irin sanyi na shiga cikin jikinsa cike da ƙarfin hali AB ya karɓi card ɗin hannun Daddy ya ɗora fuskarsa akan rubutun in a second ya daga kai yana kallon Daddy, da shi ma Daddyn shi yake kallo cikin tsananin tsoro gami da firgitarwa AB ke kallon daddy yana girgiza kai da rawar murya yake faɗin."Daddy card ɗin daurin aure nagani amman ban fahimci sunan dake jikin invitation card ɗin ba. Ka yi min bayani sosai Daddy.
AB ya faɗa muryarsa na karyewa a hankali addu'a yake Allah yasa Daddy yace ba wacce ya gani jikin invitation card ɗin bace zai haɗasa aure da ita addu'a yake Allah yasa idanunsa kurum ne suka gano masa hakan. Tun kafin Daddy ya yi magana Mami ta miƙe tsaye hankalinta a matuƙar tashe ta kalli tsakiyar idanuwan Daddy sannan ta ce "Wannan karon tunaninka bai faɗa maka daidai ba aure fa za ka yiwa Aydah kuma da yayanta Abba duka-duka shekarun Aydar nawa suke a duniya? Wannan karon kayi kuskure Alhaji ka canja shawara."
Wani kallo Daddy ya shiga aikawa Mami yana faɗin."Akwai haramci acikin Aurensu? ko shekarun Aydah ne suka zama haramta na yi mata aure a wannan lokacin?" ban amince ki fadawa kowa cikin 'ya'yanki ba har sai bayan ɗaurin aure. Za ki iya tafiya umurni nake bayarwa ba shawara ba muddin na isa da gidana abi yadda nake so na kuma tsara.
Mami kawai ta juya tabar Parlon Daddy ya dawo da dubansa akan AB yana kallon yadda ya zama wani iri
tun lokacin da Daddy ,da Mami suka fara musayar yawu ya ji duniyarsa na juya masa. "Abba ina fatar za ka ƙara yi min biyayya a karo na biyu ka karɓi zaɓin da na yi maka?"
"Amman Daddy Aydah fa?" Ya faɗa a wani irin birkice ? murmushi kurum Daddy ya yi tare da yiwa AB izinin tafiya yana ƙara faɗa masa date ɗin da ya saka na daurin aurensu babu fashi. Haka ya nufi ɓangarensa ko ganin gabansa baya yi, ko aurensa da Sadiya da aka daura bai daga masa hankali ba kamar wannan ba.
Fatansa kawai ya zama mafarki ne ya zama cikin mafarki Daddy ya faɗa masa haka a birkice Mami ta fito parlorn Daddy kai tsaye ɗakinta ta wuce harda su sakawa ƙofar ta key.
Sai safa da marwa take acikin ɗakin ga baki ɗaya ta haɗa gumi ita tasan duk duniya babu mai canja wannan ra'ayin na Daddy tunda yace haka zata kasance, ko auren Sadiya da Abba bai ɗaga mata hankali ba kamar wannan auren . Da sauri ta isa bakin gado ta zauna ta jawo wayarta ta shiga dialling lambar ƙanwarta Safeena ita ma dake aure cikin garin Kano a unguwar jambolo. bugu ɗaya Safeena ta dauka tana gaishe da yayarta tana faɗin."kamar kin san inata so na kiraki zuwa anjima kaɗan zan shigo idan yara suka tafi islamiyya.
"Safeena me zai hana ki taho yanzu wallahi ina cikin tashin hankali Alh Bashir so kawai yake ya zautar dani.
Safeena jin muryar yayarta kawai ya daga mata hankali tace mata to bari kawai ta taho sai mai'aiki ta kula dasu kuma maimoon ma tana gida wacce 'yarta ce ta biyu kuma sa'an Aydah sai yayanta Jameel sai kannensa guda biyu da macce da namiji ƙannen maimoon da mai shekara biyar da kuma shekara bakwai macce ce ƙaramar su. Mami zamanta ta yi a ɗaki dan bata son ko kaɗan 'ya'yan nata su fahimci damuwar da take ciki musamman Aydah yanzu zata kama damunta da tambayar mami baki da lafiya ne."
Siyama na kwance a parlor tana karanta English novel dake cikin wayarta ta ji muryar small Aunt ɗinsu, ta miƙe tsaye cike da murna ta rungume ta tana yimata sannu da zuwa ta amsa tana tambayar su Aydah? ta faɗa mata Sadiya ta shiga school Aydah kuma yanzu tabar Parlorn, kai tsaye ɗakin Mami Aunty Safeena ta nufa ita kuma Siyama ta juya kitchen dan kawowa Aunty nata abun motsa baki duk da tasan daga gida