Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   78 / 80

231K to 234K   out of 237.2K words

zare hular kansa kalar aikin jikin shaddar, as usual sai ƙamshi tsadadden turarensa yake. Ya yi bala'in kyau tun da ya shigo Aydah ta tsinci kanta da faduwar gaba ba inda ya baro Abbanta, abu gudu Ab zai gwada masa kuruciya amma komai nasu iri ɗaya ne kamar tasu har ta ɓaci kamar an tsaga kara. Yadda Aydah ta saki baki da hanci tana kallonsa ba ko kyaftawa yasa shi sakar mata murmushi don ya gama gano abun da take kallo saboda hotunan Ab da aka nuna masa shi kansa yaga yadda suka yi bala'in kama "innalillahi wai'inna illahim raji'un! Hatta da murmushin su iri ɗaya.
Aydah ta faɗa a bayyane wanda ita a tunaninta cikin zuciyarta ne ta yi magana batasan cewa a bayyane ta faɗa ba sai da ta ji sautin murmushin Aliyu na Uku yana faɗin "Kai my daughter yaushe za ki haɗa murmushina da na mijinki bayan kisan na fisa iya murmushi ke fa da bakinki kika gayamin bai cika dariya ba sai in tayi masa daɗi ni kuma koda yaushe fuskata cike take da fara'a.
Wata irin mashahuriyar kunya ce ta lulluɓe Aydah, tai sauri zamewa daga kan kujerar da take zaune akai ta durƙusa ta gaishesa "Ina kwana Abbu?"
"Ina kwana my daughter hope kin tashi lafiya ya jikin ummin taki?"
"Jiki al-hamdullilah! Don kuwa har ta yi wanka breakfast ma take yi yanzu.
"Ma shaa Allah! Allah Ya ƙara mata lafiya ya tashi kafanɗunta.
"Amin Abbu!
Aydah ta faɗa idonta na cikowa da ƙwalla domin ta ji irin cutar da ke damun Maysun ɗin da kuma wa'adin da likita ya faɗa akanta.
"Sababul khairi Abu Azhar.
Maysun ta faɗa idanunta akan fuskarsa murumshi ya sakar mata tare da karasa kusa da ita ya ɗago fuskarta yana kallon tsakiyar idanunta "Sababul khairi oum Azhar ya jikin naki akwai inda yake miki ciwo na kira likita ya duba ki kafin na wuce Gombe??"
Girgiza kai ta yi tana faɗin "A'ah! Bana ji komai kuzarin jikina ne kawai bai dawo ba shi ma nasan sannu a hankali zai dawo ka gaishe min da Safiya ka bata haƙuri a madadina, ka kuma roka min alfarma a wurinta da ta zo mu ga juna kamin na mutu.
Da sauri ya rungume ta yana bubbuga bayanta zuciyarsa tana masa wani irin ji yake da ba a gaban Aydah yake ba da abun da zai hana masa taya Maysun kukan da take yi, da sauri Aydah ta tashi ta fice waje zuciyata ba za ta jure kallonsu a haka ba koda ta isa parking lot kuka ya ci karfin ta a jikin wata mota ta kifa kanta tana shasshekar kuka.
Aliyu na Uku ya ɗauki dogon lokaci yana rarrashin Maysun tare da nuna mata rai fa da mutuwa duk na Allah ne sau nawa mai lafiya zai mutu ya bar mai ciwo, da zarar ya dawo zai kai ta India akwai kwararrun likitoci da suka kware akan cuta irin ta, ta wani murumshi mai ciwo Maysun tai masa cikin raunatacciya murya ta ce "kada ka wahalar kanka Abu Azhar mutuwa dole ce koda da cuta ko babu dole wata rana sai mun mutu kawai ka cigaba da yi min addu'a mutuwata ta zo min cikin sauki na tafi cikin salama.
Aliyu na Uku ya ji zuciyarsa ta karye duk yadda ya kai da jarumta sai da kuka ya kubce masa, sosai yake kuka yana ƙara matse Maysun a ƙirjinsa "Kada ki tafi ki barni Maysun ina ji a jikina Azhar yana raye bai mutu ba ko jiya nayi mafarkinsa yana faɗamin zai dawo gare mu. Idan kika tafi wa zai kula mana dashi ki sani Azhar yana bukatar mu a tare dashi.
"Ubangijin da ya ba mu shi lokacin da ba mu yi tsammani ba ya kuma raba mu dashi a lokacin da yake da watanni biyar a duniya ya kuma hada shi da iyayen nagari suka raini shi cikin da so da kauna na tabbata idan har yana raye za su cigaba da kulawa dashi.
Sosai kalamanta suka kayar mai da zuciya ya ji ba zai iya cigaba da zama a ɗakin ba saboda rauninsa ga baki ɗaya ya gama bayyana, ya sumbaci forehead ɗinta ya juya da sassarfa ya fice daga ɗakin. A parking lot ya tarar da Aydah, tana ganinsa tai sauri goge hawayen fuskarta ta kakkalo murmushin dole tai masa daga shi har ita idanuwansu sun jajir alamar sun yi kuka.
"Har ka fito Abbu?"
Aydah ta tambaya tana kokarin ɓoye damuwarta.
"Eh! Daughter zan tafi Gombe wajen ɗayar mamar ta ku, ki kula da ita sosai idan kin ga jikin nata yana so tashi ki yi gaggawar kiran likita.
"To Abbu in shaa Allahu zan kula Allah ya tsare ya kai ka lafiya.
"Amin my daughter!
Ya yi magana tare da shiga mota Kabir Umar ya ja sa zuwa airport. Aydah kuma ta koma ɗaki wurin Maysun hira Maysun take ta faman jan ta da ita har sai da taga ta saki jikinta.
*MASARAUTAR KUDU*
A yau kuma suka tashi da mummunan labari na mutuwar Kilishi, tuni 'ya'yanta na nesa da kusa sun iso masaurata aka yi mata sutura kamar yadda addini ya tanadar aka kaita gidanta na gaskiya, kana aka ci gaba da zaman makoki. Ciroma ya fi kowa shiga tashin hankali duk da matsayinsa kuka ya dinga yi Ahmadu ne ya dinga rarrashinsa.
Ta ɓangaren mai babban ɗaki ta ji sauki sosai sai dai a yanzu bata iya taka ƙafafuwanta, bayan an sallame ta daga asibiti yaya Gimbiya ta dawo da ita gidanta tana cigaba da kula da ita. Da mai babban ɗaki ta yi zaune tai nazari akan Aliyu sai tai masa uzuri duk da tasan wani bangare yana da laifi na ɓoye musu babban al'amari irin wannan da ya yi amma a matsayinta na uwa sai tai masa uzira, tun tana asibiti take zancensa ta ce Magaji ƙarami ya kira mata shi yayin da yaya Gimbiya da Gimbiya Hauwa suka yo mata caaa! Suka hanawa Magaji ƙarami kiran nasa har yaya Gimbiya tana faɗin idan har mai babban ɗaki ta kafe lallai sai Aliyu ya zo to ita za ta bar asibitin ɗin don bata ga amfani da Aliyu zai mata bayan duk irin abun kunyar da ya jawo musu. Mai babban ɗaki tana ji tana gani yaya Gimbiya da Gimbiya Hauwa suka hana ta magana da ɗanta. Ga magaji ƙarami daman can Allah ya dora masa tsoron yaya Gimbiya yasan halinta har yanzu bai wuce duka a wurinta ba, shi mutum ne mai sanyi hali bayaso hayaniya shiyasa ya bi su a yarda suke so don kawai a zauna lafiya ba don haka ba shi ma Aliyu yana cikin ransa.
Misali ƙarfe 12:44pm Aliyu na Uku ya isa masauratar Gombe sai da ya fara zuwa fada ya kwashe gaisuwa wurin yayan Safiya mai martaba sarki Haroon wanda ya kasance yaya ga Safiya. Daga nan ya nufo gidan mahaifiyar ta, ko kaɗan ban tsammaci kyakkyawar tarba daga gare su ba duba da irin girman laifinsa a wurin 'yarsu amma sai yaga sabanin tunanin nasa hatta da Safiya sai nan-nan take dashi bini-bini ta sakar masa tattausan murmushi bayan sun kebance ta dube shi cikin sanyi murya ta ce "Abbu duk ka bi ka rame dan Allah ka rage saka damu a ranka kada hakan ya shafi lafiyarka.
Ƙasa da murya ya yi ya ce "I'm sorry Safiya ban kasance mai adalci agare ki ba ka yi haƙuri ki yi min afuwa a wancan lokaci ina tunani irin abun da zai faru idan na faɗi aurena da Maysun sai dai duk abun da na yiwa gudu a wancan lokaci shi ne ya faru a yanzu.
Cigaba da rarrashinta da daddaɗan kalamai ya yi har ya bata labarin abubuwan da suka faru mutuwar Azhar da halin da Maysun take ciki, sai ga Safiya tana sharɓe hawayen tausayin mijinta abun ka da mace mai haƙuri da hangen nesa nan take ta yafe masa ta kuma yi masa alƙawari gobe za ta bishi su tafi Kano ɗin.
"Har yanzu ban sami wani labari akan Anaal ba bansani ba ko ta kira ki a waya ni dai ko kira ɗari zan mata bana samun ta a waya?"
Numfashi Safiya taja ta sauke tana ɗan murmusawa ta ce "Tana lafiya ko yau da safe ta kira ni.
Cike da mamaki ya furta "Ta kira ki fa?" To ni kuwa laifin me na yiwa Anaal da za ta ƙi kirana a tunaninta ita kadai ce bana iya ɓoyewa halin da nake ciki, hatta da mai babban ɗaki ban gayamata labarin Maysun ba amman ita Anaal tuntuni na sanar da ita. Bani da wani abokin shawara a rayuwata sai Anaal haka zalika ita ma bata ɓoye min komai nata, wannan shi ne karo na farko a rayuwarta da ta boye min abun da ke faruwa da ita. Jikina ya bani tabbas da akwai wani gagarumin al'amari da take kainta Kano. Ko kin san me take yi a Kano Safiya?"
Aliyu ya ƙarashe magana fuskarsa na nuna tsananin damuwa da ɓacin rai, Safiya cike da kulawa ta kama hannunsa ta haɗe da nata ta kalle shi tana faɗin "Karka yi fushi da ita Abbu Anaal yarinya ce mai matukar biyayya agareki ta kasance tana son farin cikinka fiye da komai da kowa, duk abun da za ta yi kaine abu na farko mai muhimmanci agareta, ni kam iya tsawon rayuwata ban taɓa gani uba da 'ya irin kai da Anaal ba. Wasu 'ya'ya sun fi so iyayensu mata amma ni tuni na dade da sani Anaal ta fi sonka akaina ta fi ƙaunar farin cikinka akan nawa, ita ɗin fura ce mai matuƙar daraja muddin tana raye ba za ta kasance mai share maka hawaye. A duk sanda nai mata ƙorafin aure ba zan manta da kalaman a koda yaushe take faɗa ba Ummi ba aure ne banaso ba, ba kuma masu sona na rasa ba, ummi tausayin Abbuna nake ji idan na yi aure dole ragamar kula da mijina zai dawo kaina, taimakawar da nake yiwa Abbuna a kasuwancinsa zai ragu, da zarar kuma na haihu na fara tara yara shi kenan nauyi ya ƙara yi min yawa, gashi ni ce koman Abbu bashi da wani ɗa da zai taimaka masa twins basa son aikin kamfani shiyasa basa maida hankali, na tabbata da zarar na bar kamfani su ma tafiyar su za su domin suna zaune a kamfani saboda ni ba wai dan suna ji daɗinsa ba. Ga Amal da Amatullah yanzu suke tasowa kuma kowacce su tana da nata ambition banaso wahala ta yiwa Abbuna yawa. Dan Allah ki ƙara daga min ƙafa akwai wani babban al'amari da na saka a gaba wanda nake tunani zai taimake rayuwar Abbuna da zarar na cika burina na yi miki alƙawari Ummi zan fito da miji na yi aure.
Tun sanda Safiya ta fara magana Aliyu na uku yake bin kalamanta yana bin su yana ɗora su a mizanin na auna fahimta, sai dai yadda ƙwaƙwalwrsa ta toshe ya kasa fahimtar kalaman Anaal. Washegari Aliyu ya juyo Kano tare da Safiya, koda suka iso hospital ɗin Mami da yaranta dukka suna asibitin kowanne yana ƙoƙarin ganin ya sanya Maysun farin ciki ta hanyar bata labarin yaya Abba, domin shi kadai ne kesa ta farin ciki har ta yi dariya zamansu Sadiya da asibitin ba ƙaramin kawar wa da Maysun damuwa suka yi ba. Shigowar Aliyu na uku da Safiya ya katse musu hirar da suke yi, Maysun da Safiya suka rungume juna tamkar sun shekara da sanin junansu komai cikin ilimi da wayewa suke gudanar dashi, tamkar ba kishiyoyi ba gwanin ban sha'awa wanda hakan ba ƙaramin burge Mami ya yi ba, har ta kudurta aranta za ta zauna lafiya da Huwaila wanda hakan yasa da dare da suka koma gida ta yi wa Daddy zance tarewar Huwaila ta ce ya kamata zuwa gobe ko jibi matarsa ta tare, sosai Daddy ya yi farin ciki yadda Allah ya shiryar masa da matarsa don dama ba ƙaramin so yake wa Mami ba ita ce dai bata zamar masa 'ya ba. Washegari da kanta ta gyarawa Huwaila ɗakunan biyu dake downstairs, ta zuba mata furnitures sababbin da dare Huwaila ta tare. Lokacin da Zeenah ta ji labarin abun da Mami ta yi tattaki ta yi ta zo gidan da zimmar ta zuga Mami sai ga Mami ta bata mamaki dan kuwa zage ta Mami ta yi tass daga ƙarshe tai mata korar kare ta kuma gargadi Balmo maigadi kada ya sake bari ta shigo mata gida.




Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.
[2/11, 2:29 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye.


105.




Sannu a hankali AB yake motsa jikinsa kafin ya shiga ware idanunsa har Allah ya bashi ikon buɗe su dukka, ya bi ɗakin da yake da kallo sai kuma ya shiga tunano abun da ya faru dashi gani ƙafarsa da kansa da bandage ya kara yarda da accident ya yi sai dai wannan ɗakin da yake ko kaɗan bai yi masa kama da ɗakin asibiti ba. A hankali yake furta "innalillahi wa'inna illahim raji'un! Daidai Anaal tana buɗe kofar bathroom ta fito da raguwar ruwan alwala a fuska da hannayenta, sauti buɗe ƙofa yasa shi juyawa da sauri a maimakon yaga Aydah ko Rumaisa ko dai wani makusancin sa, sai ya yi tozali da mss Anaal wanda hakan ba ƙaramin girgiza shi ya yi ba. "Mss Anaal!
Ya faɗa sai dai sautin bai fita sosai ba a dalilin muryarsa da take a dusashe, wani kalar zaro idanu Anaal ta yi kafin kuma ta kalli gabas ta yi sujjudi-shukur duk abun da taka yi Ab bai ɗauke idanunsa akanta ba sai mamaki ke ƙara rufe shi miye alaƙarsa da ita da har za ta kasance dashi daidai wannan lokacin?" Sai kuma ya tuna da korarsa da Daddy ya yi, sai ya lumshe idanuwansa Anaal ta ɗago da sujjadar da ta yi ta nufo wurinsa ta mai ƙara hamdallah ga Ubangiji "Sannu yayana ya kake ji jikin naka?"
"Yayana?"
AB ya furta da madaukakin mamaki iya saninsa da ita da mr Abba Bashir take kiransa dashi miyasa yau za ta kira sa da sunan da ƙannansa Sadiya, Siyama da Aydah ke kiransa dashi.
"Bara na kira Dr Maheer na sanar dashi kyakkyawar labari ka farka bayan tsawon watanni da ka dauka acikin doguwar suma.
Anaal ta faɗa tare da nufar gun da wayarta take ta dauko ta kira Dr Maheer dama ba nisa ya yi ba ya shiga asibitinsa ne kuma asibitin bashi da nisa sosai da gidan. Daf dashi Anaal ta tsaya tana kallon kyakkyawar fuskarsa da yake ta bin ta da kallon mamaki, gani yadda yake kallonta ta sakar masa murmushi ta bashi labarin yadda aka yi har ya zo nan ɗin, kyakkyawar ajiyar zuciya ya sauke kamin ya yi magana sai ga Dr Maheer ya shigo nan da nan ya shiga duba sa yaga komai nasa ya zama normal ya juya ya kalli Anaal dake ta murmushi farin cikinta ya gaza boyuwa ya ce "Congratulations Mrs Maheer m Hamza yayanki ya farfaɗo kuma cikin ƙoshin lafiya ciwon dake ƙafarsa kaɗai ya rage ya ƙarasa warkewa.
"Uhm! Gaskiya Dr Maheer ka cika zumudi duk saurinka dole dai ka jira yayana ya gama dawowa natsuwarsa domin shi ne zai ba ka aurena.
Anaal ta yi magana tana dariya shi ma Dr Maheer dariya ya yi, yayin da maganganunsa suka yi bala'in daurewa Ab kai.
Dr Maheer ya yi musu sallama ya koma asibiti saboda yana da surgery ɗin da zai shiga, bayan fitarsa AB ya kalli Anaal cikin dushewar murya ya ce "mss Anaal na ji kina waɗansu maganganu wanda nake da tabbaci suna da alaƙa dani sai dai ban fahimci komai ba, shin ko za ki ɗaure ki warware min wannan kurman allo?"
Murmushi Anaal ta yi tare da latsa wayarta ta kamu hoton Abbu ta miƙa masa wayar, daman kafin Dr Maheer ya fita ya tashi shi zaune yana jingine da pillow ne ya karɓi wayar idanunsa suka yi masa tozali da wani mutumin mai kama dashi sak kamar an tsaga kara, a matsayin sa na mutum mai cikakken hankali ko bai tambaya ba yasan wannan mahaifinsa idan ba mahaifinsa babu ta yadda za a yi su yi irin wannan kama domin duk tsawon rayuwarsa bai taɓa cin karo da mai kama dashi ba sai wannan mutumin na cikin wayar Anaal ɗagowar da ya yi da zimmar ya tambaye Anaal alaƙar ta da mutumin sai idanunsa suka sauka akan fuskarta da ke yanayi da tasa, hancinsa da nata ɗaya haka zalika shape ɗin fuskarta don kawai ta kasance ta mace shiyasa ya kasa gane kamanninsu ɗaya sai fa yau da ya yi mata kallo a tsanake, wani irin bugawa zuciyarsa ta yi daman duk tsawon wannan lokaci Anaal 'yar uwarsa ce?"
Kamar Anaal tasan tambayar da yake yiwa zuciyarsa sai ta gyada masa kai cikin raunin murya ta ce "Ni ƙanwarka ce Abba Bashir wannan na jikin waya mahaifin mu ne Aliyu na Uku, ni da kai baban mu ɗaya.
Da sauri Ab ya runtse idanunsa ya kasa yarda da abun da kunnensa ke ji masa, gani yake yi tamkar mafarki yake da zarar ya farka shi kenan, ya sake buɗe idanunsa akan fuskar Anaal wacce ke kallonsa tana hawaye.
"Na kasa gasganta abun da kike faɗa Anaal gani nake yi tamkar mafarki ne nake yi.
AB ya faɗa cikin sanyin murya.
"Yanzu kuwa zan tabbatar maka da zahirin gaskiya ta zare wayarta dake hannunsa ta cire airplane mode da take saka ta, ta yi dialling numbern Aliyu na Uku, a lokacin su dukkansu suna zaune a asibiti, har da Alh Bashir wanda shigewarsa kenan Anaal tana kira, Aliyu na Uku yana ganin sunan wacce ta kira sa jikinsa ya ɗauki rawa, ya yi saurin picking "Anaal kina ina faɗamin ina kika shiga shin kinsan irin tashin hankali da nake ciki a bisa rashin sani takamaiman inda kike?"
Kuka Anaal ta fashe dashi cikin muryar kuka ta ce "Albishirin ka Abbu.
"Bana so shirmen banza Anaal ina tambayarki inda kike ke kuma kina min shirme.
Aliyu na ukku ya faɗa ransa ɓace.
"Abbu yayana ya farfaɗo gashi nan zaune yana kallona Abbu ina tayaka murna ɗanka Muhammad Azhar yana raye...
"Me kika ce Anaal?
Aliyu na Uku ka katse ta

78 / 80