Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   10 / 80

27K to 30K   out of 237.2K words

Sadiya ɗin jinin Daddy ce da kuma Mami ,ya ture plate ɗin gabansa ya zari tissue ya goge bakinsa ya mike tsaye kitchen ya nufa ya wanko bakinsa ya dawo ya kalli Mami yana faɗin."Mami na fita.
A natse Mami ke masa addu'ar Allah ya bada sa'a ya amsa da Ameen,da sauri Sadiya ta miƙe tsaye ta marairaice fuska tana faɗin "yaya Abba, ka ɗan saukeni makarantar mana. Juyawa yayi batare da yace komai ba jin haka ta juya ita ma tabi bayansa da sauri binsu kurum mami tayi da kallo acan ƙasan ranta sai taji duk babu dadi da Daddy bai yi gaggawa ba akan yaran nan da yanzu suna ƙarƙashin innuwar aure, yadda ta lura da Sadiya kamar ta fara saukowa shi Abba ɗin ne ma kamar har yanzu bai sauko ba,
Tana tsaye ajikin motarsa tana jiran ya fito daga part ɗinsa bai jima ba ya fito dauke da briefcase ɗinsa wani irin yanayin take ji game da yayan nata
bata san Meyasa tayi gajen haƙuri ba da yanzu tana ƙarƙashin kulawar Abba Bashir, bata san Meyasa ta biyewa son zuciyarta ba da gaske yanzu tana son zaman aure tare da yayan nata sai yanzu take hango wani irin quality da attributes akan yayan nata har ya buɗe mota ya shiga Sadiya ta tafi duniyar tunani sai da ta ji wani irin gigitatcen horn da ya ratsa har tsakiyyar kwanyar kanta shi ya dawo da ita hankalinta da sauri ta buɗe front seat ta yiwa kanta masauki
gami da rufo ƙofar a hankali maigadi ya buɗe masu get suka fice daga gidan
Kai tsaye hanyar makarantarsu ya ɗauke kan motarsa banda kira'ar (Ahmad sulaiman )dake tashi cikin motar cikin suratul bakara ba kyajin komai a motar, wayarsa ce ta soma ringing ya rage volume haka ya rage gudun motar yasa wayar a speaker dama kuma ɗabi'arsa ce in har yana tuki zai yi wuya ya dauki waya sai dai ya barta a speaker."Habibi ina kwana.!
"Rumaisa!
Ya faɗa cikin muryar jan hankali wani irin dokawa kirjin Sadiya ya yi jin wata macce ta kira yaya Abbanta da Habibi, nan take farin cikin dake cikin fuskarta ya ɓace bat."Ya ki ke?"Lafiya lau ya maganar fitar mu zuwa anjima karka shanyani dan Allah nasan halinka wallahi ina buƙatar yin shopping yau kayan shafana sun kare.
Ta ƙarashe maganar cikin muryar shagwaɓa mai dauke da wani irin shauƙi "Bayan la'asar yayi maki?"yeah!
"Owk idan zan shigo zan kiraki.
Daga haka ya sauke wayar har ya kai Sadiya makaranta ranta a ɓace yake ko kallonta bai yi ba balle ya gane yanayin da ta shiga. a ranar kakaf Sadiya bata shiga lectures ɗin dake gareta ba yanayin yadda Yaya Abba, ke waya da Rumaisa ya yi mugun daga hankalin ta ƙarfe biyu nayi ta biyo Siyama zuwa gida tana jin kamar zazzaɓi zai rufeta tambayar farko da Siyama tayi mata ita ce."Bakida Lafiya ne yaya Sadiya? "kaina ke ciwo.
Sadiya ta faɗa gami da dauke kanta tana mayarwa kan titi inda ababen hawa ke kai da kawo.
A hankali Siyama tace "Allah ya sauwakke.
A parlor suka sami Mami tare da Aydah ita ma ta dawo da nata zazzaɓi, har Siyama da Sadiya suka tausayawa little sis ɗin tasu ganin yadda ta rame lokaci ɗaya.
Sun san idan yaya Abba,yayi fushi da ita duk cikinsu ita ce marar juriyar daukar fushinsa yanzu nan zata kwanta ciwo."Mami jikinta da zafi sosai kuma ba a kira family doctor ba ya dubata?" Sadiya ta faɗa da damuwa sosai a fuskarta, "kin manta baya gari sai dai idan za ki yi sallah ki ci abinci sai ku je asibiti da driver a duba ta ɗin.
Mami ta faɗa tana shafar kalabar kan Aydah.
Da sauri Aydah ta buɗe idanunta da suka kada suka canja kala "Ni bana son ta kaini wata asibiti yayamu nake so yazo ya kaini."ta karasa maganar cike da zallan rigima.
"auuhhhh Allah? kin manta fushi yaya keyi dake?" Banza Aydah ta yiwa Siyama ta koma ta kwanta cike da damuwa Sadiya ke faɗin."To ke Mami ki kirasa ya kai ta mana kin san shima yanzu zai rikice idan ya ji ance bata da lafiya.
Acan ƙasan ran sadiya kuwa har addu'a take fitar da zai yi da budurwarsa ya watse. Mami dai bata kara cewa komai ba daman Siyama, ta daɗe da wucewarta ɗaki dan zafi take ji tana buƙatar watsa ruwa yau garin an zuba rana sai kusan ƙarfe 3 Abba, ya shigo gidan ko kaɗan baya ƙaunar zafi kai tsaye part ɗinsa ya nufa ya rage kayan jikinsa ya yi wanka.
Ya shirya cikin ƙanunun kaya marar nauyi yayi matuƙar kyau acikinsu kana ya wuce cikin gida mami ce a parlor da Siyama tana danna waya da kayan shan iska ajikinta ga baki ɗaya cinyoyinta a waje suke kallo ɗaya ya yi mata ya dauke kai, mami tana kallonsa ya gaisheta ta amsa tana tambayarsa ya aiki?"ya amsa da Al-hamdullilah, Siyama ce ta kawo masa abincin rana cikin parlor ,ya kalleta in a serious note yake faɗin."Daga yau kar ki ƙara zama da waɗannan kayan acikin parlon gidan nan.
ɗaga kai kurum ta yi ta juya tabar cikin parlorn Mami tace ta fadawa Aydah ta fito idan ya gama cin abinci ya kai ta asibiti A natse Abba ke cin abincinsa yana tambayar mamin me kuma ya sami Aydan?
"Tun da ta dawo school take kwance zazzaɓi ne kawai sai dai kasan halinta da mugun raki.
Murmushi ya yiwa mami yasan gaskiya ta faɗa kuma yasan ciwon yana da alaƙa da fushin da yake da ita
Siyama ta leƙa ɗakin Aydah duk wannan uban zafin harda su lullube jiki da duvet ta kira sunanta tana faɗin "ki taso yaya Abba, ya dawo ya kai ki kiga likita.
Jin an ambaci yayanta ta cire duvet ɗin jikinta da sauri duk da jirin da take ji dan komai taki yadda taci haka ta nufi toilet ta wanko bakinta hijab ɗinta na sallah ta ɗora akan rigarta tun daga kan stairs yake kallon yadda take layi tamkar zata faɗi ita ma ta zuba idanunta acikin nasa tai wani marairaice masa har kusa dashi taje ta zauna tana gaishesa ya amsa yana tambayarta ya jikin."ta amsa da sauki ,hannunsa ya kai a forehand ɗinta saboda zafi ya yi saurin janye hannunsa, "kin ci abinci?"
Da sauri ta girgiza kanta yayin da hawaye na taruwa acikin idanunta
"Na zuba miki za ki iyaci?"
Ɗaga masa kai ta yi da sauri wani irin daɗi na lulluɓeta ,da kansa ya miƙe tsaye ya nufi cikin dining area din ya zubo mata white rice kaɗan da stew a sama da naman rago. ya dawo ya miƙa mata ta fara cin shinkafar a hankali badan tana jin daɗinta ba kaɗan taci tace ta koshi Abba ,ya miƙe tsaye yana kallonta ya ce."su je taga doctor ta marairaice masa tamkar zata yi kuka."banda allura yayanmu. Wani kallo ya yi mata kana ya miƙe tsaye ya kalli watch ɗin dake hannunsa bai fi minti ashirin ba a kira sallar la'asar yace ta jirasa kai tsaye stairs ya nufa har zuwa ɗakin Mami, sai da aka basa izinin shiga ya shiga da sallama a bakin ƙofa ya tsaya yana faɗawa Mami za su je asibiti , mami ta faɗa masa babu komai acikinta ya samu ko tea tasha
Ya faɗawa Mami ,ai ya zuba mata abinci taci ƙadan. Mami ta hararesa tana cewa "Daman ciwon nata na gulma ne.
Ya ware ido yana faɗin."Da gaske take Mami ba ki ji jikinta ba akwai zafi sosai. Mami ta taɓe baki tana faɗin."Duk ba iskanci bane ka bi ka sangartata.
Murmushi Kurum ya yi yabar ɗakin na Mami kusan cin karo suka yi da Sadiya da sauri ya ja da baya
Ta gaishesa ya amsa ya wani dauke kai ya soma sauka akan stairs da ido ta bisa har ya ɓacewa ganinta. Tun kafin su isa inda file ɗin duka yan gidan yake ya yi waya da Dr Musa akan suna hanya yasa a fitar da file ɗin Aydah zai dubata bata da lafiya.
Dr.musa yana ta yiwa Aydah tambayoyi tana basa amsa har ya gama rubutun da yake a takarda ya miƙawa AB yana masa bayanin drugs din da za a siya mata ne ya faɗa masa sai sunyi mata allura tun kafin azo kan allurar ta fara hawaye AB ya dauke kansa bai ma san tanayi ba
har nurse ta kawo allurar da za ayi mata guda biyu, tunda Dr Musa ya fara haɗa allura ta fashe da kukan da yasa Abba yimata tsawa gyara ayi miki kina ɓatamin lokaci, Abba ya faɗa yana yimata tsawa ta buɗe hannunta tana miƙawa Dr Musa dake yimata Dariyar tsoron allura a baya za a yi miki da sauri ta kalli AB kusan minti goma Aydah taki tsayawa ayi mata allura ganin tana ta ɓata masa lokaci har anyi kiran sallah ,yasa ya wani fisgota ya matseta cikin jikinsa tsit tayi har aka gama duka biyun bata san anyi ba har kuma lokacin hawaye take cikin tsokana doctor Musa ke faɗin."ke gaki kin zama yanmata amma kina tsoron allura ita dai batace komai ba ta nufi ƙofa ta fice daga office ɗin AB ya tsaya yana yiwa doctor Musa godiya kafin yabi bayan Aydah acan bakin motarsa ya cimmata tana kuka ko kallonta bai yi ba ya shiga mota dole ta buɗe ta shiga ya tsaya ya siya mata drugs "za ki sha rufaidah?"daga masa kai tayi still fuskarta na cikin hijab furar rufaidah ya siya mata har roba biyu da gasassar kaza ita ma biyu duk kayan jinya ne
Yasan Aydah dason cin nama kamar me a haka suka isa gida da kansa ya bata drugs ,ya sumbaci goshinta a hankali ya furta."get well soon little sis fita zan yi me kike so nazo miki dashi?"ice cream ta faɗa cikin sanyi murya ,daga mata hannu yayi alamar bye-bye Sadiya dake laɓe a ƙofar kitchen tana kallonsu jin tayi wani abu na tsaya mata dai-dai tsakiyar ƙirjinta musamman yadda taga Aydah tabi yayan nasu da kallo tana binsa da murmushin da ta kasa gane ma'anarsa.


#love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#team tagwaye novels
#Kurman Allo








Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/3/2023, 2:56 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


#Love Story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye novels




*RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU.*
*TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA*


PAID BOOK




014.




https://www.tiktok.com/@maims_kiddies
"Lallai Dr irin wannan kyau haka tamkar kunzo daga ƙasar UK? Gaskiya kayan jikin su Hanan sunyi matukar kyau, amma dai ba'a ƙasar nan kuka siya ba?" Cikin dariya Dr Aisha tace. "A ƙasar nan muka siya, sai dai kamar yadda kika ce ɗin haka ne, duk wannan kayan da kika gani a jikin yaran nan na ƙasar UK ne da *@Maims_kiddie* take sai da su a cikin Nigeria, muma a wajanta muka siya kuma ba tare da munje inda take ba, kayan na gani a Instagram account ɗin ta na *KIDS THRIFTY/OKRIKA STORE.* Kayane masu kyau da kwari daki bari kenan malam Khadija dan tun da na fara siyan kayan yara a wajanta shikenan na dena ganin kyawun na ko'ina. Kema/kuma zaku iya nemanta a Instagram link ɗin dake sama. Za kuma ku iya samunta a WhatsApp ta wannan link ɗin dake ƙasa. Ko lambar wayarta.
https://Wa.me//08101378616












Da mamaki take ta kallon Aydah ganin yadda ta samu sauƙi lokaci ɗaya farin cikinta da walwalarta suka dawo. Acan wani ɓangaren na zuciyar Sadiya yake faɗa mata ko dai Aydah ta faɗa son yaya Abbane?? Da sauri wata zuciyar ta kwaɓeta da ba hakanan bane shaƙuwa ce kawai,a shekarun Aydah ai ba za ta san menene ma soyayya ba. A zahirance jin tayi ƙafafunta sunyi mata wani irin nauyi na ban mamaki haka ta ja ƙafafunta ta fito daga kitchen ɗin tana ta kallon Aydah dake ta shan furarta a hankali cikin natsuwa da nishadi da sauri ta dauke kanta akan ƙanwarta ta, ta nufi stairs.
Shopping Rumaisa ta yi sosai sai wurin biya kuɗi ne AB ya bada card ɗinsa aka cire kuɗin a hanyar dawowarsu ne take faɗa masa mahaifinta baya gari da ya dawo zata zauna dashi ta fahimtar dashi ƙofar gida kawai ya ajeta batare da ya shiga ciki ba ya juya kan motar zuwa gida
yana isa ana kiran sallar magarib parking motar kawai ya yi kana ya yi alwallah ya shiga masallacin dake cikin unguwarsu bashi ya shigo gida ba sai bayan sallar isha kai tsaye cikin gida ya nufa dukkansu suna zaune a parlor ya kai kallonsa gurin Aydah dake kwance cikin doguwar kujera cike da kulawa ya ce "Ya jikin naki zafin sa ya sauka?" Ɗaga masa kai tayi alamar "eh! "kinci abinci kin sha magani?" nan ma amsa masa tayi kai tsaye parlorn Daddy ya nufa da respect ya gaishe da Daddy dan tun safe basu haɗu ba ya amsa cike da kulawa kafin ya ɗora da faɗin."hope kun samu fahimtar juna da Mufeeda?" Na faɗa maka bana son aurenku ya ɗauki dogon lokaci ko ɗazu muna tare da Alhaji Habib ,yadda yake zancenka da alamar yar tasa tayi amanna dakai ta karbeka a matsayin mijin aurenta.
Ina son ka saki jikinka Abba insha Allahu wannan auren alkhairi ne zan ƙara maka sati ɗaya kafin ku ƙara shaƙuwa da yarinyar daga nan zan tura a nemar maka aurenta.
Tun sanda Daddy, ya fara yi masa zancen auren Mufeeda komai ya kwace masa har suka gama cin abincin dare ya kasa maida walwalarsa Sadiya sai nazarta yanayinsa take bai jima tare dasu ba ya koma ɓangarensa sai bayan wucewarsa ne Daddy ke yiwa Mami zancen yar gidan Alhaji Habib,
Mami tayi Allah ya sanya Alkhairi hakama sauran ƙannen nasa Siyama da Aydah sosai suke farin ciki da auren yayan nasu banda Sadiya da ta ji komai ya fice mata arai a daren ranar ba ƙaramin kokuwa Sadiya ta dinga yi da numafashinta ba har ma da zuciyarta.
Wai yaya Abbane zai yi aure sai ta samu kanta da wani irin kishinsa na ban mamaki wanda bata taɓa jin kalarsa ba ,da alamar iyayenta sun riga sun haramta zaman aure a tsakaninsu, tasan ta yi laifi ta kuma amshi laifinta da hannu bibbiyu kuma ai saki daya ne yaya Abban ya yi mata ko yanzu yace ya mayar da ita za su ci-gaba da zaman aurensu. Har ƙarfe goma na safe Sadiya tana dunƙule a ɗaki cikin duvet dare ɗaya ta fice daga hayyacinta ta yi wani irin zuru-zuru duk akan zancen auren Abba Bashir da Daddy yasa a gaba
yau ta yi sa'a bata da lecture ko ɗaya haka kuma ranar jumu'a ne, sosai Mami ,tasha mamaki har ƙarfe goma da kusan rabi na safe bata ga wurgawar Sadiya cikin parkon ba. Bayan Daddy ya wuce office kai tsaye ta nufi ɗakin Sadiya tsayawa ta yi kanta tana kiran sunanta a hankali ta buɗe idanunta da suka canja kala, alamar dai babu wani wadatatccen bacci acikin su
"Ke lafiya meya faru? Sadiya ta miƙe zaune a hankali tana sakin 'yar ƙaramar miƙa a hankali tare da faɗin. "Mami ina kwana?"
Mami ta amsa da "lafiya lau!
Mami dai sai kallonta take kafin ta juya tana faɗin."Tun da lafiyarki ƙalau ai shike nan, daga haka Mami ta fice daga ɗakin tana son ta
yi zancen aurenta da yaya Abba da Mami sai dai bata san ta inda zata fara ba. shi ma a ɓangaren yaya Abba, yaƙi bata fuska ta tsaya tayi doguwar magana dashi duk wata hanyar da zata yi magana mai tsayi dashi ya tosheta. A haka kwanaki suka riƙa gudu Sadiya tana ta ƙunci ita ɗaya kullum tunanin yayan nata manne a zuciyarta satin da aka kai kayan auren yaya Abba har zazzaɓi tayi ita ɗaya ke jinyar zuciyarta. Sai washe gari Alh Sanusi yasan cewa 'yar gidan Alh Habeeb bichi ce Abba zai aura ranar Assabar ce ƙarfe takwas na safe ya fice daga gidansa cikin tashin hankali ko karin kumallo bai yi ba yana tuƙi yana tsinewa yayansa dan ko maganar auren Abba ɗin bata taɓa haɗasa dashi ba. Wani murmushin takaici yayi takwas da mintuna ya tsayar da motarsa a get ɗin gidan Alh Habeeb bichi da mamaki maigadi ya leiƙo ta ƙaramar ƙofa yana ƙarewa motar kallo da ta zama baƙuwa a wajensa,
A fusace Alh Sanusi ya sauke glass yana kumfar baki "Malam baka san aikin ka bane ?" Ka tsaya kana wani kallo na kamar tsohon maye, kalaman Alh Sanusi ba ƙaramin konawa maigadi rai suka yi ba shima a kufule ya ce "malam lafiya ban taba ganin koda fuskar ka ba ballatana motar da kazo da ita wurin wa kazo da sanyi safiya haka? wurin maigidan nazo ko banyi matsayin da zanzo wurinsa ba?" Wani kallo maigadi ya yi masa kafin yace "Ni babu wanda ya sanar dani zuwanka da safen nan kuma maigida yanzu haka bacci yake.
Rai bace Alh Sanusi ya fito daga motarsa tuni maigadi ya mayar da kofar ya rufe haka Alh Sanusi ya rika dukan get tamkar wani zautatce yana zagin maigadi yana kiransa matsiyaci talaka tamkar a mafarki maman Mufeeda dake kitchen taji ana buga get da ƙarfi da sauri ta fito kitchen tana kallon mai aikinta Lanto tana faɗin ta je taga ina maigadi ya shiga baya jin ana buga ƙofa ne da ladabi Lanto ta juya ta yi hanyar ficewa daga parlon ,a kan benci ta samu Mudi mai gadi ya ƙure volume ɗin redio da mamaki tace "Mudi baka jin ana buga get ne? Wani kallo ya yi mata ya dauke kansa, rai a ɓace ta nufi get ta buɗe karamar kofa suka yi ido huɗu da Alh Sanusi da ransa ya gama ɓaci
da ladabi Lanto ta gaishesa tana tambayarsa wurin wa yazo? Ya faɗa mata wurin maigidan yazo maigadi yai masa wulaƙanci ya zagesa ya rufe masa ƙofa Lanto tace ya shigo daga ciki zata je ta faɗawa Hajiyar gidan. Har cikin compound Lanto ta shigo

10 / 80