Author : EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category : KDP NOVELS
koma nasa ɗakin kwanciyya ya sake yi badan yana jin bacci ba yana ta kokayrin tuna abun da ya faru tsakaninsa da Aydah a daren jiya da ya damu kansa da sai ya tuna komai sai yaji kansa na wani irin juyawa tsaki kawai ya saki ya lumshe idanunsa, Aydah har ta gama shirin zuwa school taci indomie da Huwaila tayi mata tana ta kallon upstairs taga har lokacin AB bai fito ba idan kuma ta tuna ihun da yayi mata jiya sai taji jikinta yayi mugun sanyi, ganin 7:38 yasa ta nufi upstairs tsaye tayi bakin ƙofar ɗakinsa tayi knocking shiru taji har sau uku batareda tunanin komai ba ta murɗa ƙofar room din,hangosa tayi kwance kan soofa yana bacci ɗan ware ido tayi akansa kafin ta isa garesa sai da ta leƙa fuskarsa ƙarasawa tayi wurin kunnensa ta kira sunansa da karfi a firgice ya buɗe ido ya tashi zaune suna yin ido biyu da Aydah yaji ransa yayi mummunan ɓaci fuskarta yake kallo tamkar bakin maciji ya yi tsaki yarinyar nan.!"ubanwa ya kawoki ɗakina?"ya faɗa a tsawace ganin yadda idanunsa suka juye lokaci ɗaya yasa jikin Aydah ya soma wani irin rawa bata taɓa ganin yayanta haka ba ita idanunsa ma tsoro suke bata,bata taɓa ganinsa cikin wannan yanayin ba tamkar ba yayanta ba. Cikin rawar murya hawaye na taruwa a idonta take faɗin."nagama shirin makaranta."da mamaki yake kallonta kafin ya tattare girarsa wuri ɗaya da wata irin murya yace "Daga yau ba sai na kai ki makaranta ba zan yi kokari na samo maki driver ko ki dinga bin school bus,ita dai kallon yayan nata take da mamakinsa da ya hanata magana.ya dauko wallet ɗinsa dake kan mirror dressing ya ciro 5k ya karaso gabanta ya bata kuɗin ta karba tana kasa riƙe hawayen idanunta "ki shiga adaidaita kamin ki dawo zan yi kokari na samo maki driver ko na kira school ɗinku ki dinga bin school bus.
Juyawa kawai Aydah tayi ta fice daga room ɗin nasa hawaye suka shiga zuba akan kyakkyawar fuskarta har ta bacewa ganinsa ya kasa motsawa daga inda yake sai bayan fitarta kansa da yaji yayi masa nauyi ya sauka. kwanciyyarsa ya koma ya yi bai kara tuna wata Aydah ba daman kuma idan ya matsawa kansa da tunaninta sai ya ji wani mugun ciwon kai na shigarsa.Aydah ko sallama bata tsaya yiwa Huwaila ba ta fice daga gidan da kafa ta riƙa takawa tana yi tana tare hawayen da suka kasa tsaya mata cikin fuskarsa
ga baki ɗaya a rude take ta rasa wane irin tunani zata yi akan yayan nata ta dauka jiya cikin bacci yake shiyasa ya rika yimata ihu da tsawa yanzun ma haka,yayanta kowanne irin uzuri yake da ko bashi da lafiya sai ya kaita makaranta yau shine yake cewa ta tafi ta shiga adaidaita."ta kasa yarda yayanta ne da take matuƙar so da ƙauna, tana ta tunanin laifin da ta yiwa yayanta ta basa haƙuri ya sauko su dawo yadda suke ada, wannan bad attitude ɗin da ya tsiro mata ko kaɗan baiyi mata daɗi ba zuciyarta ba zata iya dauka ba,har taje school wannan ranar ga baki ɗaya friends ɗinta basu gane kanta ba.
Haka ta dawowa Huwaila tamkar wacce bata da lafiya,har tambayarta Huwaila tayi ko bata da lafiya ne."ta faɗa mata lafiyarta ƙalau ɗaki ta shige ta kwanta ko uniform din jikinta bata cire ba. Ƙarfe 3 daidai yaje ya dauko Daddy a Airport tare suka ƙarasa gida sosai Mami tayi mamakin ganin Daddy ya dawo ranar dan bai faɗa mata zai dawo ba Amman tunda ta gansa tareda Abba tasan ya faɗawa Abban,a wani irin wulaƙance Mami ta amsa gaisuwar Abba ta shiga hidima da Daddy kusan tare suka ci abinci rana da Daddy yayi wanka ya kimtsa.
Suna dawowa Masallaci Daddy ya yiwa Abba umurnin suje parlornsa su tattauna gaban AB banda faɗuwa babu abunda yake yabi bayan Daddy.
Daddy sai da ya gama kallon yanayin Abba ga baki ɗaya,sa'annan ya daidaita murya "Ashe kun daidaita da surukinka baka faɗamin ba?" Sai da gaban AB ya buga jin irin tambayar da Daddy yayi masa,dakyar ya tattara natsuwarsa cikin daburcewa ya soma baiwa Daddy labari babu abun da ya boye masa,sai dai har lokacin bai fito kai tsaye ya nunawa Daddy yana da ra'ayin auren Rumaisa ba.sosai Daddy,yake mamakin zurfin cikin Abba."mun haɗu da Alhaji Bello Madawaki a Abuja ya bani haƙuri acikin taron jama'a kuma yace ko yanzu kake son Auren Rumaisa zai ɗaura maku aure."sai dai har yanzu banji ra'ayinka ba."da sauri AB ya shiga shafa kansa bai san me zai cewa Daddy ba da kunya yacewa Daddy ya amince zai auri Rumaisa."mun yanke shawarar nan da sati biyu za'a daura maku aure sai ka je ka cigaba da shirye shiryen biki mahaifinta yace baya bukatar ka wahalar da kanka tunda na farko kayi kuma baka karbi lefen da kayi mata ba.mamana kuma ka barni da ita gobe ka kawomin ita zan yi mata bayanin komai. godiya AB yayiwa Daddy,ya fice daga parlor yana jin wani irin tsantsar farin ciki aransa ga mamakinsa jin yayi kamar ya jawo ranar aurensa da Rumaisa bai san yana bukatar aure ba sai yanzu bai san shima cikakken namiji ne wanda keda burikka kala-kala acikin rayuwar aure sai yanzu, sunyi waya da Rumaisa yanata tsokanarta da amaryarsa ita ma farin cikinta ya kasa boyuwa har a muryarta "habeebi anjima za ka shigo ko? "sai bayan magarib. Da haka ya sauke wayar ya kira Ak ya tambayesa yana ina?"ya faɗa masa yana (hotoro)a majalisarsu sai da AB ya ɗan yi tsaki yana faɗin."banga amfanin wannan majalissar ba.
"Kaine bata da amfani a wurinka kaima da sannu za ka zama ɗan gari tsaki AB yayi yana faɗin."ka jirani gani nan zuwa da haka AB ya sauke wayarsa ganin kiran Aydah na shigowa a wayarsa ya wani haɗe rai lokaci ɗaya yayi rejecting kiran karshe ya saka wayar a silent, a mota Ak ya cimma AB dan
Abban cewa yayi shi ba zai karasa wurin ba, "mafarkina ya kusa zama gaskiya nan da sati biyu zan zama Angon Rumaisa.!"Abba ya faɗa da wani yanayi a muryarsa yana kallon Abdulkarim ɗin da shima shi yake kallo, ganin yadda Abdulkarim ya tsura masa ido yasan karin bayani yake nema. Anan ya faɗa masa yadda suka yi da Daddy,ko kaɗan Ak bai nuna wani jin daɗinsa ba shima Abban bai damu ba fatan alkhairi kawai Abdulkarim yayi masa ya masa sallama ya wuce sai da yayi sallah ya shiga gida Aydah najin shigowarsa ta fito daga ɗakinta komai ta tuna ta koma da sauri tun kafin su kai ga haɗa ido taji zuciyarta na wani irin bugawa.gargadinsa ta tuna shima ko kallon ɗakinta baiyi ba nasa ɗakin ya nufa yayi wanka a gurguje ya shirya cikin shadda milk colour sabuwa dal ,ya kafa hula akansa sai ƙamshi ke tashi tamkar wanda yayi wanka turare yana sauka falo Huwaila ta russuna ta gaishesa ya amsa fuska babu walwala.ita kanta Huwaila sai da gabanta ya fadi ganin yadda ya haɗe fuska.cikin sarkewar harshe take faɗin."daman Aydah tunda ta dawo bata ci abinci ba ta shige a daki babu irin rarrashin da ban mata ba taki taci. "ai ba yarinya bace ki kyaleta cikinta daga yau karki kara sakani a sabgoginku kina jina kiyi aikin da ya kawoki a gidan nan."da sauri Huwaila ta daga kai ficewa yayi daga parlor batareda ya ƙara bi takanta ba.wani irin mugun sanyi jikin Huwaila yayi meke damun yaya Abba,haka da gani akwai abunda Aydah,tayi masa da zafi
kai tsaye ɗakin Aydah ta nufa tayi knocking jin shiru yasa ta tura kofar.
Aydah ce zaune akan bed ta zuba uban tagumi idonta sun kumbura da alamar tayi kuka har ta gaji da sauri Huwaila ta nufeta tana faɗin."Subahanalilah Auta meya sameki haka?"dama tamkar jira Aydah,take ta fashewa da Huwaila kuka mai cin rai tana faɗin "yayanmu baya sona Aunty Huwaila yabi ya tsaneni ban san laifin da nayi masa ba."Huwaila ta sakata ajikinta tana rarrashinta cikin taushin murya Huwaila ke faɗin."ki faɗamin me kika yi masa da zafi har haka?"da sauri Aydah ta shiga girgiza kai hawaye na rolling cikin fuskarta take faɗin.'"babu abun da nayi masa nan ta faɗawa Huwaila abun da ya faru a daren jiya har mafarkin da tayi, ita kanta Huwaila da tafi Aydah,wayau sai da ta tsorata sai dai bata bayyanasa ga Aydah ba tace "yanzu dai yace kici abinci na faɗa masa bakici abinci ba."yace kuma na tabbatar kinci na kawo maki yanzu kici?
"kaɗan zanci. Aydah ta faɗa tana komawa ta kwanta cike da matsananciyar damuwa..
#Love story2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Kurman Allo.
Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[1/4, 5:14 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye
055.
Da rarrashi hadi da daɗin baki Huwaila ta samu Aydah ta ci abinci ta fita da plate ɗin Aydah kuma ta koma ta kwanta jin kanta take yi tamkar wacce bata da lafiya ko wacce aka zarewa lakkar jiki. Bata ji kuzari ko kadan, zuciyarta ya kasa accepting wannan bakon al'amari daga yayanta iya tunani tayi ta kasa gano laifin da tayi masa da cancanci wannan zazzafan hukunci daga garesa.
Zuciyar AB fal farin ciki ya isa compound ɗin gidansu Rumaisa ya yi parking tare da kashe motar ya kira ta a waya jin kadan sai ga Rumaisa ta fito ta ci kwalliya jikinta sanye cikin light purple lace skirt and blouse sosai style ɗin ya karɓi jikinta tun kamin taƙaraso AB ya tsare ta da mayatattun idanuwansa yana kallon yadda jikinta ke jujjuyawa da yake ko mayafi bata saka ba. A zuciyarsa yake faɗin "Ka ga inda mata suke kalli yadda komai ya ji a jikinta Allah na tuba ni da zan mallaki wannan manyan kaya me zan tsinta a jikin kwaila. Rumaisa ta iso tare kwakwasa masa glass ya buɗe ƙofa ya fito yana mata wani kalar kallon kasan ido "kin yi kyau my habibty anya two weeks ɗinan ba su yi min yawa ba?"
Ɗan zaro idanuwa Rumaisa tayi tana dariya "Bana so yaudara irin taku ta maza Habibi kai da kake da sabon jini a gida.
"Mtss! Karki ɓatamin mood mana wannan yarinyar ita da babu bambanci su kaɗai ne a wurina don haka idan ba so kike ki ɓatamin rai ba kada ki sake sako min zancenta.
Ba ƙaramin kaɗuwa Rumaisa ta yi ba da ta ji irin waɗannan maganganu sun fito daga bakin AB sani da tayi masa ada idan ta dauko masa zance Aydah, baya taɓa furta kalma marar daɗi akanta. Sai kawai ta taɓe baki ba tare da ta matsantawa kanta da wani dogon tunani ba ta wuce gaba ya bi ta a baya har zuwa parlor da suka saba zama, tsarin yadda bikinsu zai kasance suka tsara. Bayan ya baro wurin Rumaisa ya shiga gari don kwata-kwata bayaso ganin fuskar Aydah gudun kada ya haɗu da ita yasa ya yi zamansa sai around ten na dare ya shigo gida sai dai abun da yake gudu shi ya tarar Aydah tana zaune a parlor ta yi tagumi idanuwanta sun yi luhu-luhu alamar tasha kuka ta yiwa kofar shigowa kurr da koɗaɗɗun idanunta, yana arba da ya ita ya ji takaici da tsanarta sun lulluɓe masa zuciya. Ya gitta ta ya wuce batareda da ya ko kalleta ba har ya fara haura mattakalar bene Aydah ta taso da gudu ta rungume shi ta baya sosai ta ƙanƙame shi tasa kuka "i'm sorry Yayanmu please forgive me ba zan sake ba, dan Allah ka daina fushi dani ko kayi min duka idan har za ka huce daga wannan fushi da kake dani kayi min duka ka zane ni.
Ta ƙarashe magana cikin gunji kuka gwanin ban tausayi Huwaila wacce ke laɓe a jikin ƙofar ɗakinta tana leƙo abun da ke faruwa babu yanda bata yi da Aydah ba akan ta je ta kwanta amman taƙi ta ce sai yayanta ya dawo ta bashi haƙuri, nan da nan idanun Huwaila suka cicciko da hawayen tausayin Aydah. Yarinyar da ke tsoron duka yau ita ce ke insisting a dake ta lallai hali da take ciki ya yi tsanani domin abu ne da bata saɓa dashi ba. A mugun fusace AB ya juyo ya fincike hannayenta daga riƙo da tai masa ya ware kyawawan zara-zaran yatsunsa ya sauke su akan tattausan kumatunta "How dare you to touch me kin ji min iskanci ni sa'anki ne? Wannan shine gargadina dake na ƙarshe karki sake wa'yannan kazaman hannuwa naki su sake gigi tabani duk abun da nayi miki ke kika siya da kudinki stupid girl!
Ya ƙarasa magana tare da kyasta mata yatsun hannunsa alamar gargaɗi kana ya haura sama abinsa, yayin da Aydah ta bishi da kallo da sauri Huwaila ta zo ta kama ta kasa kuka tayi sai kurum ta lafe a jikin Huwaila tana wani jan numfashi, a kidime Huwaila ta ƙarasa da ita dakinta ta zaunar da ita gefen gado, babu abun da Aydah ke yi sai jan numfashi gani take yi duka abubuwa nan dake faruwa tsakaninta da Yayanta mafalki ne ko illusion ta kasa yarda a zahiri ne hakan ke faruwa.
"Ki yi haƙuri Auta bawa baya zama babu jarabawa duk wanda yasan Yayanmu zai iya bata da tabbacin akan irin ƙaunar da yake min kwatsam! A waye gari yana nuna miki tsana wannan wani abu ne da hankali da tunani ba zai dauka ba. Dole akwai abun da ke faruwa.
Aydah ta ɗago soyayyun idanunta ta kalli Huwaila dasu tana girgiza kanta irin na wanda ke jin zafi acan ƙasan zuciyarsa "Ban san nayi masa wani laifi ba aunty Huwaila kawai dai ya tsaneni batare da wata hujja ba ko kuma Mami ta yi nasara akansa ta cilasta masa tsanata idan ba haka ba aunty Huwaila me na yi masa da yake min haka?"
"Allah ne masani gaibu auta ni ba zan yanke hukunci akan abun da banada masani akansa, amman ki bashi lokaci har zuwa sanda zai huce na tabbata ba zai iya dogon fushi dake ba.
Deep breath Aydah ta ja tare da jan pillow ta kwanta"Ba komai aunty Huwaila Allah shine shaida ta ina son Yayanmu banaso daidai da kwarar zarar nagansa cikin damuwa amman haka zan yi haƙuri na nisanta kaina daga gare shi.
Kalamanta suka ƙara narkarda zuciyar Huwaila ta dinga sharar hawaye a fakaice yayin da Aydah kumatunta kawai take shafa wanda har yatsunsa sun kwanta, mata radau-radau har zuwa lokaci ta kasa kuka ashe ko kuka rahama ne ashe akwai abun da zai iya faruwa da ita da zai hana mata kuka.
AB ya shiga ɗakinsa rai ɓace har ya cire kayan jikinsa zuciyarsa bata daina tafarfasa ba,tsabar ɓacin rai a naked ya shiga banɗaki yana wanka kwanyarsa ta dinga yimasa backwards ɗin abun da ya faru a tsorace ya ɗago hannunsa yana kallon palm ɗinsa wai gaske da wannan tafin hannu ya mari Aydah, shin wai me ya hau kansa ne da yake ji mahaukaciyar tsanar Babynsa me tayi masa haka da zafi ne?"Ko kaɗan ya kasa tunano laifi guda kwakkwara da tai masa da ta cancanci ya dinga treating ɗinta like this.
"Oh! God, fix my problems, I don't want to continue to mistreat this girl ni ba mugu bane and I don't want to be a merciless villain.
AB ya yi magana a bayyane can kasan zuciyarsa yake ji zafin abun da ya aikatawa Aydah ya kashe shower ya dauki towel ya ɗaura ya fito, har ya shirya cikin kayan baccinsa zuciyarsa bata masa daɗi he's feeling guilty about what he did to her, sai dai baya ji zai iya tunkarar inda take.
Washegari Aydah tana tashe ta shirya cikin school uniform ta goya backpack ɗinta ta sauko kasa a kitchen ta tarar da Huwaila cikin sanyi muryarta ta gaishe da Huwaila anan cikin kitchen ta yi breakfast, bata nemi AB ba ta wuce school during breakfast period, PC ta aiko nemanta ta je office ta same ta anan take faɗa mata yayanta ya kirata ya ce daga yanzu za ta dinga bin school bus Aydah was not happy a tunaninta yayanta ya faɗa ne kawai ba zai barta da gaske ta dinga bin bus ba, kamin ta kai class ɗinsu ta shara hawaye yafi a kirga ƙawarta shiru-shiru ƙawayeta suna jiranta ta dawo su yi breakfast amman bata dawo ba. Koda suka shigo class suka ganta ta kifa kanta a jikin desk ɗinta tana shasshekar kuka a kidime suka yo kanta "what happened, why are you crying, what did the PC say, you did something wrong?"
Dukkan waɗannan tambayoyi ƙawayenta biyu ke mata, kuma ba wanda ta amsa kurum ta cigaba da kukanta.
"Abeg Aydah tell us mana remember we're good a friends you can't sharing your problem with us ko ba haka bane Meera??"
"Kwarai kuwa Zaliha mu ƙawaye ne tun daga nursery school muke tare ba mu taɓa rabuwa ba matsalarki Aydah na mu ne Please ki faɗamin me ke faruwa tun safe da kika zo fuskarki ya nuna kina cikin damuwa.
Batareda Aydah ta yi magana ba ta fice da sauri suka bi bayanta suna kiranta sunanta can bayan ajujuwa ta nufa gun da babu hayaniya ta zauna, akan wasu chairs da aka yi su da siminti Zaliha da Ameera suka saka ta a tsakiya, sai rarrashinta suke yi Zaliha da yake tana da zuciya nan take ta fara hasala "me damuwarki ne Aydah Bashir huh? Mun tambaye ki matsalarki but you refuse to tell us, sai wani banzan kuka da kike mana kuka zai yi miki magani damuwarki ne?"
"Ki yi mata a hankali Zaliha ba ki san actual abun da yake damu ta ba.
"Duk abun da yake damunta mu ma yana damu mu she's our friend we have good time together, akan me ba za ta buɗe baki ta faɗa mana damuwarta ba