Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   46 / 80

135K to 138K   out of 237.2K words

ta dauka tana linke masa "Yayanmu ga abinci can parlorn ka na kawo maka, nasan yanda ka ɗebo gajiyar nan ba lallai bane ka iya saukowa ƙasa ba.
Da mamaki ya juya yake kallonta ita ko a jikinta aikin gabanta kawai take yi "Aydah bana gayamiki ki daina shigo min ɗaki gaba gadi ba? Ki fara neman izinina kamin ki shigo min ke duk abun da aka faɗa miki baya shiga kunnenki ko?"
Murmushi kurum tayi tare da nufar closet ɗinsa ta buɗe ta saka masa kayansa da ta linke tayi tsaye tana kallon jerin tufafinsa dake jere aciki can ta dauko masa wata riga armless coffee color, ta ajiye gefen gado ta sake buɗe bangaren da trousers dinsa suke ta ciro masa blue three quarter bai yi mamaki ciro masa kayan da zai saka da tayi tun da ba yau ne karo na farko da ta fara yi masa hakan ba.
"Wai Aydah ba magana nake miki ba ki fita kamin ki fusata ni.
"Allah ya ba ka haƙuri yayanmu in shaa Allah ba zan sake shigowa ba sai da izinin ka.
Tana karasa magana ta fice tana mai jawo masa ƙofa, ya dawo da idanunsa daga kallon da ya bi ta dashi yana kammala shafar mai ya dauki kayan da ta fito masa dasu ya saka ya fesa turare, yana fitowa parlor yaga Aydah zaune akan cushion tana jiran fitowarsa ta kasa ta tsare duk faɗa da yake mata bai sa ta fice masa a parlor ba ta nace masa sai da yaci abincin sosai yana gamawa ta tattara kayan ta fita dasu Huwaila tana ganinta ta biyo ta kitchen tana tambayar da yanda ta kaya a tsakaninsu "Allah Aunty Huwaila karo na farko da na ji tsoron Yayanmu ya fara raguwa a zuciyata.
Aydah ta faɗa very excited for all over her face.
"Maa shaa Allah! To daga yanzu haka za mu dinga yi masa sannu-sannu wata rana shaiɗanin da ke jikinsa zai fece duka, zan dinga tayaki da addu'a Allah ya daidaita tsakaninku kema ki ɗage da addu'a da sallar dare in shaa Allah komai zai dawo yanda yake.
Cike da farin ciki Aydah ta rungume Huwaila tana dariya ita kadai tasan irin mayuwaci hali da take ciki a dalili wannan sauyawar ta yayan nata.
*ALHAJI BASHIR MANSION*
Koda Mami da Sadiya suka dawo gida Daddy baya gida lokacin da Siyama tayi arba dasu wujiga-wujiga dasu daga Sadiyar har Mami sun fita daga hayyacinsu,sai da hantar cikin Siyama ta kada cikin kaɗuwa take tambayarsu meke faruwa ta dawo ta tarar da dukkansu basa gida kuma Balmo maigadi ya faɗa mata 'yan sanda ne suka zo suka tafi da Sadiya laifin me tayi musu?"
Rai ɓace Mami ta bata labari abunda ya faru, sosai Siyama ta tsorata ita kan yanzu Sadiya ta fara bata tsoro yanzu sau biyu kenan tana attempting kisan kai ta dinga mata alamar tambaya. Tsabar kaɗuwar da Siyama tayi kasa magana tayi sai kurum ta bi su da kallo har Sadiya da Mami kowacce su ta wuce ɗakinta Siyama bata dawo ainihin natsuwarta ba.
Da dare da Daddy ya dawo yasa Siyama ta kira masa Sadiya ta dukkansu Siyama da Sadiya suna zaune a kasan rug carpet, Mami tana zaune akan kujerar dake kusa da ta Daddy, ta wani kici-kici da fuska yayin da gabanta ke dokawa tana cike da zullumi haɗe da fargaba irin hukuncin da Daddy zai yanke wa shalelen 'yarta Sadiya kam ko a jikinta asalima ko dar bata ji ba.
Wani mugun kallo Daddy yake aika mata dashi kamin cikin kakkausar murya ya kira sunanta "Sadiya.
Ta ɗago shegun idanuwanta ta kalle shi sai kuma ta maida kanta ƙasa batareda da ta amsa ba.
"Sadiyaaaa!
Wannan karo a matuƙar fusace Daddy ya sake ambatar sunanta, ta ɗago tare da amsawa ciki-ciki "na'am Daddy!
"Sadiya ki shiga taitayinki dani idan ma wasu shaiɗanu ƙawaye ne kika haɗu dasu suke hora miki kunne suna dora ki a mugun tafarki, daga ke har su har gami da wannan sakarya uwar taki da ke goyon bayanki zan yi maganinku. Baki isa ki haifar min damuwa kin yi kaɗan yaushe ma aka haife ki da zan kasa bi dake?" Ina mai gargaɗin ki daga yau daga rana mai kama da yau babu ke ba Abba duk wani abu da ya shafe shi da ki cire hannunki aciki, idan kika bari na sake kama ki da aikata laifin kwatankwacin wannan da kika aikata wallahi-azim Sadiya zan yi mummunan saɓa miki. Da ace ba nina haife ki ba Sadiya da bani bane mahaifin ki ba da yau ɗinan sai ki barmin gidana,sai dai kashh jinin kai ne da baya ketare wuya kin ci albarkaci ni na haife ki. Magana ta ta karshe dake ki fito da miji idan nan da watanni biyu suka cika ba ki kawo min wanda za ki aura ba ni zan nemo miki da kaina. Ke kuma Mariya ba zan ce dake komai ba kawai dai zance ki cigaba da abin da kike yi kada ki fasa ke ɗin ma ki sani kina cin albarkacin 'ya'ya dake tsakaninmu ne mugun hali nan da kika tsirawa kanki yasa kin fice min daga rai, nan da wani lokaci zan kawo ƙarshen rashin mutuncinki. Ku tashi ku ɓace min dagani har ke Mariya bana buƙatarki ki fita.
Yanda Daddy ya yi magana a tsawace yasa a lokaci ɗaya suka miƙe tsaye sai ya tsayar da Siyama ya yi mata nasiha.
Washegari gari Aydah tana dawowa daga school kasancewar Thursday ne babu islamiyya ta shirya ita da Huwaila za su fita gyaran jiki kuma aka yi dace da AB yana gida ta je har parlornsa na sama ta same shi ta karɓo kudi adaidaita suka shiga ita da Huwaila sai Aj beauty palace and spa.


#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.




Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[1/10, 11:24 AM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye


063.


Kusan awarsu biyu cikin ta uku,aka gama yiwa Aydah duk abubuwan da ta lissafa an mata tun daga kan gyaran jiki ,saloon,kitso zanen ƙunshi da yayi matukar yimata kyau. Har suka fito bakin titi korafi take yiwa Huwaila da ita ma aka yi mata gyaran kai dan Aydah ta matsa ayi mata shine aka wankewa mata kai kurum tace bada kitso ba kuma bada zanen lalle ba haka Aydah ta haƙura badan taso ba. Korafi take yimata kanta har ya fara ciwo sun matse mata kai jin take tamkar zata yi zazzaɓi, ta faɗa tamkar zata sakawa Huwaila kuka Huwaila ta rike hannunta tana murmushi raki irin na Aydah ba zai daina bata mamaki ba tun da tun fil'azal bata san wahala komai kankantar ta ba. Basu jima ba suka samu adaidaita sahu har ƙofar gida ya sauke su har lokacin kuma AB yana gida tana ganin motarsa tun a parlor kasa ta cire mayafin kanta ta wurgar da handbag ɗinta kan doguwar soofa ɗin dake girke a parlor sai kuma ta tuna da halinsa ya tsani wannan zubar da kayan da take yi sai da tattare su ta kai ɗakinta sannan ta nufi parlorn sa dake sama tayi knocking haɗe da yin sallama jin shiru yasa ta tura ƙofar parlor baya ciki har ta nufi ƙofar ɗakinsa daidai lokacin AB ya fito daga master bedroom ɗinsa farin yadi ne ajikinsa fari kal marar zane ko kaɗan har ana hango farar shimin dake jikinsa banda ƙamshinsa da ya cika parlor babu abunda ke tashi sosai yayi mata kyau a idanu samun kanta tayi da zuwa da gudu ta shige jikinsa ta zagaye duka hannayenta ta bayansa wani irin bugawa ƙirjin AB ya shiga yi ko kafadarsa Aydah bata kai ba sai akan cikinsa ta kwantar da fuskarsa yayin da take shaƙar ƙamshin jikinsa, har natsuwa ke shigarta wanda bata san lokacin da ta fara sauke numfashi ba.
Shiru suka yi Dukansu zuciyoyinsu na irin wani dokawa cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa da sauri ta ɗago kanta tana kallon cikin kyawawan idanunsa "Yayanmu har mun dawo kaga kitsona" tana matsowa tana haɗe filin da yayi saura a tsakaninsu tana nuna masa kitson kanta wannan karan bugun zuciyarsa yake ji har cikin tafin ƙafarsa ba wannan ne karo na farko da Aydah ta saba zama kusa dashi ba ba wannan karon ne na farko da ta fara rungumarsa ba meyasa komai yanzu yake jin sa ya canja."wani irin deep breath ya shiga ja yana saukewa kafin ya kafawa kitson ta ido yayi masa kyau ainun,hannayenta duka biyu ya riƙe yana kallon yadda lallen yayi kyau.
Ganin lallenta yake kalla har ya kasa dauke idonsa cike da ɗoki Aydah ke faɗin."Yayanmu yayi kyau ko?"sakin hannun ya yi yana faɗin "Ba laifi yayi kyau" juyawa ya yi ya soma tafiya da sauri ta cimmasa tana faɗin."Yayanmu ina kuma za kaje?"
Ware ido yayi akanta cike da gajiya a muryarsa ya furta "zan je gidansu Rumaisa.!"wannan karon ya mutse fuska tayi tamkar bata ji sunan da ya kira mata ba taji zuciyarta na wani irin tafarfasa bai kara kulata ba har ya fice daga parlor tana tsaye a wurin tamkar an kafata da gaske auren Rumaisa zai yi?"wani irin abu taji yana tsaya mata a wuya,wasu irin hawaye masu radadin gaske suka rika fita daga idanunta suna sauka akan fuskarta,anan parlor ta zube ta rika rera kuks tamkar wacce aka daka ta tsani wannan Rumaisa da duk wani abu da ya shafeta bata tunanin zata taɓa sonta har abada.
Sai bayan magarib ya karasa gidansu Rumaisa ita ma bata jima ba ta fito dan mai mata gyaran jiki bata jima da tafiya ba sai da tayi wanka kamin ƙarasowar AB kallonta kawai yake Ƙamshinta yana hargitsa sa ga baki ɗaya yanayinsa ya canja kula da yanayinsa yasa tace "Habeebi lafiya?"kai yake girgiza mata yana faɗin."kamshin nan yayi yawa Rumaisa har tsakiyar kaina nake jinsa,hop cikin gida kawai kike sakawa banda waje ko?"juya ƙwayar idonta tayi tana daga masa kai "gobe Aunty Raliya suke son suje suga gida ban san wane gidan zamu zauna ba.
"Gidan da muke ciki da Aydah zai ishemu ai bana son raba hankalina na fison iyalina suna haɗe a guri ɗaya."ya faɗa mata kai tsaye, Aydah da ya kira mata taji ranta ya ɗan sosu har wani kiranta da iyalinsa yake yi wai me AB yake nufi ne?sai kawai tayi kokarin danne ɓacin ranta ta ce "To ya za'a yi kenan ya kuma tsarin gidan yake?"kasan ba wancan gidan bane wanda na zaba lokacin cikin gidajenka ni ban ma san da wannan ba.
"Wannan yafi wancan da kika taɓa zaɓa kyau da girma wannan har da swimming pool akwai ciki, gashi kuma sama da kasa ne ƙasa akwai ɗakunan bacci uku sai babban parlor sai dakin da mai aiki take ciki,sai kitchen da store sama kuma ɗakunan bacci biyu ne sai babban parlor sai master bedroom ɗina Aydah tana cikin ɗaya ɗayan babu kowa so duk inda kike so babu matsala."wani abu taji ya tsaya mata a wuya ba zata iya zama kasa ba ɗakin Aydah yana a sama,kuma ba zata iya zama da Aydah a sama ba sai dai Aydah ta bar mata sama ta dawo kasa kawai kanta tsaye ta furta "kace ta koma ƙasa sai ta bar mana sama ni da kai za mu fi sakewa.
Da sauri ya shiga girgiza kai bai san taya zai fara wannan rashin hankalin da Rumaisa take so yayi ba yanzu,Daddy ya mallaka masa gidan
ya zuba musu duka furnitures ɗin dake cikin gidan taya zai ce Aydah tabaro sama ta dawo kasa,ai ko dan rigimar Aydah yasan ba zai fara ba.
"Idan babu damuwa duka mu zauna a sama Rumaisa akwai wani extra daki sai ki zaun acikinsa ƙasa kuma ki ɗauki ɗakuna biyu ki bar mata ɗaya ni ina gani hakan zai fi batareda da kowacce acikinku an shiga hakkenta ba.
"Ban gane me kake nufi ba Abba ya za'ayi da kayan ɗakina?" wannan karon da ɓacin rai sosai a muryarsa,saboda zaman lafiya yace zai sa akwashe kayan ɗayan bedroom ɗin na sama da kuma kujerun parlor sa dake sama sai ayi mata jere kayan kitchen ɗinta tun da kitchen ɗin yana da girma tamkar ɗaki daya yake zata iya aza nata a gefe kuma ya wadace su. Rumaisa bata kara cewa komai ba ga baki ɗaya ranta a mugun ɓace yake har AB ya wuce ba suyi wata kyakkyawar sallama ba, kuma ita ta azalzale sai ya zo ta ganshi gashi ya zo ɗin daga ƙarshe ya tafi da takaici da bacin ranta. Da Rumaisa ta koma cikin gida take yiwa mahaifiyarta bayanin yadda suka yi da AB murmushin takaici kawai Raliya tayi ta cigaba da danna wayarta tana tausayawa kanwartata taga ga baki ɗaya son wannan yaron ya riga ya rufe mata ido tana tsoron ranar da zai nuna mata halinsu na maza. A yanda ta fahimta soyayyar da Rumaisa take masa tafi wacce yake mata. AB yana baro gidansu Rumaisa ya wuce majalisa wurin Abdulkarim saboda ya kira sa ya zo ga katunan daurin aure ya karbo anan Abdulkarim ya cire na 'yan zaman majalisa ya basu, duk wanda yaga sunan AB da Rumaisa a jikin katin sai ya furta albarkacin bakinsa,sun yi mamakin rashin zuciya irin na AB da har zai iya sake neman auren Rumaisa, a bisa irin mugun wulaƙanci da cin zarafin da mahaifinta ya yi masa a ranar daurin aurensu , shi ne don rashin zuciya zai sake komawa gareta. Duk abun da suke faɗa AB ya ya biris dasu saboda shi yaji ya gani shan koko ɗaukar rai.
AB bai dawo gida ba sai misalin ƙarfe goma na dare koda ya shigo main parlor babu kowa ya haura sama. Huwaila dake zaune a ɗakinta tana dakon dawowarsa da ta ji ya haura sama ta tashi da sauri ta fito ta nufi ɗakin Aydah, ta tura kofa ta shiga da sallama Aydah tana kwance da waya a hannunta tana karanta wani littafi mai suna izgilanci wanda Hajja ta rubuta sosai littafin ya yi mata daɗi daman ita tafi sha'awa littattafan soyayya. "Auta ajiye wayar nan ki zo ki kai masa abincinsa yanzu nan ya dawo.
Ya mutsa fuska Aydah tayi tashi zaune tayi tana faɗin "Ni gaskiya aunty Huwaila na gaji ki kai masa kawai, kuma yanda littafi nan ya dauko daɗi bana jin zan iya katse karatunsa.
Maka mata harara Huwaila ta fara yi tukun kafin ta isa gareta ta fincike wayar hannunta "Ka ji min shashanci wofi yanzu banda ke da abinki Auta karatun littafi yafi miki kula da mijinki?"naga dai ko cikin littafin abun da marubutan suke koya muku kenan tattali da kulawa da maigida amman shi kenan babu amfani gayamiki cigaba da karatunki kwana nakki nawa Rumaisa ya rage ta shigo gidanan na tabbata za ta bashi kulawa ta musamman anan za ki raina kanki.
Huwaila tana ƙarasa magana ta kama hannun Aydah ta dankwara mata wayarta a tafin hannunta, sunan Rumaisa da ta ambata har tana faɗin za ta kula da yayanta yasa ta ji wani irin mugun kishi da har yasa ta miƙewa tana faɗin "Wallahi babu wata Rumaisa da ta isa ta zo gidanan ta shiga tsakanina da Yayanmu.
Murmushin gefen baki Huwaila tayi "To mu je ki kai masa abincinsa amman kuma sai kin canza wannan rigar bacci kwata-kwata bata dace da zuwa turaka ba.
Ko kaɗan Aydah bata fahimci inda Huwaila ta dosa ba sai kawai ta nufi wardrobe ɗinta da sauri tana faɗin "Aunty Huwaila idan kayan bacci ne ina dasu kala-kala zo ki zaɓar min wacce ta dace na saka ai ni yanzu duk abun da zai farantawa Yayanmu rai shi nake so na kuma dauke hankalinsa daga kan wacce kodaddiya mai idanuwa irin na 'yan China.
Sosai Huwaila ke kwasar dariya jin sharrin da Aydah ta yiwa Rumaisa wai idanunta masu kama da na 'yan China, Huwaila ta ciro mata wata 'yar karamar riga mai siririn hannu wacce bata wuce cinyoyinta, rigar light purple ce a gaban rigar an yi mata ado da lace mai raga wanda ta wannan jikin lace ɗin ana iya hango 'yan matasan boobs ɗin Aydah, sau ɗaya ta taɓa saka ta yaya Abba ya ganta sanye da ita a main parlor ya yi mata faɗa tare da korata daki ta je ta canza ta tun daga lokacin bata sake marmarin sakawa ba. A takaice ma ta manta da ita sai yanzu da Huwaila ta ciro ta cikin jerin kayan baccinta wanda Siyama ce tai mata arranging ɗinsu acikin wardrob.
"Aunty Huwaila idan na saka wannan rigar Yayanmu zai yi min faɗa saboda na taɓa saka ta a lokacin muna gidan Mami ya dinga yi min faɗa har ya yi min gargadi kar na sake sakawa.
"Auta a wancan lokaci da ya hane ki ai babu aure ne a tsakaninku kema kinsan da wannan, a yanzu kuma duk abun da yake jikinki mallakinsa ne ko Rumaisa idan ta shigo gidanan fiye da wannan rigar za ta dinga sakawa don ta dauke hankalinsa.
Da sauri Aydah ta fizge rigar daga hannun Huwaila ta cire ta jikinta ta maye gurbin ta da wannan, turare kusan kala uku Huwaila ta bi jikin Aydah dasu nan da nan ta ɗauki fitinannen ƙamshi na fitar hankali. Sai faman yaba kyawun da tayi Huwaila ke yi ita kanta Aydah da ta kalli mirror sai ta sake kallawa kitson kanta ya sauka a kafaɗarta tare suka shiga kitchen Huwaila ta haɗa abincin AB kamar yanda ɗazu da rana tai masa ta miƙawa Aydah ta nufi bangaren sa dake sama yana zaune a parlor yana kallon news jikinsa sanye da kayan bacci farare kal sai dai bai rufe bottoms ɗin rigar ba kamar ma hakan ya zama masa dabi'a. Sai dai tayi knocking ya bata izinin shiga sannan ta sunkunya ta ɗauki tray ɗin ta shiga tun kamin ta iso gafda shi ƙamshinta ya gama

46 / 80