Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   3 / 80

6K to 9K   out of 237.2K words

ta tura ƙofar ɗakin Daddy da Abdulkarim Safana suna zaune akan plastic chair gaban gadon da AB yake suna kallon hawa da saukar numfashinsa. Mami da Siyama ne kaɗai suka yi sallama banda Aydah wacce tana hango AB kwance cikinsa naɗe da bandage ta fara kuka.
"Ina kwana Alhaji ya jikin nasa?"
Mami ta faɗa sa'ili da ta iso kusa da Daddy.
"Al-hamdullilah!
Daddy ya faɗa muryarsa bata fita sosai.
"Ina kwana Mami?"
"Lafiya ƙalau Abdulkarim ya jikin abokin naka?"
"Jiki Al-hamdullilah sai dai har yanzu bai falka ba.
"Zai falka da izini Ubangiji.
Mami tayi magana da damuwa akan fuskarta.
Siyama ta matso ta gaida Daddy da Abdulkarim tare da tambayar jikin AB Aydah na can rakuɓe jikin ƙofa tana kuka, shesshakar kukanta ne ya jawo hankalinsu izuwa gareta, murmusawa Daddy ya yi tun faruwar al'amari sai yanzu fuskarsa ta saki har ya sami yi murmushi, da hannu ya fito Aydah tare da faɗin "Zo nan Mamana! Da gudu ta zo ta faɗa jikin Daddy ta saki kuka a hankali Daddy ya dinga bubbuga gadon bayanta "ya isa haka ki daina kuka Mamana ki yi masa addu'a kin ji??
Aydah ta gyaɗa kai gami da barin jikin Daddy "Oya share hawaye mana.
Abdulkarim ya faɗa yana kallon fuskar Aydah.
Tasa gefen hijab ɗinta ta goge fuskarta "Yau kam akwai aiki kuka sai mun gaji dashi mun nemo auduga mu toshe kunnayen mu.
Mami tayi magana tana kallon Aydah wacce ta nufi kusa da AB tai tsaye tana kallon fuskarsa ma'aɓociya kyau da kwarjini.
Sai misali ƙarfe 11:15am AB ya falka bakinsa ɗauke da sallati kusan dukkan su a tare suka tashi tare da nufo wurinsa kowanne yana kokari yi masa sannu, kafin Daddy ya kama hannunshi ya riƙe gam! Yana kallon fuskarsa "Sannu Abba ya ka ke ji jiki naka??"
"Al-hamdullilah Daddy!
"ma-sha-Allah! Bara a kira likita ya zo ya duba ka ya gani idan babu wata matsala Abdulkarim kira likita.
Abdulkarim ya amsawa Daddy tare da ficewa da sauri.
Jim kaɗan sai ga Abdulkarim ya dawo tare da likita da wata nurse dake biye dasu hannunta dauke da ɗan ƙaramin tray silver mai ɗauke da tarkace kwalaben allurai da syringe
A firgice Aydah ta ɗago tare da bin matashin likitan da kallo yana sanye da farar long sleeve shirt haɗe da baƙin wando ya ɗaura lab coat akai wuyansa na saƙale da Stethoscope, duk duniya babu abinda ke sauri haifar mata da tsoro irin allura ta tsani allura ko syringe bata so gani.
Sai da likita ya fara duba bugun numfashin AB kafin ya miƙa hannu ya ɗauki bottle ɗin allura ya fasa kwalbar tare da ɓare syringe ya zuƙo ruwan da sauri Aydah ta runtse idanuwanta jikinta ya ɗauki rawa, zufa ya tsatsafo mata akan goshinta da ƙananu gashi yake kwance lub-lub.
A hankali ta ɗan buɗe idonta guda daidai lokaci da likita ya ɗauki auduga wacce ya jiƙa ta daga ruwan spirit ya kama tsintsiyar hannun AB sake runtse idon nata tayi ta, hawaye masu zafin gaske suka fito daga kwarmin idanuwanta. Tambayoyi da ta ji likita yana ma AB yasata buɗe idanunta.
Bayan fitar likitan Daddy da Abdulkarim suka taimakawa AB ya tashe zaune mami ta saka masa pillow a bayansa. Abdulkarim ya taimaka masa ya yi brush da alwala sai lokaci ya sami damar yi sallar asuba, sai da Daddy yaga Abba ya ɗan sha tea kana ya nufi gida ya yi wanka bayan fitar Daddy shima Abdulkarim ya yi musu sallama, aka bar Mami da girls ɗinta Aydah tana manne da AB ko nan da can bata kusa ba kuma lokaci zuwa lokaci sai ta tambaye shi ya aka yi ya ji ciwo me ya same shi ina Yaya Sadiya ko batasan cewa bashi da lafiya ba. Tambayoyi dai ga su nan birjik take masa sai dai ko guda daga ciki ya kasa amsa mata daga ƙarshe ma da yaga tana so ta matsa mishi sai kawai ya lumsashe idanuwansa tamkar ya yi bacci dole ta kyaleshi.
Kaitsaye Sadiya ta wuce ɗakinta ta faɗa kan gado tare da yi rub da ciki cigaba rera kukanta nadama babu kalar wacce bata yi ba.
A hankali Daddy yake driving tun jiya zuciyarsa take cike da mamaki ta ya aka yi ɓoyayyen sirrinsa ya fito fili, kuma bai tashi bayyana ba sai a ranar daurin auren 'yayansa. Sirri ne da aka yi haƙa rami karkashin ƙasa aka binne daga shi sai marigayi matarsa Maryam suka san dashi wacce duk duniya ta ɗauki cewa ita ce ta haifi Abba hatta da iyayenta basu san cewa Abba ba jikansu bane. Ta ya aka yi wannan sirri ya bayyana? A ina Alhaji Bello Madawaki ya sami wannan ɓoyayyen sirri? Ina son Abba tamkar raina ba zan taɓa barin fitar wannan sirri ya shafi gobensa ba. Zan iya kokarina naga na kare masa martabarsa, ita kuma Sadiya tabbas sai ta fuskanci hukunci abinda tayi ba zan kyaleta ba duk da kuwa ta kasance 'yar cikina. Da wannan zance zuci Daddy ya iso gida yana fitowa daga mota, maigadi yana ƙarasowa "Sannu da zuwa Alhaji.
"Yawwa Balmo.
"Ai Alhaji bayan kun fita sai ga Halimatu amarya ta zo fuskarta a kumbure idanuwa duk a kode alamar tasha kuka har ta gode Allah, babu kalar tam.....
Kafin Balmo ya ƙarasa magana Daddy ya nufi cikin gida da mugun sauri har wani uban tuntuɓe ya ci da interlock amma ko a jikinsa muradina ya yi ido biyu da Sadiya, rai ɓace Daddy ya tura ƙofar ɗakin Sadiya wacce har zuwa lokaci tana kwance rub da ciki yadda Daddy ya tura ƙofar da ƙarfi yai sanadi da ta zubura ta tashi zaune, idanuwanta suka bayyanar da tsanani tsorata da tayi, cikinta yai wani kalar ƙugi musamman da idanunta suka sauka akan fuskar Daddy wacce ke ɗaure tamau. Sadiya bata ƙara shiga bala'in tashin hankali ba sai da taga irin mugun kallo da Daddy yake bin ta dashi, zance ta gudu bai ma taso ba idan ma tace za ta gudu to ta je ina?
Sai kawai ta sakko daga gado ta zo ta zube guiwayoyinta biyu agaban Daddy ta sadda kanta ƙasa tare da fashewa da mahaukacin kuka "Ka hukunta ni Daddy Dan Allah ka hukunta ni daidai da laifin da na aikata ban cancanci afuwanka ba saboda I really really disappointed you Daddy ban kasan yarinya tagari ba nayi tarnishing image ɗin gidanan na jawowa zuri'arka bad record Daddy ka yi min duk abunda ka ga dama...
Muryarta yai wani kalar sarƙewa duk maganganu dake fita daga bakinta tamkar tana ƙara gayyato wa Daddy fushi da takaicinta ne, idanuwansa sun ƙara rinewa yasa hannunsa ɗaya ya cakume wuyanta ya yi dragging nashi ya ɗauke ta da gigitatcen mari na fitar hankali wata irin razanannayar ƙara ta saki sa'ili Daddy ya sake wanka mata wani mari, ba iya mari guda ko biyu ba maruka ya ci-gaba da ɗauke tasu har sai da ji da ganinta suka ɗauke hanci da bakinta na zubda jini fuskarta da ta fara hayewa Daddya ya duba "meyasa za ki nemi salwantar min da rayuwar yaro? Me ki ka fi Abba dashi da ba za ki iya rayuwar aure dashi ba? Shin ban cancanci a matsayina na mahaifinki ki fidda ni kunya a idon jama'a ba? Ɗan uwanki bai cancanci ki sadaukar masa da farin cikin ki ba? Meyasa Sadiya meyasa za ki nemi kashe Abba?
Ya ƙarashe magana da wani irin mugun fushi a muryarsa, ya sake ta ta zube ƙasa wanwar numfashinta sai ya yi sama ya dawo ƙasa, ko kaɗan Daddy bai damu da hali da take ciki ba ya fito da wayarsa ya yi dialling number CP (Commissioner of police) tare da faɗa masa ya tura masa da yaransa su zo gidansa ga suspect ɗin da suke nema, da yake tun da sassafe Daddy ya kira shi ya sanarda shi komai sai dai ya ɓoye masa bai faɗa masa cewa Sadiya 'yarsa bace.
A fusace Daddy ya rufe Sadiya a ɗakin nata ya dawo downstairs parlor ya kai gwaro ya kai mari, shi kaɗai ne zai iya iya bayyana hali da yake ciki. After twenty minutes ya ji ƙarar jiniyar motar 'yan sanda ya koma ɗaki ya jawo Sadiya kamar kayan wanki sai gunji kuka take yi.


Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.












Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[11/23/2023, 5:57 PM] Jiddarh Aliyu 2: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


#Love story
#Gwagwarmaya
#team tagwaye novels


004.


*RUBUTUN ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU.*
*TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA*


*KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?*
*INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?”
*KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.*
Mun gwada mun gani 💯
Mun gani mun shaida 💯
Anyi mun gani 💯
MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
GYARAN MAIJEGO
MALLAKAR MIJI KO MATA
SUBULU DA SCRUB
MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
MAGANIN TSUMI
INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯


08142800199
07068558096
_______________________


Wuraren sha biyu na rana Mami ta kalli su Siyama tace su tashi su wuce gida ta juya kan AB da Aydah ke gwadawa wani abu a wayarsa sai murmushi yake yi Abba me za a haɗo maka na lunch?" Ya rausayar da kai yana faɗin "Mami komai ma kika yi zanci. murmushi jin daɗi Mami ta yi ganin yadda ya sake lokaci ɗaya. "Yayanmu dan Allah ka faɗawa Mami ta barni a wurinka.
Aydah ta faɗa murya kasa-kasa ta yadda Mami, ba za ta ji ba shima murya can ciki yake faɗin."kuje tare dai nasan damuna za ki yi da surutu kuma anjima akwai islamiyya tun da ba ki samu zuwa ta safe ba.
Lokaci ɗaya Aydah ta wani haɗe rai tayi folding hands ɗinta akan ƙirjinta shi dai murmushi kawai ya yi yana ɗauke kansa tunda ya yi haka tasan ya gama magana kuma ba zai ƙara fadar komai ba. Baki buɗe Mami ke kallonta tana faɗin."ko adaidaita za ki nema mu yi tafiyar mu? Ta ɗan kalli gefen AB ganin ya ma rufe idanuwansa tamkar za ta yiwa Mami kuka cikin sanyin murya ta ce "Dan Allah Mami ki barni anan tare dashi sai ku tafi da yaya Siyama.
Da sauri Siyama tace "Nima Mami zan zauna nasan abunda take yiwa gudu dan kar a shiga kitchen tare da ita.
"Yaushe na faɗa miki haka yayanmu ka yiwa yaya Siyama magana ta daina sakamin ido a lamurranna ta daina bana so.
A hankali Abba ya buɗe idanuwansa yana kallonsu kafin ya kalli Aydah yana faɗin."Tashi ku tafi bana son rigima. Ai yana faɗar haka ta miƙe ta nufi kofa a mugun fusace. daman Mami ta daɗe da fita ganin ta fita yasa Siyama ta juya tana yiwa yaya Abba, sai anjima daman wani kallo yayi mata wanda ta riga tasan me yake nufi ganin Mami ta nufi gidan yaya Abba, da mota yasa Siyama dake zaune a front seat faɗin."Mami yaya Sadiya zamu dauko ne?" shiru Mami ta yiwa Siyama ko magana bata son yi
har suka iso ƙofar gidan Ab mami bata furta uffan ba.
A bakin gate ta yi parking ta kalli Siyama tana faɗin."taje ta shiga ta kira mata Sadiya kai tsaye Siyama ta fice daga motar a bakin gate ta tsaya tana knocking ta ƙaramar kofa a tsorace maigadi ke faɗin."wanene dan har lokacin daren jiya bai daina gilma masa cikin idanunsa yadda aka dauki mai gidansa rai a hannun Allah kwana ya yi yana zagayawa a banɗaki ya tsinewa Sadiya Kwando-kwando a wannan daren. Ya buɗe ƙofar yana kallon Siyama wanda duk a tsorace yake haushi sosai Siyama ta ji tamkar bai ganeta ba "malam Barau ka buɗemin ƙofa mana.
"Babu fa kowa a gidan Hajiya. Da mamaki Siyama ke faɗin."matar gidan nake maka magana.
"Ai matar gidan tun jiya da ta cakawa maigidan nan wuƙa aciki bata kwana gidan nan ba.
Wani irin bugawa ƙirjin Siyama ya shiga yi jin kalaman Barau maigadi wato kenan sanadin yaya Sadiya yaya Abba ya kwanta gadon asibiti, yadda Mami taga Siyama ta nufo su babu wata natsuwa a tattare da ita yasa ta tsaya tana kallonta shiga kawai tayi cikin motar har hawaye sun cika mata idanuwa cikin rawar murya ta ce."Mami ashe dama yaya Sadiya ita ce silar kwanciyar yaya Abba, a gadon asibiti ?
Siyama ta ƙarasa maganar cikin rawar murya batare da Mami ta bata amsar tambayarta ba take faɗin "ya a kayi kika tsaya wajen maigadi ba ki shiga cikin gidan ba? Anan Siyama tasake faɗawa Mami, abunda taji abakin maigadi na cewa yaya Sadiya bata kwana a gida ba kai tsaye Mami ta yiwa motar key batare da ta ƙara bin takan Aydah da Siyama ba dake mai da zance cike da mamakin yar uwar tasu.
Wanda ko a mafarki ko a gaske basu taɓa tunanin zata aikatawa yayansu haka ba. Har suka isa gida jikin Mami sanyayye maigadi ta fara tambaya ko Sadiya tazo gida ?"anan ya tabbatar mata da tazo sai dai kuma bata jima ba motar police tazo ta tafi da ita wani irin tashin hankali Mami ta ji ya cika zuciyarta still tana kallon motar Daddy, da har lokacin tana cikin compound cike da ƙarfin hali Mami ta sake kallon maigadi tana tambayarsa Alhaji yana nan lokaci da aka tafi da Sadiya? Ya tabbatar mata da yana nan. kai tsaye Mami cikin gidan ta nufa lokaci ɗaya jikinta ya yi mugun sanyi tasan Daddy ,da zuciya idan aka bata masa rai babu wanda ya isa ya tankwasa shi ko kaɗan hukuncin da Daddy ,ya ɗauka bai yi ba duk da tasan Sadiya bata kyauta ba tana bukatar a hukunta ta Amma bata hanyar miƙa ta hannun hukuma ba, tun da ma an samu abun yazo da sauki ta kalli su Siyama da har lokacin jikinsu ke a sanyayye tana faɗin."su fara yin breakfast sai su tashi su taimakawa Huwaila da girkin rana. Daman mutanen gidan indai ranakkun weekend ne basu cika yin breakfast da wuri ba sai idan sun san suna zuwa islamiyyar safe. Wacce ba kullum suke zuwan ta safe ba sun fi zuwa da yamma, ta samu Daddy a katafaren parlornsa ya yi wanka still yana sanye da jallabiyya ajikinsa ya yi nisa cikin tunanin da yake Mami ta shigo dauke da sallama a bakinta ya amsa sallamar batare da ya kalleta ba. zama ta yi a gefensa Mami ta rasa ta inda zata yiwa Daddy zancen Sadiya cike da ƙarfin hali Mami tace "Alhaji Amma kamar hukuncin da ka daukarwa Sadiya sai nake ganin kamar bai yi ba kar ayi ta yawo damu a gari.
Wani kallo Daddy ya yi mata
A matuƙar harzuƙe yake faɗin."Ita abunda ta yi ta kyauta? Sadiya ƙaramar Yarinya ce ko me?"shekarar Sadiya 25 a duniya shine kike kiranta ƙaramar Yarinya?"ki daina batamin rai dan Allah. Idan kin san ba magana mai muhimmanci zaki faɗa ba ki tashi ki fita ki barni da damuwar da nake aciki. Ran Mami ya gama ɓaci akan hukuncin da Daddy ,ya dauka tasan tana ƙaunar Abba, fiye da 'ya'yan da ta haifa da cikinta ita kanta bata ji daɗin yadda Daddy, ya yanke hukunci haɗa yaran nata aure ba. musamman Sadiya da tayi gadon kafiya a wajen mahaifinta. kai tsaye Mami parlorn tabari ta wuce ɗakinta sai kai da kawo take a tsakiyar ɗakinta da gaske Daddy yana ƙoƙarin jawo masu abunda ba zai iya gyarawa anan gaba ba, duk wanda ya ji yadda Sadiya ta yi a daren aurenta ba zai yarda ya aureta ba ko kaɗan bata so maganar nan ta kai wurin yan sanda ba. Tafiso su da suka bata komai su warware komai, mutum na farko da ya faɗo mata a wannan lokacin shine Abba, Amma kuma da kunya ta kira Abba ta shaida masa Daddy ya miƙa Sadiya a hannun hukuma mutum na ƙarshe da yazo mata wannan lokacin shine Abdulkarim za tayi magana dashi su tattauna da Abban, ko za a iya samun mafita da sallama Abdulkarim ya daga kiran Mami, ya gaisheta ta amsa shiru ya ɗan biyo na wani lokaci kafin Mami ta soma yiwa Abdulkarim bayani abunda ke faruwa, shima Abdulkarim ɗin shiru yayi yana ta nazarin maganganun Mami kafin yace mata Abba yanzu ya samu bacci idan ya tashi za su tattauna godiya Mami ta yi masa gamida sauke wayar. Wannan ƙaron driver Mami ta haɗa da Siyama da kuma Aydah su suka je asibiti kaiwa Ab abincin rana suma basu jima ba Ab ya uzura musu akan su kira driver ya mayar dasu gida lokacin islamiyya ya yi kusa shiru Aydah ta yi tare da bata rai sosai da alamar ko kaɗan zancen bai mata daɗi ba tasan haka yayan nasu yake ko kaɗan baya son ayi fashin islamiyya ko biki suke basa fashin zuwa islamiyya. Bayan isowar driver Siyama kawai ce ta yiwa Ab sallama daman Aydah tafiyarta ta yi ko kallon gefen da yake bata sake yi ba yasan fushi ta yi bayan tafiyarsu Abdulkarim dake zaune akan sofa ɗin dake girke acikin ɗakin kallon AB yayi da ya rufe idanunsa ɗan gyaran murya ya yi da yasa AB buɗe manyan fararen idanuwansa yana kallon Abdulkarim "Da tun farko wannan yarinyar Siyama ya aura maka ba wannan shashashar mahaukaciyar yarinyar ba.
Wani kallo AB ya riƙa yi masa, murya a shaƙe ya ce "ka manta cewa Siyama tana da wanda take so very soon za a sa musu rana ko Sadiya da aka auramin kasan yadda igiyoyin aurenta sukayi min tsaye akai?
"To ba ga Aydah ba amma wannan Sadiya tun farko ni dai bata kwanta

3 / 80