Author : EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category : KDP NOVELS
shigo ba Daddy ya juya kan AB da Aydah yayi masu nasiha mai taɓa zuciya da ruhi kafin Daddy ya kama hannun Aydah dana AB ya haɗe wuri ɗaya cike da wani irin raunin murya ya ce "Na baku amanar junanku dukanku ya'yana ne matsayi ɗaya kuke dashi a wurina Allah ya baku zaman lafiya kamar yadda kuka yimin biyayya Allah ya cika rayuwarku da farin ciki ya azurtaku da ya'yanda za su sakaku farin ciki Abba tashi ka dauki matarka ku tafi luggage ɗin Aydah an sakasu a mota zan yi maka transfer kuɗin lefen Aydah ta account ɗinka, miƙewa tsaye ya yi da hannun Aydah da yake cikin hannunsa har lokaci da wani kalar ɗumin da yake jin hannayen nasu ya dauka, hawaye kawai Aydah keyi tana jin zuciyarta ta yi mata wani irin mugun nauyi addu'a take Allah yasa mafarki take Allah yasa ba gaskiya bane wannan wane irin kalar ƙaddara ce da za ta yi mata shigar kutsu.
Ƙasa ƙarasawa ya yi gaban Mami yana jin yadda kafafunsa suke son kasa daukarsa kallonsu Mami keyi da wani mugun yanayi kwance acikin fuskarta karasowa Mami tayi a rude AB ya daga kai yana kallonta tunda ya tashi yayi wayau bai taɓa ganinta cikin wannan yanayin ba,har za ya buɗe baki yayi magana yaji saukar mari cikin fuskarsa a haukace mami taci kwallar rigarsa tana wani irin jijjigawa tana faɗin."Ni za ka ci wa amana Abba ni za ka yaudara?"Ni za ka watsawa kasa a ido?"
Mami ta ƙarashe magana tana zare ido tamkar wacce ta samu tabin hankali ta cigaba da faɗin "Sai naga yadda yarinyata za ta zauna da marar asali tsintatce, wulakntatcce irinka.
Mariyaa!!!"
Daddy ya kira ta da wani irin tone, wani kallo Mami ta rika aikawa ta saitinsa kafin ta mayar da kallonta kan AB "Don ubanka ka sakar min yarinya yanzu-yanzu nan!
A fusace Daddy ya karaso gabanta ya wani fisgota ya bata tagwayen mari har sau biyu a kowanne kuncenta dama da hagu cikin razana da kidima Mami ke kallon mai gidan nata kusan shekarar su Ishirin da shidda da aure Daddy bai taɓa kai hannunsa jikinta ba da sunan duka sai yau kuma duk akan ɗan tsintuwa,rai ɓace Daddy ya kalli AB Cikin kakkausar murya ya ce "ja hannun matarka ku wuce sai da safe.
Haka AB yabi umurnin Daddy don ba zai iya yi masa gardama ba ya rike hannun Aydah suka fice daga Parlor cike da wani irin raunin zuciyoyin su.
"Ki barmin gidana yanzu Mariya ki tafi sai na nemeki.
Daddy ya faɗa with angry voice
wani murmushin takaici Mami tayi tana gyada kai take faɗin."gidanka dama ba zan zauna ba
har sai na tabbatar da tsinannen yaron can ya sakar min 'ya in har ina numfashi Abba bai isa yayi zaman aure da 'yata ba ka rubuta haka ka aje.
Mami ta juya tana barin cikin parlor tamkar wata mahaukaciya.
Tun da ya bude motar ta shiga taji wani irin kuka mai cin rai na kwace mata yanayin mami kawai da ta kalla ya yi masifar birkita mata duniyarta.
Shima a bangaren AB bai yi wani yunkurin hanata kuka ba shima akwai nasa ciwon da Mami ta fama masa a kasan tashi zuciyar sai dai har lokacin ya kasa jin haushin Mami ko kankani acikin zuciyarsa, har yau soyayyar da yake yimata da 'ya'yanta babu abunda ya ragu. Sai dai bai san taya zai soma rayuwar aure da yarinyar da ya raina da hannunsa ba. Yana da lokacin daidaita komai ya kamata yayi wani abu kafin komai ya ƙarasa tarwatse masa.
#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.
Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/27/2023, 12:50 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
*AREWABOOK*: jeddah
3256
Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye
040.
(MASARAUTAR KUDU)
Tun lokacin da aka akai mai martaba sarki Mahmood na Uku asibiti har ila yau bai motsa ko ɗan yatsansa ba abinda ya ƙara tashe hankali iyalansa da ma masarauta baki ɗaya. Sarki Mahmood adalin sarki ne mai tausayi talakawansa da jiƙansu tun sanda ya hau karagar mulkin kudu ba a taɓa yi kuka dashi ba sai dai ka ji ana yabon ayyukansa na alkhairi. Kwanciyar sa jinya ya jawo ce-ce-kuce a cikin masarauta dama wajen masaurata mutane da dama sun fi ta'allaka ciwonsa da jifa (asiri) yanzu ma Yarima babba ne da Aliyu na Uku ke tsaye a ɗakin da aka kwantar dashi kwata-kwata Aliyu na Uku bai ga wani sauki ko cigaba a jikin nasa ba saboda haka ne ya kira Yarima babba kasancewar sa babban likita da ke jagorantar kula da lafiyar mai martaba yana masa complain na rashin gani sauki a jikin na mai martaba.
"Ranka ya shi dade ni ina gani kaman an yi gaggawar fita dashi waje muma yanzu mun sami cigaba sosai duk waɗansu kayan aiki da kwararru likitoci muna dasu a ƙasar mu idan ma wani abu ya shige mana duhu mu kan nemi taimakon waɗancan likitocin turawa saboda asibitin mu yana da good connection dasu, ka ba da daman a tafi dashi Alliance hospital Abuja in-sha-Allah za a dace.
Har Yarima babba ya kai aya a zancensa Aliyu na Uku bai kallesa ba idanunsa suna kan mai martaba yana kallon yadda numfashinsa ke sauka ta cikin na'urar da aka makala masa. Cike da izza nan da ta gama zagaye jinin jikinsa ya ce "A shirya mana tafiya gobe bana so a sami kowanne irin tsaiko ka tabbata daga yanzu zuwa dare ka kammala duk wani shiri na tafiyar mu.
Ajiyar zuciya Yarima babba ya yi saboda yasan halin ƙanin mahaifin nasa baya magana biyu amma duk da sai ya yi yunkurin ya lurar dashi na so a yi tafiyar agaggauce "Ranka shi dade wannan tafiya bata buƙatar gaggawa...
"Yarima!!
Ya yi sauri tarar numfashinsa tare da ɗaga masa hannu "isa bana so surutu idan ba za ka iya ba ka barmin komai a hannuna ni zan iya.
"Amman....
"Please!.
Tun kafin Yarima babba ya karasa faɗar abunda zai faɗa ya sake taka masa birki dole Yarima babba ya ja bakinsa ya tsuke, suna nan tsaye sai ga yaya Gimbiya tare da magaji ƙarami da first born ɗinta Marwan, dukkansu suka gaida Aliyu na Uku da Yarima babba, yayin da Yarima babba ya gaida yaya Gimbiya Aliyu na Uku ko kallon gefen da take bai yi ba.
Yaya Gimbiya ta karbi ledar da suka shigo da ita daga hannun Marwan ta fito da wata robar swan mai ɗauke da ruwan rubutu tana balle murfin take faɗin "Ai daman na gayamuku wannan ciwon na mai martaba da sa hannun makiya aka yi biris da magana ta yanzu daga wurin malam na tsamiya na fito ya jadadda min asiri aka yiwa mai martaba kuma rayuwarsa ake farauta.
Ta ƙarashe magana tare da nufar gadon mai martaba za ta shafa masa ruwan rubutu cikin sauri Aliyu na Uku ya tare gabanta "Miye haka yaya Gimbiya miyasa ke a koda yaushe kike so sai an yi rigima dake? Wannan abun da ke ki ƙoƙarin aikatawa ba daidai bane kowa a garinan ya sheda cewa Malam na Tsamiya malamin tsibu ne.
"Dallah dakata mai sabon birnin! banaso rashin kunya ka dai san ni ba a sa'arka ce ba akwai tazarar shekaru ɗaɗɗaya har goma sha uku na ba ka don haka ka shiga hankalinka kasan da wacce kake magana.
"Ikon Allah ai ke matsalata kenan da ke yaya Gimbiya bayaso gaskiya.
Aliyu na Uku ya faɗa tare da kaucewa ya bata hanya don ba zai iya da masifarta ba yanzu nan sai ta goranta masa har wankin kashi da taɓa yi masa a lokacin yatinta, sosai yake mamakin halin yaya Gimbiya na faɗa masiffafiyar mai rai ce duk yaran ɗakinsu ita ce ta fita dabam ko kaɗan bata biyo halin mai babban ɗaki ba saboda mai babban ɗaki akwai ta da sanyi hali ga haƙuri da kawaici ita dai barta da izza da taƙama shi ma wannan ya samu asali da fitowarta daga jinin sarauta kana kuma ta yi aure a gidan sarauta. Yawan mutane suna cewa Yaya Gimbiya halin kakarta wanda ta haifi Sarki Usman na uku ta biyo Hajja Chogidi ita ce masiffafiyar gaske, a zamanin da tana raye an ce hatta da sarki Mustapha na Uku yana shakkar ta ba don komai ba sai masifa da faɗanta. Duk yadda Aliyu na Uku yaso ya hanawa yaya Gimbiya aiwatar da kudirin ta ta ƙi ta saurare shi dole ya zuba mata ido, ya koma gefe yana kallonta tana dab da fara shafawa mai martaba ruwan rubutun Fulani karama ta turo ƙofa ta shigo, karaf idanunta suka sauka akan yaya Gimbiya wani irin faduwa gabanta ya yi, cikin kidimewa ta furta "A'ah! Yaya Gimbiya me kike shiri aikatawa haka me za ki shafawa mai martaba?"
Cak! Yaya Gimbiya ta dakatar da abunda take yi ta juya a fusace ta kalli Fulani karama "wannan wacce irin tambayar renin wayau ce kike min Fulani karama? Kin san dai ba zan taɓa yi abunda zai cutar da mai martaba ba.
Fulani karama ta yi wani kici-kici da fuska ta isa wajen gadon mai martaba tana faɗin "ban ce za ki cutar da shi ba Yaya Gimbiya amma ina so na tunarda ke abinda kika manta mai martaba ya tsani duk wani abu da ya shafi tsinbace-tsinbace idan Allah ya tashe kafaɗarsa ya sami labari kin shafa masa wannan ruwan rubutu, ba zai taba yafe miki ba. Domin a koyaushe yana gargaɗin mu da mu guje ire-iren waɗannan abubuwa na haɗa ki da Allah da manzonsa kada ki shafa masa shi idan ma kina zargin asiri ne aka yi masa ki je ki roka masa sauki wurin Allah domin shi ne ya saukar da ciwo ya kuma saukar da maganinsa.
Nan take kalaman Fulani karama suka yi tasiri akan yaya Gimbiya ta kasa furta uffan dole ta maida murfin robar ta rufe ta kalli Magaji ƙarami da marwan ta ce su wuce su tafi saboda bata ga amfani zamanta asibitin ba.
Yadda ta fice a fusace za ka zaci za ta tashi sama ne, dukkansu suka bi ta da kallo boyayyar ajiyar zuciya Fulani karama ta sauke tana kisimawa a zuciyata dole ta nemi hanyar da za ta haɗu da Galadima ta faɗa masa irin zargin da yaya Gimbiya ta fara yi akan mai martaba gara ya yiwa tufka hanci tun kafin wankin hula bai kai su dare ba.
Washegari gari da Aliyu ya je gaida mai babban ɗaki ta nuna ƙi amincewar ta akan tafiya da mai martaba Abuja ta ce su bar wa Allah ikonsa su cigaba da addu'a idan yana da raguwar kwana a gaba Allah zai tashi kafaɗarsa, kuma duk inda za su kai shi idan Allah bai nufi ya tashi ba babu abinda suka isa su yi daga ƙarshe sai haɗa kan ƴaƴan nata ta yi ta dinga yi musu nasiha mai ratsa jinin jiki tare da ƙara tunatar dasu yarda da ƙaddara yana cikin rukunan imani. Dole Aliyu na Uku ya hakura da kudirinsa.
A wannan karon Ciroma da Galadima tare suka tafi wurin boka mai Gundulelliya, bayan ya gama surkulen sa da ya share mintuna yana yi, ya ɗago fuskarsa da ke fidda wani irin maiƙo ya yi musu ƙur da dakwa-dakwan idanunsa masu masifar ban tsoro da firgitarwa har sai da Ciroma da Galadima suka tsargu da irin kallon da yake musu, gashi ba kyau gani ne da fuskar tasa ba ballantana su jure kallon nasa sai da ya gaji da kallon nasu kafin ya sheƙe da wata kalan dariya wacce bata da daɗin saurare ta fi kama da kukan jaki sai ya haɗiye dariyar tasa ya wani murtuƙe fuskarsa cikin kakkausar murya ya ce "A bisa sakaci da ka yi Ciroma ya gashi nan garin sauri ka haifar da nawa bansan ya aka yi haka ta faru ba saboda sau uku kacal mai martaba ya sha ruwan sihiri da na ba ka, hakan kuma hakan yana nufi daga yanzu zuwa kowanne lokaci zai iya samun lafiya, domin kuwa 'yar uwarsa ta fara nema masa waraka yanzu haka malamin da ta je wurinsa yana kan gabbar warware mana shiri, kuma kasani Ciroma warware wannan asiri yana nufi faɗuwarka ƙasa wanwar kai da sarautar Kudu har abada.
Wani irin gumi ne ya karyo wa Ciroma bai san sanda ya fincike rawani kansa ba tsananin tashin hankali marar adadi ya bayyana akan fuskarsa sai fiffita yake da rawaninsa.
*ALH BASHIR MANSION*
Abdulkarim ne ya zauna a mazaunin direba ya ja motar cike da rashin kwarin jiki, ba ka ji komai ackin motar sai sautin kukan Aydah. Har can cikin zuciyar AB yana so ya rarrashe ta amma rasa kwarin gwiwa yi hakan. Sai Abdulkarim ne yake bata baki a maimakon ta yi shiru sai karawa kukan nata sauti, har suka iso gidan na AB Aydah tana shesshakar kuka AB da Abdulkarim suka fito daga motar suna jiran ta fito amman ta yi zamanta sai ma sunne kanta tsakanin guiwayoyinta da ta yi AB ya buɗe murfi gefen da take cikin taushin murya ya ce "Fito mana.
Aydah ta yi banza dashi ta ci-gaba da kukanta "Baby na ce ki fito mu shiga ciki ko nai tafiyata ne?"
Nan ma bata tanka shi ba haƙurinsa yana gab da karewa saboda haka a tsawace ya furta "Za ki fito ne ko sai ɓalla miki mari?"
A tsorace ta ciro kanta tana kallonsa da rinannau idanunta tana wani girgiza kanta, hawaye na fita daga idanunta suna sauka akan tattausan kumatunta gani ya yi za ta ɓata mishi lokaci gashi baya cikin yanayi da zai jure iyashegenta domin dab yake da ya wanke fuskarta da mari saboda haka ya sunkuya tare da tura kansa cikin motar ya dauko ta in a bridal style cikin tafiyarsa ta zallan ƙasaita ya nufi entrance ɗin gidan da ita Abdulkarim ya bisu da kallo yana murmushi sai da suka ɓacewa ganinsa sannan ya ja mota ya tafi.
Yadda yake ɗauke da ita faɗaɗden ƙirjinsa ya rufe ta ruff ƙafafuwanta kaɗai ake iya gani, sai da ya kaita main parlor kana ya zaunar da ita akan two seater yana dire ta tana sake fashewa da wani sabon kuka ya yi tsaye tare da folding hannayensa a ƙirji yana kallonta kafin ya kyaɓe baki ya juya ya nufi upstairs tana Aydah tana gani zai tafi yabar ta, ta karawa kukanta sauti har tana haɗawa da kiran sunansa "Yayanmu!!
Ya tsaya cak! Ba tare da ya dawo ba ya waigo yana faɗin "Baby please karki daɗa min damuwa akan wacce nake ciki ni kaina da zan sami daman irin wacce ke ɗinan kika samu da ba abinda zai hanani kuka.
Yana ƙarashe magana ya juya tare da ci-gaba da tafiyarsa daman dauriyyarsa ta kare ƙarfin hali ne kawai yake yi idan kuma ya ce zai tsaya rarrashinta gaba ɗaya karfin halin nasa zai tafi Aydah ta bisa da kallo tana cigaba da shasshekar kukanta tana cikin kukan Abdulkarim ya turo ƙofa ya shigo da sallama hannunsa rike da bakar leda ya nemi kujera dake kallonta ya zauna a natse yake kallon yadda take kuka wanda ke nuni da zallan sangarta don har wani zuburo baki take yi "Haba Aydah kada ki bani mamaki mana yaya Abbanki ne kike irin wannan kukan saboda za ku zauna a gida za mu rayu da junanku na har abada, ko kin daina sonshi ne na faɗa masa ya haɗa kayan sa yabar muku gidanku daman Mami ba son aurenku take yi ba kinga shikenan sai ki koma gunta da zama shi kuma ya yi tafiyarsa wurin da ba za ki taba ganinsa ba zai yi nisan da ke da kara ganinsa har abada.
Da sauri Aydah ta ɗago kodadun idanunta tana kallon Abdulkarim agaggauce ta shiga goge hawaye fuskarta da tafukan hannayenta dukka "Na daina kuka yaya Abdulkarim dan Allah ka cewa Yayanmu kar ya tafi wallahi ina sonsa idan ya tafi mutuwa zan yi.
Murmushi ne ya subuce wa Abdulkarim sai ya cigaba da faɗin "idan har da gaske kina sonsa kuma bakyso ya tafi kada ki sake yi kuka, ki kwantar hankalinki ki cigaba da yi masa biyayya kaman yadda kika saba ni kuma na daukar miki alƙawari ba zan taɓa bari ya tafi yabarki ba idan ma zai tafi ɗin sai da ku tafi tare. Yanzu ki tashi ki tafi ɗakinki ga kaza mai zafi da fresh milk na kawo miki ki ci abarki sai kin ƙoshi ki kwanta ki yi bacci abinki yaya Abba ba inda zai je kuna tare ke dashi mutu karaba takalmin kaza.
Aydah ta yi murmushi ta tashi tare da amsar ledar da Abdulkarim ya miƙa mata tare suka haura bene ya nuna mata ainihin dakin Sadiya ya ce "Ki shiga ɗakinki ki tabbata kin ciye kazar dukka kada ki ragewa yaya Abba kin ji?"
Ta gyaɗa kanta ta tura ƙofar ɗakin wani irin ni'imataccen ƙamshin turaren wuta ya bugi hancinta bata san sanda ta lumshe idanunta ba, ta nufi gefen gado ta zauna tana mai yaye mayafin jikinta.
Direct Abdulkarim ya nufi ɗakin baccin AB yana tura ƙofa ya hango shi kwance akan ya yi matashi da hannayensa idanunsa suna kafe akan pop, da alamu ya yi zurfi a tunani. Wani bala'in tausayin sa ya kanainaye wa Abdulkarim zuciya, ya furzar da iska daga bakinsa jikinsa a macce ya ɗauke pillows ɗin da Ab ya matsar dasu gefe ya nemi kusa dashi ya zauna ya daura ɗaya daga cikin pillows ɗin akan cinyoyinsa, ganinsa da ya yi cikin wannan yanayi yasa zuciyarsa ta ɓaci ko kaɗan bai ji daɗin hakan ba shi yasan ko shine a matsayin Ab dole ya shiga damuwa. Cikin taushin murya ya kira sunansa bai amsa ba Abdulkarim bai damu da rashin amsawar tasa ba ya ci-gaba da faɗin "Ka yi haƙuri abokina ka daina wannan dogon tunani bashida amfani musamman idan ka yi duba da health record ɗinka kana da blood pressure, garin wannan tunani jini naka