Author : EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category : KDP NOVELS
rasa sallar juma'a ba. Domin tun yana yaro Daddy baya bari ya yi missing ɗin sallar juma'a sai gashi yau damuwa ta hana masa zuwa.
Tun kafin Abdulkarim ya ƙarasa wurin da aka tanada domin yi parking ya hango motar AB parker a wurin ya nemi wuri ya yi parking shi da Daddy suka fito direct reception suka nufa, da kyar receptionist ɗin ya faɗa musu numbern ɗakin da yake shima sai da Daddy ya faɗa masa AB ɗansa ne fushi ya yi ya baro gida sannan fa ya basu numbern ɗakin.
Da yake AB bai tsaya rufe ƙofar da key ba shiyasa Daddy yana tura ƙofar ta buɗe ya yi tozali da shalelen ɗansa kwance kamar gawa numfashinsa yana fita da kyar ga jikinsa sai kakkarwa yake yi alamar zazzaɓi mai zafi ne ya rufe shi da sassarfa Daddy ya isa kan gadon ya wani rungumo sa "innalillahi wa'inna illahim raji'um! Abba buɗe idonka ga Daddynka ya zo tashi mana yarona buɗe idonka ka ji.
Kaman daga sama AB yake ji muryar Daddy a dodon kunnensa, duk iya ƙokarin sa na so gani ya buɗe idanun nasa ya kasa da sauri Abdulkarim ya fice ya je reception ya nemo taimako mutane. Suka kama masa Ab saboda ga baki ɗaya Daddy ya gama rudewa ya fita hayyacinsa suka saka shi mota direct asibiti Abdulkarim ya wuce dasu suna zuwa aka karɓe shi cikin kankanin lokaci aka bashi taimakon gaggawa har drip an saka mishi sai lokacin Daddy ya fara dawowa cikin natsuwarsa gani AB numfashin AB ya zama normal.
Sai misali ƙarfe 5:15pm AB ya falka da salati dauke da bakinsa wani irin nauyi yake ji a idanunsa Daddy da Abdulkarim suka taso suna masa ya jiki ya amsa cike da jin kunyar Daddy cikin dashewar murya ya ce Abdulkarim ya taimaka masa zai shiga bathroom sai da ya kama ruwa ya yi alwala a zaune ya yi sallar azhar da la'asar da ya kammala sallar kasa tashi ya yi daga wurin sai kawai ya sadda kansa ƙasa, sosai yake ji kunyar haɗa ido da Daddy a natse Daddy ya isa gaban Ab ya zauna ya kama haɓarsa ya ɗago fuskarsa cikin tattausan lafazi yake faɗin "Ba dai jikin bane Abbana?"
Wani irin rauni ne ya mamaye zuciyar AB har bai san sanda ya faɗa jikin Daddy ya ƙanƙame shi ya fashe da kuka kamar ƙaramin yaro "I'm sorry for my bad attitudes Daddy ban kyauta maka ba ni ba yaron kirki bane meyasa zan butulcewa mahaifina mai ƙaunata?"
Da sauri Daddy ya ciro shi daga jikinsa ya rufe masa baki da tafin hannunsa "shhh! Banaso na sake ji ka faɗin waɗannan maganganu akanka. Abba kai ɗa ne nagari abin alfahari iyaye, kai ba butulu bane.
"To amman Daddy ban kyauta maka ba na saka ka kunya sanadin abinda na yi.
"Ba laifinka bane Abba laifin na Mariya ne da ta kasance mace mai kafirin son zuciya a sanadin son zuciyarta tana so ta wargaza min kan iyali ta haddasa min fitina a gidana amma ba komai nasan kalar matakin da zan dauka akanta.
AB ya ja deep breath ya sauke tare da kama hannun Daddy ya ce "Daddy tashi mu je ka cika burinka ka aura min Aydah idan har aurena da ita shi ne farin cikinka Daddy na shirya tsaf zan samar maka da wannan farin ciki koda kuwa ni zan rasa nawa, Daddy ina sonka fiye da komai a duniya nan you're best father in the whole world samun mahaifi kamanka a wannan zamani sai an tona a wasu lokuta ina jin zafi idan na tuna ba kai bane biological father ɗina. Amman ko a yanzu ina godiya ga Allah subhanahu wata'ala da ya bani kai I love you Daddy I love you so very much you're my world I'm nothing without you kaine komai na, na yi alkawari ba zan sake saka ka ɓacin rai ba.
Wani irin kalan murmushi Daddy ke yi farin ciki marar misaltuwa ya cika masa zuciya idanunsa suka cicciko da hawaye Allah ne kaɗai yasan adadin kaunar da yake yiwa Abba jin sa yake yi tamkar wani tsagi na jikinsa. Rungume shi Daddy ya yi yana shafar gadon bayansa yana murmushi sun dauki lokaci a haka Abdulkarim dake tsaye yana kallonsu bai ankara ba ya ji hawaye na fita daga kwarmin idonsa yana ƙara girmama hikima irin ta ubangiji iyayen AB bai buɗe idanunsa da soyayyar mahaifinsa ba sai gashi Ubangiji gwanin hikima ya haɗa shi da mahaifin da yake sonshi kamar rai da numfashi.
Daddy ya yi breaking hug ɗin ya ciro dabino daga gaban aljihun rigarsa ya ɓare ya cire kwallon ya saka wa AB a baki "Abba ci dabino na daurin aurenka da Aydah ne.
Wani mashi Ab ya ji ya dakar masa zuciya sai da ya runtse idanunsa wani irin kunci yake ji a can ƙasan zuciyarsa sai kace ba shi bane yanzu nan ya gama ikirarin Daddy ya aura masa Aydah yanzu kuma ya ya ji tabbatuwa aure nasu sai ya ji ga baki ɗaya duniya ta yi masa nauyi akai. Da kyar ya iya saita natsuwarsa tare da danne abunda yake ji ya kirkiri murmushin dole ya yafawa kumburarriyar fuskarsa, yana tauna dabino tamkar mai cin maɗaci.
Daddy ya dubi Abdulkarim ya tambaye sa likita ya amince su tafi gida da AB? Abdulkarim ya gyaɗa kai so emotional Daddy ya kama hannayen AB ya miƙe tsaye suka fice daga ɗakin.
Lokaci da Hajiya Zeena ta zo Mami ta ja ta suka shige bedroom ɗinta sai da Hajiya Zeena ta ƙare mata kallo kafin ta ce "Bani mu kashe aminiyar arziki kafin na rattabo miki labari da ɗumi-ɗuminsa don ina gani bakida labari haƙar ki ta cimma ruwa.
Cike da gundarin mamaki Mami ta miƙa mata tafin hannunta suka kashe Zeena ta karkace kai ta shiga faɗin "na tabbata ba ki da labari auren Abba da Aydah ya wargaje an fasa babu shi.
"Haba Zeena karki yi amfani da raunina ki dinga wasa da hankalina.
"Wallahi Alh Sanusi ya je min da wannan daddaɗan labari. Ta kwashe duk yadda Alh Sanusi da Alh Bashir suka ji abunda ya wakana tsakaninta da Abba ta faɗa mata ta zarce da faɗin "a gabana ya kira Alh Bashir ya tabbatar mishi Abba dai ya bar gari don sun nemi shi kaura wambai ba su ganshi ba ya yi ɓatan dabo da alama ya ɗauki shawararki.
Farin ciki ya lulluɓe Mami ranta ya yi fari tass! Ga baki ɗaya ta ji matsalolin ta sun warware saboda haka suka buɗe bajakolin hira tana faɗawa Zeena yadda aka yi auren Sadiya da Abba ya lalace wanda daga Zeena har mijinta Alh Sanusi basu da wannan labarin saboda Mami da Daddy sun boye al'amarin ne a tsakaninsu ba su bar wannan maganar ta fita ba saboda kariyar mutuncin su. Sai gashi yau Mami ta feɗewa Zeena daga biri har wutsiya.
Daddy ne ya yi driving ɗinsu shi da Abba zuwa gida yayin da Abdulkarim ya shiga motar Abba ɗin. A parking lot Daddy ya baro Abba da Abdulkarim suna zantawa shi kuma kansa tsaye ya yo bangaren Mami falon tsit babu kowa Sadiya tana ɗakinta tun sanda ta watsa kayan mayenta take tana kwasan bacci sai yamma lis ta falka Siyama kuma bata dawo daga school ba Aydah kuma tana dakinta tun lokacin da Mami ta daka mata tsawa ta shige dakinta ta rufe hatta da lunch yau bata yi ba. Kwance kawai take kamar wacce aka zarewa lakkar jiki, ta kasa fahimtar takamaiman abinda ke damunta. Direct Daddy ya yi ɗakin Aydah ya murɗa handle ya ji kofar a rufe sai kawai ya yi knocking da kyar ta sauko daga kan gado ta nufi jikin ƙofar ta zare key a tunaninta Siyama ce sai ta ga saɓanin tunanin nata "Sannu da zuwa Daddy!
Aydah ta faɗa cikin dashewar murya yadda ta ga fuskar Daddy a haɗe babu walwala ko kaɗan a tare dashi sai tasha jinin jikinta tsoro ya cika mata zuciya.
"Mu shiga daga ciki zan yi magana dake mamana.
Daddy ya yi magana tare da nuna cikin ɗakin nata jiki a sabule ta juya Daddy ya jawo stool ɗin dake girke a gaban dressing mirror ya zauna dole Aydah ta nemi gefen gado ta zauna tare da sadda kanta ƙasa zuciyarta sai bugawa take mata da ƙarfi kaman za ta fasa ƙirjinta ta fado ƙasa.
Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.
Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/26/2023, 2:22 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
*AREWABOOK*:3256
#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels
39..
Sai lokacin Daddy ya kula da yanayinta yadda tayi wani irin sanyi na lokaci ɗaya, "mamana kin kuwa ci abinci?"daddy ya faɗa cike da kulawa yana kallonta da sauri ta ɗago tana kallon daddy, kafin ta girgiza kanta
"To meyasa bakici abinci ba ko wani abu ke damunki."shiru Aydah tayi lokaci ɗaya tana jin maganganun da Mami ta rikayi wanda babu abinda ta fahimta aciki da kuma yadda take hantarar yaya Abba, a yanzu ko kaɗan bata jin daɗin yadda Mami ta zama lokaci ɗaya akan yaya Abba
Sai dai bata san ta inda zata fara yiwa Daddy bayani ba. Dogayen fingers ɗinta ta shiga ja batare da ta furtawa Daddy komai ba."mamana ki bude baki ki yi min magana idan akwai abunda ke damunki."daga kai tayi akaro na biyu idonta na cika da ƙwalla ga zuciyarta da take tsananin bugawa, cikin rawar murya take faɗin."Daddy meyasa Mami ta canjawa yayanmu meyasa yanzu ta daina sonsa?"ta karasa maganar hawayen idanunta suka cigaba da Rolling akan fuskarta wanda ta kasa tsayar dasu. Daddy kallonta yake yana jin wani abu na taɓa mai zuciya bai san Mami tayi nisa har haka ba sai yau da kunnuwansa suka ji masa muguye kalaman da take furtawa akan Abba wanda ko a mafarki bai taɓa tunanin Mami zata yiwa Abba Bashir haka ba.
"Mamana idan na daukeki daga gidan nan na kai ki gidan yayanki za ki yadda?"za ki kula dashi za ki basa farin ciki har karshen Rayuwarki?"shiru Aydah ta yi tana juya maganganun mahaifinta acikin kanta. Kafin cikin rawar murya Aydah ta ce "Daddy tayaya ?"zan zauna daga ni sai yaya Abba a gida daya, na dauka ma'aurata kawai ne suke da wannan hurumin kuma ko a islamiyya ana faɗa.
Shiru Daddy ya yi yana jinjina basira irin ta yaran yanzu kenan kananun shekaru kawai ga Aydah Amman tana da hankalin sanin wasu abubuwa anzo wurin da yake son ya wayar mata da kai ya shigo da maganar da ya shigo dashi ɗakinta. Ahankali Daddy ya riƙo hannunta yana kallon yanayin ta har fahimci wani irin sanyi da tayi lokaci ɗaya . "Mamana idan na haɗa aurenki da yayanki Abba za ki yadda ki zauna dashi har ƙarshen rayuwarki za ki yadda ki karɓi biyayyar da yar uwarki ta kasa yamin
karshe ta watsamin kasa a idanu?"
Kallon Daddy kawai take ta kasa fahimtar me maganganunsa ke nufi
Cikin sarkewar harshe Aydah ke faɗin
"Daddy Aure da kuma yayanmu?"
Ta faɗa da wani yanayi acikin muryarta, ga baki ɗaya ta ruɗe a lokaci ɗaya cikin rarrashi da ban baki Daddy ya fara magana."mamana ba wani ne fa za ki aura ba yayanki Abba wanda kuka tashi gida ɗaya dashi ko sau kike yabar rayuwarmu na har abada kamar yadda mahaifiyarki ke fata?"
Zuciyarta na bugawa ta shiga girgiza kai."ba zan iya jure rashin yayanmu a kusa dani ba Daddy dan
Allah kace kar ya tafi Daddy ka basa hakuri hakama Mami ka bata hakuri ta janye furucinta akansa.
"Mamana dole Abba yabar gidan nan a yau, ba gobe ba kamar yadda malaman makarantarku ke faɗa maku muhimmanci aure a musulunci da sharuddansa nasan kin sani Mamana, shekararki goma sha biyar ko kauye yaran da basu kai ki ba ana yimasu aure kuma su zauna da mazajensu lafiya."Mamana na daura miki aure da yayanki Abba,ya fitar da kudi acikin aljihunsa ya damƙa mata cikin tafin hannunta yana faɗin."ga sadakinki nan Mamana a hannunki Allah ya baki ikon yiwa mijinki biyayya Allah yayi miki albarka
wata irin nasiha Daddy ya rika yimata wanda tunda take a rayuwarta Daddy bai taɓa faɗa mata kalamai masu kashe jiki ba irin wannan hawaye kawai take ta kasa furtawa Daddynta komai to idan ma za ta furta me zata ce masa ta san ba za ta iya cewa wanda ya kawota duniya a'ah ba akan duk hukuncin da ya yanke acikin rayuwarta haka kuma har abada ba zata iya gudun auren wanda ya kwashe shekaru goma sha biyar yana hidima da rayuwarta shine uwarta shine ubanta ta kowanne fanni idan tace ba zata zauna dashi ba a matsayin miji ta cika butulu ,wannan mutane biyu sun sakata a tsakiya kowanne da muhimmancin da yake dashi a kasan zuciyarta tana ganin yadda Daddy ya sakata cikin jikinsa yana saka mata albarka wasu irin emotions ke taruwa a kasan zuciyar Aydah wanda batasan yadda zata fassara su ba,suna cikin wannan jimamin Siyama ta kira mahaifinta a waya, yana dauka ta faɗa masa tagama gyara ko'ina ana gama daura aure Daddy ya canja shawara gara ya nunawa Mami lallai a karkashin ikonsa take bata isa ta juya sa ba anan take ya yanke shawarar yau Aydah da Abba zasu tare a gidansu bikin ma a haƙura dashi tun da ba dole bane kawai zai saka malamai su yi masu addu'a da saukar Alkur'ani za'ayi sadaka kuma Allah ya sanya Albarka acikin rayuwar aurensu.
Nan take ya kira Siyama lokacin tana kokarin shiga lecture na karfe biyu
Yai mata umurnin ta haƙura da lecture ɗin ta wuce gidan Ƴaƴansu ta gyara masa gidansa yau Aydah zata tare, sosai Siyama tasha mamaki, kai tsaye ta cika umurnin mahaifinta nan take ta shiga cleaning clearing gidan duk da sabone komai dake ciki sabone babu abunda aka taɓa amfani dashi na gidan dan haka bata sha wahala ba."Daddy na gama komai to ki dawo gida yanzu ki zo ki taya yar uwarki shirya kayanta bayan magrib zasu wuce kallo kurum Aydah ke bin Daddy dashi har ya gama wayar da yake yi da Siyama ya kalleta yana faɗin."mamana ki jira Siyama gatanan zuwa zata tayaki shirya kayanki.
Ɗagawa daddy kai kurum tayi wani irin zazzaɓi taji yana bin jinin dake yawo lungu da sako na jikinta tsoro da fargaba suka zagaye ta lokaci ɗaya
komai ganinsa take tamkar a mafarki bata taɓa ganin irin wannan auren ba
zan dawo bayan magarib naga kun shirya bayanan Mamana ki samu kici abinci kinji kou?"ɗagawa Daddy kai tayi acikin tana kallonsa da idanunta da suka fara canza launi ya fice daga ɗakin har kuma lokacin Daddy yana jin tashin Muryar su Mami wanda bai san dawa take hira har haka ba.
Abdulkarim ya kalli AB yana kwance akan sofa tunda suka shigo Parlor yake kwance a haka babu maganar da ta haɗasa da Abdulkarim da har ya fita yayi masu oder abinci ya dawo dan yunwa yake ji sosai ko abinci rana bai samu yaci ba, agaban idanunsa Abdulkarim yaci abincinsa
wanda shi ko motsawa bai yi ba da alamar bayada niyar cin abinci."wai kai bazaka ci abinci bane?"ko mai Abdulkarim ya tuna sai kuma ya saki murmushi yana faɗin."Bara na daina yimaka zancen abincin nasan duka tunaninka yana kan amaryarka kana kamanta tunanin yadda wannan daren zai zo maka kai da babynka."
Abdulkarim ya faɗa yana sakin dariyar shakiyanci, tamkar da dutsi yake magana haka AB ya yi masa banza har bayan magarib suna tare
ko kaɗan babu karfi a jikinsa
Daddy ya kira wayar Abdulkarim yana faɗin."sun gama haɗa kayan Abban ne?"Abdulkarim ya fadawa Daddy sun gama, to ku sameni a parlor Abdulkarim ya fadawa Daddy kawai haka babu kayan da AB ya haɗa ko yace a haɗa masa bakinsa kawai zai bata daga baya abunda yake bukata sai ya dawo ya dauka idan kansa ya huce tun bayan sallar magarib da yayi wanka yama kasa saka kayan da Abdulkarim ya dauko masa zaune yake gefen bed yana dafe da kansa da yake masa wani irin ciwo tamkar bai sha magani ba. "Ka saka kayanka Daddy na jiranka shima idan taurin kai za kayi masa sai na sani."wani kallo ya yiwa Abdulkarim yana faɗin."a gabanka zan saka kayan kenan?"girarsa ɗaya Abdulkarim ya dage "To meye aciki ka juya ka saka abunka mana. Cike da izgilanci AB ya soma warware towel ɗin jikinsa da gudu Abdulkarim ya nufi kofa yana faɗin."saboda ka fara shaye-shaye za ka cire towel agabana ."Yana faɗin haka ya juya yabar cikin bedroom ɗin
Bayan tafiyar Hajiya Zeena Mami na zaune a dakinta har bayan sallar magarib gidan yayi mata wani irin shiru sai lokacin ta tuna da Aydah tun safe da tayi mata faɗa bata kara ganin wurgawarta cikin gidan ba hakama Sadiya miƙewa tayi a ɗakin Sadiya ta tsaya tana knocking kofar ɗakinta jin shiru yasa ta bugawa Aydah kofa
dai-dai lokacin Siyama ta buɗe kofar ɗakin tana rike da hannun Aydah da Siyama ta taimaka mata tayi wanka
har kayan da za ta saka ta zabar mata tayi mata simple make up, sororo Mami ta yi tsaya tana kallon ikon Allah gabanta na bugawa dake kallon Siyama tana faɗin."Da taci wannan kwaliyyar ina za ki kaita?"
"Wurin Daddy!
Siyama ta faɗa tana kallon yanayin Mami ,tamkar bata fahimci me Siyama ke nufi ba. Haka Siyama da Aydah suka bar Mami a tsaye har suka fice daga ɗakin tamkar Mami ta tuna wani abu tabi bayansu a wani irin haukace, tsaye tayi a bakin kofar parlor Daddy tana kallon mutanen dake zaune acikin parlor da mugun shock kwance acikin fuskarta,Daddy ya daga kai yana kallon yanayinta
ya sauke idanunsa cikin nata idon yana faɗin."ki karaso daman yanzu zan daga waya na kiraki sai gashi kin karaso.
Anan bakin kofa Mami ta tsaya tana girgiza kai so take kawai taji meye dalilin wannan taron daman AB tunda ya shigo Parlor na Daddy kansa ke a ƙasa ganin bazata