Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   25 / 80

72K to 75K   out of 237.2K words

sosai ya yi mata kyau yanayin shigarsa yasa ta ji yana neman dagula duk wani lissafi nata, zuciyarta ta ji tana matsewa wuri ɗaya cikin rawar murya Sadiya ke faɗin."Ina kwana yaya Abba.!" bai kalleta ba ya amsa saboda Daddy dake tsaye har lokacin, Daddy ya juya ya amshi briefcase ɗinsa yana faɗin "ka je ka huta na rabin awa lokacin sallah ya matso ka fito mu shiga masallaci a tare idan mun fito mu yi lunch, a tare ɗagawa Daddy kai Kurum ya yi ya juya yana barin cikin parlor da wani irin taku da Sadiya ke jinsa har cikin gangar jikinta da duka ruhinta. Sosai Mami ke kallon mai gidan nata bai saba dawowa gida da tsakiyar rana ba, sai dai har ya gama rage kayan jikinsa bai yiwa Mami bayanin ko kalma dayya ba har kuma lokacin Mami na tsaye tana kallonsa ya juya yana kallonta."Mariya daga yau na dakatar da Aydah daga zuwa makaranta abarsa zuwa wani satin zan faɗawa Abba, sai ya je ya yiwa shugabar makarantar bayani. numfashin Mami kusan tsayawa yaso ya yi na wucin gadi jin abunda Daddy ya faɗa. Da gaske dai wannan auren sai Daddy ya kullasa ko hankalinsa zai kwanta ya kamata fa tasan abu yi gashi lokaci yana ta tafiya. fuska babu yabo babu fallasa Mami ta ce."Insha Allah! juyawa tayi tabar cikin bedroom ɗin da wani irin kallo Daddy ya bita dashi tana fita shima ya nufi cikin bathroom.
*MADAWAKI MANSION*
"Kashe kanki ki keso yi Rumaisa akan kankanuwar damuwar da bata taka kara ta karya ba wai shin baki yadda dani bane ?"cikin wani irin rawar murya idonta na cika da kwallah take faɗin "Na yadda dake Ammi auren da zai yi shine babban damuwata Ammi idan ya auri yarinyar nan zuciyata za ta iya bugawa.
Ta faɗa da wani zafi mai dauke da yanayin kishi cikin muryarta.
"ke fa dadina dake sakarya ce akan wannan yaron bakida control ko kaɗan ki bari mu gama maganin wannan matsalar kafin mu dawo kanta. Yanzu ki fito ki ci abincinki ko na saka zuwaira ta kawo maki a daki?"cikin sanyin murya Rumaisa ta ce "Bara na watsa ruwa zan fito yanzu shafa kanta Ammi ta yi tana barin ɗakin, Allah ya gani tana son yaranta bata haɗa ƙaunarsu da kowa ba a duniya, dole ta nemo aminiyarta zulai a waya kafin Abban Rumaisa ya dawo daga kasar Thailand so take komai ya daidaita bata son tashin hankalin yaran nata ko kankani bayan fitowarta daga ɓangaren Rumaisa nata ɓangaren ta nufa cikin bedroom ɗinta ta ƙarasa ta ɗauki wayarta ta shiga kiran aminiyarta Hajiya zulai har ta katse bata dauka ba ɗan tsaki Ammi taja ta rasa meyasa zulai bata baiwa wayarta muhimmanci ka yi ta kira bata dauka, tana cikin wannan tunanin Hajiya zulai ta kira ɗagawa ta yi "afuwan hajjaju na saka wayar a caji kin san yanayin unguwarmu ba a samu wutar lantarki ko minti biyar ba tayi ba da dawowa na saka caji. batare da Ammi ta saurari surutun da Hajiya zulai ke yi mata ba tace "kina jina Hajiya zulai?"
"Eh! Ina jinki" Zuwa bayan la'asar zan fito da driver zamu biyo ta gidanki za ki rakani wurin malamin nan naki naga aikinsa yana kyau. Wannan karon ma wani aiki zai yi min, da farin ciki sosai a muryar Hajiya zulai take faɗawa Ammi sai ta ƙaraso ta san ita ma za ta samu kasonta daman kwana biyu aljihunta yayi kasa tunda Allah ya haɗata da miji ɗan iska. Da haka suka yi sallama kowanne su ya sauke wayar.
*MASARAUTAR KUDU*
Bayan jirgin dasu Alh Aliyu na uku ya yi landing direbansa ne ya zo ya yi picking nasu daga airport direct masauratar suka yo, sai da suka shigo cikin masarautar sannan Alh Aliyu ya ciro wayarsa ya kira yaya Gimbiya ta faɗawa mishi mai martaba yana kwance ne a babban asibitin masarauta har kawo yanzu babu wani takamaiman labari daga likitoci da ke kansa. Kaitsaye ya umurci direba da ya sauke su a kingdom specialist hospital a bangare vip suka nufa domin anan ne mai martaba yake kwance cikin hali rayuwa ko mutuwa bai san inda kansa yake ba numfashi dake fita daga gangar jikinsa ta jikin na'urar da aka saka masa zai ba ka tabbacin yana raye.
A babban parlor dake vip suka tarar dasu yaya Gimbiya, Magaji ƙarami, wambai, Galadima, Ciroma, har ma da madaki sai kuma Fulani babba ita kuma Fulani karama tana can ɗakin da aka kwatar da ita har yanzu bata gama dawowa hayyacinta ba. Idan ka ga yadda Galadima da Ciroma suka tashi hankulansu ba za ka taɓa zargin suna da sa hannu a kwanciyar sarki ba. Walking majestically Alh Aliyu ya iso wajen su cikin izzar nan da ta gama zagaye jinin jikinsa ya yi musu sallama tare da tambayar mai jiki.
Ciroma ne ya bashi amsa da cewa "Ba za mu iya fadar yanayin jikin nasa kaitsaye ba domin har yanzu ba mu ji daga bakin likitoci ba. Mu dai ga sai gayyato manyan likitoci suke yi daga wajen masarauta yanzu kuma Yarima babba ya iso daga Abuja yana nan ciki tare da tawagar likitocin.
Naunnayar numfashi Alh Aliyu na uku ya sauke kafin ya nemi kusa da yaya Gimbiya ya zauna Zaheed da Zeeyad suka nufi Magaji ƙarami suna neman karin bayani a wurinsa domin yanzu sun gama fahimtar abunda ke faruwa. Suna nan zaune har yamma ta yi sallah kawai ke tashe dasu sai lokacin yarima babba ya fito daga ɗakin da mai martaba yake ya yi musu bayani takamaiman abinda ke damunsa, jininsa ne ya hau sosai shine ya haifar masa da collapse ɗin da ya yi daman ya dawo daga sallar asuba ne yana fitowa daga masallaci ya yanke jiki ya faɗi.
Wani kalan kallo yaya Gimbiya ke watsawa Yarima babba kafin ta tashi a fusace tana faɗin "Anya kuwa Yarima babba kai da tawagar abokan aikinka kunsan aikin ku kuwa? Saboda duk mai cikakken hankali ya dubi mai martaba zai fahimci jifarsa ne aka yi babu wani hawan jini da yake da.
"Haba! Yaya Gimbiya ya za ki ce haka Shekara ta nawa ina wannan aiki sai akan mahaifina ne zai faɗi fake results?"
"To idan ma ba ka taɓa faɗa ba a wannan karo ka faɗa ba daidai ba. Wannan aikin magauta da mahassada ne masu son gani bayan mai martaba.
Ta ƙarashe magana tana sharar hawaye da gefen mayafin tsadaddiyar Abayar dake jikinta. Da sauri Yarima babba ya isa kusa da ita yana faɗin
"This is not a worry since we have already found out what is wrong with him if he continues to receive the medicines and doses that will be given to him immediately he will get back to his normal health.
A sheƙeƙe Yaya Gimbiya ke kallonsa kafin ta ja siririn tsaki rai bace ta ce.


#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.




Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/22/2023, 11:29 AM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


*AREWABOOK*:Jeddah 3256


Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye


034.


*MASARAUTAR KUDU*


"Dallah! Yarima babba ka rufe mana baki ga baki ɗaya halayenka dana Ahmadu da Aliyu a koda yaushe sun sha bambam da na masarautar kudu, kun ri ga kun ɗauki ɗabi'un nasara kun ɗorawa kawunan ku. Idan zan shekara ina maka bayani ba fahimta za ka yi ba, don haka ka riƙe saninka nima na riƙe nawa, zan je na sami mai babban ɗaki ita za ta fahimci ni.
Gani yadda yaya Gimbiya ta rikice da faɗa daman can ko acikinsu ita ɗin mafaɗaciya gaske ce wambai ne ya kalle ta yana faɗin "maganar Gimbiya abar dubawa ce tun da muke da mai martaba ba a taɓa binciken lafiyarsa aka tarar dashi ɗauke da matsala ta hawan jini ba. Duk da zai iya kamuwa da ita faratt ɗaya. Ke Gimbiya ki yi haƙuri mu jira zuwa wani ɗan takaitaccen lokaci idan har treatment ɗin da suke masa ba mu ga wani cigaba ba, tofa dole Yarima babba ka haƙura mu nema masa maganin gargajiya.
Wannan goyon baya da Gimbiya ta samu a gun wambai ya kawo karshen ce-ce-kuce da suke yi tsakaninta da Yarima babba, ta dauki jakkarta ta koma cikin masarauta, Aliyu ya miƙe ya nufi ɗakin da mai martaba yake sosai ya kaɗu da gani hali da yake ciki shi ba matatccen ba shi ba mai rai ba domin kuwa hatta da numfashinsa da taimakon na'ura ne yake sauka shima kaɗan-kaɗan. Ya dau lokaci tsaye a gefensa kafin ya fito daga ɗakin ya kira Yarima babba suka koma gefe "Yarima idan ban ga wani cigaba ba a jikinsa nan da sati ɗaya to kasani zan dauke shi na fita dashi ƙasar waje (abroad) domin alama ce dake nuna ba za ku iya ba.
"Amma ranka shi dade shi fa ciwo faratt ɗaya yake shiga sauki kuma sannu-sannu yake zuwa.
"Yarima wannan damar ta sati ɗaya da na ba ku shima don ya kasance mahaifi ne agare ka da ba don haka ba, da tuni na fara cuku-cuku nema mana visa.
"Shikenan ranka shi dade ai mu fatan mu duk inda za a kai shi ya sami lafiya.
Daga haka Aliyu na uku ya juya Anaal ta yi sauri bin bayansa suna fitowa farfajiyar asibitin ya dube ta tare da faɗin "Koma ciki ki kira min twins.
Anaal ta amsa da to kana ta koma sai gashi sun zo tare batare da ya yi magana ba ya nuna musu mota, su ma ba su yi gardama ba suka shiga.
Gimbiya tana zuwa kaitsaye ta wuce bangaren mai babban ɗaki a babban parlornta ta tarar da ita ta kishingiɗa bayi biyu na durƙushe suna mata massage ɗin ƙafafuwanta hannunta riƙe da counter tana yiwa Annabi sallati. Duk da a can ƙasan zuciyarta damuwa ce shimfiɗa acikinta dangane da wannan lalura da mai martaba ya waye gari dashi amma ko kaɗan fuskarta bata bayyanar da damuwarta ba. Mai babban ɗaki macce ce jarumar gaske duk bin kwakwafin ka ba za ka taɓa fahimtar rauninta ba, bata nuna gazawar ta a fili. Duk girman al'amari idan ya tunƙaro ta ko iyalinta ta kan yi tsayin daka har ta kawar da wannan matsala. Gimbiya ta nemi wuri ta zauna yanayin ta kaɗai zai tabbatar maka da tana cikin damuwa.
"Barka da hutawa ranki shi dade!
"Sannu Gimbiya ya kika baro jikin ɗan uwan naki?"
"Babu wani sauyi da yadda an ka kaishi sai dai abinda Ubangiji ya yi.
Gimbiya ta ƙarashe magana hawaye na bin kumatunta, shiru mai babban ɗaki ta yi na wasu mintuna kafin ta ce "Ki kwatar da hankalinki Gimbiya komai da kike gani muƙadarri ne daga Allah subhanahu wata'ala, yana daga cikin rukunan imani ɗan adam ya yarda da ƙaddara mai kyau ko akasin hakan.
"Ranki shi dade ni fa a nawa fahimta ciwon mai martaba bana asibiti bane duk wanda yaga yadda yini guda curr ya dawo sai ya zubda masa da hawaye, sunan kawai yana numfashi ne amma bambancin sa da matatccen kaɗan ne.
"Ki sani Gimbiya babu wani ɗan adam da yasa isa ya yi nufin wani mahaluƙi da cuta face ubangiji ya yi nufin hakan koda kuwa hasashen ki ya kasance gaskiya to ki saka aranki jarabawa ce Allah ya nufi ɗan uwanki da ita domin ya gwada ƙarfin imaninsa, ki cigaba da yi masa addu'a idan yana da sauran kwana a gaba Allah ya tashi kafaɗarsa idan kuma wa'adin sa ne ya yi to ubangiji ya yi masa masauki a gidan aljanna firdausi.
Ga baki ɗaya jikin Gimbiya ya yi matuƙar sanyi tana hamdallah can cikin zuciyarta da irin mahaifiyar da Allah ya basu macce mai tawakalli mai yarda da ƙaddara, lallai samun uwa kamarta babban abin alfahari ne. Kafin Gimbiya ta sake yi magana Aliyu na uku ya turo ƙofa ya shigo yayin da yaransa ke biye dashi a bayansa tun kafin ya ƙaraso bayi da ke yiwa mai babban ɗaki massage suka yi sauri tashi tsaye, kusan a tare da suka gaida shi bai ko kalli gun da suke ba ya ɗaga musu hannu da sauri suka nufi ƙofar fita, sun san da cewa idan har ya shigo bangaren mahaifiyarsa duk wata baiwa fita take yi. Ya durƙusa kusa da ita ya kwashe gaisuwa ta amsa mishi babu yabo ba fallasa kana ya nemi kusa da ita ya zauna twins da Anaal suka gaidata sai da ta ƙare musu kallo a sheƙeƙe kafin ta amsa tana mai taɓe baki. Shiru ya biyo baya kafin mai babban ɗaki ta tashi daga kishigiɗa da tayi ta kalli twins da Anaal dake zaune akan three seater sun saka Anaal a tsakiya suna kallo wani sabon samfurin mota da take nuna musu a wayarta "Yanzu kai mai sabon birnin rayuwar da ka zaɓawa Maryama kana gani ka yi daidai kenan? Yarinya ta kai muzali aure amman ka zuba mata ido sai yawon neman duniya kawai tasa a gaba.
"Allah ya taimake ki har yanzu bata sami miji bane da zarar Allah ya kawo mata miji babu abinda zai hanani aurar da ita ai nima burina ta yi aure.
Aliyu na uku ya yi magana cikin sanyi murya tare da sadda kansa ƙasa.
"Ya dai kamata ka yiwa kanka faɗa mai sabon birnin ka kuma tuna da mutuncin mace gidan mijinta.
A wannan karo yaya Gimbiya ce ta yi wannan maganar kallonta kawai ya yi ya kauda fuska bai ce da ita uffan ba. Anaal da twins suna gani an fara wannan zance suka sulale daga parlon. Ci-gaba da tattauna rashin lafiyar mai martaba suka yi yayin da yaya Gimbiya ke goyon bayan a nema masa maganin gargajiya, shi kuma Aliyu yana faɗin a fita dashi ƙasar waje zai fi.
Ciroma yana gani Aliyu na Uku ya bar asibitin ya yiwa Galadima alama da idonsa suka fi ce acan gidan gona Ciroma da suka saba haɗuwa suka nufa, cike da zallan takaici Ciroma ke kallon Galadima kafin cikin fushi da fusata ya ce "A ina ne aka sami wannan kuskure shin daga gare ka ne kuma daga wurin Fulani karama cikkaken bayani nake buƙata Galadima!.
Ciroma ya ƙarashe magana a tsawace, shima Galadima cikin dakakkiyar murya ya ce "Wannan ne kum bansani ba domin yadda ka yi min bayani a aiwatar da aikin haka na yi mata samun cikakkiyar amsar wannan tambayar dole sai a bakinta.
*MADAWAKI MANSION*
Cikin shigar alfarma Ammi ta fito ta saka bakin glass ta lulluɓe ƙwayar idonta wanda ya mamaye rabin fuskarta kai kace bata aje Rumaisa yar shekara Ashirin da bakwai ba a duniya da kuma wasu katon saurayi a gefe, cikin dinning area ta samu Rumaisa tana cin abinci a natse da waya a hannunta karar takalman da ta ji yasa ta daga kai tana baza idonta a sautin da take jin fitowarsu ta nata kallon mahaifiyarta yadda taga ta yi mata kyau sosai tamkar wata 'yar shekara talatin har lokacin da Ammi ta karaso wurin murmushi bai bar akan fuskar Rumaisa ba duk da yanayin da zuciyarta ke ciki."kin yi kyau sosai Ammi kamar baki aje kamar Yaya Safwan ba, murmushi Ammi ta yi tana ɗan shafa kan Rumaisa cike da so da kulawa take faɗin."Zan fita ba dadewa zan yi ba."Da sauri Rumaisa ta ce."Ammi ko na shirya na biki na gaji da zaman gidan nan wallahi, da sauri Ammi ke faɗin."No! ki yi zamanki yanzun nan zan dawo.
Ba dan Rumaisa taso ba ta yiwa mahaifiyarta fatan sauka lafiya driver na ganin fitowar Ammi daman yana zaune tareda maigadi suna hira da sauri ya karaso yana gaisheta da Respect ta amsa nan take wani tunani ya shiga kan Ammi yafi mata sauki tayi driving da kanta akan taje da driver,kasancewar inda za taje wurin sirri ne kawai ka yi zamaka Lawi zan yi driving da kaina."Lawi ya russuna tamkar zai yi mata sujada yana mata fatan sauka lafiya da haka ta shige motar ta yi mata key kafin ta karaso tuni maigadi ya buɗe mata gate kasancewar bata da cash sosai koda ana bukatar kudi sosai wurin da za taje dan tasan kuɗi ba matsalarta bane ta tsaya gefen hanya ta ciri kudi wurin mai p.o.s tana gafda isa layin gidan Hajiya Zulai ta kirata a waya ta faɗa mata ta fito gata ta kusa karasowa dan ba zata shiga ba tasan suna iya kara bata lokaci, ko minti biyu ba tayi ba a bakin kofar gidan Hajiya Zulai ta fito ta buɗe gaban motar tana yiwa Ammi kirari a hanyarsu ta zuwa wurin Malam take baiwa Hajiya Zulai labarin matsalar Rumaisa, "in banda dan yau da neman fitina Rumaisa me za tayi da marar asali, ke kuma sai kika wani biye mata a haka zata auri mijin da bakuda tabbacin yana da asali mai kyau."Ammi na juya sitiyari cikin kwarewa take faɗin."i don't bloody care akan asalinsa in har yarinya ta za ta auresa ta dawo cikin natsuwarta
ban damu da asalinsa ba tunda marikin nasa yana da kudi ba wai kananun mutane bane."
Aran Hajiya Zulai tana jinjina son 'ya'ya irin na Ammi irin sune in har za ka kwantar da kanka ka nunawa 'ya'yansu soyayya za su ba ka duk abunda kake so a duniya in har baifi karfinsu ba haka kuma za su so ka su kaunaceka duk akan soyayyar da suke yiwa 'ƴa'yansu. Mutane biyu suka samu kafin su zo kan layi, sai da layi ya kawo kanta suka shiga wani babban daki da carpet kawai ne acikinsa sai tarkacen su na kayan tsibbu daga gefe suka zauna Zulai ta russuna tana gaishesa da kalar gaisuwar da ake yi masa. Itama Ammi ta yi yadda Zulai ta yi ya amsa masu da kai yana ta can doguwar casbahar hannunsa batare da ya yi magana ba. sun kwashe kusan mintuna goma a haka ya dago yana kallon tsakanin fuskar Zulai da Ammi, kamar Zulai tasan tunanin da yake da sauri ta nuna Ammi a hankali ya miƙa mata

25 / 80