Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   17 / 80

48K to 51K   out of 237.2K words

mu.
"Faɗa mata dai bro ko ɗan saurayi nan bata dashi kuma ko last month da muka je birnin kudu sai da mai babban ɗaki ta yi zancen aurenta naga yadda za ta yi aure babu miji.
"Ya kamata ki sassauta wa kanki Anaal kalli nan. Ya nuna mata screen ɗin wayarsa hoton wani friend ɗinsu ta gani. "Na gani sai aka yi yaya? Ameer Abdallah Sambo ne inkiya AA Sambo.
"Ashe kin shaida shi.
"Ta ya za a yi na gasa shaida shi wannan baƙi mayye mai naci tsiya.
"Kinsan dai yadda guy nan ya mutu akanki dan Allah ki bashi dama Anaal.
Sai da ta ture shi kana ta diro ƙasa tana faɗin "Bai min yi ba.
Da sauri Zeeyad ya sha gabanta "Haba Anaal! wallahi guy nan ya haɗu matuƙar haɗuwa.
"Kai ka aure shi mana.
Ta faɗa tare da harararsa.
Zaro idanuwa Zeeyad ya yi yayin da Zaheed ya sheƙe da dariya.
"Haba dallah! An gayamiki ni gay ne da za ki ce na aure namiji ɗan uwana.
"To naga ka wani zakalkale ne sai koɗa sa kake yi na zaci ko you had a huge crush on him ka ga sai ka aure abinka ko Zaheed?
Ta ƙarashe magana tana kallon Zaheed dake ta kyakyalar dariya ƙeta. "Za su dace sosai da juna wa yaga ango da amarya.
Zaheed ya faɗa yana ƙara sheƙewa da dariya Anaal tana tayashi. Sosai ran Zeeyad ya ɓaci don bai ga dalili da za su dinga masa wannan mummunan wasan ba. A fusace ya bar musu office ɗin dama sun saba haɗe masa kai.
*International private hospital*
Drip ɗin jikin AB yana ƙarewa aka sake jona mishi wani sai da ya sha ledar ruwa huɗu kafin likitan ya sallame shi tare yi masa gargaɗin ya dinga sha maganinsa on time. Abdulkarim yaso daga asibiti su wuce gidan iyayen AB a ganinsa acan zai fi samun kyakkyawar kulawa fiye da gidansa tun da a gidan nasa shi kaɗai ne acan kuma ga iyayensa da kannensa, amma AB ya kafe da lallai-lallai shi gidansa zai kai sa ba don zuciyar Abdulkarim taso haka ba sai don bashi da yarda zai yi. Sai da yaga shigar AB bathroom zai yi wanka sannan ya fita ya nemo musu abinci da za su ci saboda yunwa yake ji shima AB dole yana bukatar abinci.
AB yana tsaye agaban shower ruwa na sauka akan naked body ɗinsa ya cije lips ɗinsa kafin ya kai hannu ya wargaza jiƙaƙƙiyar sumar kansa tare da lumsashe idanuwansa shi kan yaga ta kansa daga wannan sai wannan yanzu fissibillahi ta ya zai iya karɓar Aydah a matsayin matar aurensa, Sadiya ma da ta kasance cikakkiyar budurwa bai ji zai iya rayuwar aure da ita ba, balle wannan 'yar mitsiyaya yarinya wacce ya rena da hannunsa.
A bayyane cikin wata irin raunatatciya murya ya furta "Don't do this to me, Daddy, I can't accept Aydah as my wife yarinya nan fa nine na raine ta ba zan iya ba Daddy.
Ya ƙarashe magana wani irin kuka yana subuce mishi sai kawai ya zube guiwayoyinsa kan tiles ya cigaba da kukansa wanda sautin sa ya gama cika bathroom ɗin. Dawowar Abdulkarim kenan ya ji kamar kukan AB a bathroom a tsorace ya ajiye ledar takeaway ɗin da ya yi musu akan bedside drawer ya nufi ƙofar bathroom ɗin ya baza kunnuwansa yana so ya tabbatar da gaske kukan AB ne yake ji ko kuma kunnuwanshi ne ke yaudarar sa domin sani da ya yiwa Abba jarumi ne abunda zai iya saka shi kuka ba ƙaramin abu bane. Wani kalan zaro idanuwa ya yi yadda ya ji shesshakar kukan nasa ya daɗa ƙaruwa bai tsaya wani dogon tunani ba ya buɗe ƙofar ya shiga idanunsa suka yi masa tozali da AB durƙushe yana kuka, zuciyar Abdulkarim ta yi mugun bugawa da ƙarfi da sauri ya nufi hanger dake bathroom ɗin wacce ke dauke da towels haɗe da bathrobe ya zari bathrobe ɗaya ya ƙarasa wurinsa sai da ya kashe shower ɗin kafin ya nufi bayansa ya saka masa rigar ba tare da ya kalle nakedness ɗinsa ba. AB ya ɗago jajaye idanuwansa ya kalli Abdulkarim sai kawai ya sake fashewa da kuka Abdulkarim ya kama shi tare da miƙar da shi tsaye sai kawai ya faɗa jikin Abdulkarim cikin muryar kuka yake faɗin "I can't marry her. I can't see her as my wife. If Daddy marries Aydah to me, I swear to God my heart will stop beating and I will die. Ak ba zan iya ba dan Allah ka sanarwa da Daddy Aydah she is like a daughter to me, I can't live a married life with her. Zuciyana ba za ta iya jure wannan abin kunya ba.
Ya ƙarashe magana yana goga fuskarsa a shoulder ɗin Abdulkarim tsanani shock ɗin da Abdulkarim ya shiga ya hana mishi furta uffan sai kawai ya raba jikinsa da na AB kana ya riƙo hannunsa suka fito a gefen gado Abdulkarim ya yi musu masauki ya ɗauki longtime yana maimata maganganu AB ajiyar zuciya ya yi ta yafi sau ashirin kafin ya shiga rarrashin abokin nasa har ya ci nasarar shawo kansa ya daina kukan "AB yaushe Daddy ya yanke wannan hukuncin?"
Abdulkarim ya tambaya tare da tsare AB da idanunsa yana jiran ya amsar da zai basa.


#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo






Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/13/2023, 10:46 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU




#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye novels




023..


*AREWA BOOK* :jeddah3256




Kusan sau uku yana buɗe bakinsa dan zimmar ya yiwa Abdulkarim bayani sai yaji komai nasa ya tsaya ya kasa buɗe bakin nasa ya yi magana dan wata irin kunyar yin maganar yake ji duk lokacin da ya tuna da Daddy zai aura masa Aydah sai zuciyarsa ta shiga dokawa da wani irin karfi tamkar zata fito daga ƙirjinsa shi dai har lokacin Abdulkarim kallon AB kurum
yake kwantawa ya yi akan bed ɗin tare da runtse idanuwanshi gam! Ya ɗauki lokaci a haka kafin kuma ya tashi zaune ya koma ya dafe kansa da dukkan hannunsa biyu ya yi shiru har na kusan mintina biyar. Abdulkarim da ransa ya soma ɓaci ya miƙe tsaye yana mayar da wayoyinsa cikin aljihun wandonsa yana faɗin."ni zan wuce sai da safe, da sauri AB ya kallesa cikin sanyin murya yake faɗin."na dauka nan zaka kwana ae." wani banzan kallo Abdukarim ke yiwa Abban, "na kwana nayi maka uban me sau nawa ina tambayarka meye damuwarka kaki buɗe baki kayi min bayani."dama ni kaɗai ne na damu da damuwarka bance kuma dole sai ka faɗamin ba Allah ya yaye ma abunda ke damunka.
Ya faɗa sounding so fed up yana nufar ƙofar fita.
Ganin da gaske tafiya zai yi cike da karfin hali AB ya kira sunan Abdulkarim.
Dakatawa yayi Amma dai bai juyo ba gani yaƙi juyowa cikin sarkewar harshe yake faɗin."Daddy aure zai haɗani da Aydah wani satin mai zuwa har ya fitar da card na daurin aure. Ya ƙarasa magana da wani irin rauni a muryarsa.
With so much shock Abdulkarim ya juyo dukansa, ya nufi AB ɗin ya zauna gefen bed yana faɗin."kace min da wasa kake yi AB?" wani kallo AB ɗin ya yi masa jin irin maganar rainin hankalin da yake yi masa."Na taɓa yi maka kalar wannan wasar?" shine sanadin ciwona gara in mutu da in auri Aydah , yarinyar da na raina da hannu na shin idan ma mun yi auren me zan cira ajikinta."meyasa Daddy yake yanke irin wannan hukuncin batare da wani dogon tunani ba baya duba abunda zai iya faruwa a gaba.
"I know my self ko nan da shekara goma zan iya rike kaina batare da macce ba ,ban san taya zan fahimtar da Daddy ba." Ya ƙarasa maganar da wata irin rawar murya duk yadda Abdulkarim yaso hana kansa yin dariya ganin halin da abokin nasa yake ciki sai da ya ɗan dara. Kallonsa kawai AB yake zuciyarsa na tafarfasa dama yasan idan Abdukarim ya ji wannan zance ya samu abun tsokanarsa kenan gashi nan tun kafin aje ko'ina dariya yake yi masa.
On a serious note Abdulkarim ke faɗin."yanzu ne za ka fuskanci reality ɗinka AB wai kai baka san irin waya'nnan cwt 16 din ba sun fi daɗin sha'ani ba? A ko'ina ƙwaƙwalwarsu fresh sai abunda ka koyar dasu ka bai wa Aydah shekara ɗaya kaga yadda za ta zama ka koya mata training ɗinka.
Da sauri AB ya katsesa "Na koya mata me?" ka daina bata min rai Ak kana nufin me kenan, Aydah fa?"
Ak ya juya ido yana faɗin."Yes it's her ba matarka bace. Da sauri AB ya dunƙule hannunsa zai kai wa Abdulkarim wanin irin punch da sauri Ak ya janye yana zaro ido yana faɗin."Haba Angon Aydah Bashir what's the meaning of this manner?" owk na yarda ƙanwarka ce ko bayan an kai maka ita a gidanka rainonta za ka ci-gaba da yi right?" Da sauri AB ya haɗe ransa yana jin zuciyarsa na ci-gaba da tafarfasa irin maganganun da Abdulkarim ɗin ke zubawa. Nasan za ka iya rike kanka har na shekara goma kuma ka ci-gaba da zama tare da Aydah kaga sai ka ci-gaba da shan lemi ɗinka. Tun da Allah yasa baby Aydah ce ka aura. Abdukarim ya karashe magana tare da fashewa da dariyar shakiyanci yana ficewa daga ɗakin ganin yadda AB ya fusata sosai. Ranar tun da Aydah ta dawo daga school ba taga AB ba duk tabi ta damu tana dawowa daga school ta nufi ɗakin Mami ,ko uniform ɗin jikinta bata cire ba take tambayar "mami ina yaya Abba.?" Mami yin tayi kamar bata ji me take faɗa ba.
Sai da ta ƙara maimaita tambayar a fusace Mami ke faɗin."Abba yarone da za ki zo ki tsareni da tambayar ina yake." Tamkar zata yi kuka take faɗin "tun Jiya fa Mami ban ji alamarsa a gidan nan ba kuma ba tafiya ya yi ba.
Cike da gajiya da zancen Mami tace "Ki fitar min daga ɗaki bana son fitina. Juyawa Aydah ta yi ta fice daga ɗakin har tayi shirin islamiyya ranta a ɓace yake dama kuma ba tayi gigin ɗaukar wayar Mami ba da ta kira yaya Abba.
Sai da ta dawo bayan magarib ta shiga ɗakin siyama ta sameta tana waya ta zauna kan soofa tana jiran tagama wayar, Siyama tana ganin Aydah ta yi mata zaune yasata sallama da wanda take wayar, ta kalli Aydah ganin yadda ta yi fuskar tausayi lokaci ɗaya dama kuma idan ta yi haka da akwai abunda takeso a wurin Siyama ɗin."Dama yaya Siyama yayanmu za ki kira min a waya tun jiya fa ban gansa ba kodai ya yi tafiya ne bai sanar mana ba? Ba tare da Siyama ta ce komai ba ta yi dialling number AB har ta katse bai ɗaga ba nan ta sake kira tana shiga ya katse ya kirata ta dauka ta gaishesa da cool voice nasa ya amsa cike da kulawa Siyama ke fadin."Yayanmu mura kake naji muryarka wani iri....! ai kafin ya bata amsa Aydah ta fisge wayar ta nufi ƙofa Siyama ta bi da ta da kallo baki buɗe har Aydah ta fice daga ɗakin direct ɗakinta ta shiga harda su sakawa ƙofar key, dan tasan Siyama tana iya biyo bayanta."cikin sanyin muryarta ta kira sunansa "yaya Abba!
"Baby Aydah ya kike?" Ya faɗa da murya marar amo cikin rawar murya Aydah ta ce."Yayanmu bakada lafiya ne?" ina ka shiga tun jiya?" Yana jin yadda muryarta take ɗan rawa yasan za ta iya fashe masa da kuka.
Shiru yayi na kusan sakan goma.
Kafin yace "Ina hanyar dawowa kafin na shigo ki haɗamin coffee ki soya min egg. shima kawai ya faɗa ne badan wai yana jin yunwa ba.
Da farin ciki Aydah ta katse wayar ta koma ɗakin Siyama ta aje mata wayarta akan mirror dan taji kamar motsin ruwa a toilet ɗinta kai tsaye kitchen ta nufa cikin minti goma ta gama haɗawa yayan nata coffee ta zuba cikin flask ta soya masa wainar kwai ta juyeta cikin plate tana zaune a parlor tana jiran shigowar yayan nasu har kusan minti goma da zamanta,ta ji horn ɗin motarsa. kai tsaye part ɗinsa ya nufa
Daidai kuma lokacin kiran Rumaisa ya shigo a wayarsa tun daren jiya take ta kiransa a waya yaki ya daga har yau ɗin. ɗagawa ya yi a dakile ya furta "Hello! hankali tashe take faɗin."meya samu wayarka ina ta kiranka tun daren jiya baka ɗagawa?"
"Ba komai!
Ya faɗa a takaice sai kawai ta kara bashi haƙuri akan yadda ta fusata sa ranar da suka haɗu dan ta yi tunanin ko shine yasa yaki daga wayarta. "Yanzu nan na shigo gida Rumaisa idan nayi wanka na huta zan Kiraki." Ɗan shiru ta yi tana sauraresa cikin sanyin murya take faɗin."karka sa nai ta jira ka je kuma ba ka kira ba.
"Insha Allah zan kira. Da haka ya katse wayar kai tsaye master bedroom ɗinsa ya wuce yana rage kayan jikinsa. A hankali ta aje ƙaramin tray ɗin da ta riƙo akan center table ɗin dake cikin parlorn
kai tsaye bedroom ɗinsa ta nufa tana buɗe kofar tayi ido huɗu da AB just his short and singlet da sauri Aydah ta nufesa gaba ki ɗaya AB ya ruɗe ganin Aydah ta samesa a haka ba zai iya tuna lokaci na karshe da ta gansa a haka ba.
A tsawace yake faɗin "me na faɗa maki kafin ki shigowa mutum a ɗaki Aydah?" tsayawa tayi cak.! tana kallon yanayin yayan nata jin taki magana yasa yace ta fita ta jirasa a parlor juyawa kawai tayi ta fita tamkar za tayi kuka ganin irin tsawar da ya yi mata ita ta ma manta da bayaso a rika shigar masa ɗaki babu sallama. Zama ya yi gefen gado ya dafe kansa da yake jin yana masa ciwo har lokacin yafi minti biyar a haka kafin ya tashi dakyar ya nufi cikin closet nasa jallabiyya ya ciro marar nauyi ya saka ajikinsa kai tsaye parlorn ya nufa har lokacin fuskar Aydah a haɗe tamkar ba a taɓa halittar murmushi acikin fuskarta ba. Zama ya yi yana kallon yadda ta wani folding hands ɗinta akan ƙirjinta ta wani kwabe baki da alamar kiris take jira ta fashe masa da kuka. Ya zauna gafda ita ya riƙo hannunta murya kasa-kasa yake faɗin."waya tabamin baby ne.?" cike da tabara ta nunasa da hannunta wanda yasa ya ware mata manyan fararen idanunsa, wanda yasa dole sai da ta saki murmushi har kumatunta suka lotsa ya dauki coffee ɗinsa yana sha a hankali batare da ya taɓa wainar kwan dake cikin plate ba. "Yayanmu baka ci wainar kwan ba." Ya ɗan kalleta kafin yace bana jin daɗin cikina barni kawai nasha coffee ɗin har kusan 9 Aydah na bangaren AB sai da yaga ta fara masa gyangyadi yace ta tashi ta je ta kwanta ta haɗa kayan ta koma cikin gida Mami sai bin ta kawai take da kallo bata dai ce komai ba ganin ta nufi stairs yasa Mami tace "abincin fa?" Ta murza ido tana faɗin."Mami bacci nake ji na koshi" Da haka Mami ta dauke kanta dama Sadiya tunda taga Aydah ta shigo Parlon ta ji wani abu ya tsaya mata a wuya, har aranta ta fara tsanar alaƙar Aydah da Yaya Abba.
Tasan idan sune suka je part ɗinsa da yanzu ya korosu yace su tafi zai yi aiki. Amma Aydah sai tayi kusan awa biyu a part ɗinsa ba zai ce ta tashi ta tafi ba. Ganin dai babu kowa a parlorn Sadiya ta yi gyaran murya tana kallon Mami zuciyarta na ɗan bugawa ta saukar da kanta kasa dan bata san yadda Mami zata karbi zancenta ba
"Mami dama maganar aurena da yaya Abba ne dan Allah Mami, ina son ki kara bai wa Daddy, haƙuri akan abunda ya faru wallahi nayi nadama kuma hakan ba zai ƙara faruwa ba.
Na yarda na haƙura yaya Abba ya mayar dani ɗakina mu yi zaman aure na har abada."! Sadiya ta ƙarasa magana kanta a ƙasa Mami kallon Sadiya kawai take. Tamkar mai son gano abunda ke cikin zuciyarta wani murmushin takaici Mami, ta yi tana faɗin."To Allah yasa Daddy naku ya yarda.
Cike da zallar farin ciki Sadiya ke faɗin."zai ma yarda Mami kinga zai dawo yana amsa gaisuwata daidai kamar kowa Mami.
Da haka Sadiya tabar Parlon zuwa ɗakinta cike da tsananin farin ciki tamkar an dauke mata dukkan damuwarta Tasan idan Daddy yaji wannan zancen zai yi matuƙar farin ciki da haka ,sai murmushi take ita ɗaya a ɗaki tamkar wata wacce ta zauce ba ƙaramar rahama Allah yake sonta da ita ba da ta dawo hankalinta lokaci ɗaya. Samun miji irin yaya Abba a wannan zamanin ai sai an tuno har ta hango yadda yayanata zai rika sarrafata akan gadon aurensu yana kasheta da salon soyayyarsa.
Mami tafi minti biyar zaune a Parlon na Daddy sai ta ji damuwarta ta ragu saboda yadda Sadiya ta zo mata da wannan zance kamar dai tasan abunda suke shirya wa, ta rasa ta inda za ta fara yi masa bayani, cike da karfin hali ta dubi Daddy ta ce "Alhaji ɗazun nan Sadiya ta sameni da wani zance ta faɗamin na ƙara baka haƙuri kuma tana neman alfarmar a mayar da aurenta da Abba....."!
Wani tsinannen kallo Daddy ya rika yimata cike da takaici yake faɗin."mariya!" jin yadda ya kira sunanta har tsakiyar kanta kafin yace."Aure ya haramta tsakanin Sadiya da Abba har abada kin manta ƙanwarta zai aure yanzu. Ai tayi wasa da damarta har abada kuma damar ta ri ga tafi ta barta karma na kara jin wannan zancen.
Duk yadda Mami ta so fahimtar da Daddy kin saurareta ya yi kamar ma rigima yaso zamar masu acikin daren. cike da zafin zuciya Mami ta baro bangaren na Daddy ta koma nata




#Love story 2023/2024
#jeeddah Aliyu
#Asmy

17 / 80