Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   57 / 80

168K to 171K   out of 237.2K words

kofar ganin Rumaice ta mike tsaye da sauri ta kashe wayar cikin rawar jiki ta gaisheda Rumaisa. "Saboda wulakanci tun a falo nake kiran ki shine zaki shareni ?"
A tsorace Huwaila ke faɗin."dan Allah Aunty kiyi hakuri wallahi ban ji bane. wata uwar harara Rumaisar ta sakar mata tana yatsine fuska take faɗin."habeebi ya fita ne?
"eh! ya fita office tun ɗazun.
Ɗan jim Rumaisa tayi kamin kuma ta sake cewa "yayi break fast"
"ehhhh yayi.
Da haka Rumaisa ta juya tabar ɗakin da ido kurum Huwaila ta bita
"Mtss! Mazaunanta har wani rawa suke tsabar yadda sukayi mata yawa wai kuma a haka Abba Bashir ke sonta ita har ga Allah bataga abun so a wurin Rumaisa ba waya sani ma ko tana haɗawa da maganin kara girman halitta kamar yadda wasu mata keyi.
Kamar dai irin Maryama ta cikin labarin (zamanin mu a yau)tabe baki Huwaila tayi ta koma tayi kwanciyarta ta cigaba da sauraren littafinta. Anan cikin dinning area Rumaisa ta zauna tayi break fast, addu'a take aranta Allah yasa Aydah karta dawo.
Tana gamawa ta koma ɗakinta waya ta dauka ta fara kiran Aunty Raliya
tana dauka ta gaisheta ,ta amsa tana tambayarta ya gidan anan kuma suka shiga tattaunawa akan matsalarta har take bata labarin AB ya gano ta saka masa men power a abun sha sanadin haka sai da ya kwanta gadon asibiti."Ni bama wannan ne ya dameni ba Aunty Raliya jini nan yaki tsayawa,wane drugs ya kamata na sha dan ya tsaya ina bukatar mijina ina matukar bukatarsa kin san saboda wannan jinin yasa yaje wurin Aydah."zan tura maki magani sai kije pharmacy ki siya maybe zuwa dare ya tsaya.
wani dadi ne ya lullube Rumaisa da haka suka yi sallama tana aje kiran Rumaisa ta shiga kiran AB sai da ta katse ya kirata "ina kwana Habeebi ya jikin?
"kin tashi Lafia?"
AB ya faɗa "lafiya lau koda na tashi bacci Huwaila ta cemin ka tafi office,nayi mamaki gaskiya na zata ko ka dauki hutu a wurin aiki.
ta karasa maganar da rashin jin dadi a muryarta "kin tuna bashine aurena na farko ba a aurena na farko sun bani banda yanzu.
Idan tace maganarsa bata bata mata rai ba tayi karya, "shikenan Allah ya taimaka me za kaci da rana?
"Amin duk abunda ya samu.
"owk tam I love you.
sai da ya furzar da iska mai zafi kafin yace " i love You to."
Da haka suka yi sallama
Parlor sa da dakinsa taje ta share ta wanke toilet ta saka turaren wuta cikin shirin fita ta fito ta samu Huwaila tsaye a kitchen tana kokarin ɗora girkin rana ta tambayeta me zata yi ta faɗa mata rice and stew, tayi farfesu kayan ciki zan je yanzu na dawo.
Huwaila ta mata fatan sauka lafiya ,daman tun washe gari aka kawo mata motarta kai tsaye pharmacy ta nufa ta karbo magani
bata jima ba ta dawo tun kafin ta zauna tasha maganin tana ta addu'ar Allah yasa ya tsaya kafin dare.
Yana zaune a office kiran Daddy,ya shigo a wayarsa tun jiya ya kasa daga kiran Daddy,wata irin mahaukaciyar kunyar Daddy yake ji Rumaisah ta cucesa, dakyar ya daga yayi sallama, Daddy ya amsa ya gaisheda Daddy cikin girmamawa
Daddy ya ce dashi "ya jikinka?
"Na ji samu sauqi Daddy.
"Allah ya kara sauqi ya tsare gaba.
dakyar ya amsa da Ameen, ɗan shiru ne ya biyo baya kafin Daddy yace yaushe za ka zo ka dauki matarka?"ɗan jim AB yayi yana jin shakkar haɗuwa da Mami har ga Allah.
"Daman Daddy nufi na tayi kwana biyu a gida kamin ta samu sauqiInsha Allahu zuwa dare zan shigo na dubata.
"Allah ya kaimu.
Daddy ya faɗa
"Ameen!
AB yace yana sauke wayar,dafe kansa yayi duka da hannu biyu ba zai fasa faɗin Rumaisa ta cucesa ba wuraren karfe 3 ya koma gida Rumaisah an ci wanka cikin wani less riga da skirt da ya zauna sosai a jikinta tayi kyau sosai sai fitinannen ƙamshi ke tashi ajikinta da sauri ta rungume AB tana manna masa kiss a gefen checks ɗinsa
"Sannu da zuwa Habeebi wanka zaka yi ko abinci zaka fara ci?"ta faɗa tana kallon fuskarsa.
"mu fara cin abinci.
ya faɗa yana sakinta har daki ta bisa ta tayasa rage kayan jikinsa.
Jallabiya ya saka ajikinsa tana manne dashi suka sauka kasa zuwa cikin dinning area wannan karon akan cinyarsa ta zauna a haka suka ci abincin suka gama,suka kara komawa sama ruwan zafi ta haɗa masa ya shiga wanka koda ya fito wankan ita ta tayasa ya shirya cikin riga da wando tree quarter na shan iska.
Parlor suka koma kwanciya yayi akan doguwar soofa a haka tabisa
Ta kwanta ajikinsa,daga nan kuma ta rika yi masa wasanni da wata irin shakakkiyar murya yake tambayarta tayi wanka ne?"juya ido tayi tana wasa da kasumbarsa take faɗin."zuwa dare dai ɗan jim yayi bayason wasar ma tayi nisa ya hargitse tunda babu tsarki a tare da ita bai san meyasa duk yadda zai yi romance da Rumaisa baya samun gamsuwa kamar yadda yake samu a wurin Aydah ya tuna haɗuwarsu na farko yadda ya rikice akan jikinta samun kansa yayi da sakin murmushi "Habeebi wannan murmushi fa.
"Na tuna baby Aydah ne.
Da sauri tabar jikinsa wani baƙin ciki yana saukar mata a zuciya.
"Muna tare shi ne kake tunanin wata Habeebi ?"ta faɗa da mugun kishi a muryarta,da mamaki yake faɗin."ita din ba matata bace?
Rai a ɓace Rumaisa tabar jikinsa komawa tayi gefe,ya dauki remote yana canja channel shi ma bai kara magana ba sai bayan sallar la'asar ya shirya cikin shadda kalar light blue yayi kyau sosai sai ƙamshi yake fita ajikinsa.
Ya leƙa dakin Rumaisah kwance ya tarar da ita da waya a hannunta alamar chat take yo."Ni zan fita.
Da mamaki ta tashi zaune tana faɗin."zuwa ina?"
"Gari zan shiga.
Da sauri Rumaisah ta sauko kan bed tana kokarin neman mayafi tana faɗin."sai mu shiga garin tare daman duk kewa ta dameni.
"kwanan ki nawa da zuwa gidan nan?"kawai kiyi zaman ki ba daɗewa zan yi ba zuwa bayan ishaai zan dawo.
Lokaci ɗaya yanayin Rumaisah ya canja ta haɗe rai sosai "na tafi.
Da haka ya juya ya rufo mata kofar baƙin ciki kamar zai kasheta yanzu haka wurin wannan mayyar zai je daga shi har ita za tayi maganinsu bada jimawa ba.
kan sallaya Mami ta samu Aydah da alamar gama sallar ta kenan ta dubi abincin da aka kawo mata ganin bata taɓa komai ba,da mamaki Mami ke faɗin.
"abinci baki ci ba kenan?"
idanunta sunyi wani irin zuru-zuru ta turo baki tana faɗin ita ta koshi,Mami tayi kwafa tana faɗin "cikin ki kika yiwa maganar komawa gidan wancan dan iskan yaron ma ki ciresa cikin tunaninki dan ba komawa za kiyi ba. Da haka Mami ta dauki abunda zata dauka ta fice daga ɗakin ranta duk a ɓace,wannan shegen yaron duk yabi ya cinye mata kurwar ya'yanta mami bata jima da fita ba Siyama ta shigo da waya a hannunta ta tarar da Aydah na kuka ta ware ido tana faɗin."me kuma ya faru wani abu ke maki ciwo ne?
Ita dai Aydah batace komai ba sai famar sharar hawaye take "karbi waya yayanmu nason magana dake.
Da sauri Aydah ta amshi wayar."Baby ya karfin jiki?
cikin rawar murya Aydah ke faɗin "yaushe za ka zo mu tafi gida yayanmu?"
"kin ji sauki kenan?
"uhmmm!
"Did you miss me baby?"
ɓoye fuskarta tayi da tafin hannunta tamkar yana ganinta "zuwa anjima zan shigo na dubaki me zaki bani.
"komai ma yayanmu!"
ta faɗa cikin shagwabarta da yakeso tana jin sautin murmushinsa ta cikin wayar kafin ya ɗora da faɗin.
"kinyi alkawari?"
"nayi tau.
" Allah ya kaimu,
Ta amsa masa da Ameen sun dade suna magana kafin yayi mata sallama,haka yace taci abinci dan ta faɗa masa bata ci abinci ba wayar da suka yi da yayan nata ya ɗan samar mata da natsuwa haka ta sauka kasa
Ta zuba abinci ta dawo cikin parlor tana ci a hankali Mami dai ko kallonta batayi ba,tana cikin cin abinci Jamal ya shigo cikin parlor ta daga kai tana kallonsa tun da tayi aure bata gansa ba tun da ba wai anan yake karatu ba
Ko yanzun ma hutu yazo da ido yabi Aydah yana jin wani abu na taɓa masa zuciya,ta kara cikowa tayi wani irin fresh na ban mamaki duk kishi ya gama cika Jamal waya sani ma ko AB yana taɓa jikin Aydah irin wannan cikar da yaga tayi a kwanan nan,da sauri wata zuciya ta kwabesa da faɗin."ai shima yasan ba zai fara wannan gangancin ba Aydah tashi ce shi kadai babu wani namijin da ya isa ya mallaketa bayan shi. Ya zauna cikin parlor da murmushi a fuskarsa ya gaisheda Mami,ita ma Mamin da fara'a sosai ta amsa masa ya mayar da kansa gefen Aydah ya zuba mata ido ganin halin ko ina kula da take nuna masa.
"Kinfi karfin ki gaisheda mutane ko Aydah?"dan tura baki tayi tana faɗin "kai matsalata da kai yaya Jamal shegen son girma wallahi."ina wuni."ta faɗa tana tura masa ɗan mitsitsin bakinta,bakin kawai yake bi da kallo yana jin wani irin yanayi a tare dashi,ya juya kan Mami yana faɗin "Mami har yanzu bai saketa ba."
"Zai ma saketa ne Jamal yanzu baga shi tana gida ba takardar ta kawai nake jira.
ɗan sanyi Jamal yaji aransa lokaci ɗaya Aydah ta haɗe rai jin maganar da Mami keyi ta mike tsaye tana faɗin "Ni ina son mijina wallahi.!"tayi hanyar kitchen fuuuiuu daga Mami har Jamal din bin ta suke da kallon mamaki wani irin zafi-zafi kirjin Jamal ya riƙa yi,kiran waya ne ya shigo a wayar Mami dole Mami tabar parlor yana ganin haka ya nufi kitchen din a mugun fusace tana tsaye jikin sink tana wanke plate ɗin da taci abinci taji an wani irin fisgota an mannata da bango buɗe baki tayi da mamaki tana kallon yadda Jamal ya riƙeta a jikinsa duk yadda taso kwantar kanta kasawa tayi babu inda jikinta baya rawa "Yaya Jamal!!"
Yaji an kira sunansa da karfi.






#JEEDDAH ALIYU
#ASMY B ALIYU
#JAMAL
#AYDAH
#RUMAISA
#AB
#KURMAN ALLO










Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[1/23, 1:36 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels






078.






Juyawa yayi yana kallon saitin da sunansa ke fitowa Siyama ce ta karaso kitchen ɗin Aydah naganin haka ta fisge hannunta dake cikin na Jamal din ta nufi Siyama da sauri ta shige jikinta,siyama tana jin yadda kirjin Aydah ke wani irin dokawa.duk a firgice take, Siyama ta mayar da kallonta wurin Jamal da wani irin expression kwance cikin fuskarsa wanda baka bambance ɓacin rai ne ko kuma mamaki da jin haushi lokaci ɗaya suka taru suka yi masa yawa."Yaya Jamal kana cikin right mind ɗinka kuwa?"matar aure kake ƙoƙarin runguma ko ka manta Aydah tana da aure akanta?"
"Siyama!
Ya kira sunanta cikin ihu,ya tsani kalmar da za'a danganta Aydah da aure, Siyama ta kara ware idonta akansa tana ganin yadda jikinsa ke wani irin rawa.
"ƙarya nayi ko bA matar wani ce ba?"
Ganin ya nufosu gadan-gadan daga ita har Aydah suka daga kafa suka fice daga kitchen ɗin kamar kiftawar ido. Shi ma Jamal cikin zafin zuciya yabar gidan batarda yayiwa Mami sallama. Sai da Mami,ta fito ganin babu Jamal ɗin ta tambayi Siyama ya tafi ne?"
"Daman ya shigo ne?"
cewar Siyama dan ko a fuska Siyama bata nunawa Mami tasan da zuwan Jamal ɗin ba,har bayan magrib
Aydah na kwance a ɗakin Siyama,tunanin yayanta kawai take
ta kasa kunne taji karar motarsa sai dai shiru kusan ishaai taji karar horn
Da gudu ta nufi wurin window ta yaye labule a maimakon taga motar wanda take dakon jira sai taga motar Daddy ce ta shigo cikin compound ɗin gidan a hankali ta saki labulen tana jin zuciyarta wani iri, wasa-wasa har aka yi ishaai babu alamar yayan nata zai6zo duk ta zama wani iri,sai da Siyama ta shigo bayan idar da sallah ta faɗa mata Daddy yace ta fito taci abinci tamkar bata so haka tabi bayan siyama, ta gaisheda Daddy,tayi masa sannu da dawowa cikin kulawa ya amsa yana tambayarta ƙarfin jikinta tace masa ta samu sauƙi Siyama ta ɗauki plate ta shiga zubawa Aydah tuwon semovita da miyar eguisi da aka yi da naman kai,kwabe fuska tayi tamkar zata yi kuka tana faɗin "Ni yayi min yawa yaya Siyam salon ki saka mami tace ba zan bar mata ragi ba.
Siyama ta daukesa ta zuba mata wani wanda bai kai yawansa ba Sadiya,dai da Mami sai bins u take da kallo sallama suka ji ta zazzaƙar muryarsa a bayansu Ƙamshin turarensa ya fara ziyarta hancinsu tun kafin ya iso cikin dinning area ɗin.
Da kasaitatccen takunsa na jan hankali mai cike da izza da taƙama ya iso wurin,ya sunkuyar da kansa yana gaisheda Daddy,batareda ya iya haɗa ido da Daddyn ɗin ba. Daddy ya amsa yana tambayarsa karfin jiki ya amsa masa da sauƙi, mami dai sai cin abinci ta take Sadiya,da Siyama suka gaishesa ya amsa ya gaisheda Mami ko inda yake bata kalla ba Aydah sai bin sa take da kallo tana murmusawa ganin yadda yaki yadda ya kalli inda take "Yayanmu zauna nayi sarving ɗinka.
Sadiya ta faɗa da kulawa a muryarta duk yadda Mami ke aika mata harara ta bangaren ta bata ma san tana yi ba, Sadiya tayi sarving ɗinsa,kusan tare suka ci abinci banda bugawa babu abunda zuciyar Aydah keyi ganin shisshigewa da Sadiya ke yiwa yayan nasu har yaso ya wuce ka'ida.
Daddy yana gamawa ya miƙe tsaye shima Abba yai sauri miƙewa batareda ya haɗa ido da Daddy ba yace zai wuce gida. Dan jim Daddy yayi ya kalli gefen da Aydah take sai ya mayar da hankalinsa wurin Abba.
"Ko zaka tafi da Aydah ne?
Ga mamakin Aydah sai taji yayan nata na fadin."A'ah! Daddy abarta ta dai kara jin sauki da nan da can duk ɗaya ne.
A boye Mami ta sauke ajiyar zuciya ta kara tamke fuska, ahankali Daddy ya kira sunan Aydah ta tashi tazo gabansa "je ki raka yayanki Mamana.
Daga masa kai kurum tayi da sauri tabi bayan AB har tana cin tuntube kar Mami,ta hanata ganin yayanta a mota ta samesa da bottle wata a hannunsa yana wanke baki bata yi magana ba ta karbi ragowar ta wanke bakinta da fuskarta."Yayanmu Ni dai zan bika naji sauki wallahi.!
Ta faɗa tamkar zatayi kuka murmushi kurum yayi ya bude bangaren driver ya shiga ya zauna ta wani riƙe kofar tana buga kafafunta cikin tabara take faɗin."naji fa sauki.
Lokaci ɗaya taji ya fisgota dukanta sai gata acikin jikinsa,ware ido tayi tana kallonsa hannunsa yasa akaran hancinta kafin ya gangaro daidai kan ɗan mitsitsin bakinta
Yana jin yadda numfashinsa ke fisga jinta ajikinsa,ta langwabe kai tana kallon cikin fararen idanunsa cikin narkakkiyar murya ta ce "Please yayanmu mu tafi.
ƙara gyara mata zama yayi acikin jikinsa in a lower tune yake faɗin."idan muka tafi gidan me zaki bani baby?"
"komai ma!"
Ya juya ido irin da gaske ɗin nan girarta duka biyu ta dage masa,ba ƙaramin kyau tayi masa a haka ba, hannunsa yasa ya kara matseta cikin jikinsa har cikinsa na gogar nata cikin, ya haɗe fuskarsa yayi da ta,ta yana sakar mata zazzafan numfashinsa da sauri ta runtse idonta tana kara riƙe masa wuya.
A hankali ya lalubi bakinta cikin bin umarnin zuciya da gangar jiki ya shiga yi mata wani irin deep kisses ga mamakinsa Aydah tayasa ta shiga yi
wanda ya kusan zaucewa nan da nan notikkan kansa suka fara kwancewa a hankali da wani irin sauri ya kwantar da seat ta tafi baya ya mirgino da ita ta koma kasa ya koma samanta sai dai bai sakar mata nauyinsa duka ba still idanunta a lumshe suke sai numfashinta dake fita da sauri da sauri,hannu yasa kan zip ɗin rigarta yana kokarin ja da sauri ta buɗe ido ta riƙe masa hannu tamkar zata yi kuka ita bata son ana tabasu har yanzu basu dawo daidai ba zafi suke mata, murya a shake tamkar ba yayanta ba yake faɗin.
"gaisawa zamu yi baby.!
"zafi suke min yayanmu.
"zasu daina idan muka gaisa.
Ya faɗa da muryar da ba za'a iya fassara wane irin yanayi yake ciki ba a daidai wannan lokacin.
maƙe kafada tayi alamar taki.
"Naje wurin Rumaisah kenan?"
Nan take yanayinta ya canja bata san lokacin da ta ɗora hannunsa a gaban rigar ba wani irin miskilin murmushin ya saki da sauri ta runtse ido jin hannunsa a wurin cikin zaucewa da fita hayyaci ya kafa bakinsa,duk kokarinsa da son rike kansa kasawa yayi yana kokarin daga kafafunta ta riƙesa a tsorace ta fashe masa da kuka bata manta azabar da tasha ba a wancan daren lokaci ɗaya kuma yaji ana knocking glass ɗin motar daman tinted ne,daga Aydah yayi da sauri ta tsallaka back seat tana gyara zaman rigarta duk ta rikice a hankali ya tada seat ɗin ya haɗe kansa da sitiyari yana ƙoƙarin daidaita numfashinsa still jin yayi an cigaba da knocking kofar motar,a hankali ya sauke glass ɗin da mamaki yake kallon Sadiya duk a daburce take cikin rawar murya take faɗin "Daman Mami tace nazo na kira Aydah.
Tana maganar tana kokarin leƙa motar ko magana bayan sonyi saboda halin da yake ciki a gefe ɗaya kuma yana mamakin halin Sadiya,lokaci ɗaya Aydah ta buɗe backseat ta fito tun daga sama har kasa Sadiya ke bin ta da kallo ganinta duk a hargitse tasan akwai abunda ya faru cikin motar wani irin mummunan bugawa zuciyar Sadiya ta shiga yi yaushe Aydah ta zama haka?"tana mata kallon marar wayau wacce bata san komai ba akan harkar aure ashe ba haka bane. Aydah ta juya ta nufi entrance ɗin shiga gidan da sanyi jiki Sadiya tabi bayanta daidai tsakiyar parlor Sadiya ta finciko Aydah da mamaki Aydah ke kallonta Sadiya tana huci take faɗin.
"mekike yi keda Yayanmu acikin mota ji gaban rigarki.
"Kamar ya me nake yi yaya Sadiya?"me kika san macce nayi da mijinta ai ina ganin hakan ba haramun bane.
hannu Sadiya tasa da nufin ta zabgawa Aydah shegen mari taji an riƙe hannunta a fusace ta juya

57 / 80