Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   56 / 80

165K to 168K   out of 237.2K words

Ina so na nemo su at any cost su faɗa mana ina yaronmu shin har yanzu yana raye idan yana raye yana hannunsu?"
Wannan ita ce asalin damuwata Oum Azhar ki tayani da addu'a amman nasan akwai cakwakiyya a gabana ba kaɗan ba.
Wata ƙarfaffiyar ajiyar zuciya Maysun ta sauke taji aikinta komai rintsi komai wahala ba za ta sake rabuwa da Aliyu ba domin shi ne cikon farin cikinta, saboda haka ta ce "Kana ji ko Abu Azhar ka cigaba da ɓoye ni har zuwa sanda za mu gano yaronmu. Na tabbata zuwa lokacin mun nemo mafita.
Ba yadda Aliyu na Uku ya iya dole ya yi na'am da shawararta.
*KANO*
(Soft care private hospital)
Abba ya riga Aydah farfadowa yana dawowa natsuwarsa ya kalli Rumaisa duk sannu da take masa gami da tambayarsa me yake ji a jikinsa bai amsa mata ba sai kawai ya ce da ita "Ina Aydah ya jikinta na ji mata rauni ko Habibty?"
Cikin shock Rumaisa take kallonsa sai da ta haɗiye wasu busassu miyau kafin ta ce "Ban fahimce wannan tambayar taka ba Habibi wane irin rauni ka yi mata?"
Shiru AB ya yi ya kasa bata amsa "Habibi ka yi magana ka yi shiru ko dukanta ka yi?"
"Ni dai kurum ki faɗamin tana ina?"
Tana ɗaki da ke kusa da naka sai dai tun zuwan mu ban je na dubata ba saboda banaso na fita na bar ka kai kaɗai.
Da sauri AB ya sakko daga gado daman an cire masa drip, jikinsa sai rawa yake yi don har yanzu yana ji jiri sai dai ba sosai ba, Rumaisa ta bi shi da kallo ta ja tsaki ƙasa-ƙasa da har taso tayi zamanta sai kuma wani zuciya ya kwaɓe ta, ta tashi ta bishi a baya.


#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.












Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[1/22, 2:34 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels






076.




Riƙo hannunsa Rumaisa tayi da sauri da mamaki yake kallonta ya zuba mata idanunsa da suka ɗan faɗa. Yana jira dalilin da zai sa ta tsayar dashi "Habeebi kaima fa ba cikakkiyar lafiyar ne da kai ba, kuma family ɗin Aydah suna tare da ita,kaima nasan da kana da muhimmanci a wurinsu da basu tafi sun barka kai kaɗai ba sai kace wani marar gata.
Rumaisa ta ƙarasa maganar rai a haɗe ta tsani mutanen da AB ke faɗar danginsa ne alhali su ba ƙaunarsa suke yi ba, hannu yasa ya zare hannunta dake cikin nasa hannun,ya nufi ƙofa kai tsaye batareda ya tsaya kula zantuka ta ba.
Baki buɗe tabisa da kallo har ya fice daga room ɗin kai tsaye ɗakin da Aydah take ciki ya nufa a hankali ya tura kofar ɗakin,sai sukayi ido biyu da Mami samun kansa yayi da muguwar faduwar gaba ga wata matsananciyar kunya da ta lulluɓe shi, Sadiya na ganinsa da sauri ta nufo shi ta wani riƙo hannunsa daidai lokacin da Rumaisa ta ƙaraso cikin room ɗin ta biyo bayansa dan kasa daurewa tayi. Da wani irin sauri Sadiya ta Rungumesa wani irin natsuwa ta rika ji tana shigarta lokaci ɗaya duk da girman laifin da yayi mata na kusanta Aydah da ya yi bata ji soyayyarsa ta ragu ko kaɗan a zuciyarta ba."Yayanmu ya jikin?"Siyama ta faɗa tana kallonsa sai lokacin ya samu ya raba jikinsa da Sadiya ,still ta kasa barin gefensa murya a raunane ya gaisheda Mami, ko kallonsa daman Mami batayi ba wani irin ma tafarfasa zuciyarta ta riƙa yi Allah-Allah take Aydah ta farka a sallamesu su bar asibitin nan dan ta dauki alwashin daga nan sai gidanta Aydah ba zata koma gidan AB ba. Daman Rumaisa ko kallon gefen su Mami bata yi ba ta cigaba da tsayi a bakin ƙofar shigowa duk babu wata walwala a tare da ita.
Shi ma dai AB bai ƙarasa ba ganin Mami gafda Aydah ɗin tsayuwa ya cigaba dayi a haka duk da jirin dake dibarsa. Siyama data kula da yanayinsa tace yayanmu kaje ka huta kaga tana bacci na haɗa maka tea zaka sha?"murmushi kawai ya yiwa Siyama."zaka sha din na haɗa maka?
Sadiya ta faɗa tana kallonsa ɗaga mata kai kurum yayi duk daɗi ya gama cika Sadiya da sauri ta nufi wurin kayan da suka zo dasu dake cikin (basket)tsawar da Mami tayi mata ne yasa ta dakata ta haɗe rai da mamaki take kallon Mamin da ita ma ranta a ɓace yake.
"Akace maki da sunan sa na hado abinci mayya mai nacin tsiya wai sai yaushe za kiyi hankali ki daina kula wannan mutumin da ya rusa miki dukkan farin cikin ki.!"
Rumaisa ta riko hannun AB tana faɗin."Ka ga ga Habibi zo mu je na hada maka tea ɗin kasha daɗin abun bama da yunwar abincin baran tana ayi mana gori.
"Rumaisaaa!!!!
AB ya faɗa cike da kashedi a muryarsa "Mami kike yiwa rashin kunya, buɗe ido tayi cike da mamaki take faɗin."rashin kunya ita ta kama girmanta ne?"
tun da muka shigo take faɗa maka baƙaƙen maganganu.
"Kiyi shiru please.
Ya faɗa yana daka mata tsawa ita ma cikin daga murya take faɗin."meyasa zanyi shiru, hayaniyarsu yasa Aydah ta shiga buɗe idanunta da sukayyi mata nauyi wani wawan tsaki Rumaisa tayi ta fice daga ɗakin ga baki ɗaya cike da jin haushin Abban aranta. shi ma juyawa yayi yabi bayanta. Ganin Aydah ta shiga motsi Mami ta kira sunanta tana rika hannunta a hankali Aydah ta buɗe idanunta ta sauke su cikin fuskar mami cikin rawar murya Aydah ta kira sunan mami cike da kulawa Mami ke mata sannu tana tambayarta babu inda keyi mata ciwo,girgiza kai kurum take tana bin ɗakin da kallo tana so taga ta inda zata ga yayanta Siyama ta karaso tana mata sannu daman Sadiya tunda Mami ta kunyata ta agaban AB da Rumaisa tabar dakin,da taimako Siyama Aydah ta tashi zaune Siyama ta taimaka mata ta kaita toilet tamkar zata yi ihu wurin yin fitsari,ta wanke bakinta Siyama ta haɗa mata tea mami dai tana zaune sai bin ta take da kallo kaɗan tasha tea tace ta koshi maganin da doctor ya rubuta mata wanda Daddy,ya siyo Siyama ta taimaka ta bata tasha komawa tayi ta kwanta tare da lumshe idanunta zuciyarta cike da tunanin yayanta,miƙewa tsaye Mami tayi batareda tayi magana ba ta fice daga room ɗin kai tsaye office ɗin likita ta nufa sai da akayi mata izinin shiga
ta shiga,yana ganinta ya tambayeta Aydah ta farka ne ta faɗa mata ta farka,ta numfasa tana faɗin "likita zamu iya samun sallama a yanzu?" Za'a iya samu tunda dama jikinta da sauki kuma an mata ɗinki
ta dai cigaba da zama a ruwan zafi a dinga saka gishiri aciki kaɗan.
Ya rubuta masu takardar sallama Mami tayi masa godiya ban cin ta karɓi takardar tayi masa sallama, ɗakin da Aydah take ta koma ta kalli Siyama tace ta haɗa kaya su wuce gida an basu sallama.
Shiru Aydah tayi tana kallon Mami cikin sanyin murya Aydah ta ce "Mami yayanmu fa?"
A mugun hasale Mami ke kallonta kafin ta zuba mata wani uban ashar tsit Aydah tayi tamkar ruwa ya cinyeta Siyama na rike da hannunta har zuwa cikin compound inda Mami tayi parking motar ta,tunda suka shiga motar ta haɗe kanta da gwiwa bata kara magana ba har suka isa gida duk ranta a ɓace,Mami ta umarci Siyama ta haɗa mata ruwa tayi wanka ta haɗa mata wasu daban ta shiga ciki ta zauna. Tunda ya koma ɗaki ya kwanta ya rufe ido bai kara kallon Rumaisa dake ƙoƙarin haɗa masa tea babu irin maganar da bata yiwa AB ba akan ya tashi ya sha tea ba yayi mata banza.
gajiya Rumaisa tayi ta aje cup tea ɗin
tayi zaune duk abun duniya ya taru yayi mata yawa suna cikin wannan yanayin likita ya shigo room ɗin tare da nurse a bayansa ya kalli Rumaisa yana tambayarta mai jiki kuma ya farka.?"ta faɗa masa da sauƙi ya kuma farka Amman bai ci komai ba,jin likita yasa AB ya tashi zaune yana fuskantar likita, likita yayi masa ya jiki ya faɗa masa da sauƙi kafin ya ɗora da faɗin yana son a sallamesa,murmushi likitan yayi yana faɗin ,zasu basa sallama dan basu ma dade da sallamar matarsa ba kafin nan yana so ya gansa a office ɗinsa cike da mamaki AB ke kallon likita jin ance an sallami Aydah kuma har sun wuce,har office ɗin likita AB ya shiga Rumaisa na a bayansa likita ya dubi Rumaisa da ta samu wuri ta zauna "mene ne alaƙarki dashi?"Rumaisa ta daga kai tana kallon likita sosai taji haushin tambayar da yayi mata Da sauri AB ya kalli likita yana faɗin."matata ce likita.
Likita ya mayar da hankalinsa kan AB.
"kana da rai da lafiya meya kaika amfani da men power da ya kusa yi maka illah?"
Wani irin faɗuwa gaban Rumaisa yayi ko kaɗan bata taɓa kawo irin tambayar da likita zai yiwa AB kenan ba da bata yadda ta biyosu ba,da mamaki AB ke kallon likita yana girgiza kai yake faɗin "ban taɓa amfani da irin waya'annan drugs din ba na kara karfi likita kadai kara dubawa.
murmushi likita yayi ya kalli bangaren da Rumaisa take sai famar danna wayar hannunta take amman kar kuso ku shiga zuciyarta tashin hankali ne sosai acikinta ga wani irin gumi da take haɗawa duk sanyin dake cikin office ɗin zufa take haɗawa, yadda ta mayar da hankali kan wayar sai mutum ya rantse bata cikin office ɗin ake magana, karshe sai ta mike tsaye ta nufi hanyar barin office ɗin batareda ta yiwa kowa magana ba murya AB taji akanta ya kira sunanta cikin wani irin sauti tsayawa tayi batareda ta juya ba "kenan abun da likita ya faɗa gaskiya ne?"wani bangare na zuciyarsa na tambayarsa ban zuba sa da hannuna na sha ba likita sai idan matata ta zuba min cikin abun sha.
A wani irin rikice Rumaisa ta juyo ta dawo gaban AB daɗin abun bani kaɗai bace matarka ina tunanin matar taka guda ita ce wacce ta zuba maka ba dai ni ba.
Kallonta kurum yake yana mamakin karfin halinta likita ya juya yana yiwa AB bayanin ilollin dake cikin shan irin wannan maganin."kafin ma nayi maka bayani sai da na yiwa mahaifinka da mahaifiyarka bayanin haka a rude AB ke kallon likita cikin rawar murya yake faɗin "bayanin me kayi masu likita?
"wanda nayi maka yanzu dan ɗayar matarka ta auna arziki duk da har da ɗimki akayi mata gaskiya tana da dauriya sosai tamkar ba mai ƙarancin shekaru ba. AB ya murza goshinsa yana jin yadda iskar wurin keyi masa kaɗan jijiyoyin kansa suka fito sarari alamar ransa yayi bala'in ɓacin taya zai kara kallon Daddy da wannan abun kunyar?"Rumaisa ta kashesa ta cucesa,duk sauran bayanin da likita yayi masa kafin ya rubuta masa takardar sallama baya ma fahimtarsa
Wannan karon Rumaisa taja motar tunda ya shiga motar ya zauna bai ce komai ba har suka isa gida Huwaila tayi masu sannu da zuwa kai tsaye ɗakinsa ya wuce bai kara kallon bangaren da Rumaisa take ba ita ma tabe baki tayi ta nufi nata dakin,aranta take faɗin sai kace wani mugun abu tayi zai bi ya daga hankalinsa ko kaɗan bata yi nadamar abunda tayi ba.wanka yayi tare da sallar azzahar kusan karfe 3 yana zaune a parlor Rumaisa ta shigo cikin gayu ta cokare dauri gaban goshi sai uban ƙamshi ke fita ajikinta ta shigo da madaidaicin tray a hannunta har ta aje ta koma ta dauko sauran kayan AB bai kalli gefen da take ba,har ta gama sarving dinsu ya ja abinci ya fara ci ita daman tana cin abinci tana danna wayar hannunta batareda ta kara kula kan yanayinsa ba saboda Rumaisa irin matan nan ne da ko miji yana fushi dasu basa damun kansu barantana su kwantar da kai su gano kuskurensu su bada hakuri sai da ya kammala cin abincinsa a natse AB ya mayar da hankalinsa kanta ya kira sunanta ta daga kai tana kallonsa "ki aje wayar hannunki zamu yi magana,bana son ina magana ana danna min waya.
Ya faɗa da rashin walwala a fuskarsa
Aje wayar tayi tana kallonsa."waya faɗa maki ba zan iya dauke bukatar ki a gadon auren mu ba har sai kin ha'incin ni kin zubamin magani acikin abun sha?"meyasa baki jira kika ga iyawata ba ko zan iya ko ba zan iya ba?
Dan Allah dan Annabi Habeebi ka daina damun kanka akan wannan abun nifa ban ga illar dake cikinsa ba kawai dai yana karawa maza karfi ne ba wani abu na daban ba meya ma laifina dan na taimake ka?
"taimako?taimako da kike magana ya kaini gadon asibiti Rumaisa.
Ya faɗa sounding so very harsh a muryarsa,kin farasa na kasa yadda dake akan mu'amalar mu kin riga kin saka rashin yadda a tsakanin mu daga yau duk abun sha da ya fito daga hannunki inhar ba'a gama kika haɗasa a zan sha ba,ya rage naki ki gyara ko karki gyara.
Yana gama faɗar haka ya bar mata falon ya shige ɗakinsa wannan karon harda saka key ko kaɗan baya son damuwa ba karamin bata masa rai Rumaisa tayi ba,ga tunanin Aydah dake manne a zuciyarsa idan har yana da kunya ai ba zai iya haɗa ido da Mami ba, addu'a ya shigayi aransa
Allah yasa zuwa dare Aydah ta dawo
Yanayin da suka kasance tare da kanwar tasa ya kasa bacewa daga zuciyarsa har zuwa dare Aydah bata wata walwala a gidan gabaki ɗaya hankalinta na kan yayanta kuma bata ga fuskar tambayar Mami,yaushe zata wuce gidanta ba.duk a takure take jinta koda Daddy ya dawo da dare yaga Aydah ya mata ya jiki har washe gari AB yayi shirin fita office yayi dilaliing lambar Siyama lokacin ma Siyama tana bacci cikin bacci ta daga wayar tana jin shine tayi saurin tashi zaune tana murza ido take gaishesa ya amsa yana tambayarta ya jikin Aydah ta tashi jiya ta samu barci kuwa?"yana jin sautin murmushi Siyama ta ciki wayar "ta samu sauki yayanmu ni ina dakina ban sani ba ko ta tashi dan tana dakin Mami,batare muka kwana ba.
numfashi AB ya sauke yana faɗin idan ta tashi ta kirasa da haka ya sauke wayar har aran Siyama taji daɗin wannan al'amarin da ya faru tsakanin Aydah da Yayan nasu sai Mami ta haƙura ta sakawa ranta dangana ta karbi kaddarar su har AB ya gama break fast ɗin da Huwaila ta shirya masu cikin dinning area gimbiya Rumaisa tana can ɗakinta tana bacci kafin ya sauko kasa sai da ya fara leƙa dakin Rumaisa ya tarar tana bacci yana gama break fast yayi sallama ,da Huwaila har take tambayarsa yaushe Aydah zata dawo. Ya faɗa mata sai ta samu sauƙi da haka ya fice office gimbiya Rumaisa ana can an hangame baki ana bacci batare da tasan fitar mijin nata ba.


#JEEDDAH ALIYU
#ASMY B ALIYU
#AYDAH
#AB
#RUMAISA
#KURMAN ALLO








Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[1/22, 2:38 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels










077.






Da wani irin bakin ciki ta riƙa bin zanin gadonta da kallo yadda jini ya batasa ita ga baki ɗaya jinin nan tsoro yake bata bai taɓa yimata rushing yadda yake yimata yanzu ba. Ita kanta kyamar kanta take ji cire zanin gadon tayi duka ta wuce dashi toilet ta sakasa cikin washing machine ta cire kayan jikinta na bacci da suma sun gama lalacewa duka ta saka aciki washing machine. Ruwan zafi ta haɗa tayi wanka zuciyarta duk a cakude zata kira Aunty Raliya taji idan akwai mafita,ga wata irin muguwar sha'awar mijinta dake damunta a dalili kayan mata da ta dinga dirkawa cikinta.
wankan tayi ta fito ta shiga shirya kanta bacin ta gama ta saka riga da wando na English wears ajikinta ta dauko sabon zanin gado ta shimfida toilet ta koma ta wanke zanin gadon da kayan baccinta. A bayan gidan taje ta shanya,ta dawo ta shiga wankin toilet da taji yayi mata wani iri ko kaɗan bata son wanke toilet zata rika sa Huwaila tana wankewa tunda yar aiki ce,sai ta riƙa wanke na AB da kanta dan ita a tsarinta yadda take da kishi bata son yar aiki ko parlor maigidanta ta taka,share ɗakinta tayi tas ta kunna turaren wuta,ficewa tayi ta nufi part ɗin AB yunwa take ji sosai
babu kowa a parlor kai tsaye master bedroom ɗinsa ta nufa nan din ma babu kowa. kai tsaye ta karasa kofar toilet tayi knocking tana kiran sunan AB jin shiru yasa ta tura kofar toilet ɗin da mamaki babu AB babu alamarsa tambayar kanta take ina yaje?"Tasan dai ba office ya tafi ba dan suna cikin hutun cin amarci. gyara gadonsa tayi
ta fice kai tsaye kasa ta sauka tana kwallawa Huwaila kira da tayi nisa tana karanta littafin da suka saka a YouTube channel mai suna (zamanin mu A yau)tana saurara wanda Aydah keyi mata downloading ɗinsu a wayarta,sai ta tura mata duka jin shiru yasa Rumaisa ta nufi daktin da take tunanin na Huwaila ne ga mamakinta wayace kare a kunnenta ta bada dukkan hankalinta kacokam tana sauraren (mai sanyi) tana bala'in son karanta duk wani littafin da mai sanyi ya wallafa a channel ɗinsa dake YouTube mai suna(limamin tsakar gida)duk wani littafi da zai karanta acan bata danasanin karanta sa saboda yadda yake karanta sa daki-daki yana fitar da kowace kalma yadda ta dace. A fusace Rumaisa ta daki kofar,a wani irin rude Huwaila ta daga kai tana kallon

56 / 80