Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   16 / 80

45K to 48K   out of 237.2K words

take. Mami jin tayi ana knocking sai da ta tambayi wanene Aunty Safeena tace ita ce sa'annan Mami tazo ta buɗe ƙofar dama tana shigowa ta mayar da ƙofar ta rufe, ganin yadda mami ta zama lokaci ɗaya yasa aunty Safeena ta cire mayafin jikinta ta aje ƙaramar handbag ɗinta ta zauna gefen Mami tana kallonta har zata buɗe baki tayi magana taji ana knocking ɗin ƙofar sai da Mami ta tambayi waye?"Siyama ta amsa da ita ce, Aunty Safeena taje ta buɗe ƙofar da karamin tray Siyama ta shigo ta aje akan rug ɗin dake tsakiyar ɗakin na Mami. Aunty Safeena nayi mata sannu Mami ta kalli Siyama tana faɗin."kar fa ku sakarwa mai aiki kitchen ɗin dukkanku, ku tayata har Aydah.
Siyama ta amsawa Mami da to
Ta fice daga dakin."Safeena kin san me Bashir ke son ƙara yi a wannan karon?" Mami ta faɗa cike da wani irin bakon yanayi a muryarta. Ita dai Safeena kallon yayarta ta kawai take tun kafin ta sanarda da ita abunda ke faruwa ita ma ta fara ta jin hankalinta ya tashi zuciyarta na bugawa."Aure zai haɗa tsakani Aydah da Abba.!"
Ita ma Safeena kalmar ba ƙaramin razanata tayi ba ta shiga maimaita Aure da mamaki Safeena ta ce "Mijin nan naki kuwa yana cikin right mind ɗinsa kuwa?"duka -duka nawa Aydah take? Ni Ko kaɗan kin san banji daɗin hukuncin da ya yanke ba tun a auren Sadiya, sai gashi tun kafin su kwana a gidan abubuwa suka cabe."!still bai daddara ba yanzu kuma za ya ƙara haɗa wani auren. To wallahi yaya karki yadda wannan karon ke ma sanyin ki ya yi yawa haka kawai sai ki zuba masa ido yana ta yankewa 'ya'yanki hukunci kema fa kina da hakki dasu. Duka-duka nawa Aydah take? yarinyar dako matakin secondary school bata fita ba.
Mami na girgiza kai tana sakin murmushin takaici a hankali "wai sai kace baki san taurin kan Bashir bane?"kin manta waye shi babu wanda ya isa yasa ya canja masa ra'ayi.
"To shi abban meya ce?"me zai ce fa kin san kawaicinsa ai bazai iya cewa A'ah ba. Amma hakikanin gaskiya banaso haɗin nan ke kisan akwai alƙawari da muka yi na ƙara ƙarfafa zumunci tsakanin Jameel da Aydah.
"Ban manta ba yaya shi kansa Jameel ɗin a koda yaushe yana min zance Aydah ni ce nake taka masa birki na ce ya ƙara haƙuri ta kammala karatun secondary school sai ya bayyana mata sirri zuciyarsa.
"Meye mafita Safeena ga baki ɗaya kaina ya kwance?"
"To ko dai za ki gwada kira Abban ne cikin sirri ki faɗa masa ya faɗawa Daddy abar maganar nan ko duba da ƙarancin shekarun Aydah."
Mami ta girgiza kai tare da faɗin "Sam ba zan iya ba saboda nasan irin girmama zance Alhaji da Abba ke yi ko wuta ya ce yaro nan ya faɗa wallahi ko second ɗaya ba zai ƙara ba zai faɗa ciki.
Shiru kawai Aunty Safeena tayi tana jinjina ƙarfin hali irin na mijin yayartata. "Ni dai yaya ga shawara ko za ki yiwa Daddy maganar kawai ya yi haƙuri Abban ya mayar da Sadiya ɗakinta na tabbata idan ya je wa Bashir da wannan zance zai karɓe shi ko ba komai Sadiya ƙosasshiyar budurwa ce saɓani Aydah da take kwaila ko nonuwan kirki basu gama fita a ƙirjinta ba.
Shiru Mami tayi tana juya maganar Safeena cikin ranta ɗan ajiyar zuciya ta sauke "Zan gwada wannan shawarar amma kin san taurin kan Sadiya kamar na mahaifinta idan kuma taki yarda fa?" aka koma gidan jiya.
Dariya kawai Aunty Safeena ta yi tare da faɗin."Tun da ta kwana a cell ai ko a mafarki ba za ta ƙara wannan kuskuren ba. Idan kuma ba mu sami haɗin kai Sadiya ba sai ki zaunar da Aydah ki nuna mata illar da auren da Abba zai haifar mata kinsan ta da rigima take za ta bijirewa buƙatar mahaifin nata domin ya gujewa abinda zai biyo baya take zai janye kudirin sa.
Sai da Mami ta saki dariyar takaici kafin ta ɗora da faɗin "Lallai Safeena kina da sauran sani akan Aydah, ai nan da kike ganinta ko ranta za ta iya bayar wa akan Abba, ƙauna da shaƙuwar dake tsakaninsu ta zarce na misalta miki ita atake.
"Cabdijam! To kuwa Sadiyar nan ita ya dace za mu lallaɓa.
Da haka mami da ƙanwarta, ta suka yanke shawarar za tayi wa Daddy, maganar ko a mayar da auren Sadiya da Abba ne a karo na biyu kamar zai fi musu sauki akan a haɗa Abba da Aydah. Har bayan ishaai Abba yana can gidansa a kwance wani irin ciwo ƙirjinsa yake da kyar ya lalubi wayarsa ya kira layin abokinsa Abdulkarim bata jima ba tana ringing ya daga jin muryar AB kurum yasan babu lafiya cike da kulawa Abdulkarim ke faɗin."Are you owk AB.?" Sai can kuma ya bude ido yana salati cikin minti ashirin ya nufi gidan AB ɗin a ƙofar gidan yabar motarsa ya yi knocking maigadi yazo ya buɗe masa a tsaitsaye ya amsa gaisuwar da maigadi ke yi masa ya tura ƙofar parlorn yana addu'ar Allah yasa a buɗe take. Ya yi sa'a a buɗe take kai tsaye upstairs ya nufa kusan ɗakuna 3 ne a sama bai san wannne daga ciki AB yake ciki ba ya buɗe na farko baya ciki yana buɗe na biyu ya hango fitila a kunne kamar hasken rana. Ya ƙarasa da saurinsa ya Abba hango kwance akan bed ya rufe har kansa da duvet muryar Abdulkarim ya ji akansa yana kiran sunansa jin shiru yasa ya ya ye duvet ɗin. Ganin he is shivering ya fara salati yana faɗin."ba kada lafiya ne AB? Ɗaga masa kai kurum ya iya yi da sauri Abdulkarim ya ɗauki remote ɗin AC ya kashe duka yana faɗin."kana rashin lafiya still kana zaune cikin AC kodai za muje asibiti ne?" Da sauri AB ya girgiza kansa tare da lumshe idanuwansa har na kusan minti biyu
"To wai kai haka za ka ci-gaba da zama ba za ka tashi muje asibiti ba?"
Cikin rawar murya AB ke faɗin."ai ba ciwon asibiti bane wannan yafi ƙarfin asibiti." Da mamaki Abdulkarim ke cewa "To ciwon menene?" shiru AB ya yi ga zazzaɓi na cinsa idan kuma ya tuna kalaman Daddy da inviting card ɗin da ya gani na aurensa da yarinyar nan wacce ko a mafarki bai taɓa tunanin za ta zo a matsayin matarsa ba sai ya ji zazzaɓin ya ƙara lullubesa tun da Daddy ya faɗa masa aurensa da Aydah babu fashi ya ji duniyarsa ta tsaya cak!"jin ya yi kamar an ɗauki dutsi mai nauyi an ɗora masa aka. Gani yaƙi cewa komai yasa Abdulkarim yace "kasan ba zan barka cikin wannan yanayin ba dole muje na kai ka asibiti kar kace min a'ah.
Da haka Abdulkarim ya riƙe sa zuwa mota ga wani irin zafi da jikinsa ya yi.
Bayan likita ya gama duba shi ya yi masa fixing drip, kafin ya bar ɗakin ya dube Abba cike da kulawa ya ce "Abba wacce irin damuwa ce ka jefa kanka ciki? Gashi nan har jininka ya hau.
Kauda fuska Abba ya yi da barin kallon likitan shi kaɗai ne zai iya misalta adadin raɗaɗin da yake ji a ciki da wajen zuciyarsa.
"Ni fa wannan al'amari ya fara ɗaure min kai Abba haka kwanaki Alhaji ya yi jinya same case with you blood pressure Dan Allah ku dinga saka dangana a zuciyarku, duk abunda ka ga ya faru da ɗan adam muƙadarri ne daga Allah subhanahu wata'ala mu 'yan adam ba mu isa mu canza ƙaddarar mu ba. Burina na zama soja tun daga yarinta nake da wannan buri ko a mafalki ban taɓa hango kaina a matsayin likita ba. Amma sai gashi Allah ya mayar dani likita da nayi imani da babu mai yi sai Allah sai gashi a yanzu ina alfaharin kasantuwa ta a matsayin likita, tuni na manta da wancan buri nawa. Nasan kasani Abba yarda da ƙaddara yana cikin rukunan imani ɗan adam ya yi imani da ƙaddararsa mai kyau ko kuma marar kyau shiga damuwa ko tsananta tunani ba zai taɓa canzawa bawa ƙaddararsa ba. Sai ma ya daɗa jefa mutum a mugun yanayi, a matsayina, na family doctor ɗinku ina shawartar ka da ka cire damuwa aranka ka miƙawa Ubangijin talikai lamarin ka in-sha-Allahu za ka ga ribar hakan. Ka kwanta ka yi bacci domin kana buƙatar hutu zuwa anjima idan jikin naka ya yi kyau sai mu sallame ka, ka tafi gida.
Likitan ya ƙarasa magana tare da ɗan bubbuga gefen kafaɗar Abba sannan ya fi ce. Abdulkarim ya ja kujera ya kai saiti da fuskar Abba yake, ya zauna bai ce dashi uffan ba sai faman kallon fuskar Abban yake yi wacce har ta fara bayyanar da rama, Abba ya yi ƙoƙarin buɗe bakinsa ya yiwa Abdulkarim magana cikin sauri Abdulkarim ɗin ya girgiza masa kai tare da ɗora yatsansa akan lips ɗin Abba "shhh! you don't have to talk and just sleep like the doctor said you need to rest.
Sai kawai AB ya lumsashe idanuwansa babu jimawa bacci ya ɗauke shi, cike da zallan tausayinsa Abdulkarim ya kama hannunsa wanda bai da drip ya haɗe cikin nasa.
*MADAWAKI MANSION*
"Mommy gani.
Rumaisa ta faɗa sa'ili da ta shigo ɗakin mahaifiyarta Hajiya Jamila.
"Ne me wuri ki zauna za mu yi magana.
Sai da Rumaisa ta sauke ajiyar zuciya kafin ta nemi sofa dake girke a ɗakin ta zauna kallon da Hajiya Jamila ke mata yasa duk sai ta ji ta tsargu babu shiri ta sadda kanta ƙasa zuciyarta tana mata wani irin bugawa "Rumaisa!
"Na'am mommy!
"Meke damunki ne? Kwana biyu nan na kasa gane kanki kin daina ci abinci walwalarki ta ragu, kullum kina ƙunshe a ɗaki kamar wata marainiya marar gata oya tell me what's really bothering you. Remember I'm your mother and I should know your worries idan ina da maganin damuwar taki sai na taimaka miki.
Rumaisa tana ji waɗannan maganganu sun fito daga bakin mahaifiyarta sai kawai ta ji zuciyarta ta karye ta zube guiwayoyinta ƙasa ta rushe da matsanancin kuka cikin muryar kuka take faɗin "Mommy, I love him so much, I can't live without him, he is the love of my life ba zan iya jure rashin sa ba, ki taimake ni Mommy soyayyar Abba Bashir za ta kashe ni.


#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.








Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/13/2023, 10:30 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


#love Story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye novels


022.


*AREWA BOOK*: jeeddah3256








Da gundarin mamaki Hajiya Jamila ke kallon Rumaisa wacce ke wani irin gunji kuka kaman ranta zai fita wani kalan tausayin 'yarta ta ya dirar mata a ƙahon zuciya, tun farko ba ta so Alh Bello madawaki ya rushe auren Rumaisa da Abba ba. Domin Abba yaro ne mai cike da nagarta wanda kowacce uwa za ta so ta haɗa zuri'a dashi har ga Allah ita tana so Abba da 'yarta, kawai dai Alh Bello ya fi ƙarfinta ne. Amma a wannan karan ba za ta yarda sanadin son zuciyarsa 'yarta ta cutu ba. Duka 'ya'ya nawa ne da ita da za ta bari ya salwantar mata da rayuwar guda daga cikinsu musamman ma Rumaisa da take yiwa wata irin ƙauna kasancewar ta Auta.
Dukka yaranta uku Raliya ita ce babba ta yi aure tana zaune a Abuja har da albarka yara guda biyu mace da namiji sai Safwan shi kuma yana karatunsa a Cyprus.
Hajiya Jamila mace ce mai azabar son 'ya'ya sai kace magge ita idan akan yaranta ne ba abunda ba za ta iya aikatawa ba. Saboda haka rai ɓace ta baro wajen zamanta ta kama kafaɗun Rumaisa ta miƙar da ita tsaye da sauri Rumaisa ta faɗa ƙirjinta, ta ƙara sakin kuka mai ƙarfi har da wani sheɗewa take yi ta kama hannun Ammi ta ɗora a saitin da zuciyarta take, wani irin bugawa zuciyarta ta ke yi wanda ya zarce ƙa'ida wani irin ɓacin rai ne ya lulluɓe Ammi dole ta yi gaggawar ɗaukar mataki, ta nemowa 'yarta muradin zuciyarta. Cikin sigar rarrashe Ammi take shafar gadon bayanta "that's enough, and stop crying, I don't want you to cry I'll try to get to you what you want ba dai Abba ne kaɗai damuwanki ba?"
Rumaisa ta yi nodding head "To karki damu matuƙar ina numfashi sai kin zama matar Abba.
Sai ga Rumaisa ta washe haƙora tana dariya Ammi tana riƙe da hannunta suka fito zuwa dining room da kanta ta dinga feeding Rumaisa just like a baby.
*KIM'S AUTOMOBILE INDUSTRY LAGOS*
Yana zaune a office ɗinsa ya saka laptop ɗinsa a gaba yana kallon samfurin wasu motoci da za su iso nan da 30 days a kamfaninsu, dake Cotonou so yake ya gama settled ɗin abubuwa na wannan kamfani kafin ya wuce Cotonou ɗin a can ma ya tabbata zai tarar da ayyuka masu yawan gaske. Yawan aiki ko kaɗan baya damu Alh Aliyu na Uku a rayuwarsa ba abinda ya fi so da ƙauna irin ya yi keeping kansa busy akan harkokin kasuwancin sa. Ko kaɗan baya da sha'awar gidan sarauta da ita kanta sarauta he's always want to achieve his goal to be the most popular number one business tycoon hakan kuma ba zai taɓa samuwa ba idan har bai janye jikinsa daga gidan sarauta ba. Shiyasa koda yaushe yake gudun masaurata a wasu lokutan shi yake ƙiƙƙira tafiya don kawai ya yi nesa da masarautar kudu. Burinsa ace yana da ɗa namiji wanda zai dinga taimaka masa ya tabbatar da yana da yaro namiji dole zai zama jajirtatce kaman shi. Daga baya da ya zauna ya yi nazari sai yaga dacewar ya jawo 'yarsa ta fari a kasuwancin nasa ita ma za ta iya wannan ne ya bashi damar sanya Anaal ta karanci fannin ilimin kasuwanci tun daga sanda ta kammala karatunta, ta fara tayashi da wasu abubuwa sai gashi cikin ƙanƙani lokaci kwarewar Anaal ta kai matakin da bai taɓa zata ba. Yarinyar tana da wata irin baiwa ta ban mamaki ga ta dai ƙaramar yarinya she's just twenty-five years amma tana da wani irin business talent tamkar dai shi. Shiyasa bai taɓa kukan rashin haifar ɗa namiji ba.
Anaal ce ta fito daga office ɗinta jikinta sanye da Palazzo haɗe da string blouse ta ɗora ƙatuwar farar jacket wacce ta sauko har zuwa ga guiwayoyinta, saboda yau garin na Lagos an tashi da wani irin mashahurin sanyi ga baki ɗaya ta rufe maɓallai(bottoms) ɗin rigar wanda hakan ne ya rufe ainihin shigar jikinta, ta yi rolling da scarf black in colour takalmin ƙafafuwanta sneakers ne baƙaƙe sosai shigar tai bala'in yi mata kyau. Direct office ɗin Zaheed ta nufa yana zaune akan kujararsa jikinsa sanye da dark blue ɗin long sleeve shirt tare da black chino jeans ya ɗora cardigan sweater mai gajeren hannu akan rigar tasa kunnensa manne da waya tana zuwa a fusace ta jefa masa file ɗin hannunta kallon sama da kasa ya yi mata kafin ya cire wayar daga kunnensa "real disturber ya aka yi ne?"
Ya yi magana yana ƙunshe dariyarsa "whats wrong with you bro Zaheed? almost a week ace ba ka ƙarasa aikin wannan file ɗin ba. Me kike so na ce da Abbu idan ya nemi na tura masa da bayanai dake cikin file ɗin?"
Miƙewa ya yi iso gabanta ya shammace ta sai ji ta yi ya kama waist ɗinta ya yi sama da ita kaman yadda ake ɗaga yara ƙanana ya zaunar da ita kan desk ɗinsa ya yi tsaye gabanta kafin kuma ya kama kunnen sa dukka biyu "No! No! Ƙarka ma fara yau kam ko kaine shugaban masu magiya na duk duniya ba zan karasa maka aiki nan ba.
"Anaal please.
"No! Na ce a'ah.
"I swear this weekend I will take you to the beach and I will buy you everything you want.
"I am tired of the bribes you guys are giving me and leaving me with a lot of work na gaji da tarkace shopping ɗin da ku ke yi min jiya ma sai da na kai wasu kayayyaki orphanage kuma ni ba mahaukaciya bace da zan bari ka dauke ni ka kai beach cikin wannan uban sanyi salon mura ya kama ni I'm not stupid like you think I know what I'm doing saboda haka ka bani wuri na wuce na baro lot of work a office ɗina.
Da sauri ya mayar da ita zaune ya ƙara langwaɓar da kai ya ci-gaba da yi mata magiya har sai da ta amince ɗin za ta ƙarasa masa aiki cike da farin ciki ya sumbace forehead ɗinta ta kai mishi duka a shoulder "lazybones.
Ta furta tana dalla masa harara "Hey don't call me that.
Zaheed ya faɗa yana ya mutsa fuska.
"Me yasa?
"Saboda I'm not lazy kawai dai dan na faɗa soyayya ne gardin soyayya yake hana ni aiki ke ma kinsan ada ba haka nake fa don duk lazineess ɗina na fi Zeeyad.
"Hi guys whats going on here me kuke shirya wa ne da ba ku nemi ni ba tsabar ga ku one soul in two bodies ko?
Zeeyad ya yi magana tun kafin ya ƙaraso cikin office ɗin. Jikinsa sanye da exactly irin kayan jikin Zaheed.
A lokaci guda Zaheed da Anaal suka sheƙe da dariya har suna tafawa.
"Ba wani abu mai muhimmanci bane kaman dai yadda kai da shi ku ka saba yi min magiya tun muna nursery school na yi muku rubutu yanzu ma da muke age of twenty-five ba ku canza ba you guys duk ranar da na juya muku baya basan ya rayuwarku za ta kasance ba.
Anaal ta ƙarashe magana tare da sheƙewa da dariya.
Zeeyad ya dungure mata goshi yana faɗin "dallah rufe mana baki! Haka kawai da ranmu da lafiya mu mayar da kanmu agogo ba mu da hutu sai aiki mu ba irinki bane muna bukatar mu more ƙuruciyar

16 / 80