Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   7 / 80

18K to 21K   out of 237.2K words

yafi son 'ya'yansa maza ko sunyi aure su zauna a tare dashi tunda akwai filaye manyya yanka kawai za a yi ayi masu ginin gida irin na sarauta. Duk da a ɓangaren Aliyu shi ba haka yaso ba
Ko kaɗan baya sha'awar komai na rayuwar sarauta, sam bashi da ra'ayi hakan ba haka tsarin rayuwar da ya tsarawa kansa yake ba.
Babu ranar da ba zai tuna ta ba ita ɗin ta zama jinin jikinsa duk iya ƙokarin sa na gani ya nemo ta har yau ɗinan ya kasa samun ta ko sai yaushe zai sake tozali da ita??
Tambayar da yake yiwa kansa koda yaushe kenan.


#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.










Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[11/28/2023, 3:51 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU










#Love Story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels


009


*RUBUTUN YAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU.TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA*



*ALH BASHIR MANSION*


Yau tunda tayi sallar asuba bata koma bacci ba ita ta taya Mami da yan aiki suka haɗa break fast. dama kuma Mami bata yiwa ƴa'ya ta horon rashin son aiki ba. Duk da tana da masu aiki bai sa ta sakankance da cewa yan aikin zasu riƙa yi mata komai ba. Sai ga 'ya'yan nata duka sun biyota da iya girki da son shiga kitchen idan ka cire Aydah acikinsu harta AB tun baida wayau yana taya Mami shiga kitchen indai yana a gida babu makaranta. Aydah ga ta mace sai dai bata aiki da rashin motsa jiki, idan kaji masifar mami a gidan na rashin son aiki to da Aydah ce, indai AB baya gida to sai ta shiga kitchen haka Siyama za tayi rantsuwa ba zata barsu da aiki ba ta taso ko ɓarar magi ne da yanka wani ganye tayi, haka zasu ta faɗa su ce yaya Abba, ya sangarta ta tana yiwa mutane yadda taga dama da anyi magana zai fara faɗin Aydah ai Yarinya ce duka-duka nawa take?" idan yana gida a ranakun weekend baya fita tasan a weekend idan ta dawo islamiyya dole ta shiga kitchen ta riƙa wani aikin.
To watarana idan tana jin halin nata dama da driver ya sauke ta in har bada Siyama suka tafi ba, ta balcony take bi zuwa ɓangaren AB A can za ta je tayi kwanciyarta a parlornsa tana buga game da wayarsa watarana har bacci take ,sai angama zata shiga cikin gidan taje ta ɗibi abinci taci.
Kuma daga Sadiya har Siyama babu mai magana tun da sun san yaya Abba, yana gidan baya dukansu baya zaginsu fushinsa shine punishment ɗinsu ,su kuma Allah ya ɗora musu azababben ƙaunarsa ko kaɗan basa so suga yayan nasu na fushi dasu. A kitchen tayi tsaye ta haɗa tea ta zuba soyayyen chips acikin plate ta shiga break fast ɗin da sauri kar mami ta ganta tsaye tana cin abinci tayi faɗa
tasan driver sai ya fara sauke Aydah kafin ya sauketa ita kuma tana da lecture karfe 8 daidai tasan shirin Aydah idan ma aka bibbiya yanzun za ta yi wanka kafin ta shirya ta ɓata mata lokaci gara kawai ya fara ajeta
Idan ya dawo ya kai ta tun da dama ita Aydah ta saba da shiririta tana gamawa
Ta wuce kai tsaye ɗakinta ta shirya cikin doguwar rigar Atamfa da ɗan ƙaramin mayafinta ta dauki kayan karatunta ta fito ta samu Mami a parlor ta mata sallama, da mamaki Mami ke faɗin."batare zaku tafi da Siyama ba?"
"Mami Siyama bacci take maybe batada lecture din safe.
"To ita Aydah fa??"
"Mami ya fara saukeni kin san shirin Aydah inada lecture ƙarfe 8.
"Amman dai zaku wahalar dashi.
Bata tanka Mami ba ta juya tana faɗawa Mami sai ta dawo."Mami ta bita da addu'ar Allah ya tsare hanya, sai da ta shiga ɓangaren mahaifinta ta gaishesa babu yabo babu fallasa ya amsa jiki sanyayye ta fito dama duk wata yana tura masu kuɗi a account ɗinsu, dashi suke cira suyi hidimomin makaranta da kuma lalurorinsu na yau da kullum. karfe 7:30 da rabi na safe Aydah ta fito cikin shirin zuwa school sanye cikin uniform ɗinta, Mami ta kalleta tana faɗin."Sarkin shiririta sai yanzu kika gama shirin ?"
Tun asuba, ban san ubanme kike ba yanzu ko gama break fast ɗinki wani babban aiki ne sai ki kama jiki ki je ki yi kafin driver ya dawo yaje ya sauke Sadiya."
Tamkar Aydah zata yi kuka take faɗin "shi ne kuma tace ya tafi Mami bancin tasan nima zani makarantar salon ta saka nayi latti.
Wani kallo kawai Mami ,tayi mata "ai ke senior student ce bakya gudun latti.
Mami ta ƙarashe magana tana dalla mata harara, maimakon ta nufi dinning area sai kawai ta wuce parlorn daddy tana kumbure-kumbure da turo baki
ta zauna kusa ga Daddy ta gaishesa cike da kulawa ya amsa yana tambayar "me akayiwa shalelen Ya Abba?" Hawaye har sun cika idonta cike da shagwaɓa tace masa "yaya Sadiya ce tasa driver a gaba suka yi ficewarsu bancin tasan nima zan je.
Ta ƙarasa magana tana wani matso ƙwalla.
"ke mamana shirinki ne sai hamdala yanzu ki je ki faɗawa Yayanku sai ya kai ki. miƙewa tayi ta nufi ɓangaren AB a hankali ta tura ƙofar shiga Parlorn wani irin sanyi ne ke tashi acikin Parlon, baya cikin parlorn Amma ya kunna ac ta rasa soyayyar yaya Abba ,da son sanyi komai sanyi da ake sai ya kunna AC kuma tana mamakin yadda baya mura, kai tsaye master bedroom ɗinsa ta nufa jikin ƙofar ta tsaya tayi knocking har kusan sau biyu jin shiru yasa ta tura kanta akwai duhu a ɗakin.
Haka ya saukar da duka labulayya.
Da hannunta ta riƙa lalubar switch ɗin bulb ta kunna haske ya gauraye ko'ina. Hangosa tayi kwance cikin italyn bed ɗinsa ya dunkunkune kansa cikin duvet, kai tsaye kan bed ɗin ta nufa ko fuskarsa ba a gani ɗan ɗaga duvet ɗin tayi tana kiran sunansa, can cikin bacci yake jin muryar Aydah a tsakiyar kansa ɗan buɗe idanunsa yayi masu cike da bacci yana kallon fuskarta, ta wani marairaice fuska tana kallonshi "Aydah menene?" Ya faɗa da Muryar bacci nan Aydah ta faɗa masa yadda Sadiya tayi mata gashi lokaci yana ta tafiya. "je ki parlor ki jira ni na saka kaya.
miƙewa tayi ta koma parlor mintina biyar ya fito da jallabiyya ajikinsa da car key sai da suna hanya ya tambayeta tayi break fast? tace ita batajin yunwa, faɗa ya dinga yi mata ita dai tayi shiru a hanyar dawo daga kai ta makaranta kiran Rumaisa ya shigo wayarsa, ɗauka yayi yasa a speaker ta gaishesa tana tamabayarsa yau tayi mafarkinsa shiyasa ma ta kirasa dan tashinta kenan ko kan bed bata sakko ba. Tana jin sautin murmushinsa ta cikin wayar bai dai ce komai ba ,tasan halin miskilancinsa sai ita ce tace "ba ka tambaya wane kalar mafarki bane.?" "ina tuki Rumaisa idan na isa gida i will call you back." Da mamaki a muryarta take tambayar inda yaje da safe nan? dan tasan idan zai fita office yana kai 9.
"Aydah na sauke a school ina hanyar komawa gida ya faɗa sounding so very free cikin muryarsa abu taji yana tsaya mata a wuya dakyar ta iya furta "driver ba zai kai ta school ba sai kaine za ka kaita.?"
Banza ya yi mata tamkar bai ji tambayarta ta ba, ta fara sakawa shaƙuwarsa da Aydah alamar tambaya ta fara jin tsoron kulawar da AB yake yiwa Aydah ɗin. Yana nufin ma idan sunyi aure haka zai rika yi mata?"katse kiran tayi ba tare da ta ƙara furta komai ba. ƙarfe biyu Sadiya tana tashi daga lecture ma'aikatar su Hafeez Sale ta wuce kai tsay office ɗinsa ta wuce sai da sakatariyar Hafeez ta shiga ta faɗa masa ya sha mamakin nacin da Sadiya keyi masa shi tun da tayi aure ta fita ransa baya sha'awar aurenta yanzu.
Idan ya auri bazawara yace me?" Yasan mahaifinsa da mahaifiyarsa ma Ba zasu taɓa yarda ya auri Sadiya ba a yanzu ba. tun da ta shigo cikin katafaren office ɗin nasa take binsa da kallo kona sakan ɗaya bata ɗauke kanta akansa ba tana mamakin kalar son da take yi masa tamkar ba Hafeez ɗinta ba duk yabi ya canja mata. Bai mata tayi zama ba sai ita ce ta nemi wurin ta zauna, da tulin files agabansa yana dubawa cikin natsuwa. Sai da ta kira sunansa cikin raunin murya sannan ya ɗago kansa yana kallonta ido cikin ido.
"Sadiya Meya kawoki office ɗina?" kina matsayin matar wani so kike ki ja min bala'i ne?" a raunane take faɗin."meyasa baka daga kirana koda sau daya ba kaji dalilin kiran?"karshe ma sai ka buge da blocking ɗina ina soyayyar shekaru huɗu da muke yiwa junanmu.
"Soyayya !"soyayyah!"daga ranar da kika auri wani na bani ba na tsinke wannan soyayyar acikin zuciyata Sadiya, ban taɓa yaudararki ba hasalima kece kika yaudareni.
kallonsa take tana mamakin kalamansa ,wani murmushin Sadiya tayi tare da faɗin "idan nace maka na kashe aurena saboda soyayyarka Hafeez za ka yarda?"idan nace maka naki yiwa mahaifina biyayyar da ya keso nayi masa na zaman aure da yaya AB za ka yarda babu auren yaya AB akaina yanzu Hafeez ka daina shunning din soyayyata ko kwana ɗaya ban yi ba a gidan Ya AB ba kai ɗin nan shaida ne, idan da gaske kana sona mahaifina ya bani nan da sati biyu na fito da miji aure zai min.
fashewa da dariya Hafeez ya yi yana buga desk da yatsa yake nuna kansa a fusace yace "Ni kike tunanin zan auri ragin wani ?" kin rainawa kanki wayau Sadiya ba zan ɓoye miki ba ba zan iya aurenki ba koda iyayena za su yarda ke kin san kishina, ma ba zai barni na aureki ba wallahi.
wannan karon hawaye ke gudu sosai acikin fuskarta tana jin yadda zuciyarta ke wani irin bugawa ga wani irin zafi -zafi da zuciyarta taji tana yi mata.
Ƙofa ya nuna mata yana faɗin "Allah ya sadamu da alkhairi.
Sadiya miƙewa tsaye tayi ta nufi ƙofa bata ƙara waiwayen Hafeez Sale ba tana jin yadda yaja wani dogon tsaki adaidaita sahu kawai ta tare ba tare da tayi masa bayanin inda za taje ba. Sosai jikinta ke mugun rawa kalaman Hafeez ta ke ji cikin kunnuwanta haɗe kai tayi da gwiwa ta shiga rera kukan bakin ciki murya dan sahu taji yana bata haƙuri kafin ya tambayeta wacce unguwar zai kaita dakyar ta faɗa masa har ƙofar gida ya sauketa ko canji bata tsaya karɓa ba ta shiga gida, wannan ƙaron Aydah ce kaɗai a parlon zaune akan rug da uniform ajikinta wanda tunda ta dawo bata cire ba shinkafa da miya ce agabanta cikin plate da littafi a hannunta ,jin shigowar mutum cikin parlorn yasa tayi saurin tura Novel ɗin karkashin kujera ,dan kakaf gidansu babu wanda yasan tana karatun hausa novels ita ma wajen yar class ɗinsu take karbowa mai suna Zulaiha Kasim, tun basa bata sha'awa har ita ma ta fara karantawa tasan idan Mami, ta ganta da littafan soyayya a gidanta kasheta za ta yi hakama yaya Abba, mafi yawanci tafi karatunta da dare idan ta shiga ɗaki ta sakawa ƙofarta key, wannan karon ta kasa haƙura da karantawa sai da dare saboda daɗin da labarin yayi mata da kanta ta bai wa Zulaiha kuɗi ta siyomata daga na daya har na 4 kuma wai littafin yafi shekara goma Amma yadda Zulaiha ke zuzuta haɗuwarsa littafin sunansa wai (Tattalin so)har bata so ko na minti ɗaya ta daina karatun sai dai ganin yadda yaya Sadiya ta shigo a firgice kamar bata cikin natsuwarta yasa ta mayar da hankalinta sosai wajen yar uwartata da alamar idanuwa Sadiya a rufe suke ko sanin zaman Aydah ba ta yi a Parlon ba da gudu ta nufi stairs da kallo Kurum Aydah take bin ta har ta bacewa ganinta ɗan taɓe baki Aydah ta yi tana faɗin."duk bake kika jawo wa kanki abunda da ya sameki ba da yanzu kina gidan yaya Abba, hankalinki a kwance ana riritaki ana tattalinki kamar yadda yaya Aliyu na cikin littafin tattalin so yake yiwa zeee ,har hango fuskar Aliyu take kamar yaya Abbanta amma ta nacewa wannan Hafeez ɗin da bata san da me ya fi yaya Abba, dashi ba. Yayanta ya fi Hafeez komai da komai ba ma za a haɗa su ba
Jawo novel ɗinta ta yi ta cigaba da karantawa abincin da ta keci har ya yi sanyi ya sandare tana gama cin abinci har ɗaki ta samu Mami ta marairaicewa Mami ,tamkar da gaske tace kanta na ciwo dakyar idan za ta iya zuwa islamiyya za ta je ta sha magani ta kwanta, mami ta bita da addu'ar Allah ya sawwake, tana shiga ɗaki ta sakawa ƙofarta key ta faɗa kan dan kyakkyawan gadonta tayi ruf da ciki ta cigaba da karatun ta...






#Love story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo










Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[11/29/2023, 5:28 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love Story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU






#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye novels




10...




*RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU.*
*TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA*


PAID BOOK




#Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye novels








*MASARAUTAR KUDU*


Masarauta ce mai ɗimbin tarihi duk wani jinin sarautar da ya fito daga masarautar za kaga yasha bamban da normal mutane. Jinin masauratar suna da wata irin izza, taƙama, ƙasaita, za ka ga duk wanda ya fito daga wannan masauratar ɗabi'un da halayensa ba kamar na sauran mutane ba, ga su da girman kai da ɗagawa wayayyu ne suna da ilimin boko dana addini kuma gasu da wani irin kyau na ban mamaki da matuƙar wahala ka ga mummuna cikinsu sai dai abinda ba a rasa ba saboda mutum ɗan tara ne bai cika goma ba. Allah ya yi musu arziki sarauta da kuɗi gasu da mulki ga kuma tarin dukiya da Allah subhanahu wata'ala ya albarkace su da ita. A halin yanzu mai martaba sarkin kudu Mahmood Mustapha na uku shi ke mulkar wannan daula shine a matsayin sarkin kudu mahaifinsa Margayi Alhaji Usman Mustapha na uku shine Sarki bayan ya rasu aka naɗa ɗansa Mahmood Mustapha na uku. Sarki Mahmood su shidda mahaifiyarsu ta haifa wacce suke kira da mai babban ɗaki wato ita ce uwargidan sarki Usman, mai martaba sarki Usman ya mutu ya bar mata huɗu da sadaka uku tare da tarin 'ya'ya arba'in da bakwai a halin yanzu talatin da tara ke raye takwas daga ciki sun rasu.
Kafin Sarki Usman ya rasu kan zuri'arsa a haɗe yake sai ya rasu ne aka fara samun rabuwar kawunan su wannan kuma ya samu asali ne daga wurin matarsa ta biyu Hajiya Kilishi, a dalili sarautar Sarkin sabon birnin kudu da margayi Sarki Usman ya bai wa Aliyu tun yana da rai kasancewar Aliyu shine ɗansa na shidda a ganinsu
bai cancanci wannan sarautar ba tun da akwai na sama dashi. Wannan sarauta da sarki Usman ya ba wa Aliyu ita ce silar haddasa ƙiyayya tsakani yaran mai babban ɗaki da yaran Kilishi. Shi kuma Sarki Usman ya yi hakan ne a dalili fahimtar da ya yi Aliyu baya da ra'ayi sarauta ko kaɗan idan aka ɗora masa nauyi mulkin jama'a dole ya fara saka sarautar aransa. Dama shi Aliyu abarsa da kasuwanci domin kusan dukkan kamfanonin su shi ke kula dasu.
Alh Aliyu yana baro bangaren mai babban ɗaki ya wuce gidansa kaitsaye ɓangaren sa ya shiga yana shiga katafaren parlorn sa ya nemi ɗaya daga cikin royal cushion da suka daɗa ƙawata parlornsa ya zauna, ya cire rawani kansa ya ajiye kusa dashi ya tsani rawani sai dai doka ce ga duk wani jini masarautar ya saka naɗi kafin ya shiga faɗa, shiyasa yanzu ma da zai shiga faɗa ya saka ba don haka ba da ba abinda zai haɗa shi da rawani.
Hajiya Safiya ce ta turo ƙofa ta shigo cikin parlorn, ta hango mijn nata ya lafe jikin cushion idanunsa rufe tasan ba bacci yake yi ba kawai dai damuwar nan ce da ya ɗorawa kansa tasaka shi cikin irin wannan yanayi. Tambayar duniya nan idan za ka yi masa zai amsa maka ne da ba komai rana da baya ji so magana sai ya yi banza da mutum. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta nemi dab da ƙugunshi ta zauna tana matuƙar son mijinta irin son da fatar baki ba za ta iya faɗarsa ba, sai dai ta misalta. "Abbu!
Ta kira shi da sunan da yaransa ke kira shi dashi, dama a wasu lokuta haka take kiransa dashi. Bai matso ba balle ta sa ran ya ji kira da tai masa sake lankwasa muryarta ta yi ta koma kiransa "Abbu!
A hankali ya ɗage idonsa guda ya kalleta na 'yan wasu daƙiƙu kafin ya maida idonsa ya rufe, ya yi hakan ne don tasan ba bacci yake ba balle ta dame shi da kira. Sanin hali yafi sani kuma tasan halinsa fiye da yadda tasan yunwa cikinta muddin ba shi yaso yin magana ba duk nacinka dole ka kyaleshi don ba tanka ka zai yi ba.
"Abbu har sai zuwa yaushe zan daina gani wannan damuwar akan fuskarka? Dan Allah Abbu ka faɗa min idan ni ce ba ka jin daɗin zama dani ko ina maka wani abu da ba ka so wallahi a shirye nake da na gyara.
Shiru ya yi alamar ba tanka mata ba "A matsayina na matarka makusanciyarka ina da damar da zan san damuwarka idan ina da hali taimakawa Abbu sai na taimaka ma idan babu kuma sai na tayaka

7 / 80