Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   31 / 80

90K to 93K   out of 237.2K words

zai iya hawa. Nasan da matuƙar wahala ace ka karbi wannan aure faratt ɗaya amman ina son ka yi haƙuri da Aydah ka cigaba da bata kulawa kaman yadda kike acan baya sa'ilin da take a matsayin ƙanwarka. Shine kadai abunda nake tunani za ka sakawa Daddy dashi. AB Daddy yana kaunarka fiye da tunani duk wani mai tunani duk yadda na kai da son na misalta adadin kaunar da yake maka na kasa. Ina rokon ka da ka daure ka ba marasa ɗa kunya. Ka saka alkhairin Daddy ya yi maka ta hanyar riƙe masa 'ya ka kyautata mata koda kuwa baka sonta.
Deep breath AB tare da dauke ganinsa ya dawo dashi kan Abdulkarim cikin dashewar murya ya ce "Ba za ka gane bane Abdul abubuwan da nake fuskanta ba masu sauki bane, jinjirarar zuciyata ba za ta iya canzawa Aydah matsayi na daga ƙanwata ba. Babban abin kunya ne agareni ace 'yar da na raina wai yau ita ce a matsayin matata wallahi Abdul abunan yana kona min rai.
"Abokina kada ka zama cikin mutane nan marasa godiyar Allah akan ni'imar da ya yi musu, ni ina ji a jikina Aydah alkhairi ce a rayuwarka yarinya nan tun tana cikin tsumman goyonta take sonka da kaunarka ta buɗe idanun da sonka a zuciyarta duk da soyayyar da take maka ta 'yan uwantaka ce amman ka kwatanta idan wannan soyayyar ta 'yan uwantaka za ta iya rikidewa zuwa ta mata da miji wallahi-azim duk duniya ba za ka sami mace da za ta so ka kamarta ba.


Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo






Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 100[12/27/2023, 12:56 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


*AREWABOOK*:Jeddah3256




Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye


041.


Shiru AB ya yi da alamu ya shiga nazarin maganganu Abdulkarim shi kanshi shaida ne akan irin ƙaunar da Aydah take masa haka zalika shima yana ƙaunarta sai dai ba irin wancan ƙaunar ba. A gare shi ba abu mai sauki bane ya canja mata matsayi sama da wanda take dashi tun asali a wurinsa. Ya riga da ya gama tsarawa kansa mafita, mafita da yake gani ita kadai ce hanyar da za ta warware masa wannan kurman allo.
"Ni dai abokina shawarata a gare ka ka yi kokari ka danne duk abunda kake ji a duk sanda ka ji damuwa ko ƙunci a zuciyarka, ka ambaci sunan Allah ka miƙa dukka al'amurran ka a gurin sa insha Allah za ka ji sassauci Allah zai kawo maka mafita ta alkhairi, sannan kuma ka yi daure ka je ka ga halin da yarinya nan take ciki ban ce sai ka kwana guri ɗaya da ita ba at least ka nuna kulawarka akanta.
Abdulkarim ya dinga bashi shawarwari nagartattu kafin ya yi masa sallama ya rako shi har wurin mota suka sake yi sallama AB yana kara yi masa godiya sai da yaga fitar sa daga gidan kana ya juya cikin gida ya tsaya ya yi switch off ɗin bulbs, ya wuce bedroom ɗinsa ruwa ya ƙara watsawa jikinsa ya shirya cikin kayan baccinsa riga da wando masu tsantsi, jikinsa yana fidda ƙamshin turarensa mai sanyayya zuciya har ya kwanta sai kuma ya tuna da nasihar da abokinsa yai masa, "maganar Abdul gaskiya ce Aydah she's my little sister ba ta cancanci ya wofintar da almurranta ba duk da banaso wannan shaƙuwa da muka yi ta cigaba da wanzuwa a tsakanin mu, dole na canza mata daga yaya Abba da tasani zuwa wani yaya Abba na daban shi ne kadai hanya da zai kawo maslaha a yayin zamana da ita.
Duk Wadannan zantukan AB ke yi su a bayyane, sai kawai ya sauko da ƙafafunsa kasa ya zura bedroom slippers ya fice kansa tsaye ya kama handle ɗin ƙofar ɗakinta ya murɗa kofar ta buɗe ya kutsa kansa ɗakin wadace yake da haske domin bata kashe bulb ba, ya hango ta kwance akan gado, ta kunduddune kanta da duvet yanayinta kaman na wacce ke jin tsoro ƙarar buɗe ƙofar yasa ta zabura tana wuƙi-wuƙi da idanu yadda ta zubura yai masifa bashi dariya sai kawai ya yi murmushi Aydah tana ganin shi ne ta ja numfashi tare da saukewa, cikin dashewar murya ta ce "Yayanmu kaine?"
Harararta ya yi tare da zaunawa gefen gado "Bani bane.
Ya bata amsa da baƙar magana cunno baki ta yi tare da faɗin "Allah ya ba ka haƙuri yayanmu.
Banza ya yi tamkar bai ji me ta ce ba sai ma ya sauya akalar zance ta hanyar nuna ledar kazar da ta aje akan gadon nata yana faɗin "menene wannan a leda da kika barsa akan gado ba za ki iya kawar dashi ba kafin ki kwanta?"
A shagwaɓe ta ce "kaza ce da fresh milk Yaya Abdulkarim ya kawo min.
Shiru ya yi yana kallonta da girar ido ɗage can kuma ya ce "Shine tsabar lalaci ba za ki saka fridge ba za ki barshi akan gado wai Baby Aydah sai yaushe za ki daina wannan lalacin naki da son jiki?"
Rau-rau ta yi idanunta kaman za ta sa mishi kuka "Ni kam yayanmu laifi me nayi maka ka daina sona tun ɗazu sai faɗa kake min har da cewa ka yi za ka doke ni. Dan Allah ka yi hakuri Yayanmu karka tsaneni a bisa laifin da bani na aikata maka ba. Ni kaina ina ji zafi irin abubuwan da Mami take maka, haka zalika da Daddy ya fara jin ra'ayina da zan faɗa masa gaskiya ƙaunarmu ba ta aure bace ta 'yan uwantaka ce, babu aure a tsakanin mu amma sai kawai Daddy ya yi gaban kansa duk da haka ban ga laifinsa ba watakila ya hango wani alkhairi a tsakanin mu wanda mu Allah bai ba mu ikon hangon sa ba.
Tun sanda ta fara magana AB ya yi mata ƙur yana kallon ɗan mitsitsi bakinta dake rattabo wannan zance har ga Allah bai taɓa tunani ta iya magana mai cike da hikima irin wannan ba saboda koda yaushe,idan za ta yi masa magana babu ta kirki a ciki sai zallan wauta da shagwaɓa ashe akwai the other side of her da baisan wanzuwar sa ba a tattare da ita. Kyakkyawar ajiyar zuciya ya sauke yayin da tausai ya kama shi, ya matsa kusa da ita ya haɗe tazarar dake tsakaninsu ya ɗora hannunsa akan kitson kanta tun wanda ya kaita aka yi mata ne har yanzu bata tsife shi ba ya shiga shafa kitson a hankali cikin taushin murya ya ce "Baby daga yanzu karki sake tunani Daddy da Mami sun yi min laifi ni a wurina ba wani laifi da suka yi min dukkansu biyu iyayena ne bani da sama dasu duk abunda za su yi min ba zan taɓa canza musu wannan matsayin nasu ba.
Murmushi ta yi tare da tashi zaune tana faɗin "Kuma ba za ka sake cewa za ka doke ni ba ko yayanmu?"
Murmushi ya yi tare da ɗaga mata girarsa kana ya miƙa hannun ya dauki ledar kazar ya warware ta daga cikin foil paper, har yanzu da zafinta ga ƙamshin yana fita "Iyeee! Lallai Abdulkarim munafiki ne watau nufinsa ke kadai za ki cinye wannan ƙatuwar kaza to Allah ya kama ki baby tare za mu ci kazar nan.
Yadda yake magana yana zare ido irin na wanda mamaki ya kama ya ba wa Aydah dariya ta dinga kyakyalawa, AB ya yi zugun yana kallonta sai da ta yi mai isarta kafin ta kalle shi tana faɗin "Yi haƙuri yayanmu nasan ba ka son dariya Allah nima ba san lokacin da ta zo min ba.
"Burina kenan na ganki kina farin ciki Aydah na dinga gani walwala da dariya akan fuskarki saboda haka ki yi dariyarki yaya Abba ba zai hana ki ba domin kuwa farin ciki shi ke haifar da dariya.
Bai bari ta sake magana ba ya yago cinyar kazar ya dinga bata a baki har sai da ta ce ta ƙoshi ya bata fresh milk tasha ya umurce ta ta je ta wanko bakinta, ta kwanta koda ta dawo daga bathroom ya tattare raguwar kazar ya saka mata acikin ƙaramin fridge ɗin da ke cikin bedroom ɗin nata. Har za ta hau gado ya ce ta je ta canza kaya tasaka na bacci ta buɗe ɗaya daga cikin trolley ɗinta wacce Siyama ta yi mata arranging underwears da sleeping dress ɗinta ta dauko cotton night gown irin mai taushi nan sosai ta maida zip ɗin trolley ɗin ta rufe, ta miƙa hannunta da zimmar ta yi unzipping rigarta ta kasa tayi-tayi yaƙi buɗewa daman Siyama ce ta rufe mata, shi dai AB yana kallonta a fakaice can kuma sai ta matso wurinsa tana cuno baki "Yayanmu na kasa buɗe zip ɗinan.
"To me zan miki ko ni na rufe miki shi?"
Ta girgiza kai "yaya Siyam ce ta rufe min kuma yanzu bata nan balle ta buɗe min ka taimaka ka buɗe min yayanmu.
Sai da ya ɓalla mata harara kafin ya ce "Ai sai kin sunkunya ko kina nufi ni zan miƙewa tsaye kuma na zuge miki zip ɗin?"
Da sauri ta sunkunya daidai tsayin da zai iya zuge mata zip ɗin batare da ya tashi tsaye ba, yana unzipping rigar idonsa ya sauka akan black bra dake zagaye da gadon bayanta sosai bra ɗin ta yiwa bayan nata kyau, murmushi ya yi yana faɗin "Aydah yaushe kika fara saka wannan abar?
Cike da kunya Aydah ta janye jikinta ta saka night gown ɗin hannunta ta kare fuskarta ita a dole ta ji kunya "Ban taɓa sakawa ba sai yau shima yaya Siyam ce ta bani kuma fa Yayanmu har guda uku ne.
Ta ƙarashe maganar tana leƙo idanunta ta jikin rigar da ke kan fuskarta.
"Gaskiya dole na dau mataki akan Siyama akan me za ta ba ki bra yaushe kika yi nonuwan saka wa bra salon ta haifar miki da ciwon kirji, daga yau karki ƙara sakawa ki jira tukkuna har su kai muzalin da za ki saka musu bra ni kaina zan siya miki kala-kala.
Ɓata fuska Aydah ta yi har wani bubbuga ƙafafu take tana bala'in son bra saboda dukka ƙawayenta na school suna sakawa duk cikinsu ita kadai ce bata fara sakawa ba. Duk da tana cikin ɓacin rai tana gani Siyama ta bata bra ta ji ɓacin ran nata ya ragu, shine kuma yaya Abba yake so ya hana ta sakawa alhali tana so saboda haka ta langwaɓar da kai tare da sassauta murya ta ce "Allah yayanmu sun kara girma ba kaman da ba don ka daina ganinsu shiyasa kake tunani har yanzu 'yan mitsitsi ne.
Wani irin mimmiƙe wa tsigar jikinsa ya yi yana ji wani abu yana mishi tafiyar tsutsa a cikin jininsa, sai da ya yi namijin ƙoƙari kafin ya iya furta mata "To naji je ki bathroom ki canza kayan jikinki ki zo ki kwanta dare yayi sosai.
Ta juya ta nufi bathroom shi kuma ya bi ta da kallo jim kaɗan ta fito sanya da rigar wacce ta saukar mata a guiwayoyinta ta hau gado ta kwanta ya ja duvet ya rufu mata, addu'o'in tsari ya yi mata, bai baro ɗakin ba har sai da yaga ta yi bacci. Sannan ya dawo dakinsa ya wuce bathroom ya dauro alwallah gaba ɗaya daren ya raya shi ne yana kai kukansa wurin Mahaliccin sa mai kowa mai komai ya ye masa damuwar da yake ciki ya daidaita masa almurarransa. Sai around 3:30am ya kwanta.
*ALH BASHIR MANSION*
Bayan tafiyar AB da Aydah a fusace Mami ta dawo bangarenta ta harhada kayan sawarta a ƙatuwar trolley, Siyama sai kuka take yi tana mata magiya ta yi hakuri kada ta tafi, sai ma taƙara harzuƙa Mami ta sauke quarter fushinta akanta, ta kare mata zagi tass! Har cewa tayi ita ma Siyama ɗin munafuka ce da haɗin bakinta aka yi komai, har Mami ta sauko ƙasa sai ta tuna da Sadiya tun safe rabon da ta sake sakata a idanunta. Sai kawai ta ajiye trolley ɗinta ta sake haura upstairs dakin Sadiya ta buɗe ta shiga bata ko tsaya knocking ba, abu na farko da idanunta suka fara tozali dashi Sadiya tana yashe akan marbles yadda take kwance magashiyam ya sanya gaban Mami ya yi mummunan faduwa da saurin gaske ta isa gareta ta durƙusa gefen fuskarta tana kiran sunanta gami da girgiza kafaɗarta, Sadiya kam ko motsawa bata yi ba ballantana ta amsawa Mami kira da take mata. Sai lokacin Mami taga drugs da bottles ɗin tortulin da ke zube a kusa da Sadiyar ga kuma pieces ɗin bottle ɗin da ta fasa, ko ba a faɗawa Mami ba ta gama fahimtar mummunan hali da 'yarta ta jefa rayuwarta ciki nan da nan hankali Mami ya yi mugun tashi musamman da ta fahimci babu numfashi a jikin Sadiya jikinta ya sandare, wani irin razananne ihu Mami ta kwalla Siyama dake downstairs parlor tallaɓe haɓarta ta ji ihun Mami sai da ta zubura ta mike tsaye yayin da ta ci-gaba da jin ihun na Mami, da gudu ta haura staircase sau biyu tana kuskure faduwa. Yadda Siyama taga Sadiya kwance a sandare ita ma ta fasa ihu ita kuma Mami kuka "innalillahi wa'inna illahim raji'um! Mami ba dai yaya Sadiya ta mutu bane?"
"Ban sani ba Siyama amma tabbas bata numfashi gashi jikinta ya sandare yi maza ki kirawo Daddynku shikenan burinsa ya cika Sadiya ta rasa ranta akan tsinannen yaro nan marar asali.
Siyama bata bi ta kan muggan maganganu da Mami take faɗa akan yaya Abba ba ta fice da gudu, a parlor ta tarar da Daddy yana waya da rigimammen ƙaninsa Alh Sanusi sai buga wuta suke yi shi a dole so yake ya nunawa Daddy kuskurensa na aurawa Abba Aydah, kamata ya yi ya maida aurensa da Sadiya amman Aydah ta yi kankanta da aure. Shigowar Siyama a ruɗe yasa Daddy ya katse kiran batare da ya yi sallama da Alh Sanusi ba.


Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo




Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/28/2023, 11:00 AM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU




*AREWABOOK*: Jeddah 3256


#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels






42.




Rudewa da gigice yasa Mami bata kwashe kwalaben dake tarwatse a Tsakiyyar room din Sadiya ba.shigowar daddy kenan idonsa bai sauka a ko'ina ba sai kan kwalaben binsu ya shigayi da kallo kamar mai son fahimtar wani abu,sai lokacin Mami ta lura da irin kallon da daddy kebin dakin dashi nan take gabanta yayi wani irin mummunan bugawa karfin halinta ta tattara tayi dauriya cike da wata irin murya take faɗin."ka kashe Yarka da hannunka ka huta kan tsintacce wanda ba'a san Asalinsa ba.!"Mami ta faɗa cikin wani irin ihu,
"Wallahi Idan wani abu ya samu sadiya ka tabbata sai nayi Shari'a dakai da kai da wanda shine sanadiyar tarwatsewar duk wani farin ciki na gidan nan."meya samu yar uwarki siyama?"daddy ya faɗa yana kallon siyama da jikinta yayi balain sanyi tana jin Mami da idanunta ,sai take ganin kamar Mami tana da son kanta dayawa.meyasa Mami ta canja lokaci ɗaya,meyesa take kokarin yiwa Allah shishigi acikin kaddarar da ya zana masu.
"Nima ban sani ba daddy kamar bata numfashi."siyama ta faɗa cikin wani irin raunin murya."daddy ya taka da kafafunsa ya doshi inda sadiya take akan cinyar Mami,hannu daddy ya daga da nufin yakai jikin sadiya Mami,tayi saurin rike masa hannu tana aika masa da wani irin kallo
"Me kuma yayi saura karka tabamin Yarinyya wallahi kawai ka tafi Bama bukatar taimakonka.!"Runtse ido daddy yayi yana jin kalaman Mami na wani irin tafasa masa zuciya juyawa kawai yayi yabar dakin batareda yace komai ba cike da mamaki da tsoro siyama ke faɗin wai meke damunki ne Mami.?"kema ki fita!"Mami ta faɗa tana dakawa siyama tsawa."juyawa kawai siyama tayi tabar dakin..wata irin ajiyar zuciya Mami,ta shiga saukewa tanajin zuciyarta na sauka da mugun nauyin da tayi mata tun lokacin da ta fahimci irin rayuwar da sadiya ta jefa kanta taji zuciyarta tayi wani irin dokawa."firgici da tashin hankalin da ta saki ihun da ya jawo hankalin siyama ,batajin siyama kamar yadda takejin daddy idan har ya fahimci mummunar rayuwar da sadiya ta jefa kanta to tabbas ta san Daddy,zai yanke mata hukuci akan laifin data aikata.mami ta jaye sadiya daga jikinta ta jawo pillow ta ɗora mata akai miƙewa tayi tsaye kai tsaye kasa ta nufa wannan karon babu kowa a parlor kitchen ta shige ta samu huwaila na wanke-wanke tsintsiya ta dauka da parker ta koma dakin Sadiya ta tattara kwalaben da ta farfasa,karshe dai Mami dakin ta cigaba da zama wasa gaske a dakin Mami ta kwana har taga sallar asuba, Sadiya batayi koda motsi ba baccin ta take cikin natsuwa da kwanciyyar hankali da alamar kwayoyin da tasha suna da matukar ƙarfi.toilet Mami ta shige cike da bacin rai da takaicin sadiyar ruwa ta debo a bokiti kakaf ta juyesu akan sadiya wacce ke kwance akan rug,a firgice sadiya ta farka tana tunanin ta inda ruwan ke zubo mata
Ido biyu tayi da Mami dake tsaye ranta a mugun ɓace mitsittsike ido sadiya ta shigayi cike da Mamakin Meya kawo Mami a dakinta."komai ta kasa tunawa rike kanta kawai tayi da yayi mata mugun nauyi.muryar Mami taji akanta tana faɗin."na baki minti goma sha biyar kiyi wanka kiyi sallah ki sameni a daki har sallolin da kika san jia baki samu kinyi ba ki tabbata kinyi su."da haka mami ta fice daga room din na sadiya.da ido sadiya ta bita."Ya rabbi!"ta faɗa can kasan ranta me take yi haka

31 / 80