Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   33 / 80

96K to 99K   out of 237.2K words

gaba ɗaya duniya ta yi masa zafi komai ya fice masa arai. Damuwa tana neman ta kassara masa rayuwa. Kusa da ita ya zauna cikin taushin muryarsa wacce ko da yaushe take a sanyayye da matukar wahala ka ji AB ya yi magana da kaushin murya mutane ne shi mai sanyi hali da rashin so hayaniya. "Ki yi hakuri baby ki daina kuka kada kanki ya yi ciwo.
"Yaya Abba meyasa Mami za ta tsaneka me ka yi mata dan Allah?"
"Baby saboda Daddy ya ƙi amincewa da bukatarsu ita da Sadiya?"
"Wannan wacce irin bukata ce wacce za ta juyarda kauna da Mami take maka cikin ƙanƙani lokaci ta koma zazzafar kiyayya irin wannan? Dan Allah yaya Abba idan bai sabawa addini Islama ba ka yi musu abunda su keso ko hakan zai dawo da irin ƙaunar da Mami take maka.
"Abunda suke so ikonsa baya hannuna Aydah yana hannun Daddy kuma ni mai biyayya ne ga dukka abunda ya umarci ni.
Kwata-kwata Aydah bata fahimci idan kurman allon nasa ya dosa ba, sai kawai ta ce "Duk ranar da na je gida zan yiwa Daddy magana yasaka ka yi musu abunda suke so don ni gaskiya ba zan iya cigaba da jure gani Mami tana fushi da kai ba.
Murmushin gefen baki ya yi tare da jan karan hancinta tasa ihun shagwaɓa ya tashi ya je ya dauko musu takeaway ɗin da ya yo musu daga Gusto restaurant suna cikin ci abinci Rumaisa ta kira wayarsa nan take Aydah taga fuskarsa ta cika da murmushi ya dauki kiran ya tsallake abinci ya haura sama yabarta da plate ɗin abinci tana jujjuya spoon, wani kololon abu ta ji ya tokare mata maƙoshi ta kasa cigaba da ci abincinta rai ɓace ta ture plate ɗin, ita daman can ta tsani Rumaisa madawaki tun kafin tasan AB ba yayanta na jini bane. Bata ƙaunar Rumaisa ko kaɗan.
*MASARAUTAR KUDU*
(Bangaren Kilishi)
Ciroma ne ya shigo sai faman saɓa babbar rigarsa yake, yana zuwa ya zube a gaban mahaifiyar tasa "Barka da hutawa umma.
Kilishi ta yi mishi kuri da idanunta tana karanta yanayinsa cikin sarƙewar lafazi ya sake furta.
"Allah ya taimake ki gani hidima Jumma ta faɗamin kina so ganawa dani Allah yasa dai lafiya?"
Ya faɗi haka ne a dalilin yadda yaga fuskar Kilishi a haɗe sai faman karkaɗa ƙafa take lokaci zuwa lokaci tana furzar iska daga bakinta alama ce dake nuni da ranta a ɓace yake.
"Ciroma tun jiya na aika hadimi kogiji ya kira min kai kuma ya isar maka da saƙona kuma har ka ce dashi ya faɗamin za ka zo amman ba ka zo ba shin ko zan iya sani dalilinka na ƙin amsa kirana? Yaushe na zama abokiyar wasanka Ciroma?"
Zufa ce taketa ketowa Ciroma a sassan jikinsa zuciyarsa ta cika da fargaba ko Kilishi ta sami labari akan plan ɗinsa ne.
"Ciroma!!!
Ta kira sunansa a tsawace wadda har sai da Ciroma ya zabura sai kuma ya tuna matsoraci baya zama gwani idan har yana so hakarsa ta cimma ruwa to kuwa sai ya fatattake tsoro daga zuciyarsa sai ya zama jajirtaccen namiji.
"Na'am Ranki shi dade.
"Ka faɗamin hakikanin gaskiya inda kake zuwa kwana?"
"Allah ya ƙara miki lafiya ai ni sabgogina yawa ne dasu, saboda haka ko'ina ma zan iya zuwa.
Ciroma ya yi magana kansa tsaye.
"Ina so ka dakatar da duk wani shirinka Ciroma domin bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane. Kada ka kunno wutar da ba kada ruwan kashe ta.
Wani abu Ciroma ya ji ya tsarga masa rashin gaskiyar ya bayyana kiri-kiri akan fuskarsa, sai kawai ya dake tare da gyara zamansa yana tankwasa yatsun ƙafarsa ta dama sai sauti suke fitarwa ƙas!ƙas! Cikin sakakkiyar fuska ya ce "Ranka shi dade idan kika ji makaho ya ce ayi wasa 'yar jifa wallahi ya taka dutse ne Allah ya t miki nisan kwana sai nake gani kamar ruwa ne suka ƙarewa ɗan kada, kuma ni sai nake gani ranki shi dade kowa ya iya allonsa ya wanke ba laifi bane.
Wani yawu mai bala'in ɗaci Kilishi ta haɗiye tana kallon Ciroma da fusatattun idanuwanta, kamin ta ce "Umarnin nake ba ka Ciroma a matsayina, na mahaifiyarka ka watsar da kudirinka akan karagar mulkin kudu ka mayar da hankalinka akan mulkar birnin kudu.
"Ko zan iya sani dalili?".
"Dalili bai wuce mulkin kudu bai dace da kai ba.
Wata irin dariyar shakiyanci Ciroma ya sheƙe da ita sai da ya yi mai isarsa kafin ya turɓune fuska yana kallon Kilishi a ɗage tamkar ba mahaifiyarsa ba.






#Love story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#kurman Allo






Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/29/2023, 2:19 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU




*AREWABOOK*: Jeddah 3256


#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels




044.


"Baby!hayati!" Duk ni ɗaya wannan sunayen masu tsada haka?."Ya faɗa wearing a big smile shimfiɗe akan kyakkyawar fuskarsa duk da tarin damuwar dake lullube akasan zuciyarsa. bai san miyasa duk lokacin da yaji muryar Rumaisa wani farin ciki da nishadi ke saukar masa."farin cikin ki ya yi yawa,har ana jin haka cikin muryarki ki cigaba da farin ciki."yar kankanuwar dariya ta saki cikin muryar nishadi ta ce."Ina farin ciki Habibi farin ciki da nake fatar ya dore har izuwa ƙarshen rayuwata.
"Nima ina fatar haka habibty domin kuwa farin cikinki shine nawa.
"Yanzu dai albishir ka?"sai da ya juya eyes ɗinsa tamkar tana ganinsa kafin yace goro fari sol.
"Idan na faɗa me zaka bani a matsayin goro."komai ma zan baki,
"No ban yarda ba ka faɗamin me za ka bani.
Yasan jan ran Rumaisa suna iya kai dare bata faɗa masa ba.
"Komai kike so zan baki.
"ka tabbata ?"
Wannan karon ta faɗa da muryar mai shauki da nishadi.
"Rumaisa mana.!"
Yadda ya kira sunanta yasa tace "owk!Daddy yana nemanka, ya amince da aurenmu a karo na biyu hayatee.!"sai da y aji bugun zuciyarsa ya tsaya na kusan sakan biyu kafin zuciyar tasa ta cigaba da bugawa da wani irin karfi,jin ya yi shiru nasa yasa Rumaisa faɗin "Da gaske nake habeebi !"dan Allah ka zo anjima mu yi amfani da damar mu,babu Abunda Daddy, zai yi maka asalima haƙuri zai baka."zan zo Rumaisa. Ya faɗa murya can ƙasan maƙoshi sallama ya yi mata yana sauke wayar akan kunnensa zaunawa ya yi a gefen bed bai san me yake ji ba a labarin da Rumaisa ta zo masa dashi ba in har da gaske take Alh Ballo Madawaki ya amince zai karbesa a matsayin suruki a karo na biyu zai auri Rumaisa to kuwa ya fi kowa sa'a a duniya farin ciki yake ji da dukkan zuciyarsa haka zai basa kariya sosai na zamansa da Aydah a gida daya,to amman kuma Daddynsa yake ji wannan lokacin bai san taya zai dauki wannan al'amarin ba.
Sai da ya yi sallar magarib ya yi wanka cikin dakakkiyyar shadda ruwan kasa wacce tayi mugun karbarsa sai kamshin turare yake tamkar wanda yayi wankansu ajikinsa. Dakin Aydah ya leka kwance ya sameta tayi ruf da ciki jin karar buɗe kofar da kuma kamshin turarensa da ya rika ziyartar hancinta yasa ta maida kallonta kan kofar,cike da izzarsa ya ƙaraso cikin ɗakin nata suna haɗa ido ta wani haɗe rai ta turo baki tana juyar da kanta gefe ɗaya gefen bed ya zauna dai- dai wurin kanta."Baby har yanzu wai fushin ba'a gama ba ?"ni kawai ka ficemin daga daki yayanmu.
Ta faɗa sounding so very childishness, "To tashi sai na rarrasheki. Ba musu ta mike zaune ta wani harɗe hannunta akan kirjinta wayarsa ya daga ya saita camera yana daukarta snap."kukan tabara ta fashe masa dashi da sauri ya jawota jikinsa yana dan buga bayanta alamar rarrashi, lamo tayi tana shaƙar kamshin dake tashi acikin jikinsa dagota ya yi yasa yatsansa yana goge hawayen dake zubo mata."wai ke kuka baya miki wuya baby kin zama fa budurwa yanzun.
Lokaci ɗaya yanayinta ya canja ta tsani wannan kalmar ta budurwa."da sauri ya rufe bakinsa da ido yake bata haƙuri,ya mike tsaye ganin kiran Rumaisa na shigowa a wayarsa,kallonsa Aydah ke yi ya shafa kanta yana faɗin. zai je ya dawo yanzu tamkar zata yi kuka take faɗin."dan Allah ka je dani yayanmu tsoro nake ji ni kaɗai za ka bari dan Allah."ta faɗa tana wani fashe masa da wani kukan shagwaɓa.
"oya tashi ki shirya minti biyar na ba ki ina jiranki a parlor.
Da sauri ta sauka daga kan bed shi kuma ya juya yabar cikin ɗakin
zama ya yi a parlor mintunan biyar da ya bata basu idar da cika ba ta fito cikin lack Indonesiya Abaya,mai maballai ajikinta babu komai cikin fuskarta sai man bakin da ta shafawa lebunanta sai kyalli suke sai veil ɗin abayan da tayi rolling kanta dashi .
Kallonta kawai Abba yake yana kissima abubuwa da dama akanta har ta karaso gabansa ganin yadda yake kallonta yasa ta shiga juyi agabansa
tamkar yadda take masa a koda yaushe idan ta yi kwaliyya yana a wuri,yayanmu na yi kyau miƙewa ya yi tsaye ya fara tafiya da sauri ta cimmasa suka jera tana faɗin."Yayanmu B
bakace nayi kyau ba."kinyi kyau baby.!"
Tare suka jera har cikin parking lot ya danna car key tun kafin ya saka hannunsa ajikin handling ɗin motar Aydah ta rigasa ita ta buɗe masa motar kusan a tare suka saki murmushi sai da ya shiga tayi salute agabansa tamkar wata soja harararta yayi bata san lokacin da ta saki dariya ba da sauri ta zagaya frontseat ta buɗe ta shige haka ya ja motar maigadi ya wangale masu gate a hanya Rumaisa ta ƙara kiran wayarsa wannan karon dauka ya yi ya saka a speaker."ina hanya Madam!
Addu'ar isowa lafiya ta yi masa kafin ta katse kiran. Sosai ya mayar da hankalinsa kan tuki Aydah ta kara gyara zamanta tun lokacin da taga sunan Rumaisa kan wayar mood ɗinta ya canja."Yayanmu ina zamu je ne?"
"Idan mun isa zaki gani ba yawo kike so ba?"To tadi zan je duk lokacin da na kai dole ki jirani."ta wani haɗe rai tana kallon sa take faɗin."To ni ka kaini gida.
Ko kallonta bai yi ba baran tana ta saka ran zai amsa. dai-dai gate ɗin gidansu Rumaisa ya tsaya, ya kirata a waya tace ya shigo horn ya yi maigadi ya buɗe gate ɗin,har ya yi parking motar bata kalli gefen da yake ba. Ba a jima ba Rumaisa ta fito tun daga nesa ta hango Rumaisa ta ƙara bata rai sosai ta tsani wannan Rumaisa ɗin,hannu tasa ta buɗe gefen da AB yake zaune sanye take da riga da skirt na atamfa wanda ɗinkin ya dace da jikinta sosai haka ya yi mata kyau ta yi light make up akan fuskarta daman Rumaida badai gayu da iya tsara make up ba. Kallonsa ta rika yi soyayyarsa tana bin dukkan jinin jikinta ,ta yi masa kyau fiye da yadda zai iya kwanatantawa. fitowa yayi daga motar murya kasa-kasa ta yadda ita kaɗai zata iya ji ya ce mata tayi kyau."wani wide smile ta saki tana juya idonta alamar jin dadi.
Kai tsaye bangaren da Aydah take ya nufa yaga bata da alamar fitowa, hannu yasa ya buɗe motar "fito.
Ya faɗa yana daure fuska kallonsa Rumaisa take ganin wadda ta fito daga motar yasa taji zuciyarta ta yi wani mummunan bugawa, da sauri ta mayar da idanunta wurin AB dashima hankalinsa ga baki ɗaya yana kan Rumaisar, karasowa Aydah tayi tamkar bata so haka ta gaisheda Rumaisa sai da ta haɗe wani abu da taji ya tsaya mata a wuya kafin ta amsawa Aydah da kyar. Dukansu uku babu wanda ya kara magana, haka suka nufi entrance ɗin shiga gidan,
duk yadda yaso ya haɗa ido da Rumaisa ta kasa basa damar hakan
Parlor farko ta tsaya ta ɗan kalli AB tace ya jirata nan bari ta karasa da Aydah cikin gida, lokaci ɗaya Aydah ta haɗe rai taja ta tsaya gafda AB tana kallon Rumaisa take faɗin."ita nan yayi mata , "ki bita" Abba ya faɗa cikin sanyin murya yana kallon yanayin Aydah yadda ya tsareta da ido yasa tabi bayan Rumaisa da saboda yadda take jin zuciyarta tana iya kwadawa Aydahn mari."ki zauna anan Bara na saka mai aiki ta kawo maki Ruwa.
Rumaisa ta faɗa babu wani annuri akan fuskarta ta juya tabar cikin parlor bata jima ba sai ga mai aiki a bayanta anan kan rug ta aje mata madaidaicin tray da ta shigo dashi
har kuma lokacin Aydah tana tsaye taki zama. Batareda Rumaisa ta kara koda kallonta ba ta juya tabar cikin parlor, zaune ta samesa yana famar danna wayar hannunsa ɗan nesa dashi taje ta zauna, batareda ta yi magana ba har mai aiki ta shigo da tray a hannu ta aje agabansa."na tashi na tafi kenan ?"irin wannan tarbar zan samu a wurinki."
Ya fada yana kallonta daman kaman jira take cikin wata irin murya mai tattare da kishi take faɗin."Basai ka nuna min ka aureta ba ba sai ka nuna min matar ka bace nasan da wannan tun jiya da igiyoyin aurenta suka hau kanka.!"wannan ai cin fuska ne.
Ta ƙarasa maganar da karaya a muryarta runtse ido ya yi yana juya kalamanta aransa duk yadda zai yi mata bayani yasan bazata fahimta ba saboda kishin dake dawainiya da ita. "Ba dan na tozartaki na taho tare da Aydah ba, kin santa da tsoro hankalina bazai kwanta ba idan na barota ita kadai a gida.
"Saboda ita jariri ce.
Ta faɗa sounding so very jealousy "wai meyasa kike kishi da Aydah Rumaisa kin manta matsayinta a zuciyata ne kanwatace fa."
"Muje parlorn Daddy yana jiranka."
Ta faɗa tana kauda wancan zancen duk da yadda take jin zuciyarta na wani irin tafarfasa, har Parlor Alh Bello ta yi masa iso, kan rug AB ya zube yana gaisheda mahaifin Rumaisa da respect da fara'a ya amsa sa yana tambayarsa gida da kuma aikinsa.
AB ya amsa da Alhmdullahi! shiru ne ya biyo baya na kusan minti biyar kafin Alh Bello ya nisa cikin kararriyar murya ya soma baiwa AB haƙuri ya faɗa masa shi kansa bai san meyasa yayi irin wannan tunanin ba, a karo na biyu zai kara basa auren Rumaisa dan Allah kar yace a'ah haka kuma zai je har gida ya baiwa mahaifinsa haƙuri.
"Babu komai Daddy wallahi ban rike ka araina ba
"Ka fara magana da mahaifinka kafin naje da kaina dan sosai mahaifinka ya kullaceni kuma kaga ba'ayi rabuwar arziki ba."Insha Allahu Daddy."
AB ya dade sosai a Parlon Alh Bello Madawaki kamin ya koma wurin Rumaisa har yanzu babu wani sakin fuska atattare da ita kusan karfe tara ya yi mata sallama, har parlor ta samu Aydah hankalinta yana kan Tv amman gabaki ɗaya bata cikin yanayi mai daɗi ko kallon Rumaisa ba tayi ba ta fice daga parlorn, sai bayan da suka tafi ne Rumaisa ta dawo cikin gida, Ammi ta bita da kallo ta cire mayafin kanta ta aje a gefe. "Har ya tafi ne?"Ammi ta faɗa cike da kulawa tana kallon Rumaisa,"Eh! ya tafi."
Rumaisa ta bata amsa murya a sarke "Ya naga yanayinki ya canja me kuma ya faru?"
Cikin rawar murya Rumaisa ke faɗin. "Ammi kin san Bashir da shegiyar yarinyar nan yazo min."cike da mamaki Ammi ke faɗin wacce yarinya kenan?"cikin kunnar zucci Rumaisa ke faɗin."wacce aka yi masu aure.
"To ke me abun damuwa tunda yarinya ce kuma ya maki alkawarin bazai kulata ba. Cikin Rawar murya Rumaisa ta ce."Ammi tsoro nake ji baki ga yadda yake son yarinyar nan ba tun tana ƙarama wata irin shakuwace a tsakaninsu fa
"wuyarta dai ki shiga gidan da kin shiga ko kissa da kisisina za ki iya yi ki rabata da gidan rabuwa na har abada,shiru Rumaisa ta yi tana ya juya maganar mahaifiyarta aranta. kafin ta saki wani irin murmushi na gefen baki.
Ganin yanayinta na son rigima bai kulata ba,har suka karasa gida kowa ya nufi nasa ɗakin wanka ya yi ,ya fito da alwallah sallar ishaai ya yi kusan karfe goma har da rabi ya fito nasa dakyin ya leka ɗakin Aydah ya samu tayi bacci ƙara gyara mata kwanciyarta yayi tare da yi mata addu'a ya tofa mata ya ja mata duvet,samun kansa ya yi da jan gefen cheek ɗinta
Fitilar ɗakin ya kashe mata yabar mata (dim light)kasa ya sauka kitchen ya shiga ya haɗa coffee fitowa ya yi ya zauna a parlor yana sha a hankali acan kasyan ransa kuma ta yadda zai tunkari Daddy da maganar mahaifin Rumaisa kawai yake ta tunani bai san ta yadda Daddy zai dauki al'amarin ba har kusan 11 na dare yana a parlor kafin ya tashi ya kashe komai ya haura sama zuwa dakinsa,ya samu miss calls na Rumaisa har guda biyu, ya cire jallabiyyar jikinsa ya haye kan bed sai da yaja duvet ya rufe jikinsa kafin yayi dialling numberta dauka tayi da sallama a bakinta, ya faɗa mata ta kira yana down stairs yana shan coffee yanzu ya dawo ɗaki hirarsu ta masoya suka cigaba da yi cikin farin ciki kusan 12 yana ta hamma yace mata bacci yake ji "Bara na kira ka video call naga idonka.
"Ko kin kira ba dauka zan yi ba.
"Saboda me?".
"Babu riga ajikina.
'Yar siririyar dariya Rumaisa ta yi, tana faɗin "habeebi kunyarka ya yi yawa idan muka yi aure yaya za kayi."ki bari sai ranar da aka kawoki gidana za ki ga yadda zan yi.
Wannan karon ma dariya Rumaisa ta yi kafin ta sauke wayar.
*MASARAUTAR KUDU*
"Haba! Umma wannan wane irin son kaine? A matsayina na babban ɗa a gareki nine na dace ace ki yiwa yaƙi mulkar kudu ba ƙanina mai bi min ba idan kika yi haka tamkar kin fiffita Ahmadu akaina ne, alhali dukkan mu 'ya'yanki ne. Ina faɗa miki wannan maganar ne acikin tattausan kalami.
"Kai Ciroma! Ka fi kowa sani wacece ni bana magana biyu kuma duk abunda na hana dole akwai babban dalili da yasa ni yi hakan. Saboda haka ina daɗa gargaɗin ka da ka watsar da duk wani kudirinka ka dauke idonka daga masarautar kudu.
"Bantaɓa gani uwar

33 / 80