Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   48 / 80

141K to 144K   out of 237.2K words


TK sai mu kama hotel ina bukatar kaina ya dauki caji.
"Amman fa Ba zan dade ba akwai babban bakon da zan yi yana hanya daga Kaduna.
Da haka suka karasa cikin gari wurin TK ta karbi sako sai suka dauke hanyar hotel ɗin da take buƙata.
Ta tusa soyayyen dankali da ta saka huwaila tayi mata na Hausa sai kuma miyar source ta tarugu wacce taji kayan haɗi,ga cup ɗin tea a gefe,a duk lokacin da ta tuna yanayin da suka kasance tareda yayanta sai taji wani abu na bin duka jinin jikinta. Wani irin yanayi ta tsinci kanta ciki wanda ba zai fassaru ba gashi tsoron yayan nata ya hanata zuwa taga halin da yake ciki,door bell da suka ji ana dannawa Huwaila ta fito daga kitchen da sauri
baki ta buɗe tana kallon Aydah da komai bataci ba "wai har yanzu zazzabin ne?"daga kai kurum Aydah tayi kici ko kaɗan ne sai kisha magani Aydah bata dai ce komai ba Huwaila ta nufi kofa ta buɗe baƙin fuska tagani Aunty Raliya dake waya tana gamawa ta karaso tana yiwa Huwaila wani kallo sai da ta shaki numfashi ta fesar cike da izza tace."mun zo da masu haɗa kayan amarya za a shigo dasu.
Sai da zuciyar Huwaila ta kusa fitowa daga kirjinta Aunty Raliya bata tsaya sauraren Huwaila ba,tayiwa mazan dake bayanta umurni akan suje su fara shigowa da kayan a sama zasu sameta dan ranar sun zo ganin gidan,tun da Aydah taga Raliya Madawaki ,ta shigo cikin parlor take kallonta da mamaki tana ta son ta tuna inda ta san fuskar ta sai kuma ta manta ganin ta nufi up stairs tamkar wacce tasan gidan,da wani irin kallo tabi Raliya har ta bacewa ganinta wani irin miƙewa tsaye tayi tana bin upstairs ɗin da kallo kafin ta mayar da dubanta akan Huwaila ta kankance ido tana faɗin ."wacece wannan Aunty huwaila ?"shiru Huwaila tayi kafin tace ''wanda zasu jerawa Rumaisa kaya ne.
Wani irin dokawa kirjin Aydah ya shiga yi da ido take bin Huwaila tana son tantance mai kalmar jere ke nufi, kafin ta dawo cikin hankalinta a birkice Aydah ke faɗin."duk fadin ƙasa bai masu ba sai sun je sama?"bangaren yayanmu fa Aunty Huwaila."ita ma Huwailar shiru tayi tana Rasa mema zata cewa Aydah jin Huwaila tayi shiru yasa Aydah ta nufi stairs ko gani ba tayi saboda ɓacin rai har wani dishi -dishi take gani kai tsaye ɗakinta ta nufa wayarta ta dauka har hawaye sun fara Rolling cikin fuskarta lambar Yaya Abba tayi dialling,har tagama ring bai daga ba kara kira tayi nan ma shiru tana kara kira akace a kashe
Wani irin kuka ta fashe dashi tamkar wata karamar yarinya ta tsani wannan Rumaisa da duk abun da ya shafeta bata tunanin zata taɓa son Rumaisa har abada. Wani irin haushin yaya Abba yazo ya danne mata zuciya lokaci ɗaya,meyasa meyasa duk fadin ƙasa bai isheta ba sai anan?
Ana nufin kayansu za'a kwashe a saka mata nata.wannan karon babu abun da ke cikin kanta sai Siyama da ta faɗo mata lokaci ɗaya,lokacin da Siyama ta daga wayar tamkar ma bacci take sai dai kukan da Aydah take yi ta cikin wayar yasa tayi saurin miƙewa zaune,tana murza idanunta
Cikin tashin hankali take faɗin "menene ko baki da lafiya ne?"nan ma
Aydah still shiru tayi sai kukan da take yiwa Siyama din tamkar zata fasa mata dodon kunne."Aydah zan kashe wayata tunda bazakiyi magana ba.
Siyama ta faɗa a mugun hasale cikin kuka Aydah ke baiwa Siyama labari ta karashe da faɗin
"Da gaske yayanmu bai hakura da wannan Rumaisar ba Aunty siyam.!"jin nake kamar na kashe kaina zuciyata ciwo take min!"da sauri Siyama tace kina jina Aydah "idan kina ɗaki ke kaɗai ki tafi wurin Aunty Huwaila yanzun nan zan karaso kina jina?"
Daga kai kurum Aydah tayi yanayin da take jin kanta aciki ba zai barta ma tayi magana ba
Da sauri Siyama ta diro daga kan bed kai tsaye wanka ta shiga agurguje take yin komai ko tunanin karin kumallo batayi ba ta dauki karamar handbag dinta ta zuba duka abubuwan da zata bukata ,kai tsaye ɗakin Mami ta shiga ta tura kofar ɗakin da sallama,Mami ta amsa tana kallonta tsaye Siyama tayi ta rasa me zata faɗawa Mami dan har ga Allah bata taɓajin haushin yayansu ba irin wannan lokacin ace duk faɗin."gidan Rumaisa bazata zauna a kasa ba sai a sama.wannan ai zalunci ne dan anga Aydah ƙaramar Yarinya baya na nufin bata san Abun da take yi ba. Zama Siyama tayi tana tauna maganganun da zata faɗawa Mami, can dai tayi karfin halin faɗin."Mami dama zanje gidan Ahdah ne,idan kin isa ki gaisheta."Mami ta faɗa kai tsaye
Sosai Siyama ta sha mamaki dan batayi tunanin Mami zata barta taje cikin sauqi ba,dan a kwanan baya Mami har rantsuwa tayi akan idan siyama taje gidan Aidah bada yawunta ba Allah ya isa.!!"kuma har ga Allah tayi furucin ne saboda idan aidah bata ganin kowa kusa da ita bata ganin su Siyama ,na zuwa wahala zai saka ta gudu da kanta ,sai dai yanzu a kwana biyun nan Aydah na manne aranta karfin hali kawai take
Yadda ta tsani Rumaisa kamar yadda ta tsani mutuwarta. Wani bangare tana taya yar tata jimani wai kamar aidah ce za'ayiwa kishi abar maza kawai munafukai !!"yan tofin Allah tsine...!"sallama Siyama ta yiwa Mami da har takai bakin kofa ta dakatar da ita ta ce ta debi dambu ta kaiwa Aydah ,murmushi Siyama tayi tana faɗin "to ta gode Mami,sanin murmushi munafurci ne Siyama ta ke yi yasa Mami ta bita da kallo,koda Siyama ta iso Aydah na a ɗakin Huwaila tayi kuka har ta godewa Allah da ta gaji sai tayi shiru sai yawan ajiyar zuciyar da take saukewa,da sauri Siyama ta karasa wurin Aydah ta kira sunanta tana riƙota jin muryar Siyama yasa Aydah ta shiga buɗe idonta da suka yi mugun nauyi, Siyama ta rike Aydah a jikinta kamar jira Aydah ke yi ta rike Siyama tayi tana kwantar da kanta cikin kafadarta wani kuka mai cin rai ta fashe dashi dakyar Siyama ta gaisa da Huwaila ?"tana tambayar Aydah tayi karin kumallo?"girgiza kai kurum Huwaila tayi "idan babu damuwa dan Allah Aunty Huwaila a kawo min wani ni da Aydah a ɗakinta muci ki haɗamin bakin shayi da haka taja hannun Aydah suka nufi sama tana jin hayaniyar masu haɗa kayan Rumaisa a parlor da sauri Aydah ta shige ɗakinta wani irin kuka mai cin rai na kwace mata anan ta zube kan rug ta haɗe kai da gwiwa ta shiga rera kuka shiru Siyama tayi tana kallon little sis dinta wani abu taji yana karyewa acikin zuciyarta ƙarasawa tayi tana dago Aydah ta haɗata da jikinta tana dan bugun bayanta alamar rarrashi.
"Be a gud girl mana baby Aydah."har zaki daga hankalinki ban cin kin san yayanmu yafi kowa sonki me akayi-akayi Rumaisa ai bata isa ta raba ki da yayanki ba.
Cikin kuka da majina Aydah take faɗin."Ban cin gashi nan a bangarensa ake mata jeren ɗaki,
Kenan ma a ɗakin nasa zata rika kwana koni dake kanwarsa ai baya kwana tare dani sai ita, wallahi ba zan yadda ba ranar da ta gwada kwana a bangaren yayanmu zata ga hauka.
Aydah ta faɗa sounding so very jealousy a muryarta,sau ran kaɗan Siyama ta saki dariya sai dai babu halin yinta tasan rigimar Aydah ba mai sauki bane yayansu kawai ne yake iya handling dinta ko Mami da Daddy,basa iyawa Siyama ta langwabe kai tana faɗin "baby Aydah an girma daman kina kishin yayanmu har haka.
Shiru kawai Aydah ta yiwa Siyama ,tana tare hawayen da suka kasa tsayawa cikin fuskarta komai na duniyar bata jin dadinsa. Huwaila ce ta kawo masu kayan karin kumallo dakyar tasa Aydah ta sauko suka yi karin kumallon su a tare kafin ta bata sakon mami, cike da farin ciki Aydah ke faɗin "Mami ce ta baki ki kawo min da gaske yaya Siyam.?"ta faɗa da wani yanayi dauke a muryarta Juya ido Siyama tayi tana sakin murmushi take faɗin."da gaske nake baby sis.
"Ni naji ma ina so naganta kawai mu tafi gida yaya Siyam bana son ganin mutanen nan,da sauri Siyama ke faɗin "Ba gashi nazo ba muyi zaman mu anan mana,anjima kaɗan mu fita yawo daman zan je gidan Saudah kinga sai mu tafi ku gaisa duk sanda muka haɗu a school sai tayi zancenki.
Murmushi Aydah tayi ta mayar da hankalinta wurin cin dambunta
tana ta so ta yiwa yaya Siyam zancen yadda yaya Abba ya sha mata nono bata san ta inda zata fara ba ko Huwaila kasa fadawa tayi dan wata irin kunyar Huwaila take ji,dan gyaran murya Ahdah tayi tana kallon Siyama kafin tace daman yaya Siyam akwai tambayar da nakeso nayi maki dan Allah.
"ina jinki little sis.
Aydah ta shiga ja fingers dinta sai kuma ta sakasu a baki tana ɗan cizawa. "Wannan kallon fa Aydah?"
"Ban san ta inda zan fara bane Yaya Siyam.
Siyama ta warewa Aydah ido da sauri Aydah ta rufe ido tana sakin yar dariya , dariyar Siyama tayi ki faɗamin bana son gulma.
Siyama ta faɗa tana kallon Aydah ɗin,kin min alƙawari dagani sai ke ?daman tambaya kawai ce zanyi da kema ba zan faɗa maki ba sirri na ne.
gyaɗa kai Siyama kurum ta shiga yi ta zubawa Aydah ido tana sauraren me zatace "dama jiya ne uhm ummm to ki daina kallona ido cikin ido yaya Siyam.
Da sauri Siyama ta dauke kanta.
"Ba jiya bane sai yayanmu yayi min kiss ya sha min no.....da sauri Siyama ta rufe bakin Aydah tana wani irin zaro ido,baki da hankali wannan yarinyar da gaske bakida hankali
"Ubanwa ya faɗa maki ana faɗin,wannan maganar "Tamkar Aydah zata yi kuka ganin yadda Siyama ta rude lokaci ɗaya. "Nifa daman tambayarki zanyi ai naga shi yayana ne Right?"yace babu aure a tsakaninmu kuma a islamiyya ana faɗa idan babu aure tsakaninka da mutum bai kamata.....!"da sauri Siyama ta katseta ta gano dai har yau kanwar tata doluwa ce da alamar babu Abun da ya shiga tsakaninta da yaya Abba ,har lokacin kallon juna kawai suke wani irin tausayin kanwarta ya lullubeta musamman idan ta tuna wacce za'a kawo mata a matsayin kishiya. "Duk karatun littafan Hausan da kike har ma dana turanci sun tashi abanza, waya faɗa maki yaya Abba ba mijinki bane?"
Siyama aje kunya tayi ta soma yiwa kanwar tata bayani sai taga Aydah ta tura baki tana faɗin "nifa duka nasan waya'annan abubuwan yaya Siyam ni wallahi tsoron yayanmu ma nakeji tun jiha baki ga yadda ya birkice ba kamar mai dauke da jinnu akansa.
Baki sake Siyama ke kallonta
"Auh Allah ?"tsoronsa kike ji kou?"shikenan tunda bakya so ya taba ki idan Rumaisa tazo sai ya taba ta ai ta ba za ta ce bata so ba.
Nan take Aydah ta dauke wuta tamkar an aiko mata da sakon mutuwa yadda take tsare Rumaisa da ido yasa tace
"Ehhhh! kina kallona gaskiya na faɗa sai ita ya rika tabata tunda tsoro kike ji.
kwanciyya Aydah tayi tana wani juyawa Siyama ɗin baya da alamar dai maganar Siyama ta bata mata rai har ta hango yadda Rumaisa zata hau jikin yayanta haushi duk ya gama cikata ita ko hannun Rumaisa bata son ya rika barantana yayi wani abu da jikinta. Dakin Siyama ta rika kallo ta sauke numfashi tana faɗin."duk yau baki share dakin nan ba Aydah kalli kan gadonki? kamar kinyi dambe akansa halinki na nan ba zaki taɓa canjawa ba kinga idan Rumaisa tazo sai ta yiwa yayanmu gyaran ɗaki.
A wani irin zabura tayi ta mike tana kallon Siyama,sauran kaɗan Siyama ta saki dariya da gaske little sis din nata she's madly in love with Yaya Abba.! addu'a Siyama ke Allah yasa shima yayan nasu yana jin kwatankwacin abun da Aydah ke ji akansa.










#JEEDDAH ALIYU
#ASMY B ALIYU
#KURMAN ALLO






Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[1/11, 2:41 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels






066.




Sai da Siyama ta taimaka mata suka gyara ɗakin aka share akayi mopping har toilet ta kunna turaren wuta ,bayan sun gama Siyama ta koma ta kwanta ganin Aydah still tana tsaye tamkar wacce aka saka tayi tsaye ɗin.
"Ba wankan zaki shiga ba rana nayi,na fiso na koma gida da wuri?"
Siyama ta faɗa tana kallon Aydah ɗakin yayanmu zanje na gyara. Ɗan buɗe ido Siyama tayi kafin ta mike daga kwance da take tamkar wacce ta tuna wani abu tace "To muje ki gyara masa mana.
Koda suka shiga su Aunty Raliya na a parlor ana saka kujeru dama daga Siyama har Aydah babu wanda ya kulasu sukayi hanyar master bedroom ɗin yayansu da ido Aunty Raliya tabisu ta rasa ma wacece matar Abban acikinsu. tunaninta yafi karkata akan ko Siyama ce.
Siyama sai tsaki take ita ɗaya, idan banda wulakanci duk parlor gidan nan ba'a ga inda za'a aza mata kujeru ba sai a bangaren yaya Abba dan salon iyayi meyaci parlor kasa yaushe ma aka zuba kayan, ita dai Aydah batace komai ba kan soofa ta koma ta zauna duk ranta a dagule ta rasa meke mata dadi."auh zaunawa ma kikayi ko kin fasa?"ki shiga ki wanke masa toilet ki bari na gyara gadon,ai gara ɗakin yaya Abba da dakin
ki dan nasa yafi tsari duk abun da yayi amfani yana mayar dashi wurinsa. Sai kusan 2 na rana suka yi shirin fita har ɗaki Aydah ta samu Huwaila lokacin ta kammala abincin rana tana kwance kawai tana hutawa.
"Aunty Huwaila zamu fita da yaya Siyam Amman ba dadewa zamu yi ba, Huwaila tabi Aydah da kallo tana cikin riga da skirt na Atamfar kalar blue da fari ajikinta tayi kyau sosai kamar ka saceta ka gudu sallama suka yiwa Huwaila, acikin motar Siyama ta kunna wakar hamisu breaker mai suna(BURI)shiru Ahdah tayi gami da kwantar da kanta cikin seat ɗin motar tunanin yayanta duk ya cika ta yau koda ta tashi bata gansa ba. Huwaila ma tace mata bata ji fitarsa ba wata irin kewarsa ce ke zagaye mata zuciyarta
babu wanda yasan yana office dan rufe kansa yayi sai wuraren la'asar da yayi bacci ya tashi ga kansa da yayi masa wani irin nauyi ga mugun jirin da yake ji sai lokacin ya tuna da ko break
fast bai yi ba dafe kansa yayi yana karanto addu'a dan neman samun nutsuwa ,sai da ya kai minti goma a haka ya lalubi car key ɗinsa da ya aje ya mayar cikin aljihun wandonsa, ta baya ya fice daga office ɗinsa addu'a daya ya ta maimaita wa Allah yasa kar ya hadu da wani a parking lot Allah ya karbi addu'arsa har ya fice babu wanda ya lura sai maigadi da ya buɗe masa gate sai lokacin ya kunna wayarsa ya ajeta messages sun gama shigowa wanda duk na Rumaisa ne sai kuma na MTN.
Saƙon Rumaisa na farko shi ne "Habeebi inata kiran wayarka a kashe hop Lafiya?"sai kuma na biyu su Aunty Raliya zasu zo da mai jera kaya,
Na uku."ka sakani a damu dan Allah ka kunna wayarka muyi magana. haka ya ta karanta sakonanta duk na tambayar lafiarsa ne,dilaliing lambarta yayi tamkar jira take tana shiga ta dauka yana jin yadda take jan numfashi tana saukewa cikin shagwaba take faɗin."ba ka saba kashe waya ba meya samu wayarka tun safe.?"nan ma shiru yayi babu amsa shi ya daga hankalin Rumaisa?"baka da lafiya ne hayati.
"Ya kike?"ya faɗa da muryar da ta kusan karya zuciyar Rumaisa,kamar baka da lafiya Are you really owk?"Lafiya lau muryarka wani iri kana ina haka?"kamar kana driving,ina hanya Rumaisa idan na isa zan kiraki.
Bai jira me zata faɗa ba ya sauke wayar,dama bukatarsa taji lafiyarsa kuma taji baya son magana da kowa da komai duk lokacin da ya tuna abunda ya haɗasa da Aidah kwakwarsa hargitsewa take baya ma son ya tuna wani tsakar kansa da na Aydah yake jin yana sauka cikin zuciyarsa,aodaddafe ya karasa gida jikinsa gabaki ɗaya ciwo yake yana kuma bukatar yin wanka Huwaila taje ta buɗe masa kofa lokacin da ya shigo gidan gaishesa tayi batareda ya haɗa ido daita ba ya amsa kafin yace yana bukatar bakin tea ta soya masa egg ta baiwa Aydah ta kawo masa sai da zuciyar Huwaila ta tsinke.cikin rawar murya take faɗin. "Yayanmu Aydah sun fita da Siyama.!"wani irin kallo ya juya yana yimata tamkar itace Aydah
Wanda Huwaila tasa hanjin cikinta sun fara ya mutsewa bai kara cewa komai ba ya wuce sama direct zuwa lokacin su Aunty Raliya sun gama jerawa Rumaisa kayanta,bin parlor ya riƙa yi da kallo yadda aka canja sa lokaci ɗaya har aransa yaji tsarin wancan kayan yafi yimasa kyau akan wannan ko kaɗan baiga abunda ya burgesa ba acikin parlor sai window side na hotonsu da aka kafa a parlor wanda yasan aikin Rumaisa ne ire-iren hotunan da take dauka dashi ne a gidansu ta cira ta bada aka wanka mata ,hoton yayi kyau sosai duk da Rumaisa kawai ke murmushi a hoton kai tsaye master bedroom ɗinsa ya wuce,yana bin bedroom ɗin da kallo sai Ƙamshin turaren wuta ke tashi kai tsaye ransa ya faɗa masa aikin Siyama ne dan yasan Aydah son jiki ba zai barta ta gyara masa daki ba ita ma neman me gyara mata take dan haka yake gyara abunsa bai taɓa bai wa Huwaila damar shigowa bangarensa ba. Sai lokacin ma ya tuna fitar da Siyama ɗin tayi da Aydah ransa yaji yana wani irin ɓaci daukar wayarsa yayi ya shiga kiran Siyama har ta gama bata dauka ba yana kara kira ta dauka da cikakkiyar sallama bai tsaya karbar sallamarta ba yake tambayarta ina suka tafi?"da izinin wa zata zo har gidansa ta dauki Aydah su fita yawo. yadda Siyama taji yana faɗa tamkar zai canyeta a wayar da alamar ransa a ɓace yake taji idanunta sun ciko da hawaye,minti goma sha biyar

48 / 80