Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   70 / 80

207K to 210K   out of 237.2K words

kallo "Ya tafi Mami yace agaisheki.
Sadiya ta faɗa tana cigaba da tafiya hankalinta akan wayarta.
Da wani yanayi Mami ke kallon ta kafin ta kira sunan Sadiyar cikin wata irin murya da bata taɓa jin Mami,ta kirata dashi ba. Dan juyowa tayi tana fuskantar Mami.
"Da gaske za ki iya auren wannan mutumin?
Cike da mamaki Sadiya take kallan mami,kafin ta nisa tana faɗin
"Daman Mami yana da wani mugun hali ne wanda ban sani ba kuma dai naga Daddy ne ya kawosa?" Kuma ni banga illah acikin aurensa ba gwargwado Daddy yasan halinsa yana da hali mai kyau yana da asali mai kyau yana da kuɗito menene matsalar?"baki buɗe Mami ke kallon sadiya,baki san wacece matar sa ba shiyasa kike da zarar faɗar haka ko so kike ta kashemin ke ko ta yimaki wani abun da ba za ki kara muruwa ba a rayuwarki?"
Cike da gajiya Sadiya ke faɗin "wannan bai dameni ba Mami,bani da matsala da matarsa hasalima ba gida ɗaya zai ajemu ba ni ban damu da ko bokaye nawa take bi ba. Tun kafin na shiga gidan ,nima zan je wurin nawa malami dan ba'ayi diya maccen da zata hanani rawar gaban hantsi ba.
Da haka Sadiya ta juya tabar Mami sake da baki duk abun duniya ya taru yayi mata yawa ko baccin kirki bata samu ko kaɗan bata da wani kwanciyar hankali acikin kwanakin nan.bayan fitar Alhaji sammani da har lambar Sadiya ya karba ganin kamar ya samu karɓuwa a wurinta. Kiran Daddy yayi cikin farin ciki ya sanar dashi Sadiya tayi ammana dashi. sosai Daddy,yayi murna Sadiya bata taɓa saka sa farin ciki irin wannan ranar ba ,duk wata kullata da yayi mata ya ji a hankali tana warwarewa lokaci ɗaya,Allah ya karbi adduarsa.Bayan sati ɗaya aka kawo lefen Siyama,dana Sadiya aka saka rana lokaci ɗaya ,har lokacin kuma Mami bata ga alamar asirinta ya yi tasiri akansa ba sai dai Daddy,ya canja sosai kullum baya cikin walwala tana yawan farkawa da dare tagan shi zaune cikin tunani da damuwa har yar rama mamin taga ya yi.
AB yana tsaye a gaban mirror dressing yana cubbing sumar kansa,tun sanda Daddy ya kirasa da safe yace yana son ya gansa a office ya fita da wuri yake ji wata irin damuwa tana lullubesa musamman da ya ji muryar Daddy,kamar batasa ba kamar yana cikin damuwa kusan kwana biyu ya lura da haka babu irin tambayar da AB bai masa ba akan ko akwai abunda ke damunsa yace masa a'ah!.wani irin yanayi yake ji cikin jikinsa tun da suka gama waya da Daddy,bai kara samun natsuwa ba. Yana cikin wannan yanayin Aydah ta zo ta maƙalesa ta baya ta kwantar da kanta cikin bayansa ta ɗora duka hannayenta adaidai saitin zuciyarsa yadda zuciyarsa ke bugawa kamar ya wuce ka'ida yasa ta rika shafa wurin,cikin sanyin murya take faɗin."yayanmu wannan bugun zuciyar ya yi yawa meke faru ne?
"Babu komai baby muje muyi breakfast ya faɗa yana dawowa da ita gabansa ganin yadda ta kwaɓe fuska yasa yaja dogon hancinta ya russuna ya sumbaci dan ƙaramin bakinta murya can ciki yake faɗin.
"I love you baby!"
Rungumesa tayi tana fadin
"I love you more yayana.!sunfi minti uku a haka kafin ya samu ya cireta daga jikinsa,da sauri ta dafe saitin zuciyarta taji yayi wani irin dokawa wanda bata taɓa jin kalarsa ba. Dan kallonta yayi yace "Lafiya?"tamkar zata yi kuka ta ce "gabana naji ya faɗin kamar wani abu marar daɗi zai faru.
Aydah ta faɗa cikin rawar murya ɗan buɗe idonsa yayi akanta ya rike mata hannu ya fara tafiya da ita yana faɗin
"Babu abunda zai faru ki yi addu'a.
Ta gyada masa kai kurum tayi da yake ranar girkinta ne tare suka sauka kasa Huwaila ta gama jera komai cikin dinning area,daman yanzu ba koda yaushe Rumaisa ke fitowa ayi breakfast a tare da ita ba musamman idan tasan ba ranar girkinta bane,tare suka yi breakfast ya miƙe ya koma sama,ya leka ɗakin Rumaisa yaga tana bacci dakinsa ya nufa
Daidai nan wayarsa ta soma ring ɗagawa yayi ganin Daddy ke kiransa
ya dauka da sallama a bakinsa Daddy ya amsa yana faɗin."ya taso?
"yanzu zan taho Daddy! ɗan shiru Daddy,ya yi kafin yace "kana jina Abba?"
"Ina jinka Daddy.
Cike da karfin hali Daddy yace "kafin ka taho ka zo min da duk wasu documents ɗina dake wurinka wanda kasan mallakina ne!
Dan shiru AB ya yi yana sauraren Daddy da yanayin da ya kasa fahimta a muryar Daddy ɗin sai dai bai kawo komai aransa ba yace "Insha Allahu Daddy!
Da haka suka yi sallama.
Aydah ganin yayanta bai dawo ba yasa tabi bayansa baya falonsa kai tsaye master bedroom ɗinsa ta nufa ta samesa yana arranging din duk wasu kaddarori da Daddy ya mallaka masa da nasu Aydah wanda suke dauke da sunan kowa ,bai bar takarda ko ɗaya a gidansa ba ya yi wa Aydah sallama ya nufi office wurin Daddy,wani irin yanayi yakyeji ajikinsa marar Misiltawa jin yake tamkar zazzaɓi zai saukar masa dakyar yayi knocking kofar office ɗin Daddy aka yi masa izinin shiga ,suka yi ido biyu da Daddy shi ya yi saurin dauke nasa idon cikin na Daddy ya samu wuri ya zauna ,ya tura bag ɗin dake dauke da duk wasu dukiyoyin Daddy dake hannunsa da wanda ya mallaka masa da shi dasu Aydah ya tura agabansa jaye bag ɗin gefe Daddy ya yi. Ya daga kai ya kalli Daddy a karo na biyu sai da zuciyarsa ta doka da ya hango kwallah acikin idanuwan Daddy,shi baya son ganin wannan yanayi a tare da Daddy,rasa kwarin gwiwa yake yi.
Murya a harhade tamkar ba muryar Daddy ba yake kallon AB ido cikin ido "zan nemi alfarma a wurinka Abba Allah yasa zan samu.?"
A gaggauce AB ke faɗin."Daddy ka faɗi duk abunda kakeso a wurina na maka alkawarin idan bai fi karfina ba zan maka.!"
dan shiru Alhaji Bashir yayi jin yake tamkar zuciyarsa zata fito daga kirjinsa yanayin da yake ji kansa tamkar ana hura masa wuta a sassan jikinsa. "Abba ina son ka bar rayuwarmu na har abada nida iyalina ina nufin idan zai son samu ne kayi nisa damu dan Allah.
Alh Bashir ya faɗa yana haɗe hannayensa.
A razane AB ke kallon mahaifinsa sai dai ganin hawaye a idanun mahaifin nasa yasa yaji komai nasa ya tsaya tsak!
"Karka tambayeni meyasa idan zai yiwuwa yanzun Abba ka tashi ka tafi Allah yasa damu alkhari.!
har AB ya bude baki zai yi magana Daddy,ya shiga girgiza masa kai "ka tafi dan Allah karka ce komai.
Har lokacin Daddy bai sauke hannayensa ba
A hankali AB ya mike tsaye yana jin wani nauyi a kasan zuciyarsa da sauri ya juya ya nufi ƙofar ya ji waɗansu zafafan hawaye suna fitowa daga cikin idanunsa.
A hankali AB yaja kofar ya maida ya rufe da ido Daddy ya bisa kamin ya dora kansa akan desk ya fashe da wani irin kuka mai wuyar fassarawa kuka yake sosai jikinsa na wani irin kaɗawa tsanar kansa yaji tana cika masa zuciya miyasa ya aikatawa Abba haka idan Abba ya bar gidansa ina zai tafi wa yake dashi a duniyar nan sama dashi? Yana so ya tsayarda shi sai dai wani sashe na zuciyarsa yaƙi ya basa haɗin kai.
Tafiya yake bai san inda yake jefa ƙafarsa ba,saboda tsananin tashin hankalin da ya shiga bai san rashin iyaye babban haɗari bane a rayuwa sai yanzu da maganganun Daddy,ke dawo masa cikin kansa shiga motarsa yayi tare da yin reverse da wani irin gudu ya fisgi motar maigadi yana bin sa da kallon mamaki,kuka yake yi yana jin tsanar iyayensa aransa bai ga laifin Daddy ba komai ya samesa iyayensa ne suka ja masa.Yawo ya rikayi da motar dan bai san inda zai je ba daga bisani sai kawai ya dauki hanyar barin garin Kano.
Babu wani tunani akansa a wannan lokacin sai na son yin nisa da Kano baki daya addu'a ya riƙa yi Allah ya dauki ransa ga baki ɗaya kowa ma ya huta.Tun daga nesa babbar motar tankin mai keyi wa AB mahaukacin horn da aguje take shigowarta kenan cikin garin kano shi kuma yana kokarin fita ga baki ɗaya hankalinsa da natsuwarsa basa tare da shi tuki kawai yake yi bai ankara ba sai jin ya yi motarsa tayi sama dashi daga nan kuma bai kara sanin meke faruwa dashi ba.
Har bayan ishai Aydah na zaune a parlornta suna kallo da Huwaila kallon kawai take hankalinta baya tare da ita ta rasa inda yayanta ya shiga har yanzu bai dawo ba ga wayarsa bata shiga ita ma Rumaisa kusan 9 ta fito parlor ta kalli Aydah data zama wani iri lokaci ɗaya tana tambayarta har yanzu yayan nata bai dawo ba,Aydah ta dagawa Rumaisa kai kurum zuciyarta duk babu dadi.
Cikin rawar murya Aydah ke faɗin
"haƙurina ya fara karewa Aunty Rumaisa gabana sai faduwa yake yi wani irin kunci nake ji ,ki bari mu kira Daddy mu je ko yana da masaniyar inda Yayanmu yake ba ma yi ta zama haka kurum mu zuba ido muna jiran tsammani ba.
zama Rumaisa tayi gefen Aydah ita kanta bata da natsuwa gashi kwanan nan bata jin daɗi tana fama da laulayi sun je asibiti ita da AB aka yi gwaji, gwajin farko da akayi mata aka tabbatar da akwai ciki na kusan sati 3 ajikinta irin murnar da AB ya rika yi a ranar bata misaltuwa yadda ya dinga tattalinta da nuna mata kulawa ya saka ta farin ciki domin nuna farin cikinsa ya tashi sai da ya siya mata mota don kawai ya faranta mata,duk da bata shiryawa haihuwa ba a yanzu sai kawai ta haƙura ganin yadda AB ke son cikin jikinta ita ma Aydah ta yi murna amman da suka shiga daki har kuka sai da ta yiwa AB wai ita meyesa bata da ciki sai Rumaisa?"
Baki ya buɗe kawai yana kallon drama Queen ɗin tasa,shi kuma har ga Allah bai mason ta yi ciki yanzu saboda karatun ta kuma ganin yake tayi kankanta rungumeta ya yi cikin jikinsa yana faɗin."sai kin gama jami'a baby.
rigima ta rika yi masa akan tana so murmushi kawai yayi a lokacin yana faɗin."zai zo ta yi addu'a.
Da haka ya samu ya rufe bakin rigimarta.
Aydah ta kira lambar Mami,
Mami na dauka Aydah ta sakarwa Mami kuka,cikin kuka ta ke yiwa Mami bayani da sauri Mami ke tambayar Aydah tun yaushe?"ta faɗa mata tun sanda ya fita office tana jin damuwa a muryar Mami,kafin tace mata bara ta yiwa Daddy magana. Da haka Mami,ta aje wayar murna fal aranta tana tunanin Allah yasa Abba yabar garin duka da haka ta nufi bangaren Daddy,hankalin ta a tashe take faɗa masa har yanzu Abba bai koma gida ba kuma Aydah har Abdulkarim ta kira basa tare, Daddy bai kalleta ba kawai yace mata ai Abba ba yaro bane.
Kallon yanayin Daddy kawai Mami ta yi sai ta juya tabar parlorn murna fal aranta.






Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.
[2/5, 2:00 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels


095.


*LAGOS NIGERIA*


Tun bayan dawowar Aliyu na Uku lagos ya ƙara zurfafa bincike akan inda zai nemo ɗansa ga Maysun a halin yanzu gazawar sa take gani. Har ta kai ta kawo kullum sai ta ɗora masa laifi akan ɓatan ɗan nasu. Tana gani cewa don shi na da wasu 'ya'yan ne shiyasa bai damu da ya nemo mata nata ɗan ba. Ga baki ɗaya ta bi ta tashi hankalinsa bashi da natsuwa ko kaɗan, ga kuma Anaal da a yanzu ya rasa gane kanta sakaci iri-irin take masa a kamfani daman can ita ce jajirtacciyya a kamfanin ita ce mai kokarin kawo cigaba a koda yaushe saɓani yanzu da ko ayyukan office ɗinta ta daina kulawa dasu. Wani lokaci ma bata zuwa kamfani sai ta yi kwanciyar ta a gida idan ya yi magana sai ta ce bata jin daɗi.
Ƙarfaffiyar ajiyar zuciya Aliyu na Uku ya sauke ya kai dubansa akan wayarsa dake ringing ya ga kiran daga Kamfani whitepaper ne dake Germany, jikinsa babu kuzari ya yi picking.
"Hello, Mr. Aliyu, you're talking to the president of the white paper company Clark Andrew I heard that you canceled the business agreement between your company and the moonlight automobile industry company.May I know your reason for canceling the agreement.
With shock Aliyu na uku ya miƙe tsaye domin shi iya saninsa bai san sanda hakan ta faru ba. Amman dole Anaal tana da cikakkiyar masaniyar domin ita ce CEO na kamfanin dole sai da sa hannunta za a iya soke yarjejeniyar ɗin. Cikin sanyi murya ya shiga faɗin "sorry mr clark i don't know about that but give me time I'll talk to the CEO I'll contact you later thank you very much.
Bai jira me Clark ɗin zai faɗa ba next ba ya kashe wayar saboda ransa ya fara ɓaci har yana tambayar kansa yaushe Anaal ta sami power har haka da za ta zantar da hukuncin irin wannan with out his consent zuciyarsa sai tafarfasa take yi a fusace ya koma ya zauna ya dauki wayarsa ya kira layin Anaal sai dai wayarta bata shiga, secretary ɗinsa ya kira ya ce ta kira masa Anaal a office ɗinta jim kaɗan ta dawo "Sir, her office was closed and I asked her secretary and he said that she came in the morning and she left in a hurry.
"did he tell you where she went?
"No sir! he said that she didn't tell him where she was going, but she left in a hurry.
"Okay! You can go back to your work.
"Yes sir!
Ta faɗa cike da ladabi ta juya tare da ficewa, landline na office ɗin Zaheed ya kira ya ce ya zo yana so ganinsa. After some minutes sai ga Zaheed ya nemi kujerar dake gaban desk ɗin Aliyu na uku ya zauna.
"Zaheed ko kasan inda Anaal ta je na kira layin ta baya shiga, sannan kuma kana da masaniyar akan cancelling partnership ɗinmu da kamfanonin moonlight da ta yi?"
"Ban san inda ta je ba Abbu tun safe rabona da ita dangane da cancelling partnership shi ma basan komai akai ba. Amman za ka iya bincikar Zayeed maybe shi ta gayamasa.
Batareda Aliyu na Uku ya ce komai ba ya kira Zayeed.
"Ga ni Abbu!
Zayeed ya faɗa cikin russunawa.
"Zauna Zayeed.
Abbu ya faɗa tare da pointing kujera da hannunsa jikin Zayeed ne ya yi sanyi ya zauna tare da kallon Zaheed yana kifkifta masa ido alamar me ke faruwa?"
Shi ma alamar ya yi masa da jira Abbu ai zai gayamasa, sai da Abbu ya ja iska da bakinsa ya fesar kamin ya yi wa Zayeed irin tambayar da ya yi wa Zaheed.
"Eh! Na haɗu da ita a parking lot za ta fita yadda naga tana sauri ya daure min da kai domin iya tsayin zamana da ita bata taɓa ganinta tana irin wannan saurin ba, shiyasa na yi sauri fitowa daga motata na tambaye ta me ke faruwa take sauri haka. Sai ta cemin tafiyar gaggawa ce ta kama ta zuwa Kano.
Mamaki ne ya kama ni za ta je yi a Kano kuma cikin gaggawa kamin na yi mata wannan tambayar har ta ja mota ta tafi. Amma dangane da partnership ɗin ne bani da masaniyar nima.
"Kano?"
Aliyu na uku ya maimaita sunan cikin mamaki.
"Eh! Abbu.
"Anaal ce ta tafi Kano? To me za ta je yi a Kano?"
"Wallahi Abbu nima bansani ba.
Zayeed ya yi magana yana lankwasa yatsunsa.
"Abbu wannan al'amari da ɗaure kai yake iya sanina da Anaal bata da ƙawa a Kano balle mu ci ko gun ƙawarta ta je.
Zaheed ya faɗa da dimbin mamaki shimfiɗe akan fuskarsa.
Shiru ne ya biyo baya kamin Abbu ya ce su koma bakin aikinsu. Ya zurfafa tunaninsa me Anaal za ta je yi Kano batareda da neman izininsa ba. Shi kansa yasan Anaal ta canza ba haka yasan ta ba dole da akwai abun da yake damunta to mene ne wannan abun ɗin?"
Rashin sani amsa yasa ya ƙara gwada kiran wayarta still bata shiga.
*KANO NIGERIA*
Kafin mutane su kawowa Ab agaji motarsa ta kama da wuta, wani irin ci take yi da wuta bata daina ci ba har sai da ta dawo toka babu abin da mutane ke yi sai kalmar shahada akan idonsu motar ta cinye duka.
Aydah da Rumaisah har dare basu samun labari inda Ab yake ba tun Aydah tana kira Daddy da Mami suna dauka har suka daina daukar kiranta wanda hakan ya ƙara jefa ta cikin damuwa, ga Rumaisa sai amai take sheƙawa hatta da ruwa ta sha sai ta dawo dasu cikin lokaci guda sun fice daga hayyacinsu. Zaune suke a parlorn ƙasa sun yi zugu-zugun lokaci zuwa lokaci Aydah take goge hawaye da suka kasa daina fita daga idanunta, Rumaisah ce mai ɗan karfin hali rarrashinta suna cikin wannan halin Abdulkarim ya zo tare da wani abokin su Jabeer yadda Abdulkarim yaga Aydah da Rumaisah manne da junansu sai suka yi bala'in basa tausayi shi da Jabeer suka dinga rarrashesu da kwatar musu da hankali, suna baro gidan suka wuce police station suka kai report daga nan kuma suka nufo gidan Mami. Sun sami gani Daddy sai dai har Abdulkarim ya gama basa labari duk inda yake saka ran gani AB ya je bai sami shi ba hasali ma an ce bai je ba. Daddy ya dafe goshinsa yana tuna abubuwan da suka faru tsakaninsa da AB, wata irin nadama haɗe danasani marar adadi Daddy yake ji yana kama shi cikin rauni murya ya ce "Abdulkarim ku hutar da kanku da neman abokinku domin baya ciki garin kano a halin yanzu Allah kaɗai yasan inda yake. Abdulkarim bai san me ya hau kaina ba na kora Abba da kaina ni na umarce shi da yabar rayuwata da ta iyalina batare da ya yi min laifin komai ba. Abdul ni na kore ɗa na da kaina ni kam wane ne irin uba ne?
Daddy ya ƙarashe magana hawaye na bin kumatunsa daga Abdulkarim har Jabeer sun kasa cewa komai wannan al'amarin ba ƙaramin daure musu kai ya yi ba. Sun rasa ta ina za su fara ga kuma tarin tambayoyi da suka cika musu ciki daga ƙarshe dai sai sallama suka yi wa Daddy tare da basa

70 / 80