Author : EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category : KDP NOVELS
ba, sai dai babu mai karfin gwiwar da zai iya tunkararsa da maganar sai dai su koma gefe suna ƙanana maganganu.
Kilishi ta kammala kallon video da ɗaya daga cikin amintattun bayinta ya taɓa yi wa Ciroma da Galadima a gidan gona wanda suka tsara kashe sarki Mahmood na Uku, daman Kilishi ta adana wannan video ne domin zuwan irin wannan rana, sai gashi yau zai mata amfani tana kammala kallo tasaki shu'umin murmushi tare da yada ganinta akan fuskar jakadiya tana faɗin "Jakadiya lokaci ya yi da za ki fallasa wannan sirri na Ciroma da Galadima baki ɗayansu za su ƙare a maƙarma da zarar mu yi nasarar zuwansu can zan nemi wasu daga cikin amintattun bayina su je har can gidan kaso ɗin su kawar min da damuwata, domin mutuwar Ciroma shi ne kadai hanyar da rufafffen sirrina zai cigaba da zama a rufe, domin duk ranar da wani ko wata a masauratar nan yasan da cewa bani na haifi Ciroma ba, kashina ya bushe domin daga ni har ke da kika taimaka min a lokacin da na haihu 'yata bata zo da rai ba, cikin hukuncin ubangiji hidima Rahane ita ma a wannan daren kika sami labarin ita ma tana kan gwiwa (nakuda)bayan ta haihu sai jini ya buge ta, ta fita hayyancinta batare da tasan me ta haifa ba, wannan ne ya ba ki damar haɗa baki da mijinta hidimi Bawa ta hanya kwadaita masa dukiya mai tarin yawa da nuna masa da kika yi anan gaba dansa ne magajin masaurata, tsabar kwadayin hidimi Bawa yasa kamin hadima Rahane ta farfaɗo ya musanya mata, ɗanta da matatcciyar 'yata daga nan muka yi sanadin mutuwar hidimi Bawa domin mu rufa wannan sirri, haka zalika muka kawar da matarsa hadima Rahane domin dai wannan sirri ya cigaba da rufuwa, a yau kuma za mu bi wata hanya don kawar da Ciroma amfaninsa ya ƙare a halin yanzu na haife 'ya'ya maza, yanzu Ahmadu ne kaɗai magajin masaurata domin zuri'ar mai Babban ɗaki rankatakaf ɗinsu ba za su sake yin sarauta a Kudu ba. A dalilin abun kunyar da Aliyu ya janyo musu, hakikanin gaskiya Jakadiya mun sha doguwar tafiya kamin cikar burinmu lallai kisani idan har burina ya cika Ahmadu ya zama sarkin wannan daula tukuicin ki babba ne. Don haka ki yi maza ki je ki aiwatar da abun da na umarce ki.
"Allah ya taimake ki ya ƙara miki lafiya, uwargijiyata, uwa ga sarkin gobe.
Jakadiya ta faɗa tare da mikewa jikinta yana rawa ta fice daga masaurata, wata bakar van ce ta sha gaban jakadiya, wasu zaratan maza biyu ne suka fito daga van ɗin masu sanye da leather jacket fuskarsu lulluɓe da baƙin facemask, suka yi mata daukar amarya kamin ta yi wani yunkuri sun rufe mata baki da salatif, wani baƙin daji mai duhun bishiyoyi suka nufa da ita sai da suka yi mata dukan mutuwa kafin su tambaye ta ina wayar da Kilishi ta bata, anan take faɗa musu ta fadi sa'ili da suka dauko ta, ta ji sanda ta faɗo daga cikin zaninta. Wannan furuncin na ta ya fusata ɗaya daga cikinsu ya buga kanta a jikin motar nan take kanta ya fashe daga nan bata sake motsawa ba. Da suka fahimci ta mutu duk sai hankalinsu ya tashi gashi basu karɓi wayar ba, ta mutu basu san me za su ce da Ciroma ba. Daga baya suka yanke shawarar a tsakaninsu su nemo wata waya su kai masa a matsayin wacce suka karɓa hannun jakadiya, haka kuwa aka yi Ciroma ya yi murmushin mugunta yana hasaso irin mummunan kisan gillar da zai yi wa Kilishi.
*SOFTCARE PRIVATE HOSPITAL*
Aliyu na Uku zaune a gaban gadon da Maysun take kwace magashiyam! Tsananin tausayinta ya gama cika sa, musamman idan ya tuna da wa'adin da ya rage mata a duniya duk da yana gani, faɗa ce kawai irin na likitoci ba fadar Ubangiji ba. A duk sanda ya tuna da haka sai ya ji hankalinsa ya ɗan kwanta, duk da yana cikin jimamin ciwon Maysun hakan bai hana masa zurfafa tunaninsa ba Idan har da gaske Azhar ya mutu a labarin da Daddy ya basa miyasa ko burbushin gawarsa ba a gani ba, ya kamata ace koda tokar sa ne sun gani don duk yadda mutum ya kone dole za a ga wata alama tasa, wani irin bugawa zuciyarsa ta yi bai san sanda ya miƙe tsaye ba jikinsa yana rawa idan har hasashe sa ya tabbata gaskiya to tabbas kuwa Azhar ɗinsa yana raye.
Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.
[2/11, 2:28 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye.
103.
Da taimakon Hanne Mami ta kammala girka abinci da za ta kai hospital, tun sanda ta ji irin cutar dake damun Maysun ta fara jin nadamar abubuwan da ta aikata. Yanzu kam ta gama fahimtar rayuwa dan adam ba a baki komai take ba, har kwatanta kanta take yi da Maysun da ita ce ke dauke da wannan ciwo ba lallai bane ta sami tausayawar mijinta kwatakwacin yarda Aliyu ke nunawa Maysun, saboda tasan a halin yanzu bata da kyakkyawan hali ko ɗaya wanda za a iya tausaya mata saboda shi. Wannan yasa tun sanda suka baro asibiti jikinta ya yi sanyi ta ji nadama ta kamata. Har ta kudurta aranta za ta roke Daddy gafara ita rayuwa gajeriya ce idan babu cuta akwai mutuwa wacce za ta iya ɗaukar mutum a kowanne lokaci da wannan tunanin Mami ta kammala arranging abincin da za ta tafi dashi a food basket kana ta nufi bangaren Daddy jikinta a sanyayye ta tura ƙofa. Daddy ta gani tallaɓe da kamatunsa ya ya zurfi a tunani, bayan ta gama ƙare masa kallo ta zauna kusa da ƙugunsa tana jin ita ce silar shigar mutane da dama a cikin damuwa da bata yi abun da ta yi ba da wata kila har yanzu Abba yana raye sosai da sosai take tuhumar kanta tare da ba wa kanta laifi ta kuma jefa kanta a matsayin mai azababben son zuciya.
"Ka yi haƙuri Alh ka yafe min domin ni ce silar jefa ka cikin wannan yanayi, ga kuma iyayen Abba da nake ji ta dalilina suke acikin wannan matsanancin hali. Hakika ni bana cikin jerin mutane nagari, ni kaina Alh ina mamaki ta yarda na bari shaitan ya yi wasa da imanina bansan miyasa na juye daga Mariya ta mai haƙuri da takwalli mai son farin cikin iyalinta? Na tuba Alh wallahi na yi nadama Dan Allah ka yafe min ba don halina ba.
Mami ta ƙarashe magana tare da sakkowa ƙasa ta zube guiwayoyinta ƙasa, sosai mamakin sauyawarta lokaci ɗaya ya lulluɓe Daddy, sai kuma ya tuna Allah ne mai shiryarda wanda yaso a lokaci da yaso to wannan ba abun mamaki bane daga cikin kudirar ta ubangiji. Tunawa da haka da ya yi yasa ya ɗago kafanɗun Mami ya mayarda da ita kan kujera tare da kama hannunta faɗin "Al-hamdullilah! Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Ubangiji talikai mahaliccin sammai bakwai, da ya bani aron rai da numfashi da har naga wannan ranar da Mariya kika yi nadama kana kika tare da da fahimtar kurakuranki. Hakika shaitan ya yi amfani da rauninki na mace ya yi wancagali da imaninki sai gashi cikin hukunci Ubangiji kin yi yaƙi da wannan zuciyar taki da shaitan ya yi kane-kane acikinta. Na yafe miki Mariya daman tun can asali na kudurta araina na yafe miki, a yanzu ma na kara faɗa na yafe miki Mariya duniya da lahira. Je kika kira min Aydah yana da kyau nai mata bayani kamin mu tafi asibiti ɗin.
Mami ta amsa tare da miƙewa ta fice koda ta shigo ɓangarenta Aydah tana zaune a falon ƙasa goye da baby Noor, mami ta isar da sakon Daddy tare suka nufi ɓangaren Daddy still yana zaune inda Mami ta barshi. Cikin natsuwa ya shiga ba wa Aydah da Mami haɗuwarsa da Aliyu na uku a garin London har zuwa yadda AB ya zo hannunsa, lokaci da Aydah ta ji irin cutar da mahaifiyar AB ke ɗauke da ita sai ta ji wani irin rauni a zuciyata har ta kasa riƙe kanta ta dinga zubda hawaye hakikanin gaskiya ta tausayawa Maysun yadda ta ji ta ƙwallafa ranta akan Ab sai gashi Allah ya yi ikonsa ba zasu haɗu ba. Bayan sallar isha Daddy da Mami tare da Aydah suka nufi software koda suka isa Maysun ta farfaɗo har Aliyu na uku ya bata labarin Baby Noor ta kagara su zo ta ganta, suna shiga ɗakin da take Aydah ta yi arba da fuskar Maysun mai kamanceceniya da ta yayanta bata kara rudewa ba sai da taga Aliyu na Uku koman sa sak na AB, cike da farin ciki Maysun ta karbi Baby Noor a hannun Aydah ta rungumeta tsam a ƙirjinta tana jin ɗumin jikinta, ji take yi tamkar Ab ɗin ne ta rungume. Mutuwar Ab ta dawowa Aydah sabuwa sosai ta ci kuka sai da Maysun ta gama shasshafa baby Noor kana ta maida ganinta kan Aydah ta ya fito ta da hannu, hawayen idanun Aydah sun kasa tsayawa da sauri ta je ta rungumeta dukkansu biyu suka fashe da kuka, sun dau tsawon lokaci suna koke-kokensu daga bisani suka haƙura, Daddy da Aliyu na Uku suka fita hakan ne yasa Maysun ta umarci Aydah da ta bata labari Ab halayarsa abubuwa da yake so da wanda bayaso, Aydah tana kuka tana faɗa masa sai ya zamana ita tana kuka Aydah tana yi Mami dake zaune a gefe tana kallonsu tare da tayasu kukan. Cikin ɗan lokaci ƙanƙani Aydah da Maysun suka yi bala'in sabo tamkar sun shekara da sanin juna daga ƙarshe ma anan asibiti Daddy da Mami suka baro Aydah za ta kwana tare da Maysun Mami ta dawo gida da baby Noor Aliyu kuma ya nufi hotel ɗin da suka y masaukinsu. Tun haihuwar baby Noor karo na farko da Mami ta kula da ita har ta kwana ɗaki ɗaya da ita nan da nan kaunar yarinya ya sami muhalli a zuciyata, sai yanzu ta daina ganin laifin yaranta da maigidanta yadda suke bala'in son Baby Noor ashe bala'in shiga rai ne da ita, a wasu lokuta har haushi mutane take ji yadda suke nuna mata ƙauna yanzu haka kusan sai Abdulkarim ya zo duba ta kuma sai ya ɓata dogon lokaci yana mata wasa, wani lokaci ma har ya fita yake yi da ita ga yawan kyaututtuka da take samu daga wurin abokan Ab, ga 'yan uwan margayiya Rumaisah koda yaushe cikin zarya zuwa ganinta suke yi hatta da yayan Rumaisah Safwan da baya Nigeria amma kullum cikin kiran vid call yake yi Aydah ta haɗa shi da ita ya kan bata lokaci yana kallonta kamin ya kashe wayarsa. A takaice baby Noor tana da farin jini na musamman kowa sonta yake yi babu ma kamar Sadiya da duk wani kudinta ga shopping ɗin kayayyakin Baby Noor suke ƙarewa.
*MASAURATAR KUDU*
Yaran Ciroma da suka tabbatar da jakadiya ta mutu sai suka haƙa rami mai zurfin gaske suka binneta a dokar daji, daga nan suka dawo gidan gonar Ciroma suna jiran ƙarasowarsa suka nemi waya fairly used siya suka cewa Ciroma ita ce wayar da suka karbe a hannun Jakadiya, kuma sun goge duk wani vid dake ciki saboda haka ya kwantar da hankalinsa don kuwa matsalarsa ta zo. Kuɗi masu yawan gaske ya basu kana ya koma masaurata, can cikin dare ya yi ɓanda kama ya fita zuwa bangaren Kilishi, cikin kwarewa ya dinga sanɗa har ya isa ɗakinta ta yi kwance rashe-rashe tana sharar bacci duk tana cikin damuwar rashin dawowar Jakadiya amma hakan bai hana mata baccin ba.Ciroma ya yi tsaye yana kare mata kallo yana saki murmushin mugunta, sannu a hankali ya hau gadon Kilishi ya kai hannunsa ya dalla mata mugun mari, can cikin bacci Kilishi ta ji saukar mari a kumatunta ta zabura ta tashi zaune tana zare ido tana tozali da Ciroma wanda ya murtuƙe fuska hanjin cikinta ya hartsune, tsoro ya mamaye ta ko ba a faɗa mata ba ta gama wassafa abun da ya kawo sa shiyasa tun kamin ya kai da aikwatar da manufarsa akanta ta fara magiya "Dan Allah ka yi haƙuri Ciroma naci darajar rainon ka da nayi koda ban kasance wacce ta kawo ka duniya ba na ci darajar kula da kai da nayi har ka girma, na ba ka gata wanda ni ce sanadiyyar zamanka sarkin kudu.
"Haka zalika ke ce sanadiyar mutuwar iyayena ba, kuma kike ƙoƙarin fallasa sirrina, to amma kamin ki kai da yin haka ni ɗin nan zan aika ki garin da kika aika iyayena Kilishi.
"A'ah! Ciro.....
Kamin ta karasa ya cafke wuyanta ya danne ta da dukkan ƙarfinsa tun tana ƙoƙarin kwatar kanta har ƙarfin ta ya ƙare abun ka da jikin girma Ciroma bai sake ta ba har sai da ya tabbatar da cewa ta mutu, kana ya gyara mata kwanciyarta har da rufe ta da duvet ta yadda ya shigo cikin sanɗa haka ya fice zuciyarsa wasai yana gani ya kawar da damuwarsa.
*****
Tun sanda Anaal ta shiga ɗakin da AB yake bata motsa ba ko nan da can tana kwance a ƙirjinsa, sai da aka yi kiran sallar magarib sannan ta tashi ta je ta yi alwala ta gabatar da sallah rabin addu'arta duk akan ab ne ta kagara taga ya motsa koda ɗan yatsansa ne, a yanzu wata irin ƙaunarsa Allah subhanahu wata'ala ya dasa mata, tana so ya tashi su haɗa kan alhalin su domin duk abun da ke faruwa a masaurata tasani ta hanyar twins da su kaɗai take waya su ma ɗin sai in ta ce ta kira su, tana sallama sallar isha ta miƙe ta dauko ruwan zam-zam da koda yaushe take addu'a acikinsu ta bin jikin Ab ta shafa masa yau bayan ta kammala shafa masa ta kamo Alqur'ani dake cikin wayarta, ta shiga karanta masa a hankali tana kyautata yaƙini ta hanyar karatun Alkur'ani da take masa wata rana zai farfaɗo daga doguwar suman da ya shiga. Sannu a hankali AB yake motsa hannunsa mai ɗauke da drip, tun yanayi a hankali har ya shiga motsawa da karfi na'urar da ke nuna bugawar zuciyarsa ta shiga ƙara wanda hakan yasa Anaal tai sauri ta ɗago idanunta ta sauke su akansa sai taga idanunsa suna marmadi alamar yana so buɗe su. Cikin kidima ta miƙe tsaye tun idanunsa suna rawa-rawa har ya buɗe su kaɗan sai kuma ya sake rufe su cikin sauri wanda hakan yasa sautin ƙarar na'urar ya ƙara yawa, da gudu Anaal ta nufi parlor tana kwallawa Dr Maheer kira da sauri ya nufo ta dawowarsa daga kenan masallaci Anaal tana kiransa bugun zuciyarsa Dr Maheer ya fara dubawa, da sauri ya ja wata allura a syringe ya yi masa a hannunsa ya ɗauki tsawon lokaci yana duba sa ƙafin ya ja wani kalan numfashi ya ciro handkerchief daga gaban aljihunsa ya goge gumin da yake ta faman tsatsafo masa a goshi. Ya juya kalli Anaal yaga sai zarar idanuwa take yi jikinta yana rawa wani irin tausayinta ya dirar masa bayaso ya faɗa mata abun da zai ɗaga mata hankali domin yadda yaga tana zarar idanu dole ya ji shakku faɗa mata.
Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.
[2/11, 2:29 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye.
104.
Wasu busassu miyau Anaal ta haɗiye jikinta duk yai sanyi tana fargabar abun da za ta tambaya da kuma kalar amsar da Dr Maheer zai bata duk da irin fargabar da take ciki daurewa ta yi ta ce "me ke faruwa Dr Maheer me ya sami yayana?"
Ajiyar zuciya Dr Maheer ya yi cikin sanyin muryarsa mai matuƙar daɗi ya furta "Bugun zuciyarsa ya ragu da kashi takwas bisa goma idan har ya kai 24hours bugun zuciyar nasa bai daidaita ba I'm sorry to say za mu iya rasa shi.
"Innalillahi wa'inna illahim raji'un! Dr Maheer please ka ceci rayuwar ɗan uwana dan Allah kada ka bari ya mutu shi kaɗai ne ɗa namiji a wurin Abbuna shi ɗin hasken idaniyar mahaifina ne cigaba da rayuwarsa shi ne zai dawo da farin ciki da walwala ahalina, mutuwarsa kuwa za ta iya kara dagular da komai.
"Anaal ki cigaba da masa addu'a rayuwa da mutuwa duk suna hannun Allah, iyakacin mu kula da majiyaci idan kwanakin sa sun kare likita bai isa ya basa wata rayuwa ba.
Wani irin kuka Anaal ta fashe dashi tare da kama hannun Dr Maheer, cikin dushewar murya ta ce "likita ba ubangiji bane amma ubangiji ne ya basa baiwa da fikra ceto rayukan mutane idan suna cikin hali irin na jinya, jikina yana bani za ka iya Dr Maheer kada ka bari gwarin gwiwa da nake dashi akanka ya tafi a wofi idan har ka yi nasarar ceto rayuwar yayana na yi ma alƙawari zan aure ka.
"Me kika ce?"
Dr Maheer ya faɗa yana zaro ido domin abun da ya daɗe yana jiran ya fito daga bakinta ne, yau ta furta masa.
"Yes! Maheer zan aure ka zan rayuwa da kai za ka zama uban 'yayana muddin dai za ka ceci rayuwar ɗan uwana.
Sanyayyen murmushi Dr Maheer ya yi wani irin gwari gwiwa ya dinga shigarsa da sauri ya nufi Ab ya shiga baje duk wata kwarewar sa akansa, yana kuma gani nasara dan yanzu Ab sosai yake responding treatment ɗin, saɓani can baya da sai ya sha wuya kamin ya yi respond. Ga yadda Dr Maheer ke hasashe idan har ya cigaba a haka zuwa gobe zai iya tashi.
*******
Aydah ta fito daga bathroom riƙe da kafaɗar Maysun ta taimaka mata ne ta yi wanka, da yake har yanzu babu kuzari a jikinta komai Aydah ke mata zaunar da ita Aydah ta yi akan plastic rubber chair, kana ta jawo food basket ta zuba mata kunun gyaɗa da Mami ta aiko direba ya kawo musu breakfast, kamin zuwa anjima ita ma ta shigo. Aliyu na uku ne ya turo ƙofa ya shigo cikin shigarsa ta babbar riga ash color ɗin shadda wacce ta ji aiki da dark ash ɗin