Author : EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category : KDP NOVELS
ya koma parlor sa ya dauki wayarsa ya kira AB cike da girmamawa Ab ya gaishe da Daddy, Daddy ya amsa yana tambayarsa gida da kuma iyalinsa. Cike da jin kunya Abban yace duk suna lafiya nan Daddy ke sanar dashi zancen auren Siyama, sosai Abba Bashir yayi farin ciki kana ya yiwa kanwar tasa addu'ar fatan alkhairi da haka Daddy ya katse wayar yace sai sun haɗu gobe a office su ƙara tattaunawa. Siyama, Daddy ya kira a waya yace ta kira masa Sadiya.
Siyama dake zaune a parlor tare da Mami,ta kalli Mami da sauri ganin irin kallon da mami keyi mata yasa ta saurin sadda kai ƙasa Mami tace "waye ya kira ki a waya.?"
"Daddy ne wai nayi masa kiran yaya Sadiya.
Jin abun da Siyama ke faɗa yasa gaban Mami yayi mummunan bugawa, Siyama batareda ta kula da yanayin da Mami ta shiga ba ta nufi up stairs dan kiran Sadiyar zaune ta samu Sadiya da waya a kunnenta da alamar waya take ,tana jin anyi knocking kofar ɗakin daman ta katse kiran, tayi gyaran murya, Siyama ta shigo ɗakin a bakin kofa ta tsaya tana kallon Sadiyar da ta zama wata iri.
"ki je Daddy na nemanki a parlorn sa. Da haka Siyama ta juya ta rufewa Sadiya kofar ,wani irin tsoro na ban mamaki Sadiya ta shiga lokaci ɗaya hankalinta ya tashi ta shiga haɗa zufa duk Ac dake cikin ɗakin zufa take yi tashin hankali ya bayyana ƙarara akan fuskarta "na shiga Uku!"me kuma zai sa Daddy ya nemeta ko dai yaya Abba ya kawo masa ƙararta ne ya faɗawa Daddy ta je gidansa ta hau matansa da duka. Babu kalar tunanin da Sadiya bata yi ba duk hankalinta a tashe yake.
Hijab ɗinta na sallah ta dauka har kasa ta saka akan kayan baccin dake jikinta ta nufi kofa Mami dai sai bin ta take da kallo har ta shige parlorn Daddy da sanyi murya tayi sallama."
Ciki-ciki Daddy,ya amsa sallamar Sadiya ko shi dan tazamar masa dole ne adaddare Sadiya ta zauna kan rug cikin rawar murya ta gaisheda mahaifinta tana saukar da kanta kasa
bai saurari gaisuwar da take yi masa ba yace "kina da labarin nan da kwana biyu za'a kawo kudin saka ranar siyama da kayan lefenta na jiki shiru har yanzu?"maganata tana nan babu fashi keda Siyama zan aurar a rana ɗaya,wani irin tashin hankali Sadiya ta shiga lokaci ɗaya cikin rawar murya Sadiya ke faɗin "Ni fa Daddy har yanzu bani da tsayayye why not a fara yin na Siyama, ɗin in yaso daga baya ayi zancen nawa.
A mugun fusace Daddy ya dakatar da ita yana wani daka mata tsawa.
"me na faɗa maki a kwanan baya huhh?"
Idon Sadiya har sun tara kwallah ta fara yi wa Daddy rantsuwa ita fa yanzu babu wanda ke zuwa wurinta.
"Da kyau tau naji ni zan nemo maki miji da kaina.
A wani irin firgice ta daga kai tana kallon mahaifin nata babu alamar wasa a kalamansa tuni hawaye suka fara gudu cikin fuskar Sadiya wani irin kalar tashin hankali ta ji yana zagaye zuciyarta tasan tabbas tunda mahaifinta ya yanke hukunci babu wanda ya isa ya canjasa muryar Daddy,ta ji yana faɗin "tashi ki bani wuri.
A wani irin gigice Sadiya ta fito parlorn mahaifin nata hankalinta tashe tayi wurin Mami tana kwala mata kira tana gunji kuka.
#JEEDDAH ALIYU
#ASMY B ALIYU
#KURMAN ALLO
[2/2, 10:15 AM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels
093.
Mami !!Mami!!"Sadiya take kiran sunan Mami agigice, yanayin yadda take nufo Mami,cikin fita hayyaci yai bala'in tsinka zuciyar Mami da sauri ta tash ta nufi Sadiya tana ƙoƙarin riƙota zubewa kawai Sadiya tayi akan rug tana ƙara sakin wani sabon kuka mai fitowa tun daga ƙarƙashin zuciyarta, tana jin yadda zuciyarta ke wani irin zafi tana tuna yanayin yadda Daddy ke mata magana tasan waye mahaifinta dakyar idan ba sadaka zai bai wa wani ita ba.
"kiyi min bayani duk kin bi kin gigitani me Daddyn naku yace maki?ita dai Siyama tana zaune a parlor har lokacin tana danna wayar hannunta tamkar bata cikin parlor."Mami da gaske Daddy sadaka zai yi dani kiyi masa magana wallahi da gaske nake ya Mami ba zan iya zaman aure da kowane namiji ba idan ba yaya Abba ba,kiyi masa magana yadda zai fahimceki.
"shi Daddyn naku ne yace aure zai yi miki?"
Mami ta faɗa da wani tashin hankali kwance cikin fuskarta.
"Haka ya faɗa yace babu fashi tare za'a saka mana rana da Siyama.
Wani zufa Mami taji tana haɗawa ta kalli sadiya a gaggauce tace ta taso su je ɗaki daman akwai maganar da za suyi dakyar Sadiya ta miƙe tabi bayan Mami,tana jin yadda kwakwalwar kanta ke wani irin hargitsewa tana bukatar jin kanta sama na ɗan wani lokaci,da wani irin kallo siyama,ta riqa bin Mami daita da Sadiya.
Mami jin tayi kamar idanun Siyama na yawo akansu sai taji jikinta yayi sanyi ɗan juyawa tayi tana kallon saitin da Siyama take,suka haɗa ido lokaci ɗaya Mami ta haɗe rai Siyama ita kuma tayi saurin dauke kanta ta mayar akan wayarta. Mami bata ce komai ba ta juya ta nufi ɗakinta Sadiya na biye da ita tana shasshakar kukanta zama Mami tayi a gefen bed yayin da Sadiya ta zauna gefenta. Mami ta riko hannun Sadiya duka biyum ta riqe cikin nata."natsuwarki nake bukata Sadiya sai kin daidaita natsuwarki wurin ɗaya kamin na iya sani mafita da zan nemo.
Da sauri Sadiya ta girgiza kai hawaye na rolling cikin fuskarta da wani irin raunin murya Sadiya tace."Mami ta yaya?"auren dole fa Daddy yake kokarin yayi min taya kike tunanin na kwantar da hankali na kullum alkawari kike min baki taɓa cikamin ba koda sau ɗaya ne sai yaushe zan samu farin ciki ahali wanda nake so muradin zuciyata yana auren ƙanwata.
Har asiri aka yi wa yaya Abba dan ya saki Aydah ya aure ni shiru Mami kusan wata nawa da yin asirin amma har yanzu babu abun da ya canja. Sadiya ta karashe maganar cikin shesshekar kuka. Sai jikin Mami,yayi sanyi lokaci ɗaya, ta rasa wane kalar so Sadiya ke yi wa Abba Bashir bata taɓa ganin irin wannan soyayyar ba.
Yayi yawa har yana neman zauta tunanin yartata.
"maganar Abba da kin sakawa kanki salama kin ciresa acikin lissafinki dan ba zaki taɓa samun sa ba har abada.
kalaman Mami ba ƙaramin tarwatsata suka yi ba da wani irin shock take kallon Mami,sai kuma ta kwace hannayenta dake cikin na Mami tana sakin wata irin dariya da bata da alaka da farin ciki.
"Dama kin cemin wasa ne Mami!"
Karki yi wasa da hankali na,ke kika yimin alkawarin aurensa meyasa zaki ce na daina?"akan me zan daina?idan kika ga na daina sonsa bana cikin duniyar nan Mami.
Sadiya ta faɗa cikin ihu tana jin kanta a sama hannu tasa tana dafe kanta duka. Shiru ya ratsa a tsakaninsu na kusan minti biyar kafin Mami ta buɗe baki "Mun yanke shawarar haɗaki aure da Jamal,zai fi maki sauki akan ki auri mutumin da baki san waye Mahaifinki zai haɗaki dashi ba.
A wani irin birkice Sadiya ta daga kai tana kallon Mami da mugun mamaki,wani irin murmushi ta saki wanda ita kaɗai ta san ma'anarsa kafin ta miƙe tamkar wata zararra tana kallon Mami."kara ma kice min wasa ne Mami Jamal fa ƙanin baya na shi kuke tunanin na aura me zan tsinta ajikinsa?"Mami duka-duka shekarun jamal nawa?"ai wannan raini ne.
A mugun fusace Mami ta katse ta "Ko shekara ɗaya kika basa meyasa ke bakya jin magana bakya daukar shawara?"to haka naga dama na yanke akanki karki kuskura kiyi min musu Sadiya ranki zai ɓaci na gama magana zan samu mahaifinki da zancen.
Ita dai Sadiya kallon Mami kurum take tana mamakin karfin halinta juyawa kawai tayi tabarwa Mami ɗakin dan maganganun mamin,ma ciwon kai suke saka masa ko a mafarki ya za'ayi ta auri Jamal yaro dashi ai gara Daddyn ya zaba mata duk wanda yaga dama da dai ta auri Jamal yaro dashi ai wannan ma raini ne. Da ido Mami ta bita har ta fice daga ɗakin,ajiyar zuciya kawai Mami ta sauke wata kwallar takaici ce ta taru a idonta ta tsinewa Abba Bashir yafi sau dari acikin ranta duk shi ya ruguza masu dukkan wani farin cikinsu.
Washe gari karfe goma na safe bayan Daddy ya wuce office daman Mami ta kira Hajiya Zeenah a waya akan ta jirata gata nan zata taho suje wurin Malam.
Sai da Mami,ta tsaya ta ciri kuɗi tayi arranging ɗinsu cikin wata yar ƙaramar bag ta nufi gidan Hajiya Zeenah,tare suka wuce wurin Malam
A hanya Hajiya Zeenah ta kalli Mami,
Ta sauke numfashi kafin tace "Allah yasa dai kar ya canja ra'ayinsa ko ya kara mana kuɗi. kusan sati nawa da yin maganar,kin san halinsu basa son jira.
"in Allah ya yadda ma haka ba zata faru ba.
Mami ta faɗa da wani yanayi a muryarta,da dare Mami ta shiga kitchen da kanta ta yi wa Daddy abinci da tasan yafi so ko Siyama ,da ta shigo ta karbi girkin cewa ta yi kawai ta yi tafiyarta zata yi Siyama na daki bayan magarib kiran Aydah ya shigo a wayarta dauka tayi cike da farin ciki Aydah ke faɗin."congratulations yaya Siyam ,
Allah ya sanya Alkhairi kin kusa zama Mrs Saleem Sada."juya ido kawai Siyama tayi da murmushi dauke a fuskarta,tana jin yadda Aydah ke farin ciki ta cikin wayar da har ta kasa boye hakan. Ni wallahi yaya Siyam ba ƙaramin farin ciki nayi da ba da jiya yayanmu ya faɗamin ko ba komai yaya Siyam rayuwar gidan aure akwai daɗi wallahi kamar yadda dai kika san anayi a novel.
Ta faɗa tana wani fashewa da dariya "Allah ya shiryaki auta da alamar yayanmu ya sakiki a hanya dayawa.
Dariya kawai Aydah tayi ita ma dariya Siyama tayi sun daɗe suna waya sai can cike da damuwa a muryar Aydah take faɗin "to ita yaya Sadiya ta tsayar ne?"
Dan shiru Siyama ta yi kamar bazata ce komai ba sai kuma tace ":6nima ban sani ba dan ajiyar zuciya Aydah ta sauke tana bai wa Siyama labarin yadda Sadiya ta zo har gidansu tayi mata duka ita da Rumaisa baki Siyama ya buɗe tana sauraren Aydah cike da mamaki,dan babu wanda yayi zancen daga Mami har Sadiya "meyasa baki kira Daddy a waya kin faɗa masa ba.?"
Siyama ta faɗa sounding so piss up a muryarta Aydah ta saukar da murya tana faɗin."yayanmu fa ya hana na kira sa cewa yayi nabar komai a hannunsa.
ɗan tsaki Siyama taja haƙurin yayanmu yayi yawa gaskiya.
"uhmmm!"
kawai Aydah tace
"Ya Mami?"
Aydah ta canja alakar zance.
"Tana nan lafiya lau.
Cikin rvawar murya Aydah ke faɗin "Mami ta daina sona yaya Siyam,wayar ma sai taga dama take ɗagawa idan na kirata ina mata magana ta wahtsapp ko dubawa ba tayi.
Aydah ta karashe maganar cikin rawar murya ba ƙaramin ƙaryawa Siyama zuciya Aydah ta yi ba ita kanta idonta har sun ciko da kwallah karfin hali kurum take yi "ki yi wa Mami addu'a komai zai zama daidai kin san ba halin ta bane canjata aka yi lokaci ɗaya.
"Yaya Siyam a kullum ina saka Mami a addu'a ita da Daddy.
"Da kyau ki cigaba da yi komai zai wuce kamar ba'a yi ba.
Siyama sun dade suna waya da kanwartata kafin suyi sallama mami ce zaune a parlorn Daddy bayan ya gama cin abincin da yau ta sakasa cinsa shi ɗaya cikin parlornsa sai hira take masa a hankali tana yanka masa kankana cikin wani ƙaramin bowl Daddy saurarenta kurum yake,har suka zo kwanciya Mami ita dai bata ga alamar yanayin maigidan nata ya canja ba sai kawai tabar komai aranta maybe sai zuwa gobe ko washe gari lafiya lau suka rabu da Daddy har ya wuce office.
Daddy na zaune a office duk da yanayin da yake jin kansa cikinsa haka ya dauki waya ya kira Mami,akan Sadiya tana da bako bayan la'asar wannan karon umarni yake basu daga ita har Sadiya duk wanda ya kuskura yaƙi bin umarninsa wallahi sai dai yabar masa gida. Bayan ya sauke wayar Mami duk hankalinta a tashe yake bata taɓa jin Daddy yana faɗa da wannan yanayin ba,kiran lambar Hajiya Zeenah ta yi bayan ta dauka ,cikin rawar murya Mami ke faɗin."Hajiya Zeenah tun jiya nake zuba ido shiru har yanxu ban ji wani abu ya faru ba.
"kuma kin tabbata yaci abincin?"
"wallahi ina zaune yaci abinci
Kuma na zuba maganin aciki.
"kin san magani ba lokaci ɗaya yake aiki ba mu zuba ido har zuwa kwana biyu mu gani.
Da sauri cikin rawar murya Mami tace "kwana biyu ai yayi yawa Zeenah.
"dadina dake kuma gajen hakuri mariya kin san yadda aikin malamin nan yake yanayi meyasa za ki damu kanki in har kin tabbata kin zuba maganin nan komai zai faru.
Dan ajiyar zuciya Mami ta sauke tana faɗin."to Allah yasa!
Mami ta kira aunty Safeena awaya ta tambayeta sun yi magana da Jamal da kuma mahaifinsa "yaya Jamal baya ma kasar yanzu haka ya koma makaranta daman nasan haka zai faru jiyaa ina komawa nayi masa magana yau yabar kasar daman nasan ba wai yarda zai yi ba ke ce dai kika dage.
Cike da mamaki Mami,ke faɗin."sai kuma kika biye masa ke kika haifesa Safeena ko shi ya haifeki?"
Da sauri aunty Safeena ta katseta tana faɗin "Ya zan masa yaya kin san Jamal ya wuce ayi masa auren dole,kuma kin san mahaifinsa da masifar son ya'ya kamar me.
"Allah ya kyauta!
Mami ta faɗa tana katse wayar batareda ma ta ƙarashe sauraren kanwarta ta ba.
Kai tsaye Mami ɗakin Sadiya ta nufa ta sameta tana bacci tashinta ta shiga yi cikin ɓacin rai Sadiya ta juyo duk a tunaninta ko Siyama,ce ta sauke mata kwandon masifa sai taga Mami agabanta ɗan yamutse fuska tayi tana kallon Mami,
"Kina nan kina baccin asara na tabbata ko sallar azzahar baki yi ba idan kina da lokaci sai ki tashi ki shirya kina da bako bayan la'asar wannan Umarnin mahaifinki ne ba nawa bane.
D haka Mami ta juya tabarwa Sadiya ɗakin dan wani irin takaicin Sadiya take ji sai kuma ta yi wani irin murmushi da gaske ko wanene Daddy yake so ya haɗata dashi tana tausayin rayuwarsa ta yarda ta amince zata karbi duk wanda Daddy ya kawo mata a matsayin miji sai dai ta dauki alwashin ba zata taɓa basa farin ciki ba a gidan aurensu. Kusan karfe biyar maigadi yayi knocking ƙofar parlor,
Mami da kanta taje ta buɗe kofar
tana kallon maigadi ya russuna ya gaisheta kafin yace "Hajiya Sadiya nada bako a compound Alhaji sammani.
Mami ta shiga maimaita sunan aranta tana tuna inda ta san sunan nan take kwakwalwar Mami, ta tariyo mata Alh sammani abokin maigidanta ne tun suna yara kusan ma yafi Daddy kuɗi kuma yana da matar aure wacce sama-sama suke shiri da ita saboda matar tasa mugun girman kaine da ita na masifa.
Mami sosai tayi mamaki dan tasan alhaji sammani duk lokaci da ya nemi ya yi aure auren baya tabbata ko an fara maganar sai ta warware saboda yadda uwargidansa ke biyar bokaye na masifa,hankalin Mami,ya tashi sosai tasan Hajiya Saratu tasan shu'umar mace ce Daddy,yana nufin Alhaji sammani zai aurawa Sadiya
Mutuwa yake so tayi kenan,dakyar Mami tace ya kai bakon parlor baki Sadiyar tana zuwa,da haka Mami ta juya ta nufi ɗakin Sadiya duk a rikice take ta samu Sadiya zaune tana danna waya kallo ɗaya ta yi wa Mami,ta dauke kai.
"kin san dawa mahaifinki ke kokarin haɗaki aure?"
Ita dai Sadiya bata kalli Mami ba ta cigaba da danna wayar hannunta dan ita ba wai wani damuwa tayi da auren ba yanzu a fusace Mami,tace "Ina miki magana kima mayar dani wata yar iska Sadiya.
Da mamaki Sadiya ke faɗin."me zance Mami ina jin mun riga mun gama maganar nan.
A rude Mami ke faɗin "Alhaji sammani ne fa abokin Daddynku mijin Saratu!
Wani murmushi Sadiya tayi ganin yadda Mami,ta rude "Mami yana da kuɗi daman sune matsalar kowa a duniya, zan iya aurensa a haka idan bai shiga rayuwata ba nima kar na shiga tasa.
Baki buɗe Mami ke kallon Sadiya.
"Ke har kin tsarawa kanki rayuwa dashi kenan mijin Saratu ne fa?
matar dake bin bokaye har na fitar hankali shi ne kike cewa za ki aure mijinta.
Wani murmushi Sadiya ta yi tana faɗin "Ai ni nafi son haka,kinga kowa ya iya allonsa ya wanke da kansa ya ƙaraso kenan?"Mami dai saboda shock kasa cewa Sadiya komai ta yi dan jin take kamar ta kwadawa Sadiyar mari.
Sadiya daman tayi wanka ta dauki dan ƙaramin veil ɗinta mai shige da kayan ta ɗora akan kafaɗarta, ta ƙarasa gaban madubi ta ɗauki turare ta shiga shafawa da haka ta fice daga dakin tabar Mami sake da baki.
#JEEDDAH ALIYU
#ASMY B ALIYU
#KURMAN ALLO.
[2/2, 10:18 AM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels
094.
Da Siririyar sallama,ta shigo cikin parlorn kallonta kawai yake da wani yanayi shimfiɗe akan fuskarsa ga zuciyarsa dake wani irin dokawa. Da gaske bai san yana son Sadiya sosai,ba sai da ya bayyana a gabanta ta zauna akan ɗaya daga cikin kujerun da suka kawata parlor ta kalli Alhaji sammani,cikin kyakkyawar shigarsa ta alfarma ƙamshinsa ya gama cika ko'ina dake cikin parlor,yana da kyau babu laifi duk girma ya fara kama shi.
Koda yake har yanzu bata ga wani namijin da zai burgeta a duniya ba baya ga yayanta. Wani yanayi ne kwance acikin fuskarta wanda ba zai fassaru ba.
"Ina wuni ta faɗa murya can kasa.
"kina Lafiya ya gida ya karatu?"
Alhaji sammani ya faɗa cike da fara'a Sadiya ta amsa da Lafiya Alhmdullahi ya kuma yara da Madam.
tayi magana tana wani sauke idonta cikin nasa ,ba ƙaramin kokari Alhaji sammani yayi ba wurin rike kansa ganin irin kallon da Sadiya ke jifarsa dashi hira suka taba yar kaɗan yana tambayarta abubuwan da take so da wanda kuma bata so tana basa amsa sauran hirar kuma ta matarsa ne da "ya'yansu biyu maza macce ɗaya. sun yi kusan awa ɗaya tare kamin Alhaji sammani ya yi mata sallama, maigadi ya saka ya kwaso masa kayan shopping ɗin da ya biya yayi mata ya bita dasu cikin gida.
Har lokacin Mami,na zaune a parlor duk abun duniya ya dameta ganin Sadiya ta shigo Parlor yasa Mami ,ta daga kai ta kalleta ita ma Sadiyar Mami,take