Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   28 / 80

81K to 84K   out of 237.2K words

tortulin ɗin wanda bata ko tsaya yi diluting ɗinsa ba ta shiga sha tana shanye wa ta dubi jikin bango ta maka bottle ɗin ya fashe in to tiny pieces, sai kuma ta shiga fizgar sumar kanta da dukan hannayenta ta saki wani irin ihu kafin ta sulale kan marbles ta cigaba da gunji kuka wanda sautinsa baya fita sosai a dalilin dusashewar da muryata ya yi, sannu a hankali take lumshe idanuwanta da suka yi wani irin ja kamar an baɗa mata barkono, bata ɗauki dogon lokaci ba naunnayen bacci ya yi awon gaba da ita.
Aydah tana shiga ɗakinta ta cire uniform ta maye gurbin su da A-shape gown na atamfar chiganvy gold ash and sky blue in colour ta haɗe kitson kanta tun wanda yaya Abba ya kaita aka yi mata ta ɗaure shi da band ta dauko hula da aka yi mata da ɗan ƙwalin atamfarta ta kifa akanta ta daidaita zaman hular kanta, ta shafa powder da man lebe sannan ta fesa turare duk abinda take yi tana yinsa ne cikin mutuwar jiki bata ji kwari a jikinta ko kaɗan yadda take ji jikinta tamkar an ɗaɗɗaure mata shi da sassari. Ga irin fargaba da faɗuwar gaba da take yi wanda ta rasa na menene, gefen gado ta zauna tana sauke numfashi ta dauki mintuna goma a haka kafin ta miƙe ta sauko ƙasa. Siyama kaɗai ta isko a dinning area ta ja kujerar dake facing ɗinta ta zauna tana faɗin "yaya Siyam me kesa faɗuwar gaba?" Yau tun da na tashi nake jin faɗuwar gaba haɗe da wani irin tsoro-tsoro.
Aydah ta ƙarasa magana cikin raunatacciyar murya. "Ba dole ki ji faɗuwar gaba ba nan da ɗan wani lokaci za ki shiga jerin manyan mata.
Siyama ta faɗa cikin zuciyarta a bayyane kuma sai ta ce "A duk sanda kika tsinci kanki acikin irin wannan yanayi ki yawaita ambaton Hasbunallahu wal-imaal wakil! Ko menene za ki ga Ubangiji ya kawo miki shi da sauki.
"Toh!
Aydan ta faɗa a takaice kana ta zare ɗaya daga cikin plates ɗin da ke kan dinning table ɗin ta zuba chips da wainar kwai sai tea da ta haɗa, Siyama tana kammala wa ta tashi ta koma cikin parlor, chips ɗin kaɗan ta tsukura ta shanye tea ɗin hatta da bakinta bata ji daɗinsa ta rasa appetite ɗinta. Ta dawo parlor wurin Siyama ta zauna kusa da ita.
Sai da Daddy ya kira Ab a waya sannan ya falka daga naunnaye baccin da yake yi, cikin mutuwar jiki ya ɗauki kiran, Daddy ne ya faɗa masa shi kaɗai yake jira ya amsa da gashi nan zuwa nan da mintuna goma, da sauri ya sauko daga gado ya wuce bathroom ya yi wanka yana fitowa ya tsaya a gaban dressing mirror ya goge jikinsa da hand towel ya shafe lallausar fatar jikinsa da lotion mai ƙamshi gaske. Farar shadda ya dauka a closet ɗinsa dinkin babbar riga wacce aka yiwa aiki da baƙin zare, sai ya saka bakar hula da baƙeƙen takalma sawu ciki. Ya yi tsaye yana ƙarewa kyakkyawar fuskarsa mai cike da haiba da wani irin kwarjini na musamman, shi kansa sai da ya yaba da irin kyawo da ya yi duk da ya ɗan yi rama amma hakan bai dusashe kyakkyawar halittar da Allah subhanahu wata'ala ya yi masa ba.
Ya ɗauki wayoyinsa ya fice walking majestically bangaren Daddy ya nufa ya yi sallama tare kutsa kai cikin parlorn ya tarar da Daddy da Alh Sanusi sai korafi Alh Sanusi ke yi masa a rashin sanarda shi da bai yi ba "A gaskiya yaya abinda kake yi sam ba ka kyautawa yanzu ace har yau ne ɗaurin auren Abba da Aydah bansani ba da ban ji a bakin shanu talla ba da shikenan sai dai daga baya na ji zance daurin aure ko?
Kafin Daddy ya bashi amsa ya tsikayi muryar AB yana gaishe dasu ya amsa masa yayin da Alh Sanusi ko kallon gefen da AB yake bai yi ba saboda wani irin tuƙuƙi baƙin ciki ke cinsa a zuciya ji yake kamar ya taso ya shaƙewa AB wuya ba zai sake ba har sai yaga ya daina motsi. Cikin takaici da tarin baƙin ciki ya cigaba da cewa "irin wannan halin shi ke ɓata zumunci fissibillahi ina ƙaninka uwa ɗaya amma ace banida darajar da za ka sanarda ni abinda ya shafe ka, tun-tuni na gama fahimtar ba kasafai nake da amfani a wurinka ba. Na tabbata da Hajiya tana raye da ba za ka dinga nuna min irin wannan wariyar ba.
Daddy ya yi sauri tarar numfashinsa yana faɗin "Ka yi haƙuri Sanusi ni ban ɓoye maka a bisa wata mummunan manufa ba na yi haka ne saboda banaso, ce-ce-kuce amma ka yi haƙuri za a kiyaye gaba.
"Ai haka kake cewa koda yaushe za ka gyara amman...
"Dallah ya isa haka Sanusi! Ka cika mita wallahi kamar wani tsohon dan shekara tamanin, haba na ce ka yi haƙuri an yi kuskure za a gyara amman sai mita kake yi, ko na sauko ne na zube guiwayoyina a gabanka na ba ka hakuri?"
"Har ni na isa ka durƙusa min yaya kawai dai na ji ba daɗi ne da yadda ka boye min babban al'amari irin wannan, ai ka Abba daminka ne ya tsike a gindin kaba domin mai sunan Hajiya da kake gani yarinyar kirki ce za ki ji dadin zama da ita fiye da wancan sakarya da aka fara aura ma.
Murmushin gefen baki AB ya yi yana sadda kansa ƙasa.
"Ina fatar yaya ka sanar da Jamila da raguwar 'yan uwanka da kuka haɗa uba?"Duk su ɗin ba wani damuwa suka yi da shiga sabgogin ka ba. Amman duk da haka suma suna da hakkin su sani.
Alh Sanusi ya sake faɗa duk wanda ya ji bakinsa na furta waɗannan maganganu zai zaci shi ɗin cikkaken mutumin kirki ne ba a san kuwa duk faɗi da cikar nahiyar Afirka da matuƙar wahala a sami mugun mutum irinsa.
Daddy ne ya amsa mata da cewa "Na faɗa musu sai dai ita Jamila na ce ta yi zamanta ta bari sai lokacin biki ta zo ayi da Ita yanzu ɗaurin aure ne kawai za a yi.
"To ai shikenan amman bari na kira Alh Umar da wasu daga cikin team members (employees)
ɗinmu domin bai dace ayi daurin auren guda na Chief Executive officer na moonlight automobile ba su sani ba. Kafin Daddy ya dakatar dashi har ya yi dismiss numbern Alh Umar haka ya dinga kiran mutane yana sanarda su. Daddy ya kalli AB ya ce "Abba tashi ka shiga cikin gida ka yi breakfast sai ka faɗawa maminku ta haɗa breakfast ɗin ɗaya daga cikin yara nan su kawo mana domin daga gani wannan sarkin mita ɗin ko karin kumallo bai yi ba, ya nufo nan.
Ab ya miƙe tare da amsawa da to ya fi ce. Bakinsa ɗauke da siririyar sallama ya tura kofar main parlor Siyama da Aydah ya gani zaune akan kujera ɗaya Siyama tana nuna mata waɗansu pictures a wayarta. Ƙamshin turarensa ya gauraye ko'ina a cikin parlor da sauri Aydah ta waiga ta sauke dara-dara idanunta akansa wani irin kyawo ya yiwa idanunta wanda yasa ta kasa janye ganinta akansa, shima tsintar kansa ya yi da tsare ta da manyan idanunsa, kafin cikin tafiyar tasa ta izza da zallan ƙasaita ya nufi ya soma tafiya tare da nufar dinning room, Siyama ce ta fara gaida sa ya amsa mata da ƙaramin sauti. Aydah ta taso da sauri ta nufi wurinsa tana faɗin "Yayanmu yau wannan wanka naka na juma'a ya fi na kowanne sati wankuwa ka ga kuwa wani irin bala'in kyau da ka yi Allah yayanmu kai ɗin kyakkyawa ne.
Kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauki mug ya haɗa tea Aydah ta ƙaraso ta gabansa ta tsaya tare da jingina bayanta ga dinning table guiwayoyinta suna manne da nasa ta yi folding hannayenta tana masa kallon kurilla. Duk surutun da take zuba masa ba wanda ya bata amsa saboda ganinta da ya yi yanzu nan ya tado masa da tabo abinda yake ji, yana ji wani irin abu ya tokare masa a maƙoshinsa ya kasa yarda wannan 'yar firitt ɗin yarinya ita ce nan da 'yan wasu awannin za ta zama matarsa. Ko kaɗan Aydah bata damu da shiru nasa ba saboda tasan halin yayan nata da miskilanci idan abin ya motsa har wata izza da taƙama yake yi magana ma wahala take masa sai kace jinin sarauta. Fitowar Mami kenan daga ɗakinta tun kafin ta ƙarashe saukowa daga bene ta hango su takaici ne ya lulluɓeta musamman yadda Aydah ɗin take tsaye a gabansa kusanci nasu ya yi yawa, saboda haka rai ɓace ta kira sunanta "Aydahhhhh!
A tsorace Aydah ta waiga kalli Mami wacce ta yi bala'in daure fuska ranta a ɓace ta iso cikin dinning area ɗin ko gizau AB bai yi ba tea dinsa kawai yake sipping "uban me kike yi a cikin jikinsa ba nace banaso na ƙara ganin ki tare dashi ba?" Watau ke mai kunnen kashi ko? Wannan idan ban tashi tsaye akanki ba nan take wannan gabjejen kato zai kwakule ki, bace min da gani shashasha kawai ina magana kin wani tsare ni da munafukai idanuwanki.
Yadda Mami ta daka mata tsawa tare da yi kanta yasa bata tsaya dogon tunani ba, balle har ta fahimci me take cewa ba ta kwasa da gudu ta fice daga dinning ɗin.
"Kai kuma na dawo kanka marar kunya fitsararriya, butulu ɗan gaba da fatiha ina ƙara gargaɗin ka a karo na ƙarshe kar na sake ganinka kusa da 'yata wallahi-tallahi idan ka sake bari na ganka kusa da ita duk abinda na yi maka kai ka janyo ka ji na gayama.
Da haka Mami ta juya ta nufi cikin parlor tana fadar bakaken maganganu. Duk abunda Mami take faɗa bai ɗago ya kalleta ba sai jujjuya mug ɗin hannunsa yake yi, wani abu mai nauyin gaske yake ji a maƙogwaronsa ga bugun zuciyarsa ya fara zarce ƙa'ida numfashi kuwa ya sauke yafi a kirga kafin kuma ya dawo yana ambaton Allah, ya ɗauki lokaci a haka kafin ya ji sassauci abunda yake ji ya tashi cikin tafiyarsa ta natsuwa ya shiga cikin parlor yana zuwa ya zube guiwayoyinsa gaban Mami cikin dashewar murya ya ce "Da ina da iko akan abinda kike so da ba zan miki gardama ko na musanta miki ba Mami, duk yadda ki kai da jin haushina ba zan daina yi miki kallon uwa ba. Banida wata mahaifiyar a duniya nan sama dake Mami, dukka abubuwa nan da kike aikatawa a gareni ban taɓa ji haushinki ba nasani kina yi ne domin samar mana natsuwa da kwanciyar hankali. Har ga Allah zuciyarta ta fi karkata akan zaman aure da Sadiya fiye da Aydah zan iya karɓar Sadiya a matsayin matata, ta sunnah amman ba zan iya kallon Aydah da wannan matsayin ba. Ki ma jingine zance ƙarancin shekarunta Mami ni ne nan na raine ta na ci kashi da fitsarinta duk wata kulawa da uwa za ta iya ba wa ɗanta irinsa na ba wa Aydah. To ta ya kike tunani akwai abinda zai iya shiga tsakanina da ita?" Da zan iya kallon cikin idanuwan Daddy na faɗa masa banaso aure nan Mami da na faɗa masa tuntuni, sai dai idan na aikata hakan tabbas a lokaci na cancanci a kira ni da abinda yafi butulu. Daddy ya yi min gatan da na rasa ya bani matsayi da asali ya so ni ya ƙauna ce ni sai na rasa abinda zan saka masa dashi sai bijirewa. Ba zan iya ba wallahi ba zan iya ba Mami ki gafarce ni.
Yana ƙarashe magana Mami ta kalle shi da fusatattun idanuwanta ta ja dogon tsaki "mtssss! To bari ka ji na gayamaka Bashir duk abinda za ka faɗa ba shi zai sa na bar Aydah ta yi rayuwar aure da kai ba. Duk wata ƙauna da nake maka a yanzu ta rikiɗe zuwa zazzafar ƙiyayya, idan har kai ɗan halak ne ba shege ba ka tattara kayanka kafin lokaci ɗaurin aure nan ka bar gidanan. Idan Alh ya nemi ka ya rasa dole ya haƙura. Daga baya ka dawo ka bashi haƙuri a irin kaunar da yake maka nan take zai yafe maka. Idan kuma ya daidaita sai a mayar da aurenka da Sadiya domin ita ce ta fi dacewa da kai fiye da duk wata mace a duniya. Hawaye da tun ɗazu AB yake danne wa ne suka subuce masa batare da ya sake ma Mami magana ba ya miƙe ya nufi ƙofar fita ya buɗe ya fice yana tafe zuciyarsa tana kisimamai ya bar gidan kawai ta hakan ce kaɗai zai sami salama. Ya rasa me yasa zuciyarsa ta kasa dangana ta karbi Aydah ji yake idan ya aureta ga baki ɗaya daraja da mutuncinsa za su zube a idon duniya. Gudu-gudu ya isa parking lot ya shiga motarsa ya bar gidan da zimmar ya tafi kenan baya tunani zai dawo nan kusa.


Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo




Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/26/2023, 2:09 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


*AREWABOOK*:3256


Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye


038.


Tuki kawai yake yi amma natsuwarsa ta gama fice wa daga gangar jikinsa ga wani azababben ciwon kai da yake ji, instead ya nufi hanyar fita daga gari kamar yadda tun farko ya kudurta aransa, sai kuma ya tsinci kansa da ka sa bin umarnin zuciyarsa sai kawai ya sauya akalar motarsa ya nufi Quarter house hotel ya kama ɗaki aka bashi key. Yana shiga ɗakin ko takalmin ƙafarsa kasa cire wa ya yi ya faɗa kan gado ya kwanta, shi kaɗai ne zai iya misalta adadin raɗaɗin da yake ji a zuciyarsa he wish Allah ya dauki ransa ko zai huta da wannan masifa. Dame zai ji da rashin asali ko kuma da rashin natsuwa da kwanciyar hankali.
Daddy da ya ji shiru ba a kawo musu breakfast ba ya tashi ya wuce Master bedroom ɗinsa ya yi wanka tare da shirya wa cikin farar shadda hatta da hular kansa fara ce a cewarsa yau farar rana ce a gareshi. Ranar da zai sake cika burinsa na aurawa Abba 'yar da ya haifa ta cikinsa wacce yake da cikakken yaƙini akanta ba za taɓa watsa masa ƙasa a ido ba. Wacce yake da tabbaci za ta dawo da farin ciki ga rayuwar Abbansa za ta zame masa bango majigina. Yana kammala shirinsa ya dubi Alh Sanusi dake zaune ya yi zugun abin duniya ya taro ya yi masa yawa a wannan stage ɗin ba abinda zai iya komai ya zo masa ne a kurarren lokaci, Alh Bashir ya shammace sa amman duk da haka ba zai kyaleshi ba dole zai dauki mataki.
Daddy ya ce ya taso su je bangaren Mami su yi breakfast tun da har yanzu ba a kawo musu ba ga shi lokaci sai daɗa karatowa yake yi, Daddy yana gaba Alh Sanusi yana biye dashi tun kafin ya ɗora hannunsa akan handle ya tsikayi muryar Mami lokaci da ta dakawa Aydah tsawa duk abunda ya wakana tsakanin Mami da AB tass a kunnen Daddy wani irin ɓacin rai ne ya lallube Daddy irin wanda tsawon rayuwarsa bai taɓa riskar kansa acikinsa ba. Har wani huci yake yi ya so a lokacin ya shiga parlorn ya zantar da hukunci da yake gani shine daidai sai kuma zuciyarsa ta kwaɓe sa yanke hukunci cikin fushi shi ke kawo danasani ko addini yanke hukunci cikin fushi ba abu mai kyau bane kuma an hane musulmi da aikata hakan. Sai kawai ya juya rai ɓace ya shiga motarsa Alh Sanusi wanda ransa ya yi fari kaman takarda shima ya shiga tasa mota ya bi bayan Daddy yana ji tamkar an yi masa bushara da gidan aljanna. Ganin yake komai ya zo ƙarshe. Saboda haka ya nufi gidansa zuciyarsa wasai bashi da sauran damuwa yanzu kuma sai karkata tunaninsa zuwa ga cimma muradinsa.
Babban abinda ya ƙara harzuƙa Daddy ya kira duka numbers ɗin AB waya tana ringing amma bai ɗaga ba. Dole Daddy ya kira Abdulkarim ya faɗa masa hali da ake ciki daga nan ya kira amininsa Alh Abbas matawalle suka haɗu a babban masallaci da za a ɗaura aure Ab da Aydah bayan an kammala sallar juma'a dubanan mutane suka shaida ɗaurin auren Bashir da Zulaiha akan sadaki naira dubu ɗari.
Sai da jama'a suka watse sa'annan Daddy ya ja Abdulkarim gefe yana tambayarsa ina yake tunani AB zai tafi tunani ya shiga yi kafin ya ce gidansa kaitsaye can suka nufa shi da Daddy maigadi ya tabbatar musu rabon Ab da zuwa gidan an kwana biyu. Duk inda Abdulkarim yake tunani za a gansa sun je, hakan ya ƙara linkawa Daddy ɓacin rai, har sun yanke shawarar komawa gida sai Abdulkarim ya tuna da Gps maps navigation ya yi sauri dauko wayarsa ya yi ya buɗe Data ya yi tracking numbern AB take ya nuna masa location ɗin da yake "Quarter house hotel! Abdulkarim ya furta a bayyane lallai Ab ya fara zama tantiri yaushe zai kawowa ransa AB zai je ya fake a hotel sau uku suna wucewa ta gaban hotel ɗin. Da sauri Abdulkarim ya dube Daddy wanda ke ta faman gyaɗa kai yana yi ƙwafa alamar da ke nuni ba iya Mami ba har AB ɗin sai ya yi mummunan saɓa musu.
"Daddy na yi tracking numbernsa yana quarter house hotel.
Hamdallah Daddy ya yi kana Abdulkarim ya ja mota suka nufi can.
Tun sanda AB ya shiga ɗakin hotel ɗin yake kwance ya ci kuka har fuskarsa ta kumbura ta yi ja abinka da farar fata bata da juriya ko kadan. Yana nan kwance har aka gama sallar juma'a ba zai iya tuna when last da ya

28 / 80