Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   44 / 80

129K to 132K   out of 237.2K words

baki ta shiga zuba mata masifa a rikice Mami ta fizge hannunta ta miƙar da ita tsaye hijab Mami ta dauko kasa saka shi tayi, ta ja hannun Sadiya suka fice da sauri parking lot Mami ta nufa da ita ta buɗe front seat ta tura ta kana ta maida murfi ta rufe ta zagaya ta zauna a mazaunin direba ta ja mota Balmo maigadi ya buɗe musu gate "Mami ina za ki kaini ne naga sai sharara gudu kike?
"Gidan ubanki zan kai ki Sadiya shegiyar yarinya wacce ke shirin dauko min bala'i da masifa da suka fi ƙarfina ina zaman zamana kin je ki dauko mana masifa kina tsammani za ki kashe Rumaisa a banza ne wawuyar banza mahaukaciya.
Sadiya ta dafe goshinta sai lokaci ƙwaƙwalwata ta fara aiki daidai tabbas idan Rumaisa ta mutu kashinta ya bushe ita ma dole a kashe ta, domin ita ma Rumaisa tana da gata iyayenta ba za su bar kisanta ya je a banza ba. Nan da nan Sadiya ta fara nadaman abun da ta aikata ta fashe da kuka "Na shiga uku Mami.
"Baki shiga ba tukuna dai tun da ke kin zama daƙiƙƙiya Kwata-kwata bakya tunani da ƙwaƙwalwarki gashinan akan wani shege za ki jefa mu a masifa ke kuma ki kare rayuwarki a gidan kaso.
Jin abun da Mami take faɗa yasa Sadiya ta karawa kukanta sauti Mami tana tafe tana faɗa tare da zagin Sadiya. Unguwar su aunty Safeena suka nufa daidai gate ɗin gidan Mami ta tsaya tayi horn maigadi ya buɗe musu gate sai dab da entrance ɗin gidan tayi parking.






#JEEDDAH ALIYU
#ASMY B ALIYU
#KURMAN ALLO








Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[1/7, 10:22 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels




060.




Mami hankali tashe ta faɗa parlor Aunty Safeena ko sallama ba tayi ba hankalinta ga baki ɗaya baya jikinta tana riƙe da hannun Sadiya,Jamal kaɗai ne zaune a parlorn da waya a hannunsa yana dannawa daga Mami har Sadiya binsu kurum yake da kallo
"Ina Safeena?"Mami ta faɗa tana kallon Jamal da shima kallonsu yake
"Tana sama meya faru Mami?"ya faɗa yana kallon Sadiya da hawayen idanunta suka kasa tsayawa ga jikinta yadda yake rawa bata manta irin azabar na farko da tasha a cell ba.
Zama Mami tayi ɗaya daga cikin kujerun dake zagaye da parlor Mami na sauke numfashi banda bugawa babu abun da zuciyar Mami keyi.
"Kira min Safeena Jamal,ban iya ƙarasawa sama nan."Mami ta faɗa da wani yanayi a muryarta, ba jimawa Jamal ya sauko tareda mahaifiyarsa,Aunty Safeena ta nufi Mami da sauri tana faɗin."Lafiya yaya mariya?"Aunty Safeena ta faɗa tana mayar da hankalinta kan Sadiya da tayi wani irin zuru-zuru ina cikin tashin hankali Safeena, wallahi Sadiya so take taja min masifa ina zaman -zamana na.
Gaban Aunty Safeena na faduwa ta kalli Sadiya a rude take faɗin."me kuma kika yi a wannan karon?"Shiru Sadiya tayi babu magana nan Mami ta shiga zayyanawa aunty Safeena irin aika-aikar da Sadiyar tayi Jagwaf aunty Safeena ta zauna kan kujera tana salati, jin take kamar ta tashi ta rufe Sadiya da shegen duka."a sanyaye aunty Safeena ta kalli Mami,tana faɗin."menene abun yi yaya?"na tabbatar idan iyayen yarinyar nan suka gano Bazasu kyale Sadiya haka ba kar ma su kyaleta a daketa kuma a hanata kuka."Jamal ya faɗa a tsawace
Ya tsani Abba Bashir fiye da yadda ya tsani mutuwarsa tun lokacin da ya dawo hutu gida ya samu wai Aydah ta auresa yarinyar da ya dade da ƙwallafa wa zuciyarsa da gangar jikinsa ita yarinyar da yake mafarkin ta zama mallakinsa a lokacin da wannan labari ya riske shi sai da ya kwanta gadon asibiti ba ƙaramin damuwa ya shiga ba. Duk da haka har yanzu bai fidda ran zai samu Aydah ba tunda mum ɗinsa tayi masa alƙawarin ai Abba zai saki Aydah ba da jimawa ba.mami kallon Jamal kawai take batareda tace komai ba ,
daman daga shi har Sadiya babu mai cikakken hankali kusan tsarar juna suke da Sadiyar babu mai shekara talatin acikinsu "Yanzu mu jira zuwa anjima sai ki koma gida yaya kar ki taɓa nuna kin san inda Sadiya take komai haukar da mahaifinta zai yi miki
ki barta anan,daman ko giyar wake yasha ba zai yadda yazo gidan nan ba.
*BELLO MADAWAKI MANSION*
Raliya Madawaki ce ta fito daga ɗakin mahaifiyarsu kai tsaye ta nufi ɗakin Rumaisa tun kafin ta karasa kofar ɗakin take faɗa tana "ita fa haushinta da Rumaisa idan za'a fita tare sai an bata lokaci sosai idan za'a fita sai ta kwashe fiye da awa ɗaya tana tsaye a gaban mirror dressing tana tsara kwalliyya wannan kwaliyyar yafi komai batawa Raliya Madawaki rai.kai tsaye ta rika handling kofar ta tura kofar dakin
Yanayin da ta samu yar uwar Tata aciki yasa ta saki ihu mai razanarwa da duka gidan sai da ya amsa sai ga Ammi a rude ta karaso tana tambayar Raliya menene?"tun kafin idanunta su sauka akan yar Tata cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa.a rude Ammi ta nufi rumaisa ta wani irin dagowa zuciyarta banda dokawa babu abunda take.a haukace Raliya ta sauka kasa tana kwalawa mai aikinsu kira itama a rikice ta fito kitchen,waya shigo gidan nan waya shiga dakin Rumaisa
Abida?"Raliya ta faɗa a hargitse gaban Abida na dokawa take faɗin."dazun nan wata kawarta Tazo."nan Abida ta baiwa Raliya labari kin taba ganinta ne?"dama kuma tana zuwa wurinta?"da sauri Abida ta girgiza kai ,zata kara yin magana taji mahaifiyarsu na kwala mata kira a rude ta koma sama.
Cike da karfin hali Ammi ke faɗin."taimaka ki kiramin driver yanzu ya taimaka mu kaita asibiti
Da sauri Raliya ta koma,fiye da awa daya likitan da ta karbi case din Rumaisa tana aikin dubata sun tsayarda jinin dake fita ta goshinta da ya tsaga ta hanyar yimata ɗinki ,sai allurar da sukayi mata har dai bata farfaɗo ba,har Alhaji Bello Madawaki ya karaso hospital din ya rufe Ammi da faɗa yana faɗin."suna ina wannan mummunar al'amari ya samu yarsa a shigo gidansa a aikatawa yarsa ta'addanci babu wanda ya sani.har daddy yabar asibitin bata farfaɗo ba haka yayi umurnin daman da ta farfaɗo a kirasa haka ya dauki alwashin koma wanene ya aikatawa Yarinyyarsa wannan ta'addancin sai ya karbi mummunan hukunci.sai wuraren karfe biyar na yamma Rumaisa ta farfaɗo a firgice ta farka tana sakin wani irin ihu marar sauti tana kiran sunan sadiya da dukkan karfinta."da sauri Raliya ta karaso gaban gadon ta rike kanwar Tata tana tambayarta wacece sadiya?"hakama Ammi da ta karaso gaban gadon da sauri cike da karfin hali rumaisa ta shiga yimasu bayanin mai ya faru
Wani uban Ashar Raliya ta saki ta dauki key din mota kai tsaye ta fice daga dakin dan ko sauraran kiran da Ammi keyi mata batayi ba.itama Ammi duk ta shiga mamaki,kai tsaye dama Raliya police station ta wuce ta saka karar sadiya haka aka bata motar yan sanda ɗaya suka bi bayanta zuwa gidan Alhaji Bashir.
*ALHAJI BASHIR MANTION*
Daman Mami awarta ɗaya gidan kanwarta Safeena ganin babu wanda ya kirata har lokacin yasa ta koma gida tabar sadiya a gidan haka tayi mata gargadi da babbar murya akan
Karta kuskura ta baro gidan Safeena sai idan ita ta nemeta kayanta na sakawa da yamma,zata saka driver ya kawo mata sa'annan Mami tabar gidan duk da hankalinta a matukar tashe yake har lokacin,tana ta addu'ar Allah yasa Rumaisa ta rayu kodan rayuwar yarta ya tsira ,har ta dawo gida bata cikin natsuwarta daman koda suka bar gidan Siyama bata gidan sun shiga hidimar bikin kawarta,har wuraren karfe huɗu Mami bata da cikakkiyyar natsuwa duk lokacin da aka kirata a waya sai ziciyarta ta tsinke.har maigidanta Alhaji Bashir ya dawo daga office abinci kawai ta kai masa a bangarensa ta koma ɗakinta ta kwanta har wani sanyi taji yana lullubeta mai alamar zazzaɓi, keso kamata banda bugawa babu abun da zuciyarta keyi.
Tana nan kwance sai sake-sake take yi duk bai fi minti goma da kwanciyarta,taji jiniyar motar yan sanda tare da bugun gate ɗin da ake masu tamkar za'a karya kofar,da sauri ta tashi tsaye ta sakawa kofarta key da mamaki Alhaji Bashir ya nufi cikin compound ɗinsa ya yiwa Balmo Umarnin ya buɗe gate,duk a tsorace Balmo yake jin jiniyar motar yan sanda ya rasa ma ta hanyar da ake bude kofar a fusace Daddy ya karasa ya buɗe gate ɗin Raliya yaci karo da ita da police guda biyu,wata yar sanda macce ce tacewa Alhaji Bashir wajen 'yarsa Sadiya suka zo wacce tayi kokarin kisan kai, innalillah wainnah ilaihir Raji'um! Daddy ya rika maimaita wa cikin girgiza kai da cike da tashin hankali yake faɗin."bayin Allah kodai kunyi batan kai ne?"kuna nufin Sadiya ta?" Daddy ya faɗa cikin wani irin raunin murya,Raliya ta karaso gabansa tana faɗin."Bari dai nayi maka gwari-gwari ta yanda za ka gane nan take Raliya ta zayyana masa abun da Sadiya tayi har cikin gidansu yanzu haka Rumaisa na kwance a gadon asibiti dan 'yan sanda basu zo nan ba sai da suka samu kwakkwarar shaida, Daddy ya daga kai yana kallon Police ɗin dake tsaye har lokacin yace su biyosa, binsa suka yi tun cikin parlor Daddy ya rika kwallawa Mami kira kamar zai tada gidan duka,har ya haura sama yan sanda suka tsaya cikin parlor,Mami tana jin Daddy na kwalla mata kira yana dukan kofar tayi shiru sai da ya daga murya yayi rantsuwa akan idan bata fito ta buɗe masa kofa ba a bakin aurenta,haka Mami tazo ta buɗe masa kofa kallo ɗaya yayi mata yaga alamun rashin gaskiya a bayyane akan fuskarta tunda ya dawo yake kula da yanayinta."ina Sadiya take?
"Tana makaranta.
Mami ta faɗa cike da dakiya,ki fito da Sadiya ko nayi masu Umarnin ke su tafi dake daman kuma idan kika sake suka tafi dake ke da dawowa gidan nan har abada.!"Daddy ya karasa maganar cikin ɓacin rai da kakkausar murya,a rude Mami ke faɗin "Amman kasan haka kawai Sadiya ba zata farma yarinya nan ba.
"Dauko mayafinki.
Daddy ya faɗa mata yana kallon cikin tsakiyar idonta abun da ya take hanga acikin idanun Daddy,a wannan lokacin tasan tsaf yake da tsinka igiyar aurensu babu shiri ta dauki hijab ɗinta na sallah tabi bayansa ,Mami tana fitowa ko kallon Police ɗin dake tsaye cikin parlornta bata yi ba har lokacin suka nufi kofa Daddy,ya kallesu yana faɗin."mu je da mota ta nuna maku inda take da haka suka bi bayan Daddy,babu mai magana acikin su har suka karasa kofar gidan Aunty Safeena har suka tsayar da motocin su fuskar Mami a murtuƙe take
"Ki shiga ki fito da ita.
Daddy ya faɗa sounding so very command!"ficewa Mami tayi daga motar a kitchen ta samu Aunty Safeena suna haɗa abincin dare ita da yan aiki maleeka tazo ta rike Mami tana mata sannu da zuwa,jeki ki kira min momynki maleeka da gudu ta nufi kitchen tana kwallawa mum ɗinta kira babu jimawa ta fito ganin Mami yasa
Zuciyar Aunty Safeena wani irin dokawa."kafin ki zauna ki kiramin Sadiya yanzu ta fito mu tafi."cike da tsoro Aunty Safeena ke faɗin."ta je ina yaya?"cikin dakewa Mami ke faɗin "Police na jiranmu a waje.
Sallati Aunty Safeena ta rikayi da wani irin yanayi ta nufi ɗakinta ta samu Sadiya kwance sai dai ba bacci take ba
Ta mata umarnin ta dauko mayafi
Ita ma Sadiya cike da tsoro ta fito parlor ganin mami kai tsaye Mami ta riƙa hannun Sadiya suka nufi kofa a haka Aunty Safeena tabi bayansu tana kokarin dakar da Mami dabata ma tsaya sauraren ta ba,tsayawa tayi cak!'Aunty Safeena tana kallon Daddy
da ya nufi Sadiya a hargitse mari ya shiga zuba mata hagu da dama yasa kafa yayi ball da ita yana huci sai da yan sandan suka ceci Sadiya da wata irin zuciya Daddy yake yake nuna Sadiya yana faɗin."Ashe ke babbar yar iska kika zama ban sani ba ?"Yaushe kika zama yar ta'addah?"tun da na gano har yanzu baki yi hankali ba ku je gata nan ko gidan yari za'a kaiki bazan tsorata ba,kuma har abada ba zan so ooilnuhymonhbyohnje karbo belin ki ba.idan kin zama gidan kaso ki dawo gida ki karbi hukuncin da zanyi maki bancin wani abu sadiya yau da na tsine maki Albarka."a fusace daddy ya nufi motarsa cikin zafin zuciya ya tada motar ya bade su da kura ya fisgi motar da wani irin gudu,da yasa Mami tabi motar da kallo hawayen idanunta suka kasa tsayawa,nan kuma polisawa suka saka sadiya cikin motarsa suka wuce daita ,dakyar Aunty Safeena ta saka Mami cikin gida da take wani irin kuka mai sosa rai tunda har daddy yace bazaije belin sadiya ba bazai jeba daman kuma daddy ,baya magana biyu."ina cikin tashin hankali Safeena yanzu menene abun yi? Ga Abba su Jamal baya gari,ki natsu yaya musan ta inda zamu bullowa wannan al'amari har akayi sallar magarib Mami da Safeena sun kasa samun mafita.Aunty Safeena ta numfasa tana faɗin."mafita ɗaya ta rage mana yaya kawai Abba zaki kira ki basa umarni ya je ya saka baki a saki Sadiya nasan ai ba zai ki bin umarninki ba "Idan kin san yadda na tsani koda jin sunan wannan yaron Baran tana har naji muryarsa Safeena da baki kawo wannan shawarar ba Allah ya tsare na nemi alfarma a wajensa "kin fiso ta kwana a cell kenan?"kibarta ta kwana din gobe ba zata kara ba, "yaya wannan fa ba shawara bace ni bari na kira Abban
Batareda wani tunani ba ,Aunty Safeena ta kira AB ta faɗa masa tana nemansa yanzu idan babu damuwa.
Yace zai zo nan da minti talatin,da haka ya sauke wayar dan acikin dangin Rumaisa babu wanda ya kira AB har lokacin hakama Daddy,bai kirasa ba kamar yadda ya faɗa cikin minti talatin ya nufi gidan Aunty Safeena a bakin gate ya aje motar da ƙafarsa ya taka zuwa kofar gidan yayi knocking ta karamar kofar maigadi ya leƙo yana ganin Abba ne ya washe baki ya buɗe masa gate yana masa sannu da zuwa Abba ya amsa yana gaishesa daman sun saba da mai gadin,kai tsaye entrance din shiga gidan ya nufa kusan cin karo sukayi da Jamal da yafito shi kuma zai shiga jada baya suka yi suka daga kai suna kallon junansu tamkar wasu zakaru.










#JEEDDAH ALIYU
#ASMY B ALIYU
#KURMAN ALLO






Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[1/8, 9:24 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels




061.


Tsayawa suka yi suna kallon juna kamar wasu zakaru kowanne su fuskarsa tamkar an aiko masa da sakon mutuwa,haka zalika kowanne da sakon da yake tattaunawa da zuciyarsa,a bangaren AB yana tuno kalaman Jamal acikin kunnayensa yaron da ya bai wa tazarar shekaru goma, shi zai kirasa a waya yana datsa masa magana,har yake iya buɗar baki yayi masa gargaɗi gami da barazana akan Aydah har yana faɗin Aydah ta shi ce mallakinsa ce shi kaɗai ko yana so ko baya so dole ya saketa.Kallonsa AB ya cigaba da yi yana ganin shekarun da yaron da ya yi girma akan idanunsa shi ne har yayi zarrar gayamasa magana a mugun fusace Jamal,yabi ta gefensa ya wuce tamkar zai tashi sama. Murmushin gefen baki AB ya saki ya karasa cikin parlor da sallama a bakinsa, Aunty Safeena,kawai ce ta amsa masa Mami ta shiga danna wayar hannunta fuskar nan ta ta a murtuke tamkar ba'a taɓa halittar dariya ba acikin fuskarta, AB ya nemi wuri ya zauna ya gaisheda Mami da Aunty Safeena lokaci ɗaya,
Wannan karon ma Aunty Safeena ce,ta amsa masa shiru ya ratsa a tsakaninsu na kusan sakan goma.
Ganin da gaske mami, bazata yi magana ba yasa Aunty Safeena,ta sauke numfashi tayi gyaran murya tana sauke idonta akan AB ta kira sunansa dago kansa yayi ya mayar da hankalinsa wurin Aunty Safeena.
Kasan meke faruwa kuwa da yar uwarka Abba?"a gaggauce AB yace '"wacce 'yar uwar tawa Aunty??"Aunty Safeena bata boyewa masa komai ba ta yi masa bayani "mun san Sadiya tayi kuskure ka dubi girman Allah Abba ka rufawa kanwarka asiri kar ta kwana a cell yau, duk da girman kuskure da tayi Abba bai kamata yan uwan matarka su dauki irin wannan tsatsaura hukuncin ba, kaga an kusa daura muku aure bakwa gudun bakin mutane da kuma yan jarida da kiris suke jira su dinga yaɗa labarai karya da na gaskiya cike da jimami AB ke faɗin."babu wanda ya kira ni Aunty bara na je yanzu in shaa Allah zan dawo tare da Sadiya, ba zan bari wani abu ya same ta ba.
Ya ƙarasa maganar tare da mikewa tsaye Aunty tayi masa fatan sauka lafiya,a boye Mami ta rika sauke wata irin ajiyar zuciya har AB ya fice daga parlor da sassarfa. Mami ta rika bin sa da wani ɗan iskan kallo ta kalli Aunty Safeena,rai a ɓace "ke kin yarda da wannan karyar da yazo ya gilla miki yaron nan munafuki ne na karshen lissafi waya sani koda haɗin bakinsa aka kai Sadiya cell ɗin.
"Ni wallahi ina mamakin irin wannan tsanar da kike nunawa Abba,yaya mariya wanda ko a mafarki ba zan yarda zaki yi masa wannan kalar tsanar ba jikina wallahi har yayi sanyi ganinsa ya karya min zuciya, daman za mu haƙura mu zubar da makaman yakin mu akan auren Abba da Aydah haka Allah ya tsara masu mu bi su da addu'a kawai.
Saboda takaici Mami ko kallon Aunty Safeena,bata sake yi ba tun a hanya ya rika kiran wayar Rumaisa bata daga ba, lokacin an basu sallama

44 / 80