Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   21 / 80

60K to 63K   out of 237.2K words

bi ka rame Bashir ina hango tsanani damuwa cikin idanuwanka idan ka ɓoye min wa kake dashi da yafi ni ko kana da wanda ya fi ni Bashir?"
AB ya girgiza kansa duk sai ya ji zuciyarsa babu daɗi, tun da har ya ji Daddy ya kira sunansa na aihini wanda ba zai iya tuna when last da Daddy ya kira sa dashi ba. Cikin sanyi murya tare da sadda kai ƙasa AB yake faɗin "Daddy dangane da zance....
"Auren ka da zan yi maka ko Abba?
Daddy ya yi sauri katse masa hanzari "Eh! Daddy!
AB ya furta da sanyayyar muryarsa mai cike da respect.
"Abba bakason Aydah ne?"
"A'ah! Daddy ba haka nake nufi ba ai Aydah ƙanwata ce ba zan taɓa ƙin ta ba.
"To idan ba sonta ne ba za ka yi ba Abba menene ya haddasa maka shiga damuwa?
AB ya yi shiru yana wassafa ta yadda zai furtawa Daddy zance a mayar da aurensa da Sadiya, ganin shiru nasa yana neman ya yi yawa yasa Daddy ya dafa kafaɗarsa cikin kwatar da murya yake faɗin "Abba ni fa mahaifinka ne babu zance ɓoye-ɓoye atsakanin mu, ka buɗe baki ka faɗamin hakikanin gaskiyar abunda yake ranka. Karka damu zan fahimci ka. Wani kalan numfashi AB ya fesar gabansa na wani irin bugawa ya ce "Daddy na ce me zai hana ka janye aurena da Aydah ka mayar akan Sadiya tun da yanzu mun gama fahimtar juna. Sadiya ta yi nadamar abinda ta yi har ta roke ni gafara na kuma yafe mata Daddy let bygone be bygones.
Tun da ya fara magana Daddy yake karantar yanayinsa ga baki ɗaya, kafin ya ja numfashi tare da saukewa "Mariya ce ta kimtsa maka wannan maganar ko Abba?"
Daddy ya tambaya duk da yana da tabbacin wannan maganar ba daga Abban take ba amma domin ya tabbatar tare da kawar masa da kokwanto shine ya tambaya. Nan take Abba ya ruɗe ya shiga kame-kame "Ka yi haƙuri Daddy idan ranka ya ɓaci Mami tana gani is too early a yiwa Aydah aure zai zama kamar an shiga hakkin ta ne, kuma ni banaso na yi abunda zai cutar da Ayd...
"shut up, I told you to shut up before I get angry with you Abba yaushe har lalacewa ta ya kai na zantar da hukunci a gidana Mariya ta tashe shi? Kai kuma da yake shashasha ne har ka aminta da zancenta, to bari ka ji muddin na isa dakai kuma har yanzu kana kallona a matsayi mahaifi aure tsakaninka da Aydah babu fashi.
"Daddy I'm sorry please forgive me zan yi duk abinda ka umarce ni kasani har duniya ta nade bani da wani mahaifi sama da kai burina a koda yaushe na kasance ɗa mai biyayya ga iyayensa shine ma dalili da yasa na amsawa Mami bukatar ta.
"Daga yau banaso ka sake zuwa min da zancen Sadiya aure a tsakaninku ya haramta saboda kai mijin ƙanwarta ne. Tashi ka tafi sai da safe.
Batare da AB ya sake cewa komai ba ya tashi jiki sabule har ya kai kofa ya kama handle da nufi buɗe ƙofa Daddy ya dakatar dashi "Ka ɗaga tafiyarka zuwa Lagos sai bayan ɗaurin aurenka, kuma ka tabbata ka raba invitation cards ɗin da na ba ka.
"To! Daddy.
AB ya faɗa tare da buɗe ƙofa ya fita ya nufi ɓangarensa yana tafe yana haɗa hanya baisan har sai yaushe ne zai fita daga matsalolin rayuwa ba?" kullum daga wannan sai wancan, al'amurran sa sai daɗa taɓarɓarewa suke yi tun daga ranar da yasan Daddy da Umminsa ba su bane suka haife sa ba ya yi bankwana da farin ciki walwalarsa ta koma ƙunci, damuwa ta mamaye dukkan jin daɗinsa, baƙin ciki ya maye gurbin farin cikinsa. Yana tura ƙofar parlornsa idanunsa suka hasko masa Sadiya zaune ta harɗe hannuwanta a ƙirji ta yiwa ƙofar shigowa kur da idanunta, tana dubi ta inda zai bullo. Ganinta a zaune cikin parlornsa ya haifar masa da wani kalan baƙin ciki ya rasa ya ake so ya yi da rayuwarsa.
Rai ɓace ya tako zuwa tsakiyar parlorn ganinsa da ta yi yasa ta miƙewa tsaye jikinta har wani rawa yake yi ita kaɗai tasan irin azbtuwa da take yi da soyayyar yayan nata, soyayyarsa tana neman ta kaita a wani mataki mai matuƙar wahalar fassara wa. Kafin ta yi magana ya rigata ta hanyar furta "Me kika shigo yi a bangarena ke miyasa ba ki da tunani da baki san right time da ya dace ki shigo part ɗina ba??
"Ka yi hakuri yaya Abba na kasa samun natsuwar zuciya, idanuwana kai kaɗai suke da bukatar gani ruhi...
"Will you shut up!
Ya katse ta a hassale ransa na masa ƙuna ya cigaba da faɗin "Ya kamata ki iya gano wa Sadiya babu so irin wanda kike marari a tsakanin mu ban taɓa miki wani kallo na daban sama da na ƙawata wacce mu ke uba ɗaya, kuma bana tunani sauyawar hakan koda anan gaba. A shawarce ki yi gaggawa cire ni daga zuciyarki domin ƙanwarki Aydah nake so kuma ita zan aura, saboda haka ki fitar min a parlor banaso gani ki ko kaɗan Sadiya.
Ya ƙarashe magana yana wani kalan huci. Mutuwar tsaye Sadiya ta yi tare da runtse idanunta maganganun sa sun yi mata nauyi a zuciya sai faman fizgar numfashinta take yi a hankali ta shiga buɗe idanun nata akan kyakkyawar fuskarsa da take hana mata sukuni hawaye kawai ke zuba daga idanunta cikin rawar murya ta ce "zuciyata ba za ta iya jurar rabuwa da kai ba yaya Abba.
"Ni kuma zuciyata tana ga Aydah.
"Uhm! Yayanmu kawai faɗa kake yi domin kana gani ta hakan ne kaɗai za ka iya ƙonamin rai, amma ni nasan babu Aydah a zuciyarka Rumaisa madawaki kake so ba Aydah ba.
"Tun da kin san da haka me zai hana ki shafa min lafiya ki fita daga sabga ta dan Allah.
Ya ƙarashe magana tare da haɗe hannayensa wuri guda Abba mutum ne bayaso tashin hankali ko kaɗan, shiyasa yake ta lallaɓa Sadiya.
"Ba zan iya ba yayanmu da ace za a bani dama a rayuwata na canza abubuwa, bazan yi kasa a gwiwa ba wurin ganin na zabe ka a matsayin mai sarautar zuciyata. kasan irin son da nake maka kuwa? Banta ba tunanin zan so wani ɗa namiji kamar yadda nake son ka ba yaya Abba. Daga Aydah har Rumaisa ba wacce za ta iya ba ka farin ciki koda rabin kwatakwacin wanda ni ɗinan na tanadar maka dashi, yayanmu wallahi zan jiyar da kai daɗi irin wanda babu macce da ta isa ta jiyar da kai shi a shimfiɗarka zan koyi kalolin sarrafa namiji a shimfida duk don saboda kai zan zame maka tamkar sex machine ka juya ni da duk kalolin styles ɗin da kake so ba zan maka ƙorafi ba ko na nuna gajiyawa ba.
Cikin kaɗuwa AB yake kallon Sadiya ya ma rasa me zai mata domin ta shammace shi matuƙa bai taɓa tunani fitar waɗannan manya-manyan kalamai daga bakinta ba. Ya kasa yarda ƙanwarsa Sadiya ce tsaye a gabansa tana ikirarin cewa za ta sarrafa shi a shimfiɗa wannan wane irin lalatatcen zamani ne Allah ya kawo mu, yanzu kamar Sadiya as her age tasan yadda ake jiyar da ɗa namiji daɗi. Zuciyarsa sai bugawa take yi har ta zarce ƙa'ida wani deep breath ya ja yayin da tsikar jikinsa ta mimmiƙe a hankali yake furta "Hasbunallahu wal-imaal wakil! Ya furta ya fi a kirga kafin ya ji natsuwarsa ta fara dawowa a jikinsa idanuwansa dake ciki da wani irin fushi da ɓacin rai ya sauke akanta kafin cikin tsawa da hargowa ya ce "Na godewa Allah da ya bayyana min da ko ke wacece Sadiya, nagode Allah da nuna min asalin halayar ki ko kaɗan ba ki cancanci natsetse namiji kamata ba. Na tsare mutuncin kaina ban taɓa ketare iyakokin Ubangiji ba. Shiyasa Allah ya kawo ƙarshen aurena dake ki sani ko daga ni sai ke kaɗai muka rage a duniya ba zan taɓa aurenki ba. Ki yi gaggawar barmin parlor kafin na yi miki wulaƙanci da ko kare ba zai ci ba.
Da sauri ta matsa kusa dashi sautin kukanta ya ƙaru "yayanmu dan Allah ka fahimci inda kalamai na suka dosa wallahi-azim abunda kake tunani ba shi bane ba..
"Don't take my quietness for granted Sadiya just do what I say get out of my setting room, I don't want to see your feet ever again in my apartment.
Da sauri ta zube guiwayoyinta gabansa tana gunji kuka "Yayanmu karka yi min haka wallahi kaine rayuwata idan na rasa ka komai zai iya faruwa dani a wannan duniyar da muke ciki sonka zai iya jefa ni a cikin mayuwaci hali, koda za ka datse numfashina amma ba zan fasa furta maka kalmar ina sonka ba inason kasan wani abu guda ɗaya, duk halin da zan shiga ko za ka shiga ba zai sa na daina maka irin son da nake maka ba.
"Mtss! To shi kenan tun da ba za ki fata min a parlor ba ga ki nan gashi ki yi ta zama har a busa ƙaho, banza heartless.
Ya ƙarashe magana tare da nufar master bedroom ɗinsa a fusace ya datse ƙofar da key, ƙirjinsa na masa wani irin zafi ajiyar zuciya ya sauke ta ya fi a kirga ga baki ɗaya rayuwarsa ta dawo abar tausayi duk ya ta'allaka wannan masifar da yake ciki akan mahaifiyarsa data haife data jifar miyasa ma ta haife shi ba ta zubar dashi ba tun da ya zama unwanted child kamata ya yi ta kashe shi tun yana ciki da yanzu duk bai haɗu da waɗannan masifun ba. Duk dauriyarsa sai da ya zubar da hawaye sannu-sannu yake rera kukansa mai ƙaramin sauti kansa ya dau zafi ji yake tamkar zai yi hauka, baki ɗaya abubuwa sun kwace masa ya rasa ina zai jefa kansa ya ji daɗi duniya ta yi masa ɗaurin goro ji yake kamar ya tashi ya haɗa kayan sa sai dai a waye gari a nemi sa arasa, sai kuma idan ya tuna da tafiyarsa za ta cutar da mutane da yawa musamman Daddy da Aydah sai ya ji jikinsa ya yi bala'in sanyi kwarin gwiwarsa ya fice. Daren rana gaba ɗaya ya raya shi ne yana miƙa kukansa a wurin Ubangiji sammai bakwai, da safe kaitsaye ya wuce office batare da ya shiga ɓangaren Mami ba.


#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.






Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/18/2023, 10:31 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU






*AREWABOOK*: Jeddah 3256


#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels


29..


Sosai Mami tasha mamakin fitar da Abba ya yi office batareda ya shigo bangarensu ya gaisheta kamar yadda ya saba. jiya da tunani da fargaba ta kwana dan ko a fuska Daddy bai nuna mata sun yi maganar da Abba akan mayar da aurensa da Sadiya. ga baki ɗaya cikin damuwa take da zullumi tasan mijin nata koda ya yi magana da Abban ,da matuƙar wahala ya faɗa mata shima Daddy a daren ranar yana kallon yadda mami take sai mutsu-mutsu kurum take ita ɗaya.
Juya mata baya kawai Daddy ya yi ya ci-gaba da baccin sa cikin natsuwa.
A can kuma kasan ransa damuwa ce sosai yana mamakin yadda son kan matar tasa ya yi yawa da alama ita abunda Sadiya ta yiwa Abba bai dame ta ba, domin da ya dame ta ba za ta bijiro masa da zance a mayar da aurensu, duk mutumin da ya nemi ya salwanta maka rayuwa abin gudu ne. Har Daddy ya yi shirin fita office bai kula Mami ba haka zalika magana kwakwara ba ta shiga tsakanin su ba. A haka ya yi mata sallama ya fice daga gidan acikin dinning area Siyama ta samu mami kana kallon yanayinta kasan tana cikin damuwa
"Mami wai bakida lafiya ne kwanan nan sai nake ta ganinki wani iri?" Siyama ta faɗa da muryar damuwa yadda ta yi maganar itama ya nuna ta nuna damuwarta sosai akan lamarin mahaifiyar ta ta. Mami ta kalleta tana faɗin."ke kaɗai za ki shiga makaranta ne ina Sadiya ne?
"Mami yau banda lecture zan dai je wanki kaine yaya Sadiya kuma ban sanar mata ba tun da kika ga ta kai haka tana bacci ba fita zata yi ba. Mami ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin ."Allah ya tsare hanya.
Siyama ta amsa da "Ameen! Ficewa ta yi daga parlorn tana gyara veil ɗin abayar da tayi rolling kanta dashi. Mami kitchen ta shige tana faɗawa mai aikinta idan ta gama gyara kayan miyan ta fito da wake ta gyara sai tayi musu awara tun da ta iya, Aydah tanata maganar ayi masu awara,mai aikin ta amsa da to Mami ce tsaye a ƙofar ɗakin Sadiya tana ɗan buga ƙofar gami da kiran sunanta shiru ta ji da haka ta juya ta nufi nata ɗakin wayarta ta ɗauka dake kan mirror dressing tayi dialling lambar Abba, ga mamakinta wayarsa a kashe
bata yi wani mamaki ba dan tasan halin Abban, zai iya aikata fiye da haka wani murmushin takaici Mami ta saki ta lura yaron nan so yake ya yi wasa da hankalinta daga shi har mai daure masa wato Daddy, wannan karon sai ta nuna masu ainihin wacece ita wallahi ko zata yi yawo a tsirara Abba ba zai auri Aydah ba. kusan ƙarfe goma sha biyu har da rabi Sadiya ta fito daga ɗakinta cikin shirinta na zuwa makaranta kallo ɗaya zaka yiwa idanunta kasan tasha kuka har ta godewa Allah saboda kumburar da suka yi dan haka ta boye kwayar idanunta cikin glass ɗin frada ta yadda ba za ka iya kallon kwayar idonta kai tsaye, Mami ta sama a ɗaki tun da daga sama har ƙasa Mami ke kallonta cire baƙin glass ɗin da ta mannawa, suna haɗa ido da Mami sai da ta wani kalar zaro ido a rude take faɗin "ke me ya samu idanunki haka?"rasa ma me zata cewa Mami tayi dan ko kaɗan bata son tuna baƙaƙen maganganun da AB ya faɗa mata daren jiya dan hauka ne kawai bata yi ba."mami zan shiga makaranta idan na dawo zamu yi magana.
"Kina cikin wannan yanayin kike maganar wata makaranta.
"Mami pls! Sadiya ta faɗa da rauni a muryarta da gaske ko magana bataso yi saboda yadda kanta ke wani irin ciwo, Mami ta tako zuwa gabanta da car key ɗin motarta ta miƙa mata tana faɗin."ki je da mota na da dare zan yi magana da Daddynku shine ya haifar min ku ko Abba,wata nawa da ya kwace keys ɗin motarku ya kamata ya ba ku abinku haka tunda bada kuɗinsa aka siya ba.
Na gaji da ganin ya'yana suna gantali acikin adaidaita sahu sai kace wasu marar gata.
Ita dai Sadiya juyawa kawai ta yi ta fice daga ɗakin na Mami tun a hanya ta yi dialling lambar ƙawarta saratu wacce suka mayar da sunanta (sarah )yar asalin jahar taraba ce Sarah irin mutanen nan ne wayayyu gaske wanda suke da wani irin freedom suna cikin 'ya'yan da idan suka zo karatu wani gari suke yin fatali da tarbiyyar da iyayensu suka ɗora su akai, wanda a tunaninsu idan basa gaban iyayensu duk ta'asar da suke son yi zasu iya yi batare da duba da me gobensu za ta haifar musu ba.
Sarah babu kalar kayan mayen da bata sha haka ma maza tana hurda dasu sosai. Babu yarda AB bai yi da Sadiya ba akan ta daina ƙawance da Sarah da yake tun fil'azal Sadiya kunne ƙashi ne da ita sai tayi fatali da umarnin yayan nata.
"Sarah kina hostel ko kin fita gantali ki?"Sadiya ta faɗa bayan Sarah ta daga wayar "Ina hostel sai zuwa anjima kaɗan zan fita saboda ina da appointment da wani ɗan majalisa me ya faru na ji muryarki wani irin?"
"Gani nan ƙarasowa maganar ba zai yiwu a waya ba. Da haka ta katse kiran. Ta mayar da hankalinta sosai akan driving tana kissima da tana ganin Rumaisa yanzu akan titi zata iya bin takanta da mota saboda yadda ta tsaneta. Tun da ta shigo cikin ɗakin bata cewa Sarah komai ba kwanciya kawai ta yi akan bed ɗin dake cikin ɗakin.
Tana fitar da numfashi da sauri da sauri wani irin kunci take jin kanta a ciki ga baki ɗaya duniyar ta yi mata zafi, jin har lokacin taki magana
yasa Sarah ta zo ta zauna gafda ita tana ƙarewa yanayinta kallo a hankali Sadiya ta miƙe zaune ta saka bayanta kan pillow sai lokacin ta cire glass ɗin da ya mamaye rabin fuskarta idonta cikin na Sarah da take kallon fuskarta harma da idanunta. cikin rawar murya Sarah ke faɗin."ke lafiyarki kuwa?"Kinga idanunki!
"Ina cikin matsananciyar damuwa Sarah ki bani shawara na tabbata ƙwaƙwalwata tana gafda tabuwa.
Ta karasa maganar muryarta na wani irin hardewa, anan kuma ta soma bai wa Sarah labarin mutuwar aurenta dan koda wasa bata taɓa gayawa ƙawayen nata wai sun yi divorce ita da yaya Abba. Cike da tashin hankali Sarah ke faɗin."kuma mahaifin naku ya rasa wacce zai aura masa sai autarku wannan 'yar mitsiyaya yarinya yaushe za ta iya ɗaukar ƙato irin yaya Abba? inama laifin Siyama, kai gaskiya Daddyn nan naku bai yi ba Sady-B ni yanzu nama rasa wane kalar tunani zan yi ya kamata dai ki fara samun bacci dan yanzu baki da natsuwar da zamu yi magana. Duk wanda ya kalle ki zai san you're suffer from depression dole sai kin ɗan sami bacci ko da kaɗan ne da haka sarah ta dauko wata bag ta zuge bag ɗin ta fitar da wata kwalba ta kalli Sadiya da murmushi cikin fuskarta tana faɗin "yanzu dai ki shanye duka wannan haɗin Insha Allahu baƙaƙen maganganun da Abba ,ya faɗa maki tuni zasu fice miki akai ke baza ki masan wannan na musamman bane yana da dandano sai kin shanyesa

21 / 80