Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   42 / 80

123K to 126K   out of 237.2K words

ya amsa yana faɗin."muna asibiti ashe baka karasowa ba?"gaban Abba sai da yayi wata irin dokawa har ga Allah ya manta da Aydah tana kwance a asibiti mantawa yake ma da ita acikin rayuwarsa, dakyar ya haɗa kalmomin faɗawa Daddy nacewa gashi nan zuwa. "To kinji yana hanya."daddy ya faɗa yana kallon Aydah da ta koma ta kwanta bayan ya sauke wayar,lumshe ido tayi zuciyarta na wani irin bugawa samun kanta tayi da addu'ar Allah yasa yayan nata ya huce.bai taɓa fushi da ita irin wannan ba tana bala'in azabtuwa kamar da minti talatin sai ga AB ya bayyana cikin ɗakin da sallama a bakinsa har lokacin Daddy na tare da Aydah,tun kafin ta kallesa zuciyarta ke wani irin tsalle ƙamshin turarensa kurum da taji ya saukar mata da wata irin kasala.tsaye yayi a bakin kofar ya kasa shigowa Siyama tana gaishesa ta dauke kanta akansa, Daddy ya daga kai yana kallonsa da mamaki yake faɗin."ka karaso mana."tamkar wanda aka zarewa lakka ya nufi gadon da Aydah take kwance duk yadda yake jin zuciyarsa na rawa haka kafufunsa na son kasa daukarsa haka ya nufi gadon da Aydah ke kwance "mamana ki tashi ga yayan naki nan ya zo. Daddy,ya faɗa yana miƙewa tsaye yana barin wurin gadon yana baiwa AB wuri dakyar AB ya zauna kan bed ɗin yana jin kusancinsa da Aydah tamkar ana hura masa wuta a dukka sassan jikinsa nan take idanunsa suka fara juyewa suna zama wani kala tamkar ba nasa ba ,da sauri Aydah ta buɗe idonta ta riƙe masa hannu cikin rawar murya tace "Yayana!"tamkar wanda aka jonawa wayar lantarki haka yaji hannun nata kuma taki sakin hannun nasa,wayar Daddyy ce tayi kara da alamar kirana ne ya shigo masa ya fice daga room ɗin dan amsa kiran
da sauri ya fisge hannunta ya kuma mike tsaye yana bin ta da mugun kallo, daman daga shi sai ita ya rage a dakin,da sauri ta mike zaune hawaye har sun taru a idonta "kayi hakuri dan Allah Yayanmu na tuba nabi Allah na bika.
Ta faɗa cikin fashewa da kuka yana juyawa suka yi ido biyu da Mami da take tsaye a bakin ƙofa tana kallonsu, atsorace Mami ta karaso cikin ɗakin tana tambayarsa meya faru kuma.?"tsit Aydah tayi tana haɗe kukanta dan bata son Mami ta fahimci akwai matsala ita da yaya Abba,tasan wani sabon rikici ne za'a yi gara ta rufawa kanta asiri kar Mami ta hanata komawa gidan yayanta shima Abba kusan tunani ɗaya ne yayi da Aydah da sauri ya koma kan bed ya zauna ya Jawota gefensa yana tambayarta menene kuma abun Kuka?"duk da karfin hali kawai yake,tsaye Mami tayi tana kallon su zuciyarta na ɗan bugawa.
A daburce AB ke faɗin."na haɗa maki tea zaki sha?"da sauri Aydah ta daga kai tana jin wani irin farin ciki na lullube mata zuciya, a gaban Mami ya haɗa mata tea ya shiga bata da kansa duk da jin yake kamar ana zare masa rayuwa jin kusancinsu ,a haka Daddy ya dawo ɗakin ya samesa yana bata tea ita dai Mami saboda takaici ficewa tayi daga ɗakin.
Bayan fitar ta ta daga waya ta kira Hajiya Zeenah a rikice take faɗin ."wai yaushe maganin nan zai fara aiki akan Abba.?"
"kefa Hajiya mariya kin fiye gaggawa tunda malam dogo ya tabbatar mana komai zai tafi daidai ba sai mu zuba ido mugani ba in har Sadiya ta saka layar ga yadda aka umarce ta. Ajiyar zuciya Mami ta sauke tana faɗin."Sadiya lafiya lau ta saka ita kanta bata son tayi wani kuskuren da za'a samu tangarda.
"To shi kenan sai ki kwatar da hankalinki in sha Allah haƙar mu za ta cimma ruwa.
Nan take Aydah ta shanye tea Daddy sai tsokanarta yake Daddy ya fice daga asibitin ya koma gida aka bar Mami a wurin Aydah daman Siyama gida ta koma Daddy na fita ko minti biyar bai yi ba AB ya faɗawa Mami zai wuce sai zuwa anjima zai daso,ko kallon arziki bai samu daga Mami ba
da ido Aydah ta bisa har ya fice daga ɗakin nan take yanayin fuskar Aydah ya canja, komawa tayi ta kwanta
Bayan magrib aka sallami Aydah zuwa gida AB mane ya daukosu da motarsa mami ta bi ta haɗe rai tana faɗin.'can gida zai kaisu sai Aydah ta kwana biyu jikinta ya yi kyau kamin ta koma gidansa.
AB baiyi musu ba ya kai su can gida ko kaɗan Aydah bata ji daɗin wannan hukuncin da Mami,ta yanke ba har suka isa gida bata saki ranta ba kwanan ta biyu ta samu sauki sosai haka AB yana daurewa yazo kullum ya dubata sau biyu kar iyayen nasu suka fara fahimtar kamar da akwai matsala a tsakaninsu gashi sai shirye-shiryen bikin sa ake da Rumaisa, daga Mami har 'ya'yanta babu wanda ya san wainar da ake toyawa, dan har lokacin Daddy bai zauna dasu ya faɗa masu ba ,kwanan Aydah uku a gidan ana sauran kwana goma bikin Rumaisa da Abba, Daddy ya tarasu a falonsa bayan magrib har AB ya halarci taron daga nesa kawai Aydah ke hango yayan nata da yabi ya canja mata lokaci ɗaya, Sadiya sai wani shige masa take,Daddy ya saka Aydah ta buɗe taro da addu'a tayi yadda daddy ,ya umarce ta kafin Daddy ya buɗe baki ya fara yiwa kowa bayanin auren Abba da Rumaisa akan kowa yayi haƙuri ya ɗaukesa a matsayin ƙaddara daman Rumaisa tana cikin ƙaddarar Abba, Daddy yayi masu bayanin haduwarsu da mahaifin Rumaisa biki yanzun sauran kwana goma, babu wanda bai shiga shock ba,musamman Aydah da ta kafawa yayan nata ido nasiha mai ratsa jiki Daddy ya shiga yiwa Aydah wacce ta haɗe kai da gwiwa tana wani irin kuka mai sosa rai ,a mugun hasale Mami ta miƙe tsaye cikin daga murya da zafin rai take faɗin ''idan kuma Abba har ya amince zai auri wannan matsiyaciyar yarinyar da iyayenta suka wulakanta mu sai dai ya sakar masu 'ya domin shekarun Aydah ba su kai ayi mata kishiya ba. Baki buɗe daddy,ke kallon Mami rai a ɓace Daddy ya kalli Aydah da Abba yace su tashi su wuce gidansu ya sallamesu.Mami ta kalli Daddy cikin tsakiyar ido "babu fa inda yarinya ta zata je dashi kawai ya rubuta takardar saki ya bata.!"Aydah ta mike tsaye ta nufi kofa ko gabanta bata gani da nufi tabi bayan AB Mami ta wani fisgota tana faɗin "idan kika yadda kika bisa ki dauka bakida wata uwa a duniya Zulaiha na yadda ke shashasha ce kuma wawuya ina nemar maki hakkin ki shine zaki tozartani agabansa dan uwarki.!"hawaye na zuba a idon Aydah cikin rawar murya take faɗin "Mami zan bi mijina Allah ya ba shi damar ya auri macce ba daya ba ba biyu ba har huɗu kan me za'a hanasa?"zan bi mijina mami Allah ya huci zuciyarki ranar da kika huce zan dawo."ta faɗa wani kuka mai karya zuciya na kwace mata ta riga Abba ficewa daga Parlor, murmushi kurum Daddy yayi ya dauke kansa.
A mugun fusace Mami ta fice daga parlor na Daddy sai lokacin ma ta tuna da Sadiya gabanta na wani irin bugawa,ta nufi ɗakinta da sauri tana turawa ta ji sa a rufe ta shiga bugun kofar tana kiran sunanta,a lokacin Sadiya tana zube akan bed tana wani irin kuka mai sosa zuciya da ruhi gashinta ta rike taja da dukkan karfinta tana sakin wani irin ihu mai wani irin razanarwa ga jikinta dake wani irin rawa.so take kawai ta sha abun da zai kawar mata da hankalinta ,tana son ta jita cikin wata duniya ba irin wannan ba duk kalar bugun kofar da Mami keyi da irin magiyar da take yiwa Sadiya ta buɗe kofar dakinta ta yi biris da Mami. Jikin motarsa ya sameta ta kifa kanta jikin motar tana wani irin kuka kamar zata shede wani irin zafi take jin zuciyarta na yi mata da wani irin nauyi da kanta yayi mata,saboda zai auri Rumaisa shiyasa yake kakkauce mata yana wulaƙanta ta saboda rumaisa tana da abubuwan da zata basa ita kuma bata dasu ita ma macce ce lokaci zai zo da zata yi girman da yake bukata meyasa ba zai jira ba meyesa yayanta zai bari wata macce ta shiga tsakanins ,har suka isa gida kuka take kamar ranta zai fita shi dai ko kallonta bai yi ba yana gama parking ta fice daga motar da gudu da ido ya bita yana ɗan tabe bakinsa jin yayi mata ba zai iya shiga gidan ba sake ficewa daga gidan yayi bashi ya dawo ba sai wuraren karfe goma ,har lokacin kuma Huwaila tana gidan koda Aydah na asibiti,tsoron Mami ya hanata zuwa ga kuma Abba da yabi ya canja lokaci ɗaya,tana shiga cikin parlor ta saki wani irin ihu ta zube akasa ta shiga mirgina tamkar me cutar jinnu da gudu Huwaila ta fito daga ɗakinta ta nufi Aydah tana tambayarta menene."da sauri ta faɗa jikin Huwaila ta riketa gagam jikinta na wani irin rawa take faɗin."ki tadani daga wannan mummunan mafarkin aunty Huwaila ki tadani kice Aydah mafarki ne ba gaskiya bane."dan Allah Huwaila kice yayanmu kar ya auri wannan Rumaisar na yadda ya auri duk wacce yake so amman banda rumaisa bana sonta na tsaneta ta karashe maganar cikin gunjin kuka, haka Huwaila taja Aydah har ɗakinta tana famar rarrashinta Amman kamar dada tunzurata take yi,Huwaila ta rasa yadda zata yi da ita ta samu dakyar tabar kukan sai dai har lokacin tana zube ajikin Huwaila tana kuka mai sosai rai tana faɗin. Huwaila ta roƙar mata yayanta kar ya auri Rumaisa sun fi awa biyu a haka ana abu ɗaya banda addu'a babu abun da Huwaila ke tofawa mata da haka ta samu ta natsu tayi bacci kallo ɗaya za kayi mata kasan baccin wahala take yi, Huwaila tayi tagumi tana ta kallon innocent face ɗin Aydah.


#Love sory2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Kurman Allo.








Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[1/7, 10:17 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


#Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye


058.


Washegari da Zazzafan zazzaɓi Aydah ta tashi dashi gaba ɗaya ciwonta ya dawo sabo ko sau ɗaya AB bai neme ta ba, sabgogin gabansa kawai ya saka a gaba Huwaila kaɗai ce ke dawainiya da ita da gashi Aydah taƙi ci komai ta kunduddune kanta cikin duvet tana kuka, ba kalar lallaɓa ta da Huwaila bata yi ba. Amman taƙi ta saurarareta abu ɗaya take ta faɗa tana nanata wa bataso yayanta ya aure Rumaisa, wanda tuni Huwaila ta fahimceta kishi ne ke damunta, gudun kada mummunan abu ya faru da 'yar mutane yasa Huwaila ta danne duk wani tsoronta ta haura sama falon AB dake sama ta nufa gabanta yana dukan tara-tara ta kai hannunta tayi knocking ƙofar tana jin muryarsa yana waya hakan yasa ta ɗan dakata da knocking ɗin har sai da ya kammala wayar ɗin kana ta sake buga ƙofar sai gashi ya zo ya buɗe yana gani ita ce ya ɓata fuska "ya aka yi ne Huwaila?
Sai da Huwaila ta ɗan runsuna tare da marairaice murya ta dawo kalar tausayi, kamin ta ce "Dan girman Allah yayanmu Dan darajar soyayyarka da Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam! Ka zo ka duba yarinya nan wallahi-azim tana cikin mummunan yanayi tun jiya take tana kuka yanzu ma ta wayi gari tana cigaba da kuka nan jikinta ya yi bala'in zafi taƙi taci komai sunanka kurum take ambata.
Bai yi gigi katse Huwaila ba har sai da ta kai ƙarshen zancenta, kana ya rausayar da kai ba don haɗa shi da Allah da Manzonsa da tayi ba da ba abun da zai kai shi wurin Aydah, wata kalar tsanarta yake ji tana huda kasusuwan jikinsa tana bin jini da ɓargon sa, sai da ya furzar da iska daga bakinsa kamin ya ce da Huwaila ta tafi idan ya yi wanka zai shigo ya duba ta. Huwaila ta kara runsunawa tayi mishi godiya kana ta juya, kitchen ta wuce ta dafa wa Aydah noodles koda AB ya fito ya cilasta mata ko ita ne ta ci. After some minutes Huwaila ta ji footsteps ɗinsa yana saukowa ƙasa, ga kuma Ƙamshin fitinannen turarensa da ya gama cika sassan gidan. Da sauri ta fito daga kitchen tana gani ya nufi ƙofar fita tayi sauri tuna masa da Aydah ya juyo yana mata wani irin kallo, da sauri ta sadda kanta ƙasa, batareda da yace komai ba ya sake haurawa sama direct ɗakin Aydah ya nufo duk da yana ji yadda zuciyarsa ke masa wani irin dokawa da ƙarfi, ga ƙunci da takaicin Aydah ɗin dake ƙara lulluɓe shi. Cike da ƙarfin hali ya tura ƙofa ɗin kakkarin amanta ya ji a banɗaki tsintar kansa ya yi da nufar bathroom ɗin da saurinsa tana zube akan tiles ta dafe cikinta da dukkan hannayenta, wani irin kumfa ke fita daga cikinta a dalili babu komai acikin nata da sassarfa ya isa wurinta ba ƙaramin namijin ƙoƙari ya yi ba tare da danne abun da yake ji ya ɗago ta Aydah tana shaƙar ƙamshin turarensa ta saki kuka irin mai cin zuciya ɗinan ta rirriƙe shi tana nuna masa ƙirjinta so take tayi magana amman ta kasa, saboda wani irin nauyi da ƙirjin nata ya yi tausayinta ne ya yi masa dirar makiya duk da wani ɓangare na zuciyarsa yana jin haushi da tsanarta kasancewarsa mutum mai tsananin tausayi, sai ya ji duk ta karya masa zuciya rigar baccin jikinta ya fara cire mata ta dawo daga ita sai pant saboda duk ta jiƙa rigar bai damu da nakedness ɗinta ba ya fito daga banɗaki dauke da ita ya shimfiɗe ta akan gado, ta sauri Aydah ta riƙe masa hannu tana fizgar numfashi cikin harɗewa harshe ta furta "Yayanmu mutuwa zan yi ƙirjina ciwo yake min.
Ƙaramin tsaki marar sauti ya ja har ya juya da zimmar yai tafiyarsa sai kuma ji ba zai iya tafiya yabarta a haka ba, ya dawo ya zauna kusa da ita ya kai hannayensa ya jawo ta zuwa jikinsa har zuwa lokaci babu kaya a jikinta zafin da ya ji jikin nata ya yi gashi sai rawar sanyi take yi yasa shi sakata a ƙirjinsa Aydah tana jin kanta a jikinsa tasaka hannayenta ta gazaye shi tare da ƙanƙame shi like whole her life depend on him sai kawai ta ƙara fashewa da kuka cikin dushewar murya take faɗin "yayanmu ƙirjina yana min ciwo sosai zuciyata tana zafi kamar za ta kama da wuta bana ji daɗin komai ji nake tamkar rayuwata za ta fita daga gangar jikina, a duk sanda na tuna kana fushi dani za ka yi aure yayanmu hakan yana min zafi da raɗaɗi a zuciyana.
Ta ƙarashe magana tana wani kalan sheɗewa tamkar numfashinta zai fice daga jikinta, hakan ya ƙara tsorata AB ya har ya iya hugging nata back 'yan matasan boobs ɗinta manne a ƙirjinsa duk da yana sanye da kaya a jikinsa hakan bai hanani shi jin tsini nipples ɗinta, a jikinsa nan da nan tsigar jikinsa ta shiga mimmiƙewa a ƙoƙarinsa na so ya cireta daga jikinsa ita kuma sai kara manne masa take a dalili dumin jikinsa da take ji a nata jiki ba ƙaramin daɗi da natsuwa hakan ya haifar mata ba. Huwaila ce ta turo ƙofa ta shigo hannunta ɗauke da tray silver wanda ta ɗora breakfast ɗin da ta yiwa Aydah idanunta suna sauka akansu tai maza ta juya bata taɓa kawowa zuciyarta za ta riske su cikin wannan yanayin ba "Huwaila dawo ki kawo mata abinci mana.
AB ya faɗa cikin rawar murya tare da yakice Aydah daga jikinsa ya jawo duvet ya rufa mata, cike da matsananciyar kunya Huwaila ta dawo ta ajiye tray ɗin ta fice da sauri zuciyata cike da farin ciki, na gani AB ya sauko har wani babban al'amari yana shirin wakana tsakanin sa da Aydah har ta isa cikin kitchen tana yiwa Allah godiya. AB ya miƙa hannunsa ya dauko tray ɗin ya haɗa mata tea ya miƙa mata ta karba ya saka ta a gaba sai da ta shanye shi tass ya kuma zuba mata noodles ɗin da Huwaila ta dafa mata, ta ci kaɗan tace ta ƙoshi ya karɓi plate ɗin ya ajiye ya ce tashi ta je tayi wanka noke kafaɗa tayi tana turo baki "tashi mana ki je ki yi wanka in kika fito ki sha magani yatsine fuska tayi cikin shagwaɓe murya ta furta "banaso magani Yayanmu.
Mugun kallo da watsa mata yasa ta sauri shigewa bathroom shi kuma ya juya ya fice sai da ya fara leiƙawa kitchen ya faɗawa Huwaila taje ta gyara mata ɗaki ta kuma tabbata tasha maganinta yana fita gidansu Rumaisa ya nufo, su ƙarasa shirye-shiryen bikinsu duk abun da Rumaisa tace da AB baya musanta mata party kusan kala uku tace za a yi duk da bashi da ra'ayi ire-iren bidi'o'i nan amman haka ya biye mata yana gudu abun da zai ɓata mata shiyasa duk abun da ta tsara ya zauna koda kuwa zuciyarsa bata so. Sai misali ƙarfe 10:30pm ya dawo gida zuwa lokacin Aydah tayi bacci ya wuce ɗakinsa ya yi wanka bai bi ta kan abinci ba saboda Rumaisa ta cika masa cikinsa, kamin ya kwanta sai da ya ƙarasa wasu ayyuka da ya fara a company da bai ƙarasa su ba ya zo dasu gida. Washegari gari kamin ya fita office sai da ya fara lekawa dakin Aydah ya duba lafiyarta daidai ta fito daga wanka waist ɗinta ɗaure da towel tana fitowa tai arba dashi tsaye ya jingina bayansa ga dressing mirror ɗinta farin cikinta kasa boyuwa ya yi sai fara'a da take yi "Good morning Yayanmu!
"How are you feeling today?"
"A little better!
Aydah ta faɗa tana wani narkewa murmushi ya yi tare da taɓe baki "shi kenan ki shirya mu je ki

42 / 80