Author : EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category : KDP NOVELS
kokarin riƙe hannun Siyama ɗin tana cigaba da kukanta wanda sautinsa ya gama cika ɗakin. Hannunsa ya harɗe akan ƙirjinsa yana kallon yadda baby face ɗinta ta zama saboda kukan da tasha
har wani kumburi saman idanunta yayi. Dakyar Siyama ta haɗe abun da take ji ta gaisheda yayanta amsawa yayi yana kallonta yana faɗin."wa zai maida ki gida?
"Daman da mota nazo.
Ta faɗa fuska babu walwala,ya lura da haka murmushi ya ɗan saki yasan tana taya yar uwarta kishine kawai ba wani abu ba. Ya duba agogon rolex ɗin dake cikin tsintsiyar hannunsa,yaga har kusan karfe goma da rabi na dare, dare yayi sosai ya dubeta a natse ya ce "Ki kwana anan ki bari sai gobe.
Da sauri ta girgiza kai tana faɗin."mami za tayi faɗa.
Dan shiru yayi da gaskiyarta Mami za tayi faɗa,wani numfashi ya sauke yana faɗin."kibar motarki zan saka Abdulkarim ya mayar dake,daga kai tayi kurum tana ficewa daga room ɗin dan ta lura hankalinsa ga baki ɗaya yana kan Aydah daman tana fita Aydah tabi bayanta caraf! Taji ya riƙe mata hannu duk yadda taso ta kwace hannunta ta kasa gashi ko kaɗan bata son haɗa ido dashi jawota yayi ga baki ɗaya cikin jikinsa, tamkar jira take ta sakar masa kuka zagaye hannunta yayi da bayansa cikin taushin murya ya kira sunanta ga baki ɗaya kukanta neman yake ya hargitsa masa ƙwaƙwalwa, kukanta ta cigaba dayi yana rike da ita."Baby so kike nima na tayaki kukan ne?
Ya faɗa da ƙaramar murya har sai da Aydah ta dago kumburrun idanunta ta saukesa cikin nasa,wannan karon abun da yake gani cikin ƙwayar idanunta yasa shi saurin dauke idanunsa cikin nata. Zuciyarsa wani irin bugawa take da kalar bugun da bai taɓa jin irinsa ba, addu'a yake Allah yasa abun da yake gani cikin ƙwayar idanun kanwar tasa ba gaskiya bane. Allah yasa matsayinsa na yayanta bai canja ba a zuciyarta dama duniyarta ga baki ɗaya "Bana son na kara jin wannan kukan kina jina?" Ya faɗa yana tallabe da haɓarta
daga masa kai kurum tayi tana jin kusancinsu da ƙamshin turarensa yana haifar mata da wata irin kasala wacce bata taɓa tsintar kanta acikinta ba. "Ina son naje wurin Mami ina son na kwana tare da Mami.
Ta karasa maganar cikin rawar murya, girgiza mata kai ya yi cikin ido yake kallonta kamin ya haɗe goshinsa da nata ,cikin wata murya yake faɗin."Ni kuma kiyi yaya dani?" Tamkar a mafarki ya ji ta ce "Baga aunty Rumaisa nan ba burin ranka matar so ai atare za ku kwana.
Ta faɗa da murya mai rauni mai haɗe da zallar kishi tana jin hawaye na zuba cikin fuskarta. With shock yake kallonta bai taɓa tunanin tana da wayon fahimtar abubuwa kamar waya'anan ba,tsoro gami da mamaki ne shimfiɗe akan fuskarsa taya ma Aydah tasan a ɗakin Rumaisa zai kwana a yau?"shi da yake mata kallon batada wayau tamkar bata san wasu abubuwa ba ashe shine marar wayau, hannu yasa yana goge mata hawayen idonta da suka kasa tsayawa har lokaci suna zuba, ya ɗan haɗe rai yana faɗin."Bana son na sake ganin kina kuka kuma bana son na kara jin kince za ki bi Siyama,na maki alkawarin gobe da kaina zan dauko miki ita.
Batace komai ba sai kallonsa kurum take yayi kyau sosai acikin farar shaddar dake jikinsa da aka yiwa hadi da babbar riga,sai lokacin ta lura da hodar da ta gama goge masa akan farar shaddarsa bata san lokacin da murmushi ya kubuce mata ba tana juya masa baya,inda tabi da kallo tana murmushi ya kalla da sauri,ganin yayi duk hodar dake kan fuskarta ta dawo a farar shaddarsa ware ido yayi yana kallonta hankali tashe ya kira sunanta "Baby!
Juyowa tayi ta saki dariya ganin yadda firgici ya bayyana sosai akan fuskarsa "Kinga yadda kika batamin farar shadda haka kikeso naje wurin amaryarta.?"
Jin kalmomin da yayi amfani dasu yasa ta haɗe rai lokaci ɗaya tamkar ba ita bace ke dariya yanzu nan ba,da sauri ya riƙo hannunta "Da wasa nake mu je mu raka su Siyama,dare yanayi. Ya faɗa yana ƙara tamƙe hannunta cikin nasa suka koma parlor kowa bin su yake da kallo da alamar AB ya manta amarya aka kawo masa wata ƙawar Rumaisa ce ta sauko ƙasa da mamaki take kallon AB da Aydah da ya rike hannunta ficewa tayi daga parlor dama fitowa tayi amsa waya,ta matsu ta gama wayar taje ta fesawa Rumaisa labari tun ɗazu ango ya shigo shine dan kuturun wulaƙanci zai wani shanyasu ya tsaya yana biyewa wannan kwailar yarinya dako nonon kirki bata dashi a kirjinta lallai akwai aiki agaban Rumaisa.
Har bakin motar Abdulkarim Aydah da AB suka raka Siyama sauran friends ɗinsa guda biyu daman a mota ɗaya suka zo suka ce su sun wuce sai ya sallami friends ɗin amarya. Kallon Siyama kawai Aydah take ga baki ɗaya jikinta yayi sanyi wani irin tsoro taji yana cika mata zuciya suna tsaye maigadi ya buɗe masu gate suna ficewa Aydah ta fisge hannunta dake cikin na AB ta fashe da kuka da sauri AB ya fisgota cikin jikinsa yayi sauri saka ɗayan hannunsa ya rufe mata baki,murya can ciki ya furta"Meye haka?"sai kin sa mutane sun taru su dauka wani mummunan abu nayi maki, bana son wannan sakarci mu je ki canja kaya ki kwanta.
Ya faɗa cike da bada umarni yana ɗan haɗe rai da haka yaja hannunta suka koma ciki komai da ya faru akan idanun Kamila ƙawar Rumaisa AB yana rike da hannun Aydah har cikin ɗakin baccinta. Kamila na tsaye tana bai wa kawayensu labarin yadda AB yake ta nan-nan da Aydah tamkar zai mayar da ita ciki,Rumaisa bata dai ce komai ba Amman kana ganin yanayin fuskarta kasan acike take kowane ya miƙe tsaye yana faɗin."Bari mu wuce sai gobe,muhibba tace "Sai kin tashi tsaye ƙawata dan wallahi irin waya'anann cwt 16 ɗin bala'i ne idan suka samu zama lashe zuciyar namiji suke saboda iskanci cikakkiyyar halitta ce kawai basa da Amman wallahi sun iya sace zuciyar namiji.
"Ku tafi dan Allah karku ƙara min wani ciwo.
Rumaisa ta faɗa cikin rawar murya basu jima da fita ba AB ya shigo ɗakin nata kanta na a kasa da mayafin data mayar akanta da sallama ya shigo cikin ɗakin,ya aje bakar ledar da ya shigo da ita akan side table ɗin dake gefen ɗakin,ya cire takalmin ƙafarsa ya karaso cikin ɗakin da ƙamshi ke tashi acikinsa da kuma ƙamshin turaren wuta zama yayi a gefen Rumaisa ya jawota ajikinsa zuciyarsa na tsananin bugawa yana addu'a yana kabbara kamin ya sassauta rikon da yayi mata a hankali ya dage mayafin dake saman kanta yana ganin yadda idanunta suka yi canja saboda kukan da tasha da za'a kawota gidansa.
"Habibaty!
Ya faɗa yana kamo hannunta a hankali ya sumbaci hannun nata sai da tsikar jikinta ya tashi yarrrr! Irin sumbar da yayi mata,haka yasa ta runtse ido da sauri kafin kuma ta janye hannunta tana barin fili a tsakaninsu,da wani irin yanayi da kuma kishi mai tsanani cikin muryarta ta ce ."Na dauka acan za ka kwana a wurin babyn naka.
Ta karasa tana zube idanunta cikin farar shaddar jikinsa daidai inda Aydah ta kwanta ta saka masa hoda runtse idonta tayi tana jin ƙirjinta na wani irin zafi yana sama da kasa. Bai ce komai ba ya miƙe tsaye yana faɗin."Kiyi wanka bara naje nayi wanka na dawo,da ido kawai ta bisa cike da takaici bayan fitarsa tayi kwafa aranta tana faɗin."duk wannnan girman kan nasa sauke mata shi zai yi a daren yau ta tuna maganin da Aunty Raliya ta bata tace ta saka masa cikin abun shan sa kaɗan,na.maza ne kamar ruwa yake ko an saka ba'a ganewa da sauri ta buɗe handbag ɗinta ta dauko karamar kwalbar ledar da ya shigo da ita ta buɗe kwallin fresh milk ne,batareda wani tunani ba ta buɗe ta zuba kusan rabi ta mayar ta rufe ta jujjuya kwalin ya haɗe wuri ɗaya ta mayar da kwalin da sauri cikin ledar,
kayan jikinta ta shiga ragewa daman tamkar kan ƙaya haka take jin kanta saboda nauyin da suka yi mata,kai tsaye wanka ta shiga duk turarrukanta na wanka da mai mata gyaran jiki ta haɗa mata tazo da abunta Aunty Raliya ta jera mata su cikin toilet ,wanka tayi ta fito daure da towel a ƙirjinta sai yanzu take jin gajiyar da ta tara tana saukar mata.
Ga baki ɗaya gabobbin jikinta wani irin ciwo suke mata. A bangaren AB kuwa shima wanka yayi ya saka Black jallabiyya ajikinsa marar nauyi mai gajeren hannu,ya saka (casual slippers a ƙafarsa ya nufi ɗakin Aydah yana tura kofar ɗakin nata ya sameta bakin gado zaune tayi tagumi daga ita sai baby pink,towel a jikinta suna haɗa ido tayi saurin sauke idonta a ƙasa,karasowa yayi ya zauna gafda ita murya ƙasa-ƙasa yace "Baby ya baki saka kayan bacci ba?"
Shiru Aydah tayi babu amsa sai famar jan dogayen fingers ɗinta take yi
AB bai kara kulata ba ya tashi ya karasa gaban closet nata ya ciro mata riga da wando na bacci ya miƙa mata yace ta shiga toilet ta saka ta amsa tana kallonsa aranta take faɗin."idan Rumaisa ce ai ba za ka ce ta shiga toilet ta saka ba ni anan zan saka abuna ta faɗa aranta batareda wani tunani ba ta kwance towel ɗin jikinta a wani irin kidime AB ya kauda kansa ya shiga tari babu kakkautawa. Hakan ba ƙaramin bata dariya yayi ba ganin yadda yayanta ya rude dan kawai ta saki towel agabansa wandon kawai ta saka ta karasa gaban bedside drawer ta dauko masa water bottle ta tsaya agabansa ta miƙa masa daga kai yayi ya wani fisge bottle ɗin idonsa suka sauka akan matasan ƙirjinta "Aydah bakida hankali ne?" Ya yi magana yana buɗe marfin ruwan ya kafa kai ya shiga sha sai da ya sha fiye da rabi ya sauke yana kallonta zuwa lokacin ta saka rigar.
"Je ki dauko plate a kitchen ki zo kici kazarki kartayi sanyi.
Daman har huwaila sai da ya riƙowa ledarta da zai shigo kai tsaye kitchen ta nufa plate ta wanko da glass cup har biyu dan ta dauka tare zasu ci kazar tana ta jin dadi yayan nata ba zai wulaƙanta ta ba dan yaga Rumaisa dama tana haurowa sama ta wani kafe ɗakin Rumaisa da ido ta murguda baki tana wani irin juya ido,sai ta koyawa Rumaisa hankali a gidanan za ta ga yadda za ta kwana da yayanta ayau ɗinan. Da haka ta shige ɗakinta har lokacin AB na zaune yana jiranta ya karbi plate ɗin ya ciro kazar ya aza mata da kansa ya shiga bata kazar ganin baya ci yasa tace "Yayanmu kai bazaka ci bane?" g
Girgiza kai yayi yana faɗin."Tawa da ta Rumaisa tana a ɗakinta wannan naki ne.
Lokaci ɗaya yanayin Aydah ya canja zai kara kai wata a bakinta tace ta koshi ya tsiyaya mata fresh milk a glass cup ya nufi bakinta dashi dai-dai kuma lokacin aka turo kofar dakin da suke suran kaɗan AB ya saki glass cup ɗin hannunsa.
#JEEDDAH ALIYU
#ASMY B ALIYU
#KURMAN ALLO.
Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[1/16, 11:11 AM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels
070.
Shiru AB yayi yana bin Rumaisa da ido da mamaki shi bai kuma jaye cup ɗin ba a bakin Aydah. Dan murmushi AB ya kirkira yana faɗin "ki ƙaraso Habeebty,ki tayani rarrashin wannan rigimammiyar kanwar taki.
Cikin murmushi mai kama dana yan duniya Rumaisa ta ƙaraso cikin ɗakin ƙamshinta ga baki ɗaya ya gama cika ko'ina a ɗakin rigar bacci ce ajikinta mai kauri doguwa har ƙasa kalar sky blue sai hular net data aza akanta, wanda har ake iya hango gashinta.
Zama Rumaisa tayi cikin soofar dake girke acikin dakin ta wani harɗe hannayenta tana bin Aydah da kallo tana kula da yanayinta ,Aydah ta karbi cup ɗin dake hannun AB ta kafa kai sai da tasha rabi ta sauke,cike da karfin hali AB ke faɗin "baby baki gaisheda aunty Rumaisa ba,cikin rawar murya Aydah ta gaishe da Rumaisa ta miƙe tsaye ta nufi toilet batareda tasan me zata yi acikin toilet ɗin ba daga AB har Rumaisa bin ta suka yi da kallo,har kusan minti biyar da Rumaisa taga AB bayada alamar tashi su tafi su kwanta tasan da gangan Aydah ta shige toilet ta miƙe tsaye tana murza ido "Ni kam Habibi mu tafi mu kwanta bacci ne sosai a idona da kuma gajiya.
Ba haka AB yaso ba yabi bayan Rumaisa dan baya son bata ranta ko kaɗan,daman Aydah najin fitarsu ta haɗa kai ga bangon toilet din ta shiga rera kuka. Sallah ya jasu raka'a biyu,kamar yadda addini ya tsara ya dade dafe da kanta yana karanto mata addu'oin tsari ya tambayeta kaɗan daga cikin addininta babu laifi tana da sani akan addini,ganin yadda take jera hamma yasa shi jawo kazar da ya shigo masu da ita ya juye cikin plate,shiya rika ciyar da ita kazar ita ma tana basa a haka har suka cinye kaza ɗaya. Daman kowanne su da yunwa a tare dashi AB ya zuba musu fresh milk cikin glass cup ya nufi bakin Rumaisa da sauri ta dauke kai tana faɗin."cikina ya cika dayawa Habeebi kasha kawai bara na sha ruwa,shi kaɗai ya riƙa shan fresh milk ɗinsa kusan cup biyu yasha duk Rumaisa na kallonsa kasa-kasa kai tsaye toilet ta wuce ta kara yin brush
tana fitowa tabi jikinta da khumurah
Ta hau gado tayi kwanciyarta. Still AB yana zaune a wurin na kusan minti goma yana jin wani irin yanayi a tare dashi wanda bai taɓa jin kalarsa ba.
dakyar ya shiga toilet yayi brush ya fito yana kallon yanayinsa da ya canja cikin mintuna ƙalilan,cire jallabiyyar jikinsa yayi ya ninke ya ajeta a wurin da ya dace,ya rage daga shi sai boxer ajikinsa kai tsaye kan gadon ya nufa yana kashe fitillun dake da haske a ɗakin yana barin mai duhu,Rumaisa tana jin lokacin da ya kwanta sai ta kara runtse ido sosai zuciyarta na wani irin harbawa da karfi. Shiru AB yayi yana ɗora tafin hannunsa akan shafaffen cikinta ya runtse ido sosai
yanayin yana kara shiga jikinta sosai har na kusan mintuna goma Rumaisa bata ji AB ya fara tabata tanata mamaki tana karawa kodai ba maganin bane Aunty Raliya ta karbo mata yadda ta rika bata labarinsa ita ba haka ta gani ba. (Nasiha da tuni ga duk wata budurwa kafin aure dan Allah dan Annabi karki kuskura a matsayin ki na budurwa daren da za'a kaiki a gidan miji kiyi amfani da maganin maza ki zubawa namiji acikin abun sha,wannan babbar illah ne sosai ke baki san illar da hakan zai yi masa ba kema baki san illar da haka zai yi maki ba a matsayin ki na budurwa)Gaban Rumaisa yayi bala'in faɗuwa ganin AB zaune ya haɗe kansa da gwiwowinsa jikinsa banda shaking babu abun da yake tamkar wanda aka sakawa wayoyin wutar lantarki acikin jikinsa. Yanayinsa yayi bala'in ba ta tsoro da sauri ta dawo kusa garesa ta dagosa wannan karon abun da ta gani acikin idanunsa yayi bala'in shallake tunaninta rike fuskarsa tayi cikin fitilar da bata da haske take karewa fuskarsa kallo,samun kanta tayi da shigewa cikin jikinsa zuciyarta na tsananin bugawa. Kamar jira yake yayi wani irin sakata cikin jikinsa yana lalubarta a gigice tamkar wani mayunwacin zaki ,halin da Rumaisa ta shiga a hannun Abba Bashir halin a tausaya matane dan tamkar an cirewa Abba Bashir tausayi a wannan daren kansa kawai ya sani ciwon da yake tare dashi yake so kawai yabar jikinsa tun yana bin Rumaisa cikin sauki har yazo ya haukace mata tun tana dauriya har ta kasa duka da yakushe da kuka da majina duk yasha sa a wannan daren bai ma san tana yi ba dan jinsa yayi a wata duniya ta daban wacce bai taɓa jin kansa aciki ba duk wani girmansa sai da ya tabbatar ya juyewa Rumaisa shi duka. A wannan daren daga shi har Rumaisa sun wahala ko sallar asuba basu samu ba sai kusan 6 suka yi wanka suka yi sallar asuba,duk da haka AB yaga jarumtar Rumaisa da ta iya yin wanka tayi sallah batareda taimakonsa ba sai lokacin ta samu wani wahalallen bacci ya dauketa ko ina gabobbin jikinta ciwo yake. Kwamciya yayi agefenta yana jawota ga baki ɗaya cikin jikinsa sai da ta tsorata irin rikon da yayi mata murmushi yayi cikin muryar rada yake faɗin."Babu abun da zan yi miki bacci zamu yi. Thank you habibty kin bani farin cikin da babu wanda ya taɓa bani kalarsa Allah yayi miki albarka matata. Shigewa tayi cikin jikinsa tana sauke wata irin ajiyar zuciya tana godiya ga Allah da ya mallaka mata abun da takeso a rayuwarta daren jiya kawai ya tabbatar mata da Abba Bashir nata ne ita ɗaya yadda ya riƙa yimata ne jiya tasan babu abun da ya taɓa shiga tsakaninsa da Aydah wani irin daɗi da farin ciki ya lulluɓeta. Baccinsu suka koma cikin natsuwa sai wuraren ƙarfe goma na safe suka farka ko shi sai da hasken rana ya haske fuskokinsu,ya rigata shiga wanka koda ya fito ta gyara gadonta tsaf yana bin ta da ido sai sannu yake mata da kanta ta ƙaraso inda yake tasa hannu ta amshi karamin towel ɗin dake hannunsa ta shiga goge masa sumar kansa tsaf! Jallabiyarsa ya mayar ya faɗa mata zai ƙarasa bangarensa ya shirya wani iri taji kyau ace komai nasu na haɗe a wuri ɗaya tayi mai fari da ido tana faɗin "Ya kamata dai ace komai namu yana a haɗe wuri ɗaya,ina ganin haka zai fi. Dan jim AB yayi tamkar mai tunanin wani abu sai kuma ya girgiza kai yana faɗin."kin manta ku biyu ne kar a shiga hakkin baby Aydah kuma.
Juyawa kawai Rumaisa