Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   41 / 80

120K to 123K   out of 237.2K words

ko dai bata dauke mu ƙawayeta ba?"
Aydah ta ɗago kodadun idanunta ta kalli Zaliha, sai kuma ta goge fuskarta da tafukan hannayenta tana jan majina irin ta wanda yaci kuka har ya godewa Allah. Cikin sanyi murya ta faɗa musu abun da ya faru tsakaninta da yayanta, sai kawai Zaliha ta sa dariya tare da rungume Aydah "OMG! Aydah Bashir when will you grow up? Just because your brother is angry with you sai ki dinga wannan uban kuka.
"Gaskiya Aydah Bashir ya kamata ki rage shagwaɓa gaba ɗaya kin tashe hankalin mu akan abun da bai taka kara ya karya ba. Idan kin koma gida ki bashi haƙuri in sha Allah zai haƙura kin ji crying baby?
Ameera ta faɗa tana kwantowa jikin Aydah shiru kawai Aydah ta yi tana bin su da ido tasan ba za su fahimci abun da take ji ba.
Bayan an tashi daga school ta bi school bus kamar yadda AB ya bukata.
Bangaren AB da ya tashi ya shirya abinsa ya wuce office bayan ya je ne ya kira principal ɗin su Aydah ya gayamata aiki ya yi masa yawa daga yanzu Aydah za ta dinga bi school bus.
***********
Sannu a hankali Ciroma ke samun nasara akan muradinsa a wannan zaman na ƙarshe da za a yi sai da ya kai wa bokansa ziyara ya sake basa wani turare ya ce idan za a yi zaman ya shafe jikinsa dashi, zai ga abin mamaki haka kowa aka yi kamin ya shiga ɗakin da za a gudanar da taron ya bade jikinsa da turare da bashi da daɗi ko kaɗan kamar turaren 'yan bore sai azabar hawan kai, a haka ya kutse ɗakin manyan fada suna shaƙar ƙamshin kowanne su ya sha jinin jikinsa Ciroma ya nemi wuri ya kame sai hura hanci yake yana kallonsu ɗaɗɗaya, yana jiran me za su ce wambai ne ya yi gyaran murya da kalle shi za ka gane a tsorace yake da har wani rawa muryarsa ke yi "Dangane da tsari na wannan masarautar ta mu mai albarka muka yi duba da cancanta ne mu naɗa sarki, da farin dukanmu kowa anan yasan Ciroma shine yafi dacewa haɗe da cancanta da ya zama sarkin mu saboda haka mu 'yan majalisar sarki mu yanke shawarar naɗa Ciroma a matsayin sarkin wannan masarauta kun amince ko kuma akwai wani mai ja?"
"A'ah!mun amince mun amince.
Kusan a tare manyan fada suka haɗa baki, wannan al'amari ba ƙaramin daɗi ya yiwa Ciroma ba don sai wani kaɗa kai yake yi kamar kadangare.
"To Al-hamdullilah tun da kowa anan ya yi na'am sai mu fara shirye-shirye naɗin sa nan da sati mai zuwa.
Aliyu na Uku ne ya fara miƙewa ya fice daga ɗakin taron bayaso sarautar nan ko kaɗan amman ya rasa dalili da yasa yake ji babu daɗi da ya kasance Ciroma ne ya same ta, yana ji a jikinsa kamar hawan Ciroma a karagar mulki kudu tamkar wani mummunan al'amari ne zai faru.






#Love story2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Kurman Aliyu








Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[1/5, 8:02 AM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels






056.


AB bai samu kai Aidah gida ba sai a washe garin kamar yadda Daddy yayi masa umarni kuma an shiga hutun weekend,a kitchen ya samu Huwaila tana 'yan aikace-aikace wake-wakenta take yi cikin nishadi amman acan kasan ranta damuwa ce a tattare da ita ganin uwar ɗakinta cikin mugun yanayin da ko a mafarki bata taɓa tunanin zuwansa ba ita kanta taga yadda yaya Abba ya canja lokaci ɗaya tamkar mai cutar jinnu har tsoron haɗa hanya take dashi.tamkar ance ta juya bayanta taga Abba,tsaye a bakin ƙofar shigowa kitchen ya harɗe hannunsa a kirjinsa yana kallonta fuskarsa babu annuri acikinta nan take jikin Huwaila ya fara rawa tsoronta Allah kar ya rabata da gidan nan tasan idan bata cikinsa waye zai kula da Aydah wa zai riƙa cewa taci abinci. Gyaran murya yayi yana faɗin."ina yarinyar nan take ?"a tsorace Huwaila ta bashi amsa."tana ɗaki!
"Kice ta sameni a mota. Da haka ya juya ya bar kofar kitchen ɗin,da sauri Huwaila ta haura sama ɗakin Aydah ta tura ta sameta kwance akan bed tayi rubda ciki taji ta ɗan samu natsuwa ganin break fast ɗin da ta kawo mata ta ɗan ci haka zalika tayi wanka tana sanye da doguwar atamfa ajikinta kanta babu ɗan kwali
Huwaila ta kira sunanta a hankali,shiru Aydah tayi mata kanta ciwo yake kamar zai rabe mata gida biyu "Auta ki tashi Yayanmu na jiranki a mota. Ai tana jin sunan yayanmu lokaci ɗaya ta buɗe ido kuma ta miƙe zaune tana kallon Huwaila "ki saka hijab ɗinki yana jiranki."wani murmushi ne Aydah ke yi nan da nan fuskarta ta cika da fara'a tace"Da gaske Aunty Huwaila yayanmu ne ke kirana?ta faɗa sounding so very emotional hawaye na taruwa a idanunta,da sauri Huwaila ta daga mata kai alamar tabbatarwa , "Na canja kaya Aunty ko na tafi a haka?"Aydah ta faɗa tana nufar wurin kayanta,wannan ma yayi Amman ki canja da sauri Aydah ta buɗe closet ɗinta tana bincike duka kayanta tana faɗin Huwaila ta ƙaraso ta tayata zaben wanda zata saka,Huwaila jiki a sanyaye ta karaso tana ganin irin murnar da Aydah keyi tamkar ba ita ba tana ta addu'a Allah yasa ta tarar da farin ciki a wurin Abba."Yayanmu yana son abaya Aunty Huwaila ki zabar min wacce zan saka. Ta faɗa tana kaita gaban dogayen rigunanta masu kyau da tsadar gaske wata maroon color Huwaila ta dauko mata mai adon duwatsu ajikinta nan take Aydah ta shiga shirya kanta ta saka powder a fuskarta har kwalli ta saka da man baki , takalminta ta saka ta dauki handbag ɗinsu juya kanta ta shigayi a gaban huwaila tana faɗin "nayi kyau Aunty Huwaila?"dariya Huwaila tayi tana faɗin "kinyi kyau sosai Auta har ƙofar parlor Huwaila ta rakata tayi mata fatan dawowa lafiya. Koda ta iso waya yake da sahibarsa Rumaisa har ta buɗe motar ta shiga ta zauna bai katse wayar da yake da rumaisa ba, tafi minti goma zaune a motar tana jin yanda ranta ya sosu sosai, ya katse wayar tana jin yana faɗawa Rumaisa zuwa anjima zai shigo wurinta yaci abincin rana, sai da bugun zuciyar Aydah ya tsaya na kusan sakan talatin bai damu da yanayin da Aydah ta shiga ba,yaja motar batareda ya kalleta ba ballantana ta saka ran zai mata magana. Har zata buɗe baki tayi masa magana tuna irin marin da yayi mata jiya sai ta fasa daidai kofar gidansu taga yayi parking motar batareda ta kallesa ba ta balle marfin motar daman duk lokacin da taga yayi haka ba shiga zai yi ba.tana rufe ƙofar motar ya wani fisge motar da wani irin gudu ya badeta da kura.wani irin mugun rauni taji zuciyarta tayi duk yadda taso rike hawayenta kasawa tayi sai da suka zubo da sauri tasa hannu ta goge cike da sagewar gwiwa ta doshi gate ɗin gidansu....ido biyu suka yi da Siyama dake zaune cikin parlor Siyama,ta ware ido tana kallon little sis ɗin tata da sauri ta karasa ta rungume Aydah ita ma Aydah,rungume Siyama tayi wani kuka ta fashewa da Siyama dashi mai fitowa tun daga karkashin zuciya.
A rude Siyama ta ɗagota tana ta kallon parlor kar wani ya fito yaga Aydah tana kuka a gigice ta riƙa hannunta tayi hanyar kofar ɗakinta ,har cikin ɗakinta Siyama ta jata anan kasan rug ta zube ta rika rerawa Siyama kuka na fitar hankali duk Siyama ta rude ta jawo kanwar tata murya can ciki take faɗin."ki natsu Aydah ki rage wannan kukan kar Mami,taji kiyi min bayani wani abu ya samu yayanmu ne?"Siyama ta faɗa cikin rawar murya cikin kuks Aydah ke faɗin."ban san me na yiwa yayanmu ba duk yabi ya tsaneni yaya Siyam, Yayanmu ya daina sona.
Sai da gaban Siyama yayi wani irin buguwa kallon Aydah take ganin yadda tayi rama lokaci ɗaya "ke me kika yi ma yayan namu nasan bakida gaskiya Aydah ba haka kawai zai yi fushi dake ba."Ni fa yaya Siyam babu abunda nayi masa."shiru kawai Siyam tayi ta zuba tagumi tana kallon kanwartata dake famar sharar hawaye.dialling lambar Yaya Abba,tayi yana ɗagawa yace Siyam ya akayi ne?"gaishesa tukun siyama ta fara yi sai kuma tayi shiru ta rasa abun da za ta ce masa jin shirun ya yi yawa yasa yace "Ya aka yi ne Siyama.?"cikin rawar murya Siyama tace "Daman Aydah ce ta zo tana kuka yaya."sai tace maki wani abu nayi mata dan ni mugune kou?"Abba ya faɗa da wata irin murya wacce Siyama bata taɓa jinsa da ita ba, rudewa da gigicewa yasa Siyama ta rasa me zata faɗa masa sai kawai ya kashe wayar,da ido kawai Aydah take bin ta batace komai ba ta koma kan bed din Siyama ta cire doguwar rigar jikinta daman akwai riga da skirt na english wears ajikinta taja duvet ɗin Siyama ta rufe har kanta batareda tace komai ba da ido Siyama ta bita ta kira sunanta a hankali sai dai Aydah tana jinta tayi mata shiru hawayen idonta sun kasa tsayawa wani irin rauni zuciyarta tayi har lokacin ta kasa yadda yayanta ne yake hukuntata da laifin da bata san ta aikata ba.da haka wani nauyayyen bacci ya dauketa bar mata dakin Siyama tayi ita ma jikinta yayi mugun sanyi,zamanta ta cigaba dayi a parlor suna chat da Saleem,sama-sama sai kusan la'asar ta koma ɗakin har lokacin kuma aAydah bacci take wanka tayi ta dauro alwallah tana zaune a gaban mirror dressing tana shafa cream ɗinta da take using,taga Aydah ta cire duvet din jikinta da sauri ta sauka daga kan bed ɗin tayi saurin rufe bakinta da hannunta biyu da gudu ta nufi toilet tun kafin ta karasa ta durkushe a wurin ta rika amai tsoro da gigicewa yasa Siyama ta karaso wurinta ta riketa duk ta gama galabaita ga jikinta yayi wani irin saki ga shi yayi zafi sosai ,Siyama ta taimaka mata ta wanke bakinta a kan rug ta kwanta tana mayar da numfashi ,kai tsaye Siyama ta nufi ɗakin Mami a tsorace ,zaune ta samu Mami da Sadiya da alamar magana suke suna ganin Siyama suka yi tsit daman Sadiya ko kallon Siyama bata yi ba ta cigaba da danna wayar hannunta. Lafiya kika shigo mana a gigice sai kace mutuwa akayi."tuni Siyama ta fara hawaye cikin rawar baki take cewa Mami,Aydah ce keta amai a dakina.!"Siyama ta faɗa hawaye idonta suka kasa tsayawa daga Mami har Sadiya sai da zuciyarsu tayi tsalle cikin rawar baki Sadiya tace yaushe ta zo gidan."tun wuraren 12,ai tuni mami tayi waje bata tsaya jiran bayanin da Siyama ke yiwa Sadiya ,ba da sauri Siyama ta bi bayan Mami aka bar Sadiya cikin gigicewa da kidemewa ,hannu ta ɗora akai tuni hawaye suka fara rolling cikin fuskarta zagaye dakin Mami ta soma yi shikenan yaya Abba ,ya haɗa gado da Aydah dah tunda har amai take duk wani buri da ta ɗora akan yayan nata a hankali taji yana rugujewa ,Aydah ta cuceta ta cuci rayuwarta bata taɓajin tsanar wani a rayuwarta ba kamar yadda ta tsani Aydah bata san me zata yi mata ba ta ɗandana mata bakin cikin da ta dasa mata acikin zuciyarta har abada bazai gogu ba ,tayi alkawari kamar yadda Aydah tayi gudu da rayuwarta sai ta tarwatsa mata rayuwarta ta dauki alwashin ko da shine abu na karshe da zata aikata cikin rayuwarta sai ta san yadda cikin nan ya fita ajikin Aydah da haka ta dauki wayarta ta fice daga ɗakin na Mami ko kallon dakin Siyama batayi ba ɗakinta ta shige ta rufo kofa.babu irin lallashin da Mami bata yiwa Aydah ba akan ta faɗa mata meke damunta banda kuka babu abunda Aydah take, haushi duk ya kama Mami tsoronta Allah kar ace ciki ne ajikin Aydah da Abba ya cuceta ya gama da rayuwarta.ta dubi Siyama tace ki fito da ita muje asibiti
Da haka Mami ta fice daga dakin tashin hankali bayyane cikin fuskarta
dialling ɗin lambar AB tayi a wayrta harta katse bai dauka ba tana kokarin kara kiransa sai ga kiran sa ya shigo da respect ya gaisheta ,bata ko saurari gaisuwarsa ba cikin bala'i da masifa tac "Bashir uban me ka yiwa yarinyata?"ciki kayi mata ko tsoron Allah bakaji me zaka tsinta a jikin Aydah don ubanka?"Mami ta faɗa a tsawace juya maganganun Mami,ya shiga yi aransa gabaki ɗaya kansa ya daure wallahi-tallahi idan wani abu ya sameta sai na tsine maka Abba ."Mami ta faɗa so pissed up tana sauke wayar. "Na kawo maki abinci kici?"Siyama ta faɗa tana kallon Aydah dake mayar da numfashi dakyar,daga kai kurum Aydah tayi da sauri Siyama ta fita dan kawowa Aydah abinci,
cikin kayan Siyama ta nufa ta ciro pant sabo da pad ta nufi toilet dakyar ta shirya kanta daman duk zata yi period sai tayi rashin lafiya ,har da kwanciya a asibiti haka take duk wata a gidan har fargabar zuwan period ɗin Aydah suke yadda take cin wahala tamkar wata mai ciki. Koda Siyama ta kawo mata abincin tana toilet sai bayan ta fito ne ta samu Siyama ta kawo mata abinci kallon abincin kurum da tayi sai da taji zuciyarta na yamutsewa wani amai taji yana zo mata da gudu ta koma toilet nan ma aman ta ƙara yi kamar zata amayar da duka hanjin cikinta
Siyama dai sai sannu take mata.
Siyama ta fito rike da ita daidai lokacin da Mami,ta shigo dakin da hijab ajikinta da car key.wani aman ta sake yi. Siyama ta ɗagawa Mami kai
Ki saka mata hijab muje asibiti yanzun nan,in banda jaraba uban me zai tsinta acikin Aydah idan ma cikine wallahi Ba zasu dawo gidan nan ba sai an zubar dashi. Daga Mami sai Siyama suka kai Aydah asibiti. Dr.firdausi ce suka samu ita ta duba Aydah ta kalli Mami,tana faɗin."Hajiya ko period ɗinta yazo ?"sai lokacin Mami ta tuna da idan tana period tana ciwo kamar zata mutu. "Bana tunanin haka doctor.
Dr. Firdausi ta dubi Aydah tana faɗin."Autar Mami,period ɗinki yazo?"daga kai kurum tayi ko magana bata son yi, wani numfashi Mami ta rika saukewa gigicewa ma yasa bata yi wannan tunanin ba sai yanzu hankalinta ya kwanta sai da aka kwantar da Aydah ganin yadda take amai sosai duk ta galabaita ta fice daga hayyacinta dole aka saka mata drip.har bayan magrib Siyama na tare da Aydah ,lokacin Mami ta koma gida
har lokacin Aydah bacci take. Siyama na sallar ishaai Daddy,da AB suka shigo (amenity room) ɗin da aka kai Aydah,tunda ya shigo idonsa ya sauke akanta tayi rama ba yar kaɗan ba.da sauri ya dauke kansa kuma ya kasa ƙarasawa cikin room ɗin,Siyama sai kallon yayan nasu take da mamaki, Daddy ne ke yiwa Siyama tambayoyi taci abinci?"tea kaɗai ta sha daddy kasan idan tana ciwon nan bata cin abinci."har kusan 9 Daddy,da AB na asibitin kuma har lokacin bai ƙarasa wurin Aydah ba ita ma lokacin ta falka hankalinta Ga baki ɗaya yana wurin yayan nata.daman shi ya dauko Daddy,sallama suka yiwa Siyama Daddy yana faɗin."idan da matsala ta kirasa,Mamana ko kina bukatar wani abu?"da sauri ta girgiza kai hawaye na taruwa a idonta tana kallon saitin da AB ɗin yake ,danna wayar hannunsa kurum yake ganin saitin da take kallo yasa Daddy ya saki murmushi yana faɗin."Ni ina maki magana yayanki kike kallo tau shikenan sai da safe Daddy,ya faɗa yana shafa kanta. bayan fitar daddy, still AB bai karasa gaban Aydah ba ya juya yana yiwa Siyama sallama,yace idan suna bukatar wani abu su kirasa daga masa kai Kurum tayi.






#love story2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#kurman Allo.








Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[1/5, 8:07 AM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels






057


Washe gari wuraren karfe 9 na safe sai ga Mami,ita da Daddy sun shigo ɗakin,daidai lokacin da Aydah ta fito daga wanka.kallonta kawai Mami take ganin yadda Aydah ta zabge lokaci ɗaya,daga Mami har Daddy sannu suke yimata Siyama ta gaishe da iyayen nata,ganin su mami yasa Aydah ta dauki kayanta ta koma toilet ta shirya,tana fitowa Mami da Daddy suka sake yi mata sannu da jiki. Mami ta kalli Siyama tace ta haɗa mata tea nan take yanayin fuskar Aydah ya canja ta kalli Mami kamar zata yi kuka take "ni sai na jira yayanmu."baki sake Mami ke kallonta ,cikin banbamin faɗa Mami ta ce ."cikin uban waye idan baki sha ba munafuka da ya damu dake ai da ya zo ya kwana tare dake,da sauri Daddy ya katse Mami ,yana faɗin "Haba Mariya menene abun faɗa aciki ?"tace zata jira yayanta ba sai ki lallabata ba.
Takaici yasa Mami tabar masu ɗakin tana jin ranta na bala'in ɓacin ,acan kasan ranta kuma tana ta tunanin ko maganin da aka yiwa Abba,yayi tasiri akansa ne?"akwai ayar tambaya, da yanzu yana asibiti ko shine zai kwana tare da ita duk soyayyar da yake yiwa Aydah ace ta kwanta asibiti bai kwana tare da ita ba wannan al'amari abun dubawa ne, dan sanyin Mami taji aranta tana ta addu'a Allah yasa ma maganin ya kamasa zamanta tayi anan waje
batareda ta koma ciki ba. Babu yadda Daddy,bai lallaba Aydah ba akan ko tea ne tasha idan yayan nata yazo sai suyi break fast tare taki yadda,daga waya Daddy yayi ya kira Abba with respect Abba ya daga yana gaishe da Daddy, cikin sakin fuska Daddy

41 / 80