Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   61 / 80

180K to 183K   out of 237.2K words

dasu ba.
"Ko ba kifin rijiya ba.
AB ya faɗa yana mata malalaci kallo.
"Habibi da gaske idan ka bani special gift ni kuma nayi maka alƙawari da zarar wannan munafukin jini ya ɗauke sai na gwagwaje ka da zafafan styles har sai ka ce ka ƙoshi.
"Uhm! Ina fatar dai ba men power za ki sake bani ba?"
"Kai Habibi abun da ya wuce ka daina tado shi nima bansan yana haifar da illa ba da ko kusa ba zan ba ka ba ai kasan ina sonka ko kusa ba zan so abun da zai cutar da kai ba.
"To gayamin me kike so na ba ki a matsayin tukuici ɗin tun da kika fara wannan zance na tabbata idan har ba tukuici na bayar ba za ki barni na huta ba amman dai ki tuna da alkawarin da kika ɗauka.
"In shaa Allah ba zan manta ba wayoyina nake so ka canza min kasan latest one sun fito.
"Ya za a yi nasani tun ba wayoyi nake sayarwa ba da dai motoci kika ce wannan ne nake da cikakkiyar masaniya akai.
"Ai kuwa dai to ni dai iphone 15 pro max nake so da samsung galaxy s24 ultra as my gift.
Ta ƙarashe magana tana wani narkewa.
"To su kuma waɗannan na hannunki, ki yi yaya dasu?"
"Sayarwa zan yi nasha shagalina da kuɗin.
Girgiza kai kurum AB ya yi tun ba yau ba ya fahimci halin Rumaisa naso spending kuɗi a wofi don kawai a zauna lafiya yasa ya biye mata suka je shagon siyar da waya ta zabi dukka wayoyin biyu da tace tana so ya biya kuɗin suka nufo gida, tsabar farin ciki da Rumaisa take ciki har baya misaltuwa, koda suka iso gida ana kiran sallar isha Ab ya wuce masallaci ita kuma ta kwaso tarkace shopping bags ɗinta ta shigo gida a main parlor ta tarar da Aydah da Huwaila, Aydah tana zaune ta ɗora ƙafafunta akan centre table Huwaila tana cire mata farce, batareda da sallama ba Rumaisa ta ƙaraso tana zuwa gaban Aydah ta zube shopping bags ɗinta ta faɗa kan kujera dake kusa da Aydah tana faɗin "Washhh! Allahna na gaji sosai jikina duk ciwo yake Habibi ya gajiyar dani ba kaɗan ba Aydah kin ga yawon da muka dinga yi sai da na fara masa kuka sannan fa ya amince muka dawo gida da har yace a hotel za mu kwana naƙi amincewa, na ce ba za a yi haka dani ba mubar 'yar yarinya mu ita kaɗai a gida.
Ta ƙarashe magana tana shafa kamatun Aydah tare da sakar mata shu'umin murmushi, nan da nan fuskar Aydah ta canza tayi kici-kici wani irin malolo abu ya zo ya tokare mata ƙahon zuciya. Huwaila ta dakatar da abun da take yi ta zubawa Rumaisa ido sai lokaci Rumaisa ta kalleta a sheƙeƙe ta ce "Ke mai aiki tashi ki bar cikin parlor nan idan kika ga matan gida suna conversation a tsakanin su ki daina baza kunnuwa kina saurare wannan ai salon munafuci ne da so haɗa husuma, duk iya munafucin ki da kutunguilarki ba ki isa ki raba mana kawunan mu ba don ni da Aydah kanmu a haɗe yake tamkar ya da ƙanwa muke ko babyn yaya Abba?"
Ta ƙarashe magana tana kashe wa Aydah ido. Tuni idanuwa Aydah sun fara ciccikowa da hawaye.
"Tashi mana munafukar banza da wofi kina gafda da bari gidanan ba zan yi sake ki raba mana zaman lafiyarmu.
Rumaisa ta faɗa a tsawace da sauri Huwaila ta tashi ta nufi ɗakinta.
"Baby Aydah zo ki tayani duba kyaututtukan nan da yayanki ya yi min idan ma da akwai abun da kike so a ciki ki ɗauka ni da ke ai mun zama abu ɗaya.
Gani yadda Aydah take mutso-mutso da baki tana ƙoƙarin danne hawaye Rumaisa ta saki murmushin mugunta ta soma firfito da kayayyakin dake cikin bags ɗin tana zubewa a gaban Aydah daga ƙarshe ta fito da wayoyinta "Aydah kin ga wayoyina da habibi ya siya min a matsayin tukuici budurcina da na kawo masa kin san fa haka maza suke yi da zarar su ji daɗin mace sun dinga kashe mata kuɗi kenan tamkar ba su san zafin neman su ba. Yanzu ki duba wayoyina duka yaushe ya siya min su amman har ya sake siya min wasu kai Abba Bashir duniya ne.
Hawaye da Aydah take ɓoyewa ne suka kubce mata Rumaisa tana gani ta zaro idanuwa "la hula wala kuwwati illah billah! Aydah kuka fa kike yi? Ke kuwa me ya same ki haka kike zubda hawaye zo, nan ƙanwata faɗamin waya taɓa ki?"
Buge mata hannu Aydah tayi ta miƙe da gudu ta haura sama tana gunji kuka, Rumaisa ta bi ta kallo sai kuma ta kece da muguwar dariya, har da su buga ƙafa a tiles "shegiyar yarinya mai baƙin kishin tsiya da sannu zan fitar dake gidanan sai na nuna miki bambancin dake tsakani babba da yaro.
Tana magana haɗe da mayar da kayanta cikin shopping bags ta haura ɗakinta, zuciyarta wasai!
AB yana dawowa daga masallaci sai ga Abdulkarim ya kawo masa ziyara suka tsaya a parking lot cikin motar Abdulkarim ɗin.
"Ak saukar yaushe?"
AB ya faɗa yana kallon Abdulkarim.
"Ɗazu da yamma hankalina yana gunka tun sanda ka bani labari abun da Rumaisa tayi maka.
"Uhm! Bari kawai abokina Rumaisa ta kashe ni tasa na aikata abin kunya na je na haikewa 'yar mutane sai da ta kwanta gadon asibiti.
AB yana dasa aya Abdulkarim ya kece da dariya "Kai dai ba wani nan daman can ranka ya biye shi ne fa ka maida mugun yawu.
"Mtss! Matsalata da kai Abdulkarim mugun ɗan iska ne kai ina faɗa maka gaskiyar abun da ya faru kai kuma kana shigowa da salon iskanci.
"To na ji na daina amma wane irin mataki ka dauka akan Rumaisa?"
"En! To na daina nuna mata fushina na kuma gargade ta kar ta kuskura ta sake zuba min komai a abun sha.
"Mtss! Ni na zaci ka tura ta gidan ubanta a koya mata tarbiyya da ba a mata ba tun farko.
"Akan me zan tura ta gidansu bayan ina sonta kuskure ne kuma ba wanda baya kuskure.
"To ita kuma Aydah fa a wane matsayi ka ajiye ta kasan dai yanzu ta zama bazawara dole ka zauna da ita tunda dai kaine wanda ya kawar mata da budurcinta?" Ko kuma dai har yanzu kana nan akan bakarka na sakinta da ka ce za ka yi?"
AB ya shafa kwatancce sajensa yana kallon Abdulkarim a dage kafin ya ce "Banaso bin diddigi Abdulkarim Aydah dai mata ta ce ba ruwanka da yadda zan yi da ita ban da ma kana munafuki yaushe na ce da kai zan sake ta?"
Zaro idanuwa Abdulkarim ya yi "Ni ne munafuki Ab?"
"Kai ɗin ko tsoronka nake ji da ba zan kira ka da munafuki ba?"
Sheƙewa da dariya Abdulkarim ya yi har yana dukan dashboard ɗin mota "wallahi-azim AB ka ji kunya ka yi amanka ka lashe ɗan iska kawai mai cika bakin banza dallah kalle ka shirgegen ƙato da kai kana shigewa ɗaka da kwaila ko ba haka ka kira ta dashi ba?"
"Mtss! Banza munafuki wanda bashida mantuwa koma dai mene ne ba haramun na aikata ba ehee barantana mutum ya dinga ya madidi dani.
"Yoo amman dai ka yi abun kunya.
"Idan mutum ya cika shi ma ya je ya yi abin kunya irin wanda nayi.
"Allah ya tsare gatari da sarar shuka ni bana cika baki irin naka.
Dariya kurum AB ya yi tare da faɗin "Ai sai ka yi Baby dai ta zama ni na zama ita tun da almurranmu sun daidaita na kuma riga na zura ƙwallo a raga duk abun da za ka faɗa ba zai dame ni ba domin ni kaɗai nasan irin duniyar da kwailata ta kaini, kai bari kawai Abdulkarim idan ana sallah ba'a magana Baby Aydah tayi hundred percent Baby Aydah wata duniya ce ta daban.
Zaro idanuwa Abdulkarim ya yi cikin kaɗuwa yake kallon Ab ya kasa yarda waɗannan maganganu daga bakinsa suke fitowa anya kuwa Ab kansa ƙalau ko kuma dai ya zare ne. Fitilar dake cikin mota Abdulkarim ya kunna ya shiga ƙarewa kyakkyawar fuskar AB kallo yayin da AB ya dage girar ido ya yi masa kur da nasa idanuwa.
"Ni ne dai Abba Bashir abokinka.
"Wallahi kuwa kaine Abba Bashir amma kuwa Abba kai ɗin tantiri ɗan iska ne lamba ɗaya.
Abdulkarim ya faɗa yana tu'ajjabin.
"Yanzu kam ka yarda dani ni ne ko?"
"Uhm! Na yarda amman Dan Allah ka dinga lallaɓa 'yar mutane kada ka mayar da ita sex addict.
"Wannan kuma babu ruwanka tsakanina ne da matata.
Har suka yi sallama Abdulkarim bai daina mamakin Ab ba duk da daman can ya sa ran faruwar hakan amman bai zaci hakan da wurwure ba.
Direct Ab ya wuce ɗakinsa ya yi wanka ya sako dark green ɗin pajama yana zuba ƙamshin turarensa ya fito parlornsa ya zauna ya kunna tv yana kallon news sai ga Rumaisa ta shigo cikin ɗaya daga cikin sexy transparent night gown ɗin da ta siyo sosai rigar tayi bala'in yi mata kyau cikin tafiyar jan hankali ta nufi socket ta saka sababbin wayoyinta a charging. Ta dawo kusa da AB ta zauna ta dauke hannunsa dake kan hannun kujera ta haɗe da nata a hankali take massage ɗin tafin hannun nasa.


#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.










Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[1/26, 2:28 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels






083.






Har kusan ƙarfe goma na dare bai ga Aydah tazo wurinsa ba A hankali ya zare jikin Rumaisah daga nasa ya miƙe tsaye ya saka (casual slippers)a kafafunsa,da mamaki Rumaisah ke faɗin."ina kuma zaka je?"
"Bara na duba baby Aydah nayi mata sai da safe.
Ya faɗa batareda ya kalleta ba ya juya ya nufi ƙofar barin parlorn banda bugawa babu abunda zuciyar Rumaisah keyi,idan kuma daga nan ya kwana a dakin Aydah fa.?"nan take wata zuciya ta kwabeta akan faɗin.
"Ai idan yana da kunya shi ma bazai farawa ba.
Akan idanunta ya fice daga parlorn tana jin yadda zuciyarta tayi wani irin nauyi tana addu'a kafin ta gama shan maganin nan jinin ya tsaya,kafin kwanakin amarcinta su kare ta fara raba kwana da Aydah sai da yayi knocking yaji shiru ya kama handling ya ɗan tura ga mamakinsa a rufe yaji ta da alamar tasa key ta ciki ɗan kwankwasa wa ya shiga yi yana kiran sunan Aydah lokacin tana kwance akan bed ɗinta tayi ruf da ciki da rigar bacci ajikinta marar nauyi tana jin yadda yayanta ke kiran sunanta yana famar bugun kofa tayi masa banza haushinsa shi da Rumaisah take ji matuƙa kenan yayan nata ya fara zama munafuki mai son kansa da yawa meyasa itama da ya karbi budurcinta bai yi tunanin yimata kyauta komai kankantar ta ba.?"sai Rumaisah zaɓin ransa wacce zuciya da ruhinsa ke so sai ita wacce aka yi masa auren huce haushi da ita.
Idan ta tuna siyayyar da Rumaisa ta zube mata a gabanta sai taji wani irin raɗaɗi a ƙirjinta duk bugun da AB ya riƙa yiwa kofa bai sa Aydah ta buɗe ba. Sai ma bin kofar tayi da wata irin harara tamkar yana ganinta a zuciye AB yabar kofar room ɗin yana tunanin wane irin iskanci ne ke damun Aydah yana buga mata kofa tayi masa banza. Yasan in har bacci take bata da nauyin bacci da gangan kawai taki buɗe masa kofa zuwa yayi ya wuce Rumaisah ya nufi master bedroom ɗinsa batareda yayi mata magana ba. Da kallo Rumaisa ta bisa tana sakin Murmushin mugunta
Dan tana jin irin bugun kofar da yake yiwa Aydah Amman taki budewa.
Koda ta samesa dakin har yayi light 0ff yabar (dim light.)a hankali Rumaisa ta hau kan bed ɗin tana kwantar da kanta a bayansa tana shafa ƙirjinsa cikin wani irin salo.
Ƙoƙarin cire hannunta yake cikin jikinsa ko kaɗan baya cikin yanayin da zai biyewa Rumaisah ɗin,kuma baya so tafiya tayi nisa tunda ba lafiya gareta ba komai ya kwace masa juyowa yayi yana sakata cikin jikinsa duka cikin sanyin murya yake faɗin."muyi bacci Rumaisah,ɗan haɗe fuska tayi tana faɗin."saboda baka da lokacina baka bukata ta saboda kaga bani da lafiya.!"
Ta ƙarasa magana cikin rawar muryar da AB yaji wani iri
"Haba Rumaisah!
Ya faɗa da wani yanayi a muryarsa. "Haka ne mana da ina da amfani a wurinka ba zan taɓa ka ba ka nuna baka so.
Tana rufe baki ya shiga romancing ɗinta dan kurum ya faran ta mata rai sai da ta samu natsuwar da take buƙata ya juya mata baya yana sauke wani irin numfashi mai wahala,a daren ba wani baccin kirki ya samu yayi ba yayin da Rumaisah tayi baccinta cikin jin dadi da natsuwa. Yana dawowa sallar Asuba,ya koma ya kwanta daman saboda fushin da yake yi da Aydah ko kofar ɗakinta bai kalla ba baran tana ya tasheta tayi sallah.
Haka ba ƙaramin faran tawa Rumaisah yayi ba. Ashe Aydah har yanzu wawuya ce doluwa ce ta gaske bata ma san menene kissa da makircin kishiya ba da sannu zata koya mata hankali.
Karfe bakwai Rumaisah ta nufi kitchen daidai lokacin Huwaila ta fito
Huwaila ta gaisheta babu yabo babu fallasa ta amsa tana faɗin."kawai tayi tafiyarta yau ita da kanta zata haɗawa mijinta break fast. Dan kallonta Huwaila tayi kafin ta juya tabar kofar kitchen ɗin. Duk gatan Rumaisa babu kalar abincin da bata iya sarrafawa ba,Ammi batayi wasa da wannan bangaren ba duk son da take yiwa ya'yanta. Cikin ƙanƙanin lokaci gidan ga baki ɗaya ya haɗe da ƙamshin girkin Rumaisah. Ko Huwaila da take zaune a ɗaki ta jinjina wa iya girkin Rumaisa a gefe tana ta tunanin yadda
Aydah zata mayar da hankali ta koyi girki, dan da alama ko ta bangaren girki kawai Rumaisa zata iya sace zuciyar AB kusan ƙarfe takwas da mintuna goma,Rumaisah ta gama jera komai akan dinning table kai tsaye ɗakinta ta koma daman kafin ta sauko kasa ta gyara ɗakin haka ma parlor AB ta share wanka tayi ta haɗe cikin wata bingilar rigar kanti wacce rabin cibiyar ta a waje sai skirt da bai gama rufe cinyoyinta ba. Kwaliyya tayi sosai tayi wankan turare da khumra sauka kasa tayi zuwa ɗakin Huwaila,a bakin kofa ta tsaya tayi gyaran murya
Da izza take kallon Huwaila tamkar bata son magana ta fara da cewa "waye ma kike da suna?"
Da sauri Huwaila ta saukar da kanta ƙasa ta ce.
"Huwaila!
Dan tabe baki Rumaisa tayi tana faɗin."mu je ki yimin mopping ki wanke min toilet.
Da haka ta juya huwaila na biye da ita a baya tana mamakin muguwar kissa irin na Rumaisah lallai sai tayi da gaske akan baby Aydah da mugun son jiki yayi mata yawa kai tsaye Rumaisah ta gwadawa Huwaila yadda zata wanke mata toilet tana gama nuna mata ta fito da burner a hannunta ta zuba turaren wuta ta nufi part ɗin AB har cikin bedroom ɗinsa ta shiga da burner ɗin bed kawai ne bata gyara ba dan yana bacci akai zama tayi a gefensa ta cigaba da kallon kyakkyawar fuskarsa ta dauki tsawon lokaci tana kallonsa tamkar zata cinyesa dan so.
A hankali ta hau gadon ta kwanta gafda fuskarsa har tana jin saukar numfashinsa tsinin hancinta ta rika goga masa tana ganin yadda ya shiga ya motse fuskarsa still bai buɗe idon ba cigaba da goga tsinin hancinsa tayi
wanda yasa dole ya shiga buɗe idonsa
masu cike da bacci ya ɗora fuskarsa acikin fuskar Rumaisah yana jin yadda jikinta ke fitar da wani irin kamshi, ta langwabe kai tana kallon sa sai kuma ta sumbaci gefen fuskarsa
"Mun gaisa,mu kara gaisawa.
Ta faɗa tana sumbatar goshinsa kanne masa ido tayi cikin taushin murya take faɗin."wanka ko break fast?
miƙewa yayi zaune gamida jawota dukka cikin jikinsa a hankali ya ɗora hannunsa akan abunda yafiso da kauna ajikinta ɗan shagwabe fuska tayi sai da ya gaisa dasu iya son ransa, sa'annan ta haɗa masa ruwan wanka a toilet yayi wanka ita ta taimaka ta fito masa kayan da zai saka tunda tasan dole zai je office sai kusan ƙarfe 9 suka fito kasa hannunsu sarƙe cikin na juna dan yau Rumaisah ta faɗa masa acikin dinning area take so suyi break fast.
"Habeebi yau da kaina na shiga kitchen na yi maka break fast idan ka gama ci ina sauraran tukuici ba zan yi saurin yabon kaina ta wannan bangaren ba.
Ta faɗa da murmushi a fuskarta tasa hannu tana buɗe warmers ɗin wasu irin yawu AB ya shiga hadewa da sauri dan yasan ƙamshin girkin huwaila, ya ji wannan its so different akan nata,tana kallon yadda yake wani lumshe ido yana buɗewa sarving ɗinsa tayi ,ta zuba masa hadadden kunun gyadar da tayi mai madara.
"Yau fa ni zan ciyar da mijina.
Ta faɗa a ɗan shagwaɓe,murmushi yayi yana ware mata manyan idanunsa,daga nan cikin dinning ɗin AB ya daga murya yana kiran Huwaila da sauri ta ƙaraso wurinsa ta zube gabansa tana gaishesa ya amsa yana faɗin taje ta kira Aydah suyi break fast nan take annurin fuskar Rumaisah ya canja har ga Allah bata ji daɗin yadda AB yace a kira Aydah ba. kwankwasa kofar ɗakin Aydah Huwaila tayi jin shiru yasa ta kira sunanta Aydah na jin muryar Huwaila tayi saurin saukowa daga kan bed ɗin still kayan bacci ne ajikinta tazo ta buɗewa Huwaila kofa.
Sororo! Huwaila ta tsaya tana kallon
Aydah ganin ko wanka ba tayi ba kayan bacci ne ajikinta,tana ganin irin wankan da Rumaisa tayi ita da Abba ya kamata ta zauna ko yaya ne ta yiwa Aydah karatun ta natsu,da kyar Aydah ta gaisheda Huwaila ita dai Huwaila bin ta kawai take da kallo ganin yadda idonta ya ɗan kumbura alamar dai tayi kuka.
"ki sauko yanzu yayanmu na jiranki zaku yi break fast idan kin natsu mayi magana dan na lura kamar bakya cikin natsuwarki.
Da sauri Aydah ta katse Huwaila tana faɗin."Ni na faɗa masa ina jin yunwa ne?"kawai suyi abin

61 / 80