Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   55 / 80

162K to 165K   out of 237.2K words

haka daga gareta ba. Ransa farin tass! Ya kammala wankansa har zuwa lokaci yana ji zazzaɓi a jikinsa ga ciwon kai da jiri adaddafe ya yi sallah koda ya gama sallah kamar kansa zai rabe gida biyu, dakyar ya tashi ya hau gado ya shige cikin duvet yana rawar sanyi.
Sa'ili da AB ya kwakwasa wa Huwaila ƙofa tana zaune akan praymat tana lazimi, a tunaninta ko Aydah ce ta taso da sauri ta zare sakata sai kurum idanunta suka faɗa kansa,da farin jallabiya jikinsa da yasaka a bai-bai ta fara bi da kallo ga wani ɗan uban squeezing da tayi shi kansa AB ɗin a birkice yake sai kace wanda ya yi dambe da kura, ga baki ɗaya ya dawo wani kala na daban. Maganar da ya yi yasa Huwaila ta dawo natsuwarta ta gaishesa bai amsa ba sai ya ce ta je Aydah bata da lafiya, da yake Huwaila ba yarinya bace tuni ta fahimci abun da ya faru Ab yana juyawa ta washe baki ko hijab ɗin jikinta bata cire ba ta ruga ɗakin Aydah, tana tura ƙofa Aydah da ke bin bango za ta shiga bathroom ta juya a rikice sai tana gani Huwaila ce sai kawai tasaki kukan shagwaɓa, cikin sauri Huwaila ta cire hijab ɗin jikinta ta kama Aydah suka ƙarasa bathroom ruwa masu zafi ta sirka a bathtub ta zuba dentol kaɗan ta umarce Aydah da ta shiga tai ka ji ihun da Aydaah ta kurma sai da Huwaila ta gwada mata ƙarfi ta danne ta cikin ruwa. Sosai Huwaila ta gasa Aydah ita kanta Aydah ɗin ta ji daɗin ƙasanta sai dai zazzaɓi da take ji ya hana ta ji daɗin jikinta, a zaune tayi sallah Huwaila ta kawo mata tea mai zafi dakyar tasha rabin cup sakamakon appetite da bata dashi anan wurin da tayi sallah ta dunƙule jikin hijabin jikinta, Huwaila tana taɓa jikin Aydah ta ji wani irin mugun zafi daman ta zaci faruwar haka saboda shi ne farko yi ta gashi abun ya haɗu da ƙarancin shekaru. Panadol ta nemo ta bata tasha ta dauko duvet ta rufa mata, sannan ta cire bedsheet da ya yi kaca-kaca da jini ta jifa shi cikin washing machine ta wanke ta nufi backyard inda igiyar shanya take ta shanya shi ta dawo gun Aydah sai da tayi bacci sa'annan Huwaila ta fice kitchen ta shiga ta soma haɗa breakfast.
Gimbiya Rumaisa yau baccinta tasha mai rai da lafiya ba ita ta tashi ba sai misalin ƙarfe 11:07am ta yi miƙa tare da doguwar hamma kana ta ture duvet ɗin jikinta ta zuro ƙafafuwanta akan tiles ta sauka daga kan gado ta wuce bathroom lokacin da ta cire rigar jikinta mamaki ne ya rufe ta gani yadda rigar tayi staining da jini bata taɓa period tayi rushing irin wannan ba duk tsoro da fargaba ya gama cikata cike da rashin natsuwa tayi wanka ta fito, tana kammala shiryawa ta daga waya ta kira aunty Raliya ta zayyana mata halin da take ciki, Raliya ta ce ta kwantar da hankalinta jinin al'ada yanayin haka nan ta jira idan har ta cika wa'adin kwanaki da take yi bai dauke ba to dole ta tafi asibiti taga likita. Wannan bayanin na Aunty Raliya ya kwantar wa da Rumaisa da hankali har ta sami kwarin gwiwa zuwa ɗakin Ab, a kwance ta iske shi kunduddune cikin duvet mamaki ne ya kamata sai kuma ta tuna da halin da jiya ta jefa shi nan da nan tausayinsa ya rufe ta, ta hayo gadon tana kiransa "Habibi!Habibi lafiyar ka kuwa kake bacci har yanzu ba ka tashi ba?"
A wahale Ab ya buɗe idanunsa kaɗan ya kalleta yadda Rumaisa taga ƙwayar idonsa ta koma jaa ta kara tsorata ta shiga tattaɓa jikinsa "Na shiga uku Habibi bakada lafiya jikinka ya yi bala'in zafi.
AB ya ja numfashi tare da saukewa zazzafar iska ta fita daga ƙofufin hancinsa ya maida idanunsa ya rufe ya ɗora hannunsa a goshinsa saboda sarawar da kansa ke masa, Rumaisa ta sake cewa "Habibi za ka iya tashi na kai ka asibiti?"
Batareda da AB ya buɗe idanunsa ba ya kaɗa mata ɗan yatsansa alamar ba zai iya ba. Gani yadda ya yi yasa Rumaisa ta bi ta ruɗe a rikice ta sauko ƙasa jin motsin Huwaila a kitchen yasa ta nufar can cikin rawar murya ta ce da Huwaila "Ke Huwaila ajiye aiki nan ki je bakin gate ki kira min maigadi ya zo ya taimaka min mu saka Habibi a mota na kai shi asibiti bashida lafiya. Da sauri Huwaila ta aje wuƙa hannunta ta fi ce bata daɗe da fita ba sai gata ta dawo tare da maigadi, tunawa da tayi da halin da ta baro Aydah a ciki sai ta nufi ɗakinta domin ta ƙara dubata duk da dazu kamin ta baro ɗakin tayi bacci tana tura ƙofa tayi turus sakamakon gani Aydah ta yi yarshe a kasan tiles tana amai har ta galabaita kamar ma bata numfashi a ruɗe Huwaila tayi kanta tana kiran sunanta da taga tabbas bata motsi ta fice da gudu daidai sanda maigadi ya fito tallaɓe da gefen kafadar AB a jikinsa yana dagawa dakyar don har yanzu jiri yake ji Rumaisa na biye dasu cikin tashin hankali Huwaila ta ce "Aunty Rumaisa zo ki gani kamar Aydah bata numfashi.
Duk Ab yana cikin hali jin jiki hakan bai hana shi zare jikinsa daga jikin maigadi, da nufi ya je yaga halin da Aydah take ciki, yana ɗaga ƙafarsa sau ɗaya jiri ya watsar dashi "Subhanalillah! Yallaɓai ba za ka iya ba ka bari madam su daukata mu tafi asibiti duka.
Maigadi ya faɗa tare da ɗaga Ab da sauri Rumaisa ta bi bayan Huwaila suka shiga ɗakin Aydah tana nan kwance magashiyam yadda Huwaila ta ganta, Rumaisa ta kara hannunta a ƙofufin hancin Aydah ta ji da gaske bata numfashi, a rikice ta ce Huwaila ta kamata su kai ta mota yadda AB yaga sun fito da Aydah kamar gawa hankalinsa yai bala'in tashi kaitsaye asibitin da suke zuwa Rumaisa ta wuce dasu sai lokacin Huwaila ta yi tunanin ta kira Siyama ta faɗa mata hali da Abba da Aydah suke ciki, ta ciro wayarta da ta sakade a zaninta ta kira Siyama.


#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.








Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[1/19, 2:50 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye


075.


Koda kiran Huwaila ya shigo wayar Siyama gaba ɗaya ahalin gidan suna kan dinning table suna taking breakfast, yau har da Daddy yana gida saboda haka suke yi breakfast ɗin a tare. Siyama tana gani sunan Huwaila sai da gabanta ya faɗi cikin sauri tayi picking muryar Huwaila ta karaɗe mata kunne cikin tashin hankali take magana "Siyama gamu a asibiti Abba da Aydah duka basuda lafiya, ita Aydah ma koda muka kawo ta asibiti bata motsi.
"Innalillahi wa'inna illahim raji'un! Meyasa me su ne alokaci ɗaya za su kamu da rashin lafiya kodai food poisoning ne?"
Shiru Huwaila tayi dan ita kam tana jin tsoro a ji mutuwar sarki a bakinta yoo ta isa ma ta faɗi abun da ya faru wannan sirrin Abba da Aydah ne, sai dai kuma in likita ne ya fadi musanbabbin ciwon nasu.
"Hello! Huwaila ina magana kin yi shiru ki faɗamin gaskiyar abun da ya same su?"
"Da dai hakuri kika yi Siyama ki zo asibitin da kanki dan tun sanda aka shiga dasu wani ɗaki har yanzu ba wanda ya ce damu komai.
"Shi kenan ga mu nan zuwa.
Siyama ta faɗa tare da katse kiran ta kalli su Daddy da suka yi tsuru-tsuru sunan kallonta cikin rawar murya ta kwashe abun da Huwaila ta faɗa mata ta gayamusu, Daddy ya riga su fita saboda su sun tafi neman veil shi kuma daga nan kan dinning waje ya nufa direbansa yana ganinsa hankalinsa tashe ya jawo mota, koda su Mami suka fito tuni Daddy ya daɗe da barin gida Siyama ke driving Sadiya tana zaune a front seat yayin da Mami ke zaune a gidan baya.
Koda suka iso asibiti kowanne su hankalinsa ya yi bala'in tashi Daddy sai kai da kawo yake yi daga Mami har su Sadiya sun yi zugu-zugun Sadiya sai addu'a take yi a zuciyarta Allah ya tashi kafaɗar Abba ita kuma Aydah Allah yasa ta mutu. Sun fi one hour a tsaye kafin likitocin da suka duba su mace ɗaya da namiji biyu suka fito sai kuma nurses biyu da suka turo Aydah akan kujera daukar marasa lafiya suka kai ta wani ɗaki daban shi ma Ab aka kai shi nasa daga nan Daddy ya bi bayan likitocin domin jin Musababbin ciwon yaransa, Mami tana gani Daddy ya bisu ita ma ta bi bayansa a ofishin babban likitar suka shiga dukka, bayan Daddy ya zauna likita ya zare eyeglasses ɗin idonsa ya dubi Daddy da Mami dake tsaye a bayan Daddy ya furzar da numfashi kafin ya ce "A bincike da muka yi akan Abba ya nuna ya yi amfani da wani men power da yake mugun hatsari ga lafiyar namiji, kuma wani abun takaici yana amfani dashi ba a bisa ka'ida ba yana over dosage ɗinsa wanda hakan ne ya haifar masa da matsanancin zazzaɓi.
"To kuma ita Aydah me ya same ta?"
Mami tayi tambaya gabanta na mugun bugawa.
Likitan ya kalli mace likita ɗin wacce ita ce ta duba Aydah cikin kamilalliyar muryarta ta soma magana "ita Aydah ɗin case ɗinta ba wani babba bane hakan yana faru akan wasu mata har ma da maza idan ya kasance shi ne first sexy ɗinsu za su kamu da zazzaɓi mai zafi waɗansu har ma sai sun kwanta jinya kamar dai yarda ya faru da ita Aydah ɗin. In shaa Allah da zarar ta farka za ta wartsake sai dai ta dinga zama a cikin ruwan dumi saboda ya ɗan farka ta kaɗan an mata ɗimki idan tana shiga ruwan ɗumi hakan zai sa wurin ya yi saurin healing
Likita tana dasa aya Mami ta ɗauki dogon sallati taɓa tafa hannuwa "Yanzu dan Abba yana tsinannen wannan 'yar ƙaramar alhakki ce zai sha wa men power nufin sa ya kashe ta ko me? To wallahi ba zan lamunta ba Alhaji dole ka ɗauki mataki ai wannan child abuse ne.
A fusace Daddy ya ɗago ya gallawa Mami harara rai ɓace yake faɗin "Child abuse a ina?" Na ga dai Aydah matarsa ce addini ya halatta masa ita kuma ban aurar da ita ba sai da ta kai muzalin balaga dan kina mahaukaciya za ki buɗe baki kina faɗar maganar banza.
"To idan ma ba child abuse bane sexual violence ne kuma wallahi sai na shigar da ƙara an kwatowa 'yata hakkinta kana ji fa likita ya ce men power ya sha kuma over dosage, har fa farka ta ya yi Alhaji ka kuwa san irin azabar da ɗinki yake dashi kasan irin azabar raɗaɗin da ake ji yayin yinsa?"
Mami ta ƙarashe magana tare da ɗora hannu aka ta rushewa da kuka, duk sai kuma jikin Daddy ya yi bala'in sanyi ya kasa mayar wa da Mami magana hakan da Mami ta gani ya bata karfin gwiwa cigaba da fadar maganganu ta dubi likita da hawaye akan fuskarta ta ce "likita ka faɗi tsakanin ka da Allah ka cire son zuciya Abba yana da rashin kuzari da zai sa sai ya sha maganin ƙarin ƙarfi a yayin mu'amala da iyalinsa?"
Likita ya girgiza kansa cikin sanyi murya ya ce "zance na gaskiya Abba yana da cikakkiyar lafiya wanda ko mace mace huɗu zai iya sarrafawa, sannan dadin daɗawa zai iya taɓa lafiyar jikinsa.
Shi kansa likitan Abba ya yi bala'in basa mamaki ace duk iliminsa da wayewarsa ya rasa abun da zai sha saboda kuzari sai wannan guba.
Ai kuwa Mami ta ƙara samun kwarin gwiwa zazzaga masifa sai muggan maganganu take faɗa akan Abba, daga ƙarshe ma sai ta baro office ɗin a fusace har ta iso ɗakin da Aydah take tana sharar hawaye ta nufi gadon da Aydah take kwance da cannula manne a hannunta ana ƙara mata ruwa sai bacci take abin ta, Sadiya da Siyama suka yo kan Mami har suna haɗa baki wurin tambayarta dalilin kukanta Sadiya ta ƙagu ta ji wane mummunan abu ne ya sami Aydah da Mami take kallonta tana kuka, sai da Mami ta share hawaye kafin ta basu labari abun da ya faru wani irin mugun shock Sadiya ta ji ya kamata, zuciyata tayi baƙi ƙirim! Ji take kamar ta shaƙewa Aydah wuya har taƙarasa ta, Aydah ta gama da ita da kwanta da muradin zuciyarta shi kenan Abba Bashir yasan Aydah 'ya mace ta dandani zumar Abba Bashir , lallai ta cika cikakkiyar marar nasara a rayuwa. Shin ina asiri da suka yiwa Abba da zai tsani Aydah ana nufi bai kama sa bane ko kuma tsanarta ce kawai amman zai iya haɗa shimfiɗa da ita?" Tunda taga AB ya yi tarayya da Aydah alhali ga amaryarsa Rumaisa wacce duka kwananta biyu a gidansa hakan na nuni da cewa asiri da ta yiwa Rumaisa ya kamata, da tasani dukkansu za ta saka a sako musu zubar jini. (Kashh! Sadiya dokin inda baya sukuwa kin ri ga da kin makaro)
Sadiya bata ankara ba ta ji hawayen baƙin ciki na bin kumatunta.
Siyama ta yi ajiyar zuciya ta ce "Mami dan Allah ki daina fadar za ki shigar da Yayanmu ƙara da Aydah da Yayanmu duka yayanki ne.
"Ke dallah rufe min bakinki ta ina ya zama ɗana ke ko kishi 'yar uwarki bakya yi meyasa ita Rumaisa bai yi using men power akanta ba sai akan Aydah?"
"Uhm! Koma mene ne haƙuri za ki yi Mami.
"To ba zan haƙura ba na ce ba zan haƙura ba Siyama.
Mami ta faɗa tana zarewa Siyama idanu dole Siyama taja bakinta tayi gun!
Daddy yana baro office ɗin likita ya wuce ɗakin da AB yake Rumaisa ce kaɗai a ɗakin shi ma Ab da drip ɗinsa a hannu yana bacci Daddy ya tambaye Rumaisa jikinsa ta ce ya ji sauki don har zazzabin jikinsa ya sauka, Daddy ya daɗe cikin ɗakin kafin ya nufo na Aydah Mami tana ganinsa ta tada masifa sai faɗar take kotu ce za ta rabata da Abba. A fusace Daddy ya kalleta ya ce idan ya sake jin kalmar sexual violence da kotu a bakinta sai ya yi mummunan saɓa mata yadda taga idanun Daddy sun yi jajir ta tabbatar da cewa da gaske yake yi dole ta ja bakinta ta tsuke amma acikin zuciyarta ta kudurta ko ana ha maza ha mata sai ta raba auren Abba da Aydah don taga cuta acikinsa ƙarara.
*VICTORIA ISLAND LAGOS*
(The George hotel)


Aliyu na Uku yana kwance akan katafaren gadon hotel ɗin the george hotel ɗin da ya kamawa Maysun, yau kwana su uku da sauka a Lagos bai je gidansa ba dukka wayoyinsa rufe su ya yi sai amarci suke ci shi da Maysun ɗinsa wacce yake jin ta tamkar yau ne ya fara tarayya da ita, ya rasa gane irin matsanancin so sa yake mata cikin kwanaki uku nan da suka yi a tare ji wata irin natsuwa da kwanciyar hankali wanda ya manta rabon da ya ji irinsu. Duk iya kyautatawa da Safiya ke masa baya samun gamsuwar da ya samu a kwanaki uku ɗinan a tare da Maysun tabbas sai yanzu ya ƙara tabbatar da cewa alaƙa aure bata yiyuwa sai da soyayya, bai taɓa jin son Safiya a zuciyarsa ba amman yana gani girmanta da ƙimarta yana daraja ta, sai dai zuciyarsa tana ga Maysun.
Yayi nisa a tunanin rayuwarsa da Maysun a garin London karar buɗe ƙofar bathroom da Maysun ta yi ya dawo masa da natsuwarsa ya kalleta cike da shaukin so tana sanye da white bathrobe ta yane kanta da farin ƙaramin towel, wani bala'in kyau yaga tayi masa ga zazzafar soyayyarta da ke ratsa sassan jikinsa, duk da yana cikin farin ciki kasancewa tare da ita amman hakan bai hana masa hasaso irin kalubalen da zai fuskanta akanta, har kawo yau ɗinan kaf zuri'arsa ba wanda yasan ya taɓa aure har da ɗa sai Anaal ita kaɗai ce tasan da wannan ɓoyayyen sirri. Yana cike da alhini ta wacce fuska zai fuskanci masauratar kudu ya gabatar da Maysun a matsayin matarsa da farko wannan Kurman allo ba kowa ne zai fahimce sa cikin sauki ba. Yasani idan ya bayyana Maysun a yanzu a matsayin matarsa zai iya rasa sarautarsa wacce a yanzu yake da burin akanta saboda ya farantawa mai babban ɗaki a dalilin fahimtar da ya yi batada da wani buri da ya wuce taga ya hau karagar mulkin sabon birnin kudu. Maysun tana zuwa ta zauna daidai fuskarsa cikin zazzaƙar muryarta da ya fi so ta ce "Abu Azhar me ke damunka ne kasan duk duniya ba abin da yake saurin ɗaga min hankali irin naganka cikin damuwa saboda haka kada ka ɓoye min komai ka tuna mu yi alkawari wa junan mu za mu dinga sharing damuwarmu?"
A kasalance ya tashi zaune sai da ya jawo ta cikin jikinsa ta kwantar da kanta a faffadan ƙirjinsa jiƙaƙƙiyar sumarta ta baje masa a ƙirji, a hankali yake shafar sumarta ta, kamin cikin raunin murya ya ce "Oum Azhar ina cikin damuwa zuciyata tana cike da son bayyana ki ga dangina sai dai ina fargaba irin karɓar da za su yi miki. Na kuma tabbata bayyana ki ɗin zai iya jawo min matsaloli da dama daga cikinsu har da rasa sarauta ta, wacce mahaifiyarta ta ƙwallafa ranta akai. Ga kuma ɗan mu da ya ɓata wanda nake so na fara neman sa, sai dai na rasa ta ina zan fara neman nasa domin bana da cikakken bayani akan garin da Bashir da matarsa Maryam suke da zama anan Nigeria .

55 / 80