Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   13 / 80

36K to 39K   out of 237.2K words

ya zaunar da ita yake faɗa mata zance aure ta da AB ya rushe dan kawai ya kasance adopted child ba shi da asali ba a san su waye biological parents ɗinsa ba, har ga Allah ita bata ɗauki wannan a matsayin ƙarfaffiyar hujjar da zai sa ya hanata aurensa ba. Domin Abba Bashir yana da nagarta da ko'ina za a iya bashi mata ya aura rashin asalinsa bai dame ta ba. Da farko ta yi tunani ba za ta shiga damuwa ba, a dalilin mahaifinta shi ne ya zaɓar mata AB ta kuma yi masa biyayya tare da karɓa zaɓin nasa da hannu bibbiyu yanzu kuma shine ya dawo da kansa ya ce ya fasa ta zaci cewa tun anan wuri za ta manta da Abba Bashir sai gashi ɗan taliki nan ya hana mata ci abinci ya kuma hana mata bacci, ga baki ɗaya ya yi awon gaba da farin cikinta. Batasan cewa soyayyar AB ta mata mummunan kamu ba har haka ba.
Ƙanwarta wacce ke bi mata Jalila ta turo ƙofar ɗakinta ta shigo dawowar Jalila kenan daga school tana karatu a BUK ta shigo ɗakin na Mufeeda ne da zimmar ta saka wayarta charging a dalilin charger ɗinta ya lalace, tana gani halin da yayarta ta, take ciki tayi tsaye turus! Ta daɗe tana kallonta kafin ta tako a hankali kamar mai sanɗa ta zauna daf da Mufeeda sai da ta fara leƙa screen ɗin wayar Mufeeda ta ga picture ɗin da take kallo, kana maida ganinta akan hawaye da Mufeeda batasan suna zuba daga idanuwanta ta sauke numfashi ta kai hannunta ta fincike wayar da Mufeeda ta yiwa wani kalar riƙo tamkar rayuwarta ce aciki.
"Yaya Mufeeda kar dai ki ce min kin kamu da soyayyar guy din nan??"
Sai da Mufeeda ta tashi zaune ta jefa pillow a bayanta ta jingina gadon bayanta, ta ja wata 'yar siririyar majina ta koma cikin ƙoƙon kanta cikin rauni murya ta furta "Ga alama kin gani azahiri miye na tambaya.
"Cab! Amma kuwa kina da aiki yaya Mufeeda domin sanin kanki ne Abba yanka ɗaya ne da matuƙar wahala ya sauya kalamansa. Don haka tun wuri ki gaggauta yaƙi da yaudararriyar zuciyarki, ki yaƙe ta, ta raba ki da son abinda ba za ki taɓa samu ba.
Ba abinda maganganu Jalila suka ƙara wa Mufeeda face fushi da ɓacin rai don haka sai da ta baro fizge wayarta daga hannun Jalila ɗin kafin cikin ɓacin rai ta ce "Lokaci da na fara son AB bai yi shawara da kowa ba daga ciki kuwa har Abban da kike tsorata ni akansa, kuma ina so kisani Jalila ita soyayya da kike gani wata aba ce wacce bata neman shawara ko yarjewa, haka zalika bata neman izni kutsa wa a cikin zuciyar ɗan adam. Jalila soyayya halitta ce da Allah subhanahu wata'ala ya halicce ta sannan ya dasa ta a duk wata halitta zuciya mai rai. Soyayya wani sashe ne mai matuƙar wahalar da ruhi gami da gangar jiki kalmar so yana da sauƙi faɗa fiye da kowacce kalma sai dai ma'anar sa ta fi kowacce kalma raunata ruhi da gangar jiki. Ba lallai bane ki fahimci kurman allo da nake miki ba saboda ba ki taɓa riskar kanki a koramar so ba.
Kyakkyawar numfashi Jalila ta ja tare da saukewa cike da sanyi jikinta ta dafa kafaɗar Mufeeda "ki yi haƙuri idan furunci nayi ya ɓata miki rai bana nufi na ƙara miki damuwa kawai dai ina ƙoƙari tunatar dake kaman abunda kika manta akan Abban mu zan fi kowa farin ciki idan kika sami cikar muradinki.
"Addu'a ya kamata ki tayani da ita idan har akwai alkhairi a tarayya ta da AB Allah ya karkato da hankalin Abban mu idan kuma akasin hakan ne Allah ya musanya min da mafi alkhairi.
"Shi kenan yaya Mufeeda Allah ya zaɓi miki mafi alkhairi.
"Amin!
Mufeeda ta faɗa tana mai sauka daga gado ta shiga bathroom Jalila kuma ta saka wayarta a charging ta fice zuwa babban parlorn gidan.
*ALH BASHIR MANSION*
AB yana dawowa daga office ya wuce bangaren sa ya yi wanka koda ya fito daga wanka ana kiran sallar magarib agurguje ya shirya cikin silk jallabiya brown in color ya fesa turare kaɗan, ya wuce masallaci bayan an gama sallar isha ya shigo gida kaitsaye ɓangaren Mami ya nufa a babban parlor ya tarar da Sadiya da Siyama kowacce tana sabgar gabanta, Sadiya tana rubutun project ɗinta a laptop yayin da Siyama take chat da Saleem fiancé ɗinta sai uban murmushi take zabgawa alamar hirar da suke yi tayi mata mugun daɗi. Ƙamshin perfume ɗinsa ya ankarar dasu wanzuwar sa a cikin parlor, kusan a tare suka ɗago "Ya Abba ina wuni?
Sadiya ta faɗa cikin rawar murya banza ya yi mata "Ya Abba barka da dare?
Siyama ta gaida shi ba tare da la'akari da ƙin amsawa Sadiya da ya yi ba.
"Siyam ya karatu?
"Al-hamdullilah Ya Abba!
"Ina Baby Aydah?
Da sauri Siyama taso ta matso daf da yaya Abba ta yi ƙasa da muryar kamar munafuka "Yaya Abba wallahi ina zargi Aydah da akwai abunda take aikata wa a ɓoye duk bin kwakwafi na, na kasa gano mene ne. Da zarar ta dawo daga islamiyya za ta ƙunshe kanta a ɗaki hatta da abinci ta rage ci haka zalika ta daina fitowa a babban parlor.
"Uhm! Tun yaushe ta fara wannan halaya?
AB ya yi magana cikin ƙaramin sauti.
"Za kai three weeks.
"Three weeks! Meyasa tun lokaci ba ki faɗamin ba?
"Ya Abba na zaci za ta daina ne yanzu ma naga abun nata ya ta'azzara sosai.
"Je ki kira min ita.
Da sauri Siyama ta nufi mattakalar bene zuciyarta cike da murna yau za su sha kallo, tana murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin Aydah ta ji shi a ƙargame da sauri ta sakko daga bene sai da tazo kusa da Ya Abba sannan ta yi magana "Ya Abba ɗakinta a rufe yake.
"Je ki yi mata knocking ki faɗa mata ni nake so ganinta.
Har Siyama ta juya sai kuma ya dakatar da ita "Siyama! Yi zaman ki kawai bara na je da kaina idan ma tana ɓoye wani abu ne zan gani da idanuna.
Hakan da ya faɗa ba ƙaramin daɗi Siyama ta ji ba tana da yaƙini dole ya kamata da laifi musamman ɗazu taga sanda Aydah ɗin ta fito da wayar Mami tana ɓoyewa batasan cewa ta ganta ba, tasan Ya Abba baya so tana riƙe waya a cewarsa har yanzu bata yi girman da za ta riƙe waya ba. Don haka yanzu idan ya kamata da wayar Mami mai hana shi yai mata duka sai Allah.
Duk abunda ke wakana tsakani AB da Siyama Sadiya ta tattara hankali da natsuwarta kacokan akan su yanzu ma da ya juya ya haura bene, ta bishi da kallo a hankali yake knocking ƙofar ɗakin Aydah, tun yanayi a sannu har ya dawo yi da ɗan ƙarfi Aydah wacce tayi nisa a karatun littafin secret relationship na Asmy b Aliyu sosai take enjoying littafin ba ƙaramin tausayin Jiddah ya kamata na gani yadda ta kamu da zazzafar soyayya Junaid Dikko alhali shi kuma baya ji sonta a zuciyarsa.
"Aydahhh! Me kike yi a ɗaki zo buɗe ƙofar nan tun kafin ranki ya ɓaci.
Kaman daga saman ta ji muryar ya Abba a kausashe. Wani kalan wutsillowa ta yi daga gado ta faɗo ƙasa "Na shiga uku! Kaman muryar Ya Abba nake ji.
Aydah ta faɗa cikin zare idanuwa kafin ta gama tu'ajjabi ta sake ji ya kira sunanta a fusace "Aydah kina ji na fa.
"Na'am! Ya Abba gani nan zuwa.
Ta faɗa cikin harɗewa harshe ta tashi da sauri ta ɗaga pillow dake kwance akai ta ɓoye wayar ɗayan wayar Mami da ta dauko, sai dai ta daidaita natsuwarta kafin ta nufi ƙofar ta buɗe idanuwanta suka sarƙe da na Ya Abba wanda yai bala'in haɗe fuska "Ya Ab...ba!
Yadda ta furta sunansa da kuma yadda idanuwanta suka firfito wannan kaɗai ya isa ya tabbatar mishi da bata da gaskiya, tun tana yarinya idan tai laifi ta ƙwayar idanuwanta yake ganewa "Me kike yi ke kaɗai ƙunshe a ɗaki ba sannan kuma ba kallo kike yi ba saboda ban ji ƙarar sauti tv ba?"
"Uhm! Uhm! Ya Abba headache ke damu na.
Ta gama kame-kamenta ta da kyar ta lallaɓo wannan karya ta faɗa kallon da yake bin ta dashi duk sai ta ji ta tsargu ta shiga cukuɗaɗɗiyar kalabar kanta wacce tsabar tsofa har ta fara tsife kanta da yake gashinta yana da tsatsin mayar da ganinsa ya yi kan gashin nata, take ya ɓata fuska cike da ba da umarni ya ce "Ban yarda dake ba Aydah ki faɗa min gaskiyar abinda kike yi idan kuma kika sake na bincika da kaina na gano ki to ki kuka da kanki.
Idanuwanta suka cicciko da hawaye ta wani langwaɓar da kai ita dole sai ta bashi tausayi cikin muryar so ya kuka take faɗin."Ya Abba game ne nake yi da wayar Mami.
Wani kalan ajiyar zuciya ya yi kafin ya ture ta ya wuce cikin ɗakin nata ya ɗinga dube-dube can idanunsa suka kai ga pillow da tashi ya ɗauke shi ya ciro wayar Mami, ya ɗan jujjuya ta sai kuma ya mayar da ganinsa akan fuskarta "Wato saboda game shiyasa kika zaɓi ki dinga rufe kanki a ɗaki ko? Wai ke ga ki mayyar games.
"Ya Abba I'm sorry!
Tayi magana tare da kama fatun kunnenta biyu.
"Wannan shine kashedi na ƙarshe da zan miki akan ki daina daukar wa Mami waya saboda ba sana'arki bace kin ji ko?"
"Tohm!
Ta faɗa cikin ƙaramin sauti "Dama kina ji magana da watakila na runtse idanu na siya miki tab ki ta buga game tun da kin dawo mayyar sa.
Sauri ta ƙaraso gabansa ta shiga zuba mishi taɓara tana wani bubbuga ƙafafuwanta akan marbles hakan ya haifar wa da ilahirin jikinta motsawa 'yan matasan boobs ɗinta sai rawa suke yi ta jikin 'yar fingilalliyar half gown ɗin jikinta wacce ko santala-santala cinyoyinta bata rufe da sauri AB ya kauda fuskarsa yayin da Aydah sai zuba shagwaɓar take yi har tana ƙoƙari kama mishi hannu ya yi sauri ja da baya cikin kakkausar murya ya ce "Baby Aydah banaso rigima idan kina min wannan taɓarar sai ki sa na fasa.
"Na daina Ya Abba Allah na daina.
"To shi kenan ki canza kayan jikinki ki sakko ƙasa mu yi dinner.
Yana ƙarashe magana ya nufi ƙofar fita ba tare da ya sake kallonta ba.


#Love story 2023/2024
#Jeedah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#team tagwaye novels
#Kurman Allo








Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/11/2023, 10:04 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU




#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels




018..


*RUBUTUN ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU.*
*TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA*


*KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?*
*INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?”*
*KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.*
Mun gwada mun gani 💯
Mun gani mun shaida 💯
Anyi mun gani 💯
MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
GYARAN MAIJEGO
MALLAKAR MIJI KO MATA
SUBULU DA SCRUB
MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
MAGANIN TSUMI
INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯


08142800199
07068558096








Agurguje ta canza rigar jikinta zuwa bubu na material hularta a hannu ta fito da ɗan gudunta ta sakko ƙasa yadda ta fito tana fara'a yasa Siyama ta ɓata rai wato ƙararta da ta yi wurin Ya Abba ta tsalleke shi. Yau su uku suka ci abinci Sadiya, AB da Aydah, Siyama taci abinci da yamma lis da ta dawo daga school Mami kuma azumi ta yi a parlonta dake sama ta yi buɗa baki tuni Sadiya ta ƙoshi amma ta kasa tashi ba ƙaramin daɗi take ji idan tana kallon kyakkyawar fuskarsa ba. AB ya ture plate ɗin gabansa ya kalli Aydah wacce ke tsotsar ƙashin miya "Aydah!
"Na'am!
"Ki shirya gobe da yamma na kai ki saloon a wanke miki kai ayi miki kitso Allah na gaji da ganinki da wannan ƙazantar dake kanki.
Ya ƙarashe maganae yana ya mutsa fuska irin da gaske kyakyamin ta yake ji. Kafin Aydah ta yi magana Sadiya ta rigata ta hanyar cewa "Gaskiya Ya Abba ka rage sangarta Aydah she's mature enough and she can take care of herself haba hatta da kitso ace kaine za ka kaita sai kace wata yarinyar goye.
"Mtss! Ya ja dogon tsaki tare da miƙewa ya ture kujera ya nufi ƙofar fita Aydah ta kalli Sadiya taga yadda ta bi shi da kallo har idanuwanta sun kawo ƙwalla ta fashe da dariya, hakan ya fusata Sadiya ta tashi rai ɓace ta tsike Aydah da wawan mari har sai da Aydah ta faɗo ƙasa ta takarkare ta tsandara mahaukacin ihu wanda yasa Siyama ta jefar da wayarta ta kwaso da gudu ta shigo dining area ɗin ta sauke idanunta akan fuskar Sadiya wacce ke cika tana batsewa Siyama ta sunkuya ta ɗago da Aydah wacce ta saki baki sai kuka take yi tana kiran wayyo Allah idonta yaya Sadiya ta fasa mata ido. "Wannan ya zama miki na farko kuma na ƙarshe da za ki sake yi min dariya 'yar iska yarinya kawai wacce ta gama raina mutane.
AB har ya gama ficewa daga entrance ɗin part ɗin Mami ya ji ihun Aydah a rikice ya dawo daidai furunci Sadiya yana faɗawa kunnensa dukkan su basu lura da shigowarsa dining area ɗin ba yana zuwa ba tare da ka-ce-na-ce ba ya ɗauke Sadiya da lafiyayyen mari tana ɗagowa buɗe da baki ya sake dallawa ɗayan kumatunta cikin tsanani fushi da ɓacin rai ya nuna ta da yatsa cikin kakkausar murya ya ce "Daga yau daga yanzun nan da nake tsaye a gabanki idan kika kara taɓa lafiyar Aydah acikin gidan nan wallahi tallahi sai na baki mugun mamaki,with shock Sadiya ke kallon Abba,tana ganin yadda jikinsa ke wani irin rawa saboda tsananin ɓacin rai. marin da ya mata bai ɓata mata rai ba kamar yadda ransa ya ɓaci akan marin Aydah da ta yi zuciyarta ta fara kokonto akan yayan nasu akan kulawar da yake baiwa Aydah fiye dasu. "Hayaniyar me nakeji anan?" Mami ta faɗa tana tsaye akan stairs dan hayaniyarsu yasata fitowa Siyama da Aydah suka yi tsuru-tsuru saboda ɓacin rai AB ko kallon wurin Mami, bai yi ba ya juya a mugun fusace ya fice daga Parlon ita ma Sadiya ta juya ta nufi nata ɗakin cike da shakku da wani irin tsoro dake cika zuciyarta. Sai lokacin Siyama ta korawa Mami abunda ya faru. Mami tabi Aydah kawai da mugun kallo ta juya ta koma sama. Da dare sai dai AB ya kira siyama a waya ta kai masa coffee a part ɗinsa har lokacin bai gama fushin da ya dauka da Sadiya ba dama kuma tara mata yake yi. Har zuwa washegari bai huce daga fushin da ya yi ba, shiyasa ko breakfast bai fito ba. Sai da Daddy ya tambaya me aka yi masa da bai fito ba? Mami tace "kannensa ne suka ɓata masa rai kai ma kasan ba zai zo ba Siyama ta zuba masa ta kai masa.
Daddy ya juya kan Aydah da take zaune a wurin tana juya spoon ɗin a hannunta ɗan murmushi Daddy ya yi yana faɗin."mamana meyasa kike tsokanar yayunki bancin kin san yayanki baya da haƙuri a wannan ɓangaren?"
Hawaye suka fara sauka a fuskar Aydah cikin shesshekar kukan ta ."Daddy ban mata komai ba kawai ta mareni.!
Mami ta wani daka mata tsawa tana faɗin."tashi ki bar gabana kar na kwada maki mari, da sauri Aydah ta mike tsaye tana ture plate ɗin gabanta cikin banbamin faɗa Mami ke faɗin."Ba dole ta yiwa mutane rashin kunya ba duk yabi ya sangarta yarinya ya lalata ta bata respecting ɗin kowa. Na sha faɗawa Abba ba so ɗaya ba biyu ba wannan ba gata bane macce ce gidan wani zata tafi wallahi wahala za tayi. Da zarar ya buɗe baki sai ka ji ya ce ba zai taɓa bari ta wahala ba, haka zalika babu shegen da ya isa ya wulakanta masa kanwa. Ai zamu dai gani mu je zuwa.
Mami ta ƙarashe magana a mugun fusace wani murmushi mai sautin gaske Daddy ya yi shi dai bai ce komai ba sai yanzu wani tunani ya shiga kansa meyasa tun farko bai aurawa Abba, Aydah ba? Tun da har akwai irin wannan muguwar shaƙuwar a tsakaninsu yasan ba zai taɓa kin amincewa ba wata irin shaƙuwa ce dake tsakanin Abba da Aydah tun tana ƙarama yake nuna mata matsananciyar ƙauna ya sha canja mata school don kawai ta yi laifi an hukunta ta, ko bata mata rai akayi shi kenan ba za ta ƙara zuwa ba school ɗin ba. Babu irin faɗan da bai yi masa ba akan wannan canje-canjen makarantar da yake mata har yanzu da take secondary school haka suke kullum yana sintiri zuwa makarantarsu Aydah sulhu da malaman makaranta. Kamar yadda ya saba yana gama shirin fita office cikin shigar suit maroon in colour sai da ya tsaya a mota ya aje briefcase ɗinsa ya nufi cikin gida Mami da Sadiya kaɗai ya tarar cikin dining area ɗin.
Ita ma Sadiya saboda ta saka yayan nata a ido ta fito cikin dining area ɗin fuskarsa a tamke ya ja kujera ya zauna daf ta Mami yana gaisheta cike da respect ta amsa. Cikin rawar murya Sadiya ta gaishesa ko kallon inda take bai yi ba ballantana tasa ran zai amsa Mami dai bata ce komai ba tana ta sipping

13 / 80