Author : EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category : KDP NOVELS
da addu'a. Ni da kai abu ɗaya ne damuwarka nima tawa ce hakazalika farin cikinka shine nawa matuƙar kana cikin damuwa ba yadda za a yi na kasance cikin walwala.
Har ta kai ƙarshen zance ta idanunsa suna a rufe "Safiya ina buƙatar hutawa za ki iya tafiya.
Ya yi magana still idanunsa na rufe.
"Amma Abb..
"Safiya please.
Yai sauri katse mata hanzari a wannan karo ya buɗe idanuwansa suka fara canza launi, jikinta a sanyayye ta miƙe ta baro ɓangaren nasa, ba tun yau ba take ayyana cewa gangar jikinsa ta aura ruhinshi yana wani gun daban.
*RUMAISA MADAWAKI*
Rumaisa ta fito daga cikin gida jikinta sanye da straight gown na lace pitch in color gaban rigar har zuwa ƙasanta an mata beads work, sosai shigar tai mata kyau hannunta riƙe da purse ɗinta wacce tayi match da heel ɗin ƙafarta ɗayan hannunta ke ɗauke da car key ɗinta. Fitar nan da za ta yi za ta je gyaran gashi da body waxing da take zuwa duk ƙarshen wata yadda take tafiya tamkar wacce bata kashi sai wani yatsine fuska take yi ga idanuwanta ta lulluɓe su da sunglass. Ta shiga motarta tare da yi reverse ta fito da ita daga parking lot kana ta daidai motar ta ja ta zuwa gate wanda tuni maigadi ya buɗe mata. Kai tsaye Aj beauty palace and spa ta nufa dama can ake mata duk wani gyaran jiki, tana shiga wurin ta haɗu da old friend ɗinta Aneesa Baffa wacce suka yi karatun sakandare tare tun daga lokaci basu sake haɗuwa ba sai yau da suka haɗu a Aj beauty palace and spa.
Aneesa Baffa kyakkyawar matashiyar budurwa wacce ke ji da naira saboda mahaifinta Alhaji Baffa ya mutu yabar musu tarin dukiya wannan yasa ta fara business ɗinta tana da manya-manyan boutiques na siyar da expensive clothes na mata da maza har ma dana yara Aneesa Baffa she's independent woman wacce ke cin kashin kanta sai dai har yanzu bata yi katari da namiji da take gani ya dace da ita ba duk da tana da farin jini wurin maza. Cike da wayewa ta mata da idanuwansu suka gama buɗewa suka rungume juna ita da Rumaisa daga nan hira ta barke a tsakanin su daga nan suka yi exchange ɗin contact, da yake ita Aneesa har an kammala mata abunda ta zo yi saboda haka suka yi sallama tare da alƙawari kai wa junansu ziyara.
*ALH BASHIR MANSION*
Sosai Sadiya ke rera kuka kaman ba gobe Allah na tuba ko uwarta da ubanta suka mutu iya kukan da za ta yi kenan, wani kololon abu take ji ya danne mata zuciya saboda tsanani kukan da take yi she can't even breathe sai wani irin sheɗewa take yi tasha baƙar wahala kafin ta samu numfashinta ya daidaita a jikinta, she didn't think Hafeez would break her heart like this ta ɗauki soyayya da yarda ta bashi sai gashi ya barta da dafi a ƙahon zuciya, wani kalan mahaukaci so take mishi shiyasa ta kasa karɓa Ya Abba a matsayin mijinta sai gashi tayi biyu babu ta rasa Ya Abba shi kuma Hafeez Sale ya guje ta.
*AYDAH*
Hankali kwance take karanta novel ɗinta duk gun da ya yi mata daɗi sai tai wani lumsashe idanu, tana rausayar da kai kiran sallah magarib ya tashe ta ba don ranta ya so ba ta ajiye littafin sai lokaci ta cire uniform ɗin jikinta ta ɗaura light pink towel ɗin ta ta shiga wanka agaggauce ta fito ta zura plain cotton gown mai gajeren hannu tayi sallah bata tashi ba sai tayi sallah isha kana ta fito main parlor, babu kowa sai mai aikinsu da ta hango a dining area tana arranging table, saboda haka ta wuce ɗakin Siyama tana tura ƙofa Siyama was busy with her laptop turo ƙofar ɗakin nata da Aydah tayi yasa ta ɗagowa Aydah ta ƙaraso ta zauna kusa da ita "me kike yi ne yaya Siyam?"
"Ina ruwanki da abunda nake yi?
Siyama ta faɗa tana mayar da idanuwanta kan laptop ɗin.
Sai da Aydah ta galla mata harara a fakaice ta wani turo baki tare da leƙa screen ɗin laptop ɗin ita a dole sai ta ga abunda Siyama take yi cikin sauri Siyama ta janye laptop ɗin tana faɗin "what's wrong with you?
"I just want to see what you are doing in the laptop ko haramun ne don na ga abinda kike yi?
Wani kallo Siyama ta wulga mata sosai iskanci Aydah ke sauri hasala ta kalli yadda tai mata magana kaman wata sa'anta "Get up and get out of my room before naci ƙarniyarki.
Miƙewa Aydah ta yi tana gunguni ƙasa-ƙasa magana ne take mayar mata, rai ɓace Siyama ta kalleta taga sai da take da ɗan mitsitsi bakinta ko ba tambaya ba tasan maganganu banza ne take faɗa mata "Why don't you respect me, Aydah?, I am your sister ina gaba dake you have to respect me.
"Haba dallah Yaya Siyam sai faɗa kike kina nanata wa sai kace wasu shekaru kika bani masu yawa.
"Iyeee! Aydah yau kuma iskancin naki akaina ya dira?
Kallo sama da ƙasa Aydah ta yi mata hakan ya ƙara harzuƙa Siyama ta zabura ta miƙe tsaye da zimmar idan ta kama Aydah sau ta yabawa aya zaƙinta, Aydah tana ganin yadda ta miƙe ɗinan da gaske za ta iya dukanta saboda haka ta juya da gudu ta buɗe ƙofa ta fita, ita ma Siyama da rashin haƙuri ta biyo ta da gudu suka sakko ƙasa dai-dai Sadiya tana fitowa kitchen hannunta riƙe da mug ta haɗo tea, ta gaji da kukanta na rashin dalili ta fito yunwar da ta dinga naniƙar hanjinta yasa ta fitowa babu shiri sai dai ta rasa appetite babu ɗanɗano ko kaɗan a bakinta wani ɗaci-ɗaci ma yake mata shiyasa ta yi deciding ta sha tea. Sai kuma ga waɗannan rigimammun siblings ɗin nata da basa gajiya da rigima, Aydah da ta zo da gudu bata lura da Sadiya ba tai bala'in bangaje ta mug ɗin hannunta ya subuce ya faɗi kan marbles ya tarwatse tea ɗin ya zuba a ƙafarta, duk dai bai da zafi sosai hakan bai hanawa Sadiya tsandara ihu tana kira ƙafarta sai tsalle take Siyama ta nufe ta, tana ƙoƙari kamata Aydah tana gani yadda jikin Sadiya ke motsawa sai kawai abin ya bata dariya ta fashe da dariyar harda su riqa ciki .a fusace su dukka biyu Sadiya, Siyama suka yi kanta ta sake kwasa da gudu ta fice zuwa compound tana dariya abinta, a bayyane ta ce "Cabdijam! Wallahi yaya Sadiya buhun banza ce dallah kalli yadda naman jikinta ke rawa dama za ta ɗauki shawara ta fara rage fat.
Ta ƙarashe magana tare da kwatanta yadda Sadiyar ke tsalle sai kawai ta sake sheƙewa da dariya. Motar Ya Abba da ta hango yana shigowa ta nufi wurinsa tana ƙoƙarin haɗiye dariyarta saboda tasan halinsa ba kasafai yake son dariya ba.
"Sannu da dawowa Ya Abba!
Ta faɗa sa'ili da ya fito briefcase ɗinsa ta karɓa ya sakar mata yana faɗin "Me kike yi a waje Aydah?"
"Yaya Sadiya da yaya Siyama ne za su yi min duka shine na gudu waje.
Sai da ya ƙare mata kallo kafin ya furta "Hauka suke yi da za su yi miki taron dangi? Ban da mugunta me za su daka anan? Sai dai in kasusuwan ki za su karya.
Ya ƙarashe magana yana nuna jikinta cunno baki tayi "A'ah! Ya Abba bangane ba wannan yabo ne ko zagi?
Murmushi mai sauti ya yi tare da dungure mata goshi "bansani ba.
Ya yi magana tare da nufar flat ɗinsa tayi tsaye tare da bin sa da ido tana kallon yadda yake tafiya cike da izza da ƙasaita a zuciyarta tace "Anya kuwa Ya Abba ɗinan ba daga royal family ya fito ba? OMG! ji tafiya irin na hamshaƙai sarakuna. Tuni AB ya yi gaba yabar ta tsaye tana sambatunta na shirme yana dab da isa entrance ɗin flat ɗinsa ta kwasa da gudu ta cimmasa tana "Ya aka yi yau yaya Abba ka yi saurin dawowa?"
Bai bata amsa ba har sai da suka shiga parlornsa ya ce "Ko na koma ne?
"Ni na isa na ce ka koma.
Ya ajiye wayoyinsa kan centre table yana faɗin "Ki jira ni zan yi wanka.
Ya ƙarasa magana gami da karɓar briefcase ɗinsa dake hannunta ya nufi master bedroom ɗinsa "A fito lafiya!
Aydah ta faɗa tana mai zaunawa akan cushion.
#Love Story 2023/2024
#Jiddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye Novels
#Kurman Allo
Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[11/30/2023, 1:53 PM] Jiddarh Aliyu 2: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
#Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye novels
011.
Daya daga cikin wayoyinsa ta ɗauka wacce ta kasance ita ce babba iphone 14 pro max, ba ta tasha wahala wajen cire code saboda sunanta ne, yawanci dukka pics ɗin dake ciki nata ne, ta shiga nan ta fita nan sai kace ta bashi ajiya a wayar ne. Text message ya shigo daga habibty, ɗan ƙaramin tsaki taja tare da buɗe text ɗin "Habibi ka buɗe Data na tura maka pics ɗin kitso da aka yi min yau ka gani ko ya yi kyau.
"Mtss! Aikin banza tsabar iskanci hatta da kitso tayi sai ta nuna masa.
Aydah ta yi magana a bayyane sai kawai ta buɗe Data ɗin jim kaɗan sai ga pics ɗin sun shigo kusan guda biyar wanda har sun buɗe "mtsss! Ta sake jan tsaki har yafi na farko a dalili kitso da aka yiwa Rumaisa na attachment ne irin gana waving ɗinan ƙanana ya sauka har gadon bayanta, tsabar ɗaukar magana irin na Aydah sai kawai ta yi tagging guda daga cikin pics ɗin ta rubuta "Bai yi kyau ba ko kaɗan saboda ba da ainihin gashinki kika yi ba sai da kika haɗa da gashin doki kuma Allah ya la'anci mai ƙara gashi. Sai kawai ta tura mata tana gani text ɗin ya tafi ta kashe Data ɗin ta ci-gaba da sabgar gabanta.
AB ya fito sanye da farar jallabiya sai zabga ƙamshi yake ya dubi Aydah ya ce "tashi mu tafi yunwa nake ji tun breakfast ban sake saka komai a cikina ba.
Aydah ta tashi da sauri suka nufo flat ɗin Mami koda suka shigo hatta da Mami jiraye take da ita ganinta tare da AB yasa dole suka shafa mata lafiya saboda sun san in har yana wurin ba dakuwa za ta yi ba.
Bayan sun kammala ci abinci AB ya wuce parlorn Daddy saboda tun a kamfani Daddy yace yana so su tattauna magana mai muhimmanci. Bayan ya yi sallama Daddy ya amsa masa kana ya ɗan runsuna ya gaida Daddy, ya nemi wurin ya zauna yana faɗin.
"Daddy ka ce za mu yi magana.
AB ya yi magana yana kallon Daddy wanda hankalinsa ke kan akwatin talabijin yana kallon news.
Sai kawai Daddy ya tattaro hankalinsa ya mayar kan AB "Abba dangane da zance aurenka ne nayi magana da Alhaji Habibu Bichi akwai 'yarsa da ta kammala karatun ta na pharmacy yarinya ce mai cike da nagarta ka shirya gobe idan Allah ya kai mu ka je ku dai-daita bana so al'amari ya dauki dogon lokaci.
Wani irin gumi ne ya karyowa AB a jiki ya kasa furta uffan sai bin Daddy da idanu yake yi, da Daddy ya ji ya yi shiru bai ce komai ba ya kuma san halinsa da kawaici da matuƙar wahala yai mishi musu saboda haka ya umurce shi da ya tashi ya tafi amma ya tabbata gobe ya je sun gana da yarinyar. AB ya baro parlorn Daddy tamkar zai rusa ihu, meyasa Daddy zai kafe lallai-lallai sai ya yi masa aure? Shi ba wani mummuna abu yake yi ba da zai sa Daddy ya matsawa kansa. Tun sanda aka fasa aurensa da Rumaisa aure ya gama fice masa arai Rumaisa ita ce zaɓinsa ita ce mace da yake ganin zai iya zama da ita a karkashin inuwar aure. Da wannan tunani ya dawo bangarensa ya cire jallabiya jikinsa ya hau gado ya kwanta ba don yana ji bacci ba sai don yana ji kaman kwanciya zai iya sassauta mishi halin da yake ciki a koda yaushe yana ƙoƙarin danne damuwar da yake ciki don gani ya farantawa Daddy yasani muddin ya bari damuwar da yake ciki tai tasiri za ta shafi makusantan shi da dama abunda baya fatan faruwarsa shiyasa yake pretending as yana cikin farin ciki alhali azahirance ne kawai amma badilinsa abu ba haka bane. Yana so sanin wani abu da ya danganci asalin iyayensa komai ƙanƙatarsa amma babu hali yin hakan saboda Daddy ya gargaɗe sa akan zancensu. Daren rana AB bai yi bacci ba sai tufka da warwara yake. Shiyasa washe gari ya tashi da wani irin azababben migraine headache, adaddafe ya je sallar asuba yana dawowa ya sake kwantawa sai lokaci ya sami bacci.
Yau trouble maker Aydah an auna arziki ta shirya da wuri, yau su dukka uku za su fita Siyama da Sadiya dukkansu biyu lectures ɗin safe suke da. A parking lot suka rutsa Aydah kowane su da kalan muguntar da yai mata Sadiya ta fara kai mata rankwashi yayin da Siyama ta sakar mata mugun dundu saboda azaba sai da Aydah ta fasa ihu ido ya raina fata har ta isa school tana matsar idanuwa sai tsokana amma babu juriya.
Sai misali ƙarfe 11:00am AB ya falka zuwa lokaci ciwon kai ya ragu sosai agaggauce ya yi wanka ya shirya ko breakfast bai tsaya yi ba ya wuce kamfani saboda yana da meeting da team members (employees) wannan meeting ɗin har da Daddy zai yi attending ƙarfe 11:40am dukkansu sun hallara a conference hall dake cikin kamfanin bayan AB ya gabatar da sabuwar motar da za su kawo bayan dogon bayani da ya ɗauke shi tsawon awannin yana yiwa team members dangane da mota ɗin wani abin burgewa kamfanin su shine kamfani na biyu da zai fara shigowa da irinta a Nigeria, cike da kwarewa ya kammala jawabin nasa, sannan ya zauna nan take hall ɗin ya kaure da tafi da sowa. Daddy sai gyaɗa kai yake yi cike da alfahari kasancewarsa mahaifi ga AB idan ka cire mutane biyu Alh Sanusi da Alh Umar dake ciki hall ɗin kowanne team member za ka hango fuskarsa lulluɓe da farin ciki domin nasarar kamfani nasarar su ce dukka. Bayan an watse daga meeting ɗin a jigace AB ya wuce ofishinsa wani irin jiri ke ɗibarsa bai daɗe da zama ba ya ji muryar Secretary shi Skyler a dai-dai ƙofar shigowa ofishinsa da alama akwai wanda take sa'in-sa dashi, da ƙarfi aka banko ƙofar ofis ɗin nasa ya ɗago yana dafe da forhead ɗinsa "Madam! Madam, I told you that you're not allowed because you do not have an appointment with him, Come back and wait. Lemme ask him first if he wants to meet you.
Duk maganganu da secretary Skyler ke yiwa Rumaisa bai sa ta tsaya ba har sai da ta iso tsakiyar ofishin ɗin na AB alama AB ya yiwa Skyler da hannu ta juya tare da rufu ƙofa ta koma baki aikinta cike da jin haushin Rumaisa.
"What's all this Abba? Na ce menene wannan miyasa za ka yi min wulaƙanci irin wannan?
if you really want to break up with me, you should not follow this way Abba. Sai da ta fesar da wani kalan iska mai zafi daga bakinta muryarta yana rawa ta cigaba da faɗin "I know all this time I was the only one who loved you and you didn't love me ba ka sona Abba ina yaudara kaina ne kawai.
Ta ƙarasa magana hawaye yana bin kumatunta Abba bai ce komai ba sai komawa ya yi jikin kujera ya jinginar da bayansa tare da lumshe idanuwansa yana ji yadda kansa ke wani irin sara mishi kwata-kwata bai san abunda take magana akai ba kuma ko za su kai gobe ba zai iya buɗe bakinsa ya tambaye ta ba. Da ta gaji da masifarta ta nemi kujera ta zauna sun ɗauki tsawon lokaci ba wanda ya yi magana Rumaisa tasan waye AB ciki da wajensa, shiyasa ta saukar da fushinta cikin sanyi murya kaman za ta yi kuka ta ce
"Please Abba, talk to me, why did you humiliate me? Na je na ɓata lokaci aka yi min kitso da body waxing don dai kawai na burgeka ka soni ni kaɗai amma ka rasa kalma da za ka jefe ni da ita sai wannan.
Ta nuna masa wayarta duk da azababben ciwon kan da yake ji hakan bai hana shi bi text message ɗin ya karata take ya gane ko aiki waye.
"Idan ma baka so ina ƙara gashi sai ka faɗa min ta siga mai daɗi sai na daina duk abunda ba ka so Abba duk son da nake masa wallahi zan daina.
Rumaisa ta faɗa tana wani langwaɓar da kai.
"Rumaisa ki tafi gida za mu yi waya,
Ya faɗa kamar mai ciwon haƙora.
"Abb...
"Please go!!
Yai sauri tarar numfashinta ba tare da ta sake magana ba ta tashi ta nufi ƙofar fita tana sharar hawaye tana fita ya sauke naunnayar numfashi.
*MASARAUTAR KUDU*
Alh Aliyu na uku yana gani Hajiya Safiya ta fita ya miƙe ya nufi master bedroom ɗinsa kai tsaye wardrobe ɗinsa ya nufa bangaren da ya ajiye safe ɗinsa ya saka lambobin sirri (code) ya buɗe safe ɗin yana ɗauke da muhimman takardun sa wasu hotuna ya ɗauko ya nufi gefen gadonsa ya zauna hoton farko ya fara ƙurawa idanu na wata kyakkyawar baturiya tana tsaye jikin wata bishiya wacce samanta ke ɗauke da furanni ja da fari tana sanye ne da half blouse pattern gown red in colour rigar da kaɗan ta wuce gwiwoyinta, gashin kanta ya sauka har gadon bayanta, mace ce kyakkyawar gaske wacce kallo ɗaya za ka yi mata ka tabbatar da kyawon nata yakai maƙura. Ya ɓata lokaci sosai yana kallonta yana sauke numfashi a jere kafin ya aje hoton gefensa, idanuwansa suka sauka