Author : EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category : KDP NOVELS
?"badai Mami tasan abunda take sha a boye ba.?"tafi minti biyar a haka kafin ta mike dakyar da jikakken kayanta ta nufi toilet,Mami na barin dakin na sadiya ta koma kasa ta tarar da mai masu shara tana sharar parlor,murjaa kibar gyaran parlor kije ki gyara dakin Sadiya,da girmamawa murjaa ta amsawa Mami da to,koda sadiya ta fito wanka murjaa har ta fitar da rug din da ta jike da ruwa ,ta canja bedshirt ta goge ruwan da suka sauka akan marbles.kallo ɗaya sadiya tayiwa murja ta wani haɗe rai tamkar ba'a taba halittar murmushi a fuskarta ba take faɗin."ke fita zan shirya."da haka murjaa ta juya tabar dakin sai da ta rama duka sallolin da ake binta ta nufi bangaren Mami,
Ta sameta gefen gado zaune kallo daya zakayi mata ka fahimci matsananciyar damuwar da Mami ke cikinta ,nan take sadiya ta sha jinin jikinta akan soofa ta zauna tana kallon Mami,kafin ta gaisheta.mami bata damu da gaisuwar da take mata ba ta kira sunanta har sau ukku."kafin tace yaushe soyayyar ɗa namiji zata saka ki lalata Rayuwarki har haka?"shiru sadiya tayi dan ko kaɗan bata fahimci me Mami ke magana akai ba."mami ban fahimceki ba soyayya kuma bani na sakawa kaina ba Allah ne ya jarabceni Mami ,ko kema kin fara gajia bazaki tayani faɗa akan abunda nakeso ba."don kazan -kazan ubanki soyayyar taci uwarta da ubanta nabi soyayyar da gudu nasa talkami masu tsini na tattake yar banza."ina maki maganar Rayuwarki kina min maganar wani shege marar asali ki shiga hankalin ki sadiya naga alamar baki da hankali bakuma san ciwon kanki ba."Yanxu uban waye ya baki Shawarar ki fara shaye-shaye sadiya kina cikin ruwan Right mind dinki kuwa?"Mami ta faɗa da wani irin sauti a Muryarta wanda uwa kaɗai ce zata fahimci wannan yanayin.gaban sadiya banda faduwa babu Abunda yake ta dafe kanta tana tunanin ya akayi Mami Tasan wannan bangaren nata.?cikin gigicewa da rudewa sadiya ta rarrafo zuwa gaban Mami ta dafe kafafunta cikin zubar hawaye da wani irin rauni a Muryar sadiya take faɗin."Mami ba halina bane wallahi na rasa yadda zanyi da rayuwata jin nake kamar na kai karshen rayuwata na huta da ina da iko da na hana zuciyata tayiwa yaya Abba irin wannan kalar soyayyar dai dai bani da iko a wannan bangaren bazan iya jayayya da kaddarata ba
Mami ina sonsa ina matukar kaunarsa idan ban zauna cikin duniyarsa ba komai zai iya faruwa da rayuwata Mami ki taimakeni na samu abunda nakeso!"sadiya ta faɗa tana fashewa da wani irin kuka mai sosa rai ,a fakaice mami ta tare hawayen dake son zubo mata duk wata hanya da ya kamata tabi tayi amfani daita dan ganin Abba bai auri Aydah ba daddy ya bata komai ya rusa masu dukkan farin cikinsu sai dai idan duk duniya zata taru akanta bazata taba karbar Abba Bashir a mijin auren yarta ba ,sai ta nunawa duniya matsayin da take dauke dashi a matsayinta Na uwa."idan na kara kamaki da laifi mafi muni irin wannan Sadiya karki tuhumeni akan matakin da zan dauka akanki tashi kibani wuri."Mami ta faɗa babu walwala akan fuskarta ,jiki sabule sadiya tabar dakin Acan kasan ranta banda kunci babu abunda takeji idan kuma ta tuna da Aydah a gida ɗaya suka kwana da yaya Abba a matsayin mata da miji sai taji duniyar na birkice mata tareda wani mahaukacin kishin da takeji akan kanwar Tata.
Har yaje ya siyo masu abunda zasuyi break fast dashi Aydah bata tashi daga bacci ba.yana mamakin son bacci irin nata,dole ma ya tsara yadda zasuyi rayuwa cikin gidan nan shida Aydah idan ba haka ba Dukansu zasu wahala ,musamman ita da ya riga ya gama sangartawa ko Kitchen baya bari ta shiga to mema Aydah ta iya Bancin ta dafa ruwan tea sai dafa indomi ko kuma white rice,shara Kuma baida tabbacin tanayi duk da yawancin lokutta itake share masa bangarensa jin ana jan dogon hancinta da kuma kamshin da take shaka yasa ta shiga buɗe fararen idanunta tana zubasu cikin doguwar fuskarsa da ta kara ganin ta kara mata kyau sosai."kallonta yayi yana ɗan harararta murmushi tayi tana rufe duka fuskarta da tafukkan hannunta
Cikin yanayin shawagaba take faɗin."sabahool khair yayanmu."sabahool Noor baby."how was ur night?"ta langabe kai cikin rawar murya take faɗin."nayi ta mafarkin Mami tana yimin faɗa."ta faɗa kwallah na taruwa cikin idonta,
Wani irin abu yaji ya tsaya masa a wuya,sai da yayi kokarin kawar da yanayin acikin ransa.ya mike tsaye hannayensa zube cikin aljihun wandonsa na jeans yake faɗin."ki shiga kiyi wanka ki wanke toilet ki gyara dakin nan tas ki fito muyi break fast sai na kira maki Mami.!"ta ɗan ji sanyi Aranta jin zai kira mata Mami,
Sai dai ayukkan da ya jero mata sunyi mata yawa murjaa itake gyara mata daki ita ke mata wankin uniform da inneawears dinta ita ke wanke mata toilet ta gyara mata gado shine Yaya Abba ke zayyano mata wannan uban aikin ashe kenan bazata gama ba sai kusan la'asar tana kokarin sauke rigar bacci agabansa yayi saurin dakatar Daita yana wani haɗe rai yake faɗin."baby fa kin girma agabana zaki cire riga ?"ta ware ido akansa tana faɗin."kai yayana ne Meye aciki sau nawa ina cire riga agabanka.banda bugawa babu abunda zuciyar Abba Bashir keyi,kofa ya nufa sai kuma ta tura baki ta kira sunanta dan tsayawa yayi ya juya yana kallon yadda ta saukar da rigar baccinta sai dai ta rufe matsanan kirjinta murmushi yayi Aransa yake faɗin."baby aydah an girma.Yayanmu wannan aikin yayi min yawa gaskiyya idan nayi wanka sai ka tayani na gyara dakin hakama toilet ,ke zaki wanke toilet da kanki bari na gyara maki dakin dai ɗan murmushi tayi ta juya ta nufi cikin toilet shi kuma ya nufi kan bed din yana gyarawa rigar baccin da ta cire ya rike yana kallo da wani yanayi da yakeji har cikin ruhinsa banda kamshin turarenta babu abunda rigar keyi.basu suka karya ba sai kusan 11 duk Aydah ta canye lokacin da wankin toilet karshe ma dai kusan shine ya wanke toilet din.cike da jin haushin kanwar tasa,bai taɓa tunanin sangartawar da yake yimata zata zamar masa matsala ba irin haka sai yanzu.'da suka gama karin kumallo
Ita ta wanke plate da cup da spoon din da suka bata sai korafi take yiwa yayan nata ita ta gaji bayanta ciwo yake.kan kujerar parlor yayi kwanciyarsa itama tana kwance akan 2searter tayi dialling number mami harta katse bata dauka ba haka ta rika jerawa Mami kira ba'a daga wayar tamkar zatayi kuka take kallon Abba da kwance yake idonsa a lumshe sai dai ba bacci yake ba."ta kira sunansa cikin muryar kuka buɗe idanunsa yayi yana kallonta Mami taki ta daga wayar sai kuka baki kawai ya saki yana kallonta."Yayanmu ko mu tafi can gidan ina son naganta ,ki bari zuwa anjima ki kira maybe tana aiki shiyasa bata daga ba."shiru kawai tayi har lokacin hawayenta sun kasa tsayawa samun kanta tayi da dialling lambar siyama bugu ɗaya ta dauka
Cikin Muryar kuka Aydah ke faɗin."Yaya siyam Mami fa?"ɗan shiru siyama tayi jin yanayin Muryar Aydah din ,Aydah ta cigaba da faɗin."na kira Wayarta bata dauka ba
Ki kai mata dan Allah."cike da karfin hali siyama ke fadin."Mami fa na bacci."dan shiru Aydah tayi da sauri siyama tace ina yayanmu ki basa."da haka Aydah ta mike tsaye ta nufi AB ta mika masa wayar fuskarta babu wata walwala sun kai minti biyu suna waya da siyama kafin ya katse kiran
Sai da azzahar tayi ya dauki car key
Cike da tsoro take kallonsa yin yayi kamar bai kula da yanayinta ba yace zaije ya nemo masu lunch."zan bika dan Allah yayanmu Ni tsoro nakeji."
Zan tsaya masallaci nayi sallah kema ki shiga kiyi sallah kafin na dawo bai jira me zatace ba ya fice daga Parlor
da ido ta bisa tana jin hawaye na sauka akan fuskarta a hankali wannan wace irin rayuwace ita bata saba zama wuri ita ɗaya ba.ko a gida tana kallon su yaya siyam,da Mami suna cire mata kewa kuma tana karatun Hausa books a wayar Mami
Anya zata iya cigaba da wannan kalar rayuwar."daman shine auren."komai ta tuna sai kuma ta Turo bakinta.aranta take faɗin."Allah ya kiyaye tayi zaman aure da yanyanta bata taɓa jin matsayinsa ya canja a zuciyarta ba.
#love story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye Novels
#Kurman Allo
Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/28/2023, 11:06 AM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
*AREWABOOK*:Jeddah3256
#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels
043.
Baki sake Aunty Safeena ke kallon Mami bayan ta faɗa mata yadda Daddy, yaci mutuncinta kuma yasa Abba ya dauki Aydah suka fice daga gidan akan idanunta."innalillah wa'inna ilaihir Raji'un!"Gaskiya yaya Mariya Daddyn su Sadiya ya samu matsala anya ba asiri yaron nan Abba ya yi masa ba?"yanzu kamar Aydah za a haɗa da wannan zabgagen ƙato mai kama da wrestler. Wallahi yaya Mariya muddin Abba ya yi tarayya da Aydah ba abunda zai hana ya kakkarya miki kasusuwanta, za ta sha dinkin kaman kwarya yaushe Aydah take da kwari ɗaukar bajimin namiji ingarma irin Abba?"
"Kema dai kya faɗa Safeena ni fa na raini Abba koda uwar rikonsa ta mutu yana da shekara biyu da watanni uku kacal a duniya, tun daga lokaci na gama tantance girman halittarsa wallahi ba ƙaramar mace ce za ta iya daukarsa a shimfiɗa ba. Ni kam na shiga uku Safeena ina matukar tausayin Aydah yarinya jikin ɗan firitt kaman ki hura ta faɗi, ba gaba ba baya.
"Duk laifin Daddyn su Sadiya ne shi bashida idanuna ne ko kuma bashi da hankali ne da kamin ya yanke wannan hukuncin bai yi duba da girman Abba da ƙarancin shekarun Aydah ba.
"Bari kawai Safeena Alh Bashir ya riga ya cuce ni ga Sadiya nan ta silar wannan shegen yaron tana kokarin ɓata rayuwarta a wofi.
"Ai ta ma riga da ta gamawa ɓata yaya Allah na tuba me ya rage.
Safeena ta faɗa da sauri tana wani kalan taɓe baki.
"Yanzu Safeena menene mafita?"
"Mafita ɗaya ce ki tashi mu tafi can gidan Abba ɗin ki kashe masa gargadi da kakkausar murya kar ya sake ya taɓa miki 'ya yadda nasan shi da biyayya zai ji maganarki kafin mu nemo saukaƙkiyar hanya da za mu raba Aydah dashi. Idan ba haka ba kina ji kina gani zai yaga miki 'ya a banza watakila ma ya haifar mata da yoyon fitsari.
Sosai Mami ta kaɗu da jin waɗannan zantuka daga bakin Safeena ba tare da dogon tunani ba ta tashi suka fi ce Safeena ke driving Mami tana gefenta gabanta sai faɗuwa yake yi ta kasa samun natsuwa, zuciyarta sai wassafa mata take yi tun da jiya a guri ɗaya Abba da Aydah suka kwana koda bai yi mata komai ba ya tattaba mata jiki. Horn aunty Safeena ta yi maigadi ya zo ya buɗe musu gate ta nufi parking lot ta yi parking kusan a tare suka fito daga mota koda suka shigo main parlor yana gyara tsaf sai ƙamshin turaren wuta ke tashi, bayan fitar AB Aydah da ta ji motsi komai ƙanƙatarsa sai ta zubura, duk ta bi ta tukura kanta da ta kasa samun natsuwa shine ta tashi ta koma can bayan cushion ta zauna tare da taƙure jikinta guri ɗaya turo ƙofar dasu Mami suka yi ya sa ta zubura da sauri ta miƙe tsaye idanunta suka faɗa cikin na Mami da gudu ta zo ta rungume Mami, uwa da ɗa sai Allah duk da Mami tana ji haushi Aydah saboda yadda ta ƙi yiwa Daddy bore akan wannan aure da ya yi mata don har ga Allah so tayi Aydah ta bijirewa Daddy, yanzu da ta ji Aydah a jikinta sai ta ji zuciyata ya karye har ta yi hugging nata back kukan shagwaɓa Aydah tasa "I miss you Mami I absolutely miss you ina Daddy, yaya Siyam, da yaya Sadiya meyasa Mami ba ku zo tare ba? Mami ɗazu na kiraki da wayan yayanmu you refuse to pick the call why Mami miyasa?"
Yadda ta karasa magana tana zuba shagwaɓa har wanin cuno baki gaba take yi, da sauri Mami ta cireta daga jikinta har tana haɗawa da ture ta "Saboda ban ga amfani magana dake ba Aydah, lokaci da labari ya riske kika ji Daddynku ya aura miki da wancan ɗan iska yaro marar asali meyasa ba ki yi bore ba kaman yadda Sadiya ta yiwa Daddynku da ya aura mata shi. Sai gashi kin kwana gidansa cikin kwanciya hankali da walwala ko Aydah?"
"Ni gaskiya Mami sai dai ki yi haƙuri ba zan iya kallon Daddy na ce masa bana so aure nan ba. Daddy yana da yakini akaina ni ce zan kawowa yaya Abba farin ciki wa rayuwar...... kafin Aydah ta ƙarashe magana Mami ta buge mata baki wani kalan raɗaɗi Aydah ta ji a bakinta sakamakon buge shi da Mami ta yi haƙora ta suka datse mata lebben ta na sama har sai da ya yi jini shafa bakin nata ta yi tana gani jini a tafin hannunta ba ma wani sosai ba ta tsandara ihu mai ƙarar gaske, daidai AB yana parking motarsa wannan ihun nata yai masifar gigitashi ya balle murfin mota ya fito ko takeaway ɗin da ya yo musu bai tsaya dauka ba ya, nufi cikin gida cikin saurinsa yana tura ƙofa daidai sanda Mami ta dakawa Aydah tsawa "ke rufe mana bakinki sakarya yarinya kawai marar kishi kai ga baki ɗaya Aydah ba kisan ciwo kanki ba.
Aunty Safeena ta karɓe zancen tana faɗin "Ke yanzu banda daƙiƙanci idan aka barki da wannan gabjejen kato sai ki yi zaman aure dashi? To bari ki ji duk ranar da kika bari wannan murɗaɗɗen kato ya buɗa ki kwanakin sun ƙare ba abinda zai hanaki kamuwa da yoyon fitsari idan ma an taki sa'a kin rayu kenan ba ki mutu ba.
Masifar da suke ta zubawa Aydah ya hana su ji ƙarar buɗe ƙofa da AB ya yi sai kawai ya ya yi tsaye yana saurarensu, suka cigaba da fadar maganganu marasa kyau da daɗi akansa.
"Wai Mami me yayanmu ya yi miki ne da kika tsane shi har haka?"
Aydah ta tambaya tana sharar hawaye da suka gama wanke mata kumatunta.
"Ubanki ya yi min na ce ubanki ya yi min Aydah ana nuna miki Annabi kina runtse ido sakarya yarinya shashasha kawai to bari ki ji idan har ina ƙaunar mutuwata to ina ƙaunar wannan auren naku, maza wuce ki kira min Abba saboda duk abunda zan faɗa sakarcin ki ba zai barki ki fahimta ba.
Aydah ta yi banza da Mami tana cigaba da sharɓe hawaye, damtse hannunta Mami ta kama ta girgiza ta da ƙarfi kafin ta ingiza ƙeyarta "Wuce ki je ki kira min shi tun kafin nayi mugun ɓata miki rai.
Yadda Mami ta ingiza ta yasa ta yi tangal-tangal ta fadi daman ga yadda ɗan jikin yake sai a hankali ba wani karfi ne da ita ba. AB yana gani Mami tana shiri yiwa Aydah rauni ya karasa shiga parlorn yana faɗin.
"Mami!!"
Daga Mami har aunty Safeena waigawa suka yi, da sauri ya nufi wurin da Aydah take yashe tana gunji kuka ya ɗago ta "Sannu baby in ji ba ki ji ciwo ba??" Yana magana tare da sa ta a jikinsa daman haka ya saba rarrashinta duk lokacin datake kuka, kafin Aydah ta bashi amsa aunty Safeena ta ce "iyeee! Ba shakka Abba a gabanmu kake kwakume 'yar jinjira yarinya nan saboda ba kada kunya ba ka gaje ta ba ko?"
Ran AB ya sosu da jin wannan furuncin na aunty Safeena sai dai bai isa ya mayar mata da magana ba saboda har gobe yana mata kallon ƙanwar mahaifiyarsa.
"Ai idan bai yi mata hakan a gabanmu bai cika cikkaken tsintaccen, ɗa shege ba. Abba ka zama annoba gashi nan ta silarka rayuwar Sadiya tana neman gurbacewa mijina da muka yi aure shekara da shekaru ko kallon banza bai taɓa haɗani dashi ba amman saboda kai Abba ya wanke min fuska da mari.
Mami ta faɗa tana huci dan ba ƙaramin haushi da tsanar Abba take ji deep down na zuciyarta sai lokaci Abba ya ɗan runsuna ya gaishesu a tsawace Mami ta ce "Kai dakata! Ban zo nan don ka gaishe ni ba na zo na kashe maka gargadi da kakkausar murya karka sake ka nemi ka haɗa shimfiɗa da 'yata domin Aydah yarinya ce ba za ta iya ɗaukar ƙato kamar ka ba. Ba zan zuba ido ka cutar min da yarinya ba ko ɗan yatsanta ka taɓa da niyar jin daɗi Allah ya isa dawainiya da na yi da kai.
Kuma ka sani Abba ko tsine maka nayi wallahi tsinuwata za ta bi ka domin ba kalar wahalar da ban yi da kai ba.
Har Mami ta kai ƙarshen zancenta kansa yana kasa wata zufa ce taketa keto mishi a can kasan zuciyarsa yana ta auna maganganu Mami, dukka ya danganta su da tsanar da take masa daman tana so taci zarafin sa shine ta fake da wannan zance da hankali ba zai dauka ba ko giyar wake ya sha ba zai tunkari Aydah da wata bukatarsa ba. Mami da aunty Safeena sai da suka kare masa zagi da gori kamin su fi ce jikinsa a mace ya bi su ya raka su har waje mota yana musu fatan sauka lafiya, muguwar harara aunty Safeena ta galla masa Mami kuma ta ja tsaki. Wannan irin abu ya ji ya danne masa kirji ya ja sanyayyu ƙafafuwansa ya koma cikin gida Aydah tana zaune a two seater ta kifa kanta a hannun kujarar tana abunda da ta saba, tausayin kansa da nata yake ji domin yasan duk wannan abun da Mami da aunty Safeena suka yi mata duk ta dalilinsa ne. Tausayin kansa da yake ji kuma yana tuna irin kalubalen da yake ta facing daga wannan sai wancan