Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   11 / 80

30K to 33K   out of 237.2K words

da Alh Sanusi dake famar dokawa maigadi harara da yake kare da dan redionsa a kunne tamkar bai san da zamansu ba ,a lokacin Alh Sanusi jin yake tamkar ya je ya kwaɗawa maigadi mari da mamaki maman Mufeeda ke kallon Lanto dake kora mata zancen yadda maigadi ya yiwa bakon Alhaji koda ta tarar da Alhaji Habeeb ya tashi daga bacci sai dai da alamar bai daɗe da tashi ba.
Tambayar da ya fara yi mata shine wa ke ta buga get haka bugun ne ya tashesa daga bacci tace masa shine dalilin da ya kawota ta faɗa masa yana da bako a waje maigadi ne ya hanasa shigowa shine ya rika buga get Alh Habeeb dai yana ta juya kalmar bako aransa da safiyar nan,
Daman akwai jallabiyya ajikinsa casual slippers kawai ya saka wa ƙafarsa ya bi ta cikin balcony, zuwa cikin compound Alh Sanusi na hango fitowarsa ya washe haƙora tun kafin ya ƙaraso gun sa ya taresa ya saukar da kai ya basa hannu with respect suka yi musabaha, Sanusi kaine da safen nan haka? Allah yasa lafiya?"
Alh Habeeb ya ƙarasa zancen yana kallon Alh. Sanusi dake famar shafa kansa "wallahi kuwa Alh wata magana ce mai muhimmanci nazo muyi da kai.
"To mu ƙarasa daga ciki har cikin balcony ya kai sa wurin akwai kujeru acikinsa suka zauna suka ƙara gaisawa kafin Alh Sanusi ya nisa yana faɗin."Ashe yar wajenka ce zata auri Abba Alh? murmushi Alh Habeeb ya yi yana faɗin "kaima dai Sanusi da son zance kake kar dai ka ce min ba ka da labari zance aure nasu? Wasu yawun baƙin ciki Alh Sanusi ya haɗe yana faɗin "Aini wallahi yaya Bashir ya bani mamaki ace ya rasa wanda zai cuta sai kai.
Da mamaki Alh Habeeb ke kallon fuskar Alh Sanusi dan ko kaɗan bai dago zancen nasa ba "Sanusi wacce irin magana kake faɗa haka? Ban gane ba.
"Ai ba zaka gane ba Alh Habeeb yaya ya faɗa ma dalilin fasa auren Abba na farko?"
Ɗan shiru Alh Habeeb,ya yi kafin yace "kasan lokacin da aka yi auren bana gari so yace matsala aka samu ba a ma daura auren ba.
Alh Sanusi ya riƙe baki yana ƙara gyara zama ya ce "waton dai aminci ya yi wuya yanzu a wannan duniyar, nan take Alh Sanusi ya fara bai wa Alh Habeeb labari akan rashin yiyuwar auren Abba ,na farko har Alh Bashir ya aura masa Sadiya yar wajensa yanzun ma haka sun rabu ta dalilin daren aurensu na farko ta caka masa wuka.
Sosai Alh Habeeb ya tsorata da lamarin jikinsa lokaci ɗaya ya yi sanyi ransa yai masifaffen ɓaci akan ha'intarsa da Alh bashir ya yi ai ba irin wannan maganar ake ɓoyewa ba
wato shiyasa ya rika yi masa zarya a office yana son a saka auren Abban da Mufeeda da wuri ,ta yadda ba zai ɗauki lokaci ba yasan yaron ma shege ne bai da uba bai da asali azo a kakkabawa 'yarsa ko 'yarsa ta rasa mijin aure ba zata auri marar asali tsintatce ba.
Haka dai Alh Sanusi ya baro gidan ransa fess! Da yake ranar Assabar ne ana hutun ƙarshen mako ba a fita aiki Alh Habeeb yana gama karin kumallo ya ɗauki motarsa sai gidan Alh Bashir
wanda sosai Alh Bashir ya yi mamakin ganin aminin nasa har parlorn sa suka ƙarasa sama-sama suka gaisa ganin yadda fuskar Alh Habeeb take a mugun murtuƙe sai da ya daga hankalin Daddy
A natse Alh Habeeb ke faɗin."Dama Alh Bashir Abba ,ba ɗan cikin ka bane?" kuma da gaske shege ne ba kai ka haifesa ba?"
A razane Daddy ke kallon Alh Habeeb jin irin kalaman da yake jifar Abba dasu.
Rai a ɓace Daddy ke fadin "Habibu kana cikin right mind ɗinka kuwa?"
Shi ma Alh Habeeb a hasale ya katse sa ta hanyar faɗin "Da hankali na Bashir ka amsa min tambayar da nayi maka a farko.
"Abba ɗana ne sai dai bani bane biological father ɗinsa he's adopted child by me and I love him more than my own childrens.
murmushin takaici Alh Habeeb ya yi yana huci yake faɗin "Amma gaskiya Alh Bashir ba kada cikkaken hankali ta ya za ka yi adopting ɗa ba kasan ta wacce hanya siga aka samar dashi ba. Ka garwaye shi cikin 'ya'yanka na halak gudan jininka har kana kirari ka fi sonshi fiye da 'ya'yan da ka haifa. Wannan wane irin sakalci ne?
"Alh Habeeb ka faɗamin inda aka haramta adoption?
"Babu inda aka haramta adoption Alh Bashir sai dai ya haramta ta hanyar da kai ka yi shi meyasa ka ɓoyewa duniya sahihiyar gaskiya akan Abba?"
"Saboda bana kallonsa a matsayin adopted child face ɗan da na haifa da jini jikina.
"Amma ina fatar kasan da cewa Abba bayada gadonka?
"Na sani mana tun da ni ba jahili bane.
"To da ace wannan sirri bai fito ba ta Allah ta kasance da kai kuma shikenan sai Abba ya ci gadonka?
"Alh Habeeb ka daina yi min kallo jahili mutum tun-tuni na rubuta (wasiyya) na ware kason Abba a cikin dukiya ta.
Sosai Alh Habeeb yasa dariya mai cike da zallan takaici kafin ya kalli Alh Bashir a shaƙeƙe ya ce "Yarka taƙi zaman aure dashi ni kuma kake son kakkabawa tawa 'ya lallai Bashir baka da ta ido wallahi, to kasani ko dukka dukiyarka kabar wasiyya a ba wa Abba aure tsakanin sa da 'yata ba zai yiwu ba wallahi. A je can a samu wata shegiyar a aura masa ba dai 'yata ba.
Alh Habeeb yana gama faɗar haka ya kakkaɓe babbar rigarsa yabar parlon a mugun fusace karo suka ci da Mami, wacce ko takan gaisuwarta bai bi ba sai da gabanta ya fadi ganin yadda Alh Habeeb ɗin ya fito a parlon maigidan nata da sauri ta faɗa parlorn Daddy ta isko shi dafe da ƙirjinsa yana ta kokuwa da numfashinsa Mami ta kwala ihu tayi kansa a guje tana kiran sunansa ta kama shi ga baki ɗaya Daddy sai zufa yake haɗawa jikinsa na wata irin kakkarwa da dukkan ƙarfinta Mami ta shiga kiran 'ya'yanta kusan a guje suka shigo parlon na Daddyn nasu ganin halin da mahaifinsu yake ciki duk suka yi kansa a guje ,a ruɗe Mami ta ce a kira mata Abba duk ƙarfin zuciya irin na mami wannan karon hawaye ke fita acikin fuskarta.


#love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#team tagwaye novels
#Kurman Allo.






Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/4/2023, 8:35 AM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU




#Love story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye novels


*LAST FREE PAGE.*


*RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU.*
*TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA*
PAID BOOK


015..


Siyama ce ta kwasa da gudu ta nufi part ɗin AB yana zaune a parlor da laptop a gabansa online meeting suke yi da Kamfani whitepaper Automotive industry Germany tare da haɗin gwiwar kamfanin Two stars Automobile industry wanda suma suna da hannun jari da whitepaper yanzu kuma suna buƙatar ƙula yarjejeniyar kasuwanci da kamfani su AB saboda kusan duk wasu sababbin motoci a tare kamfani na whitepaper ke turo musu. Yadda Siyama ta turo ƙofa da ƙarfi ya jawo hankali AB zuwa gare ta sai uban haki take "Ya Abba kazo Daddy ba shi da lafiya dakyar yake iya numfashi.
Siyama tayi magana cikin harɗewa harshe, duk da hankali Abba ya yi mugun tashi sai dai ba za ka taɓa fahimtar hakan ba, saboda a natse ya kalli team members da suke meeting ɗin ya faɗa musu uzurinsa kana suka yiwa Daddy fatan samun lafiya ya rufe laptop ɗin. Ya nufi ƙofar fita cikin tafiyarsa ta natsuwa tuni Siyama ta wuce shi hali da yaga Daddy aciki ya yi masifar ɗaga masa hankali, da taimakon direban gidan suka ka kai Daddy cikin mota AB bai tsaya jiran su Mami su fito ba ya umurce direban da ya ja mota su tafi. Koda Mami da girls ɗinta suka fito su AB sun wuce sai Aydah ce ta koma ciki gida ta daukowa Mami makullin mota hankali tashe Mami ta iso farfajiyar International private hospital wanda shine asibiti da suke da file. Su Mami basu sha wahala gani AB da direba dake safa da marwa a ƙofar ɗakin da aka shigar da Daddy. Dukkansu tsaye suka yi cirko-cirko Aydah sarkin kuka gaba ɗaya fuskarta ta kwabe da hawaye da majina.


*KIM'S AUTOMOBILE INDUSTRY LAGOS*
Kyakkyawar matashiyar budurwa ce ta fito daga ofishinta dake hawa na biyu jikinta sanye da california pink gown wacce ta bayyanar da sirri kyawonta, hannunta ɗauke da wasu tarin files kaitsaye elevator ta hau wanda zai kaita hawa na biyar idan ofishin Chairman na kamfani yake. Sai da ta tsaya suka gaisa da ASM na Kamfani (Assistant stage manage) da shima ya fito daga office ɗin Chairman, sun ɓata almost a ten good minutes suna tattaunawa dangane da sababbin motoci da wani ƙaramin kamfani ke so. Sai da tayi using da key card ɗinta kana ƙofar ta buɗe ta shiga wani irin ni'imatatcen sanyi mai ɗauke da tsadadden ƙamshin turarensa ya lulluɓeta har batasan sanda ta lumsashe ƙanana idanuwanta kafin ta buɗe su ta ci-gaba da takawa har izuwa gaban desk ɗinsa ya juya mata baya iya gadon bayansa take iya gani sai kuma fararen hannayensa da ya haɗe su guri guda, cikin sanyi muryata ta furta "Welcome back Abbu!
Sai da ya kusan share 60 seconds kafin ya juyo da kujerar izuwa gareta fuskarsa a haɗe as usual Alhaji Aliyu Usman Mustapha na uku kenan Chairman of Kim's Automobile industry. "Anaal ina raguwar 'yan uwanki ne da na ganki ke kaɗai ko su ba su sami sako neman su da nake ba? I have some important issue to discuss it with you.
"Abbu all of them are not in the company tun sanda ka yi tafiya suka daina zuwa I am the only one who takes care of the company.
Ta ƙarasa maganar kaman za ta sa kuka irin wahala ta yi mata yawa.
Sosai ran Alhaji Aliyu ya ɓace ya rasa gane me ke damun Zeeyad da Zaheed da basan so maida hankali akan aikinsu, Anaal da take macce ma ta fi su maida hankali, a fusace ya furta "kira su a waya ki faɗa masu ina so ganinsu nan da ten minutes a conference hall, muna da meeting na gaggawa don ba zan ci-gaba da zuba musu ido suna yiwa kamfani riƙo sakainiyar kashi.
Ran Anaal ya yi fari tass! Cike da zumuɗi ta yi dialling numbern Zaheed kuma tsabar mugunta sai ta saka wayar a speaker "real disturber ya aka yi ne?"
"Yaya Abbu ya ce na sanarda kai yana so ganinka nan da ten minutes a conference hall.
"Ke banaso karya ko Abbu zai dawo sai next week saboda haka ki je ki cigaba da aikin gabanki agogo sarkin aiki.
"I swear to God Abbu ya dawo.
"What! Yaushe ya dawo?
"Yesterday night!
"To dan ƙaniyarki me ya hana ki faɗamin tun jiya ɗin?
"Yaya Zaheed na saka wayan a speaker duk abunda kake faɗa Abbu yana ji ka kuma san baya so kalaman rashin ɗa'a.
Ai kuwa da sauri Zaheed ya yi hanging up. Ta kira Zeeyad koda kiranta ya shigo yana sharar bacci abinsa dakyar ma ya yi picking call ɗinta cikin muryar bacci ya fara zazzaga mata masifa, sai da ya yi mai isarsa kafin ta sanarda shi saƙon Abbu, a firgice ya ture duvet ɗin jikinsa ya faɗa bathroom da gudu.
Anaal sai faman ƙunshe dariyarta take yi dakyar ta saita kanta cike da respect ta miƙawa Abbu files ɗin hannunta "Abbu ga files ɗin kula yarjejeniyar kasuwanci da kamfanoni dake da sha'awar motocin mu. Sai kuma ɗayan file ɗin na mr Anthony ne yana so Kamfani ta bashi motoci ɗari zai yi half payment saboda kamfaninsa yana fuskantar financial crisis yana so ya farfaɗo.
Sai kuma wannan file ɗin kamfani whitepaper Automotive Germany suna buƙatar saka hannun jari a kamfanin mu amma fa haɗin gwiwa ne da kamfani moonlight dake Kano. Abbu idan za ka tuna na taɓa ba ka labari wannan kamfani ɗin da yadda suka yi shura wajen kawo latest cars and car accessories ko lokaci da Mercedes Benz C43-four door ta fito sun ri ga mu shigowa da ita nayi following Instagram handle na Chief Executive officer na kamfani Abba Bashir Abbu jiya-jiya nan ya ɗora the upcoming 2024 model C63 bai kamata mu jinkirta accepting offer ɗinsu ba. Saboda idan muka haɗa gwiwa dasu za mu ƙaru dasu duk faɗin arewacin Najeriya sune lamba ta ɗaya wajen shigowa da sababbin motoci, kaman yadda kamfanin mu ya cire tuta a kudancin Najeriya.
Har Anaal ta dasa aya a dogon sharhinta Abbu bai tofa uffan ba hakazalika bai katse ta ba. Gani ta kai ƙarshen zance nata ya ɗan murmusa cike da izzarsa da jini sarauta da ya gama ratsa jikinsa yace "Ki haɗa mana zama dasu amma ki tabbata su ne za su zo ba mune za mu je musu ba.
"Okay Abbu!
Anaal ta faɗa cike da farin ciki saboda tun lokaci da ta yi following ɗin Abba Bashir a Instagram ta ji yana burge ta musamman yadda yake hardworking tana so taga mutum ya ɗauki aikinsa da muhimmanci ba kaman stupid twins cousin ɗinta ba da abinda suka iya sai lalaci da shegen son jiki tsiya ko ita da take ta mace ta fi su.
Da fice daga office ɗin tana ƙoƙari shiga elevator sai ga Zaheed, mugun kallo ya wulga mata ya yi ƙwafa kana ya wuce office ɗin Abbu.
Bayan sun fito daga meeting wanda kusan rabinsa faɗa ne Abbu ya dinga yiwa twins akan rashin maida hankali da suke yiwa kamfani. Abbu yana ficewa daga hall ɗin cikin sauri Anaal ta kwashe wayoyinta, da nufi ta gudu domin ta tabbata idan twins suka rutsa ta za ta ji jiki. Da sauri ta kutsa cikin ayarin team members da suke ƙoƙari fita daga hall ɗin, karaf ta ji an riƙe mata hannu a tsorace ta sauke ƙanana idanuwanta akan fuskar Zeeyad ɗayan hannunta ta ji an sake kamawa tana juya wa taga Zaheed suna haɗa idanu ya kashe idonsa ɗaya yana mata murmushi mugunta "Meye haka? Me nayi da za ku wani rirriƙe ni kaman wata ɓarauniya?
"Anaal abunda ke ɗinan ki ka yi mana gwada ɓarauniya dake. Kinsan tun jiya Abbu ya dawo meyasa ba ki sanar mana ba?
Zaheed ya yi magana yana zare mata idanuwansa.
Ta sheƙe da dariya tana faɗin "Akan me zan sanar daku, wato kun manta yadda ku ka barni da aiki ni kaɗai.
Zeeyad ya mitsine mata fatar hannu yana faɗin "ai kuwa jikinki ne zai gayamiki ba dai taƙamar mugunta ba.
Shi ma Zaheed mitsine ta ya yi sai ihu take tare da neman agaji dakyar ta samu suka sake ta farar fatar hannunta tayi shatin farce su ga Anaal da ɗan neman raki sai yarfe hannaye take tana hawaye, yayin da su kuma sai dariya suke mata kafin kuma suka dawo rarrashinta har da yi mata alƙawari kai ta shopping sai ga Anaal tana dariya.
*INTERNATIONAL PRIVATE HOSPITAL KANO*
Da taimakon likitoci numfashin Daddy ya daidaita kana aka yi masa fixing drip mai ɗauke da allurai saboda jininsa ne ya yi mugun hawa a lokaci da su Mami suka shiga ɗakin da aka kwatar da Daddy yana kwance magashiyam hannunsa na dama manne da drip yayin da numfashinsa na hawa da sauka alamar bacci yake yi. Jikin Mami a sanyayye ta ja plastic chair ta zauna a gefen gadonsa daidai fuskarsa Siyama da Sadiya kowacce ta ja kujera ta zauna tallaɓe da kumatu suna kallon mahaifin nasu. Aydah ce kaɗai ta kasa zama sai ta koma daidai fuskarsa Daddy ta tai tsaye lokaci zuwa lokaci take goge hawaye da bayan hannunta. Lokaci da likita ke sanar da AB makasudin ciwo Daddy sai da girgiza domin iya saninsa Daddy ba shi da cutar hawan jini, baya kuma ciki wata damuwa da za ta haddasa wa jininsa muguwar hawa, domin likitan ya faɗa masa jinin Daddy ya yi matuƙar hawa kusan 140 jikinsa a mace ya dawo ɗakin da Daddy yake ya nemi kusa da Aydah ya tsaya shi ma ya bi sahun su na kallon hawa da saukar numfashin Daddy da suke yi. Cikin sanyi murya Mami ta kira sunan AB "Abba!
"Na'am Mami!
"Halan me likita ya ce yana damunsa ne?"
Sai da AB ya ja ƙarfaffiyar ajiyar zuciya kafin ya ce "Bai ce komai ba Mami.
"A'ah! Kaman ya Abba?" ya kamata musan musababbin faruwar wannan ciwo nasa saboda na ci karo da Alh Habeeb bichi ya fito daga parlornsa kuma ga dukkan alamu ransa a ɓace yake domin ko tsayawa bai yi ba muka gaisa ina ƙarasa shiga parlorn na tarar da Alhaji yana fizgar numfashi.
Ciki kaɗuwa AB yake kallon Mami sai kuma ya yi sauri kawar da fuskarsa tare da ƙoƙarin saita natsuwarsa.
"Mami kada mu yi gaggawar yanke hukunci mu jira sakamakon bincike da likitoci suka yi, sune suke da hurumin yanke hukunci abinda ke damunsa.
AB ya faɗa da so kawar ma Mami da zarginta. Jim kaɗan AB ya umarce Mami dasu koma gida saboda sun baro gida ba kowa Aydah bataso ta bi su Mami ba sai da AB ya yi mata tsawa kana ta fice tana sharar hawaye. Bayan tafiyarsu Mami AB ya tsunduma kogin tunani idan har lissafin sa ya tafi daidai Alh Habeeb Bichi ya zo ne akan zancen aurensa da 'yarsa Mufeeda watakila shima ya sami labari akan rashin asalinsa.
Lumshe idanuwansa ya yi can ƙasan zuciyarsa yake ji wani irin tuƙuƙi baƙin ciki, shiyasa ya ce da Daddy ya jingine zance aurensa a gefe a halin da yake ciki zai iya riƙe kansa har ƙarshen rayuwarsa ba tare da aure ba. Kwata-kwata aure ya fice masa arai ƙanwarsa ma ta kasa zama dashi wa Daddy yake tunani iyayenta za su karɓe shi a yadda yake. AB bai ankara ba ya ji zafafan hawaye na bin kumatunsa.
Sai dab da magarib Mami da girls ɗinta suka dawo ɗauke da luxury warmers zuwa lokaci Daddy ya farfaɗo

11 / 80