Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   39 / 80

114K to 117K   out of 237.2K words

haife shi baya mata ƙaunar da yake yiwa Maryama. To daman an ce wanda Allah ke yiwa faɗa baya faɗa dukkanin bukatun Maryama wurin Ubangiji talikai ta ke miƙa su shiyasa duk biye-biye bokaye Umaima har yau ta kasa cin nasara akanta, haka zalika ta kasa farraka zamanta da Ciroma.
"Kai kuma ku fice ku ba mu wuri manyan suna magana kun yi tsaye cirko-cirko kuma baza kunnuwa ku fita mana!
Ciroma ya yi magana cikin hargowa yana kallon yaransa ƙanana, da gudu suka fice kowanne ya nufi ɓangaren mahaifiyarsa.
"Meyasa Ciroma? Na ce meyasa za ka biyewa shaɗaniyar matarka har ta kai ka da aikata mummunan aiki irin wannan?"
Ciroma ya yi shiru ya rasa abun faɗa cike da tsanarsa Maryama take kallonsa kamin ta girgiza kai ta nufi ƙofar fita da sauri ya bi ta yana kiran sunanta ko waigowa bata yi ba balle ta tsaya ta riga tasan duk abun da zai mata ba zai ƙara ta da komai ba. Tun da aikin gama ya riga da ya gama burinsa mai martaba ya mutu ya kuma mutu to me ya rage?"
Kamin ka ce kwabo masarautar ta cika da mutane babu masaka tsinke ƙarfe 2:00pm za a yi jana'izar koda ƙarfe 1:00pm ta yi Aliyu na uku da yaransa sun iso mai babban ɗaki ta yi tawakalli sosai domin ita ma ke rarrashin ƙannai mai martaba take ta faman kukan saboda tashin hankali yaya Gimbiya har da suma tayi sai aka zuba mata ruwa ta farfaɗo. Mai martaba ya yi jama'a ta ko'ina zuwa ake ƙarfe 2:00pm aka masa sallah kamar yadda addini musulunci ya tanada aka wuce dashi makwacinsa na gaskiya da yake akwai maƙabarta acikin masaurata duk wani sarki ko jinin sarauta anan ake binne shi.
Wani abun da zai ba ka mamaki tun kamin adawo daga kai mai martaba maƙabarta Ciroma ya fara shige da fice na neman sarauta, idanunsa sun rufe da kwaɗayin mulki kamar shi ba zai mutu ba.




#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.
[1/3, 3:55 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels






051.




Koda ta dawo makaranta da rana Huwaila tayi masu abincin rana gidan sai kyalli yake ko'ina fes daman Huwaila badai tsafta ba ,anan cikin parlor ta wullar da bag dinta ta makaranta ta cire takalmin kafarta
da ƙaramin hijab ɗinta na uniform ta wullar cikin parlor fitowar Huwaila daga ɗakin bakin dake cikin down stairs ta hango Aydah cikin parlor,da fara'a sosai Huwaila ta ƙaraso gabanta tana faɗin "Auta har an taso makaranta Aydah na zama cikin kujera take ɗagawa Huwaila kai,
"Abinci za kici ko wanka?"duka ina bukatar kowane Aunty huwaila ,Amman zan fara cin abincin tukuna daidai lokacin Abba Bashir ya ƙaraso cikin parlor kuma yabi kayan da Aydah ta yasar a kasa. Fuska a daure yake faɗin."wannan kayan fa wa zai kwashe?"da sauri Huwaila ta nufi kayan tana kokarin daukewa AB ya dakatar da ita ya kalli Aydah yace ta kwashi kayanta ta kai ɗaki,yadda yayi mata babu wata cikakkiyar fara'a akan fuskarsa yasa tabi umurnin yayan nata ranta ita ma a ɓace tun jiya da suka dawo daga gidan Mami yabi ya canja mata,abu kankani zata yi masa ya hauta da faɗa a karo na farko da taji tana jin haushin yayan nata har cikin ranta. Har tayi wanka bata fito daga dakin ba ,kwanciyarta tayi a ɗaki har Abba yayi wanka ya sauka kasa yaci abincin da Huwaila ta jera cikin dinning area baiji alamar motsin Aydah ba.yana gama ci ya koma sama murda handling din kofar ɗakinta yayi ya shiga kwance ya sameta kan bed tayi ruf da ciki idonta a rufe suke kuma yana jin yadda numafashinta ke fita da alamar bacci ne ya dauketa yafi minti ɗaya tsaye akanta dogayen yatsun kafanta ya shiga ja , buɗe idonta tayi da suka sauya kala saboda bacci.Ba za ki ci abinci ba kika dawo ɗaki kika kwanta?"
"idan na tashi bacci zan ci yayanmu."ta faɗa tana son ta kara rufe idanunta ,tashi muje kici abinci ki gama ci na saukeki a islamiyya yau babu fashi."yayi maganar sounding so very serious tamkar zata yi kuka ta tashi zaune tana murza ido tana jin yadda kanta ke wani irin juyawa ,da gaske bacci takeji kamar yadda ta faɗa masa kallon yanayinta kawai yasan bacci takeji sai dai ba zai yadda tayi bacci ba taki zuwa islamiyya
Shiya dauki plate ya zuba mata shinkafa da miyar da Huwaila tayi masu da naman kaza a sama,haka Aydah ta rika ci kamar ana sakata dole yana zaune a gefe yana danna wayar hannunsa,akai akai yake dagowa ya kalli gefen da take idan zata kai lomar abinci a bakinta tamkar zata fashe da kuma kamar yadda take yi da fuska.sai dai yayi murmushin gefen baki ya dauke kansa akanta.Baccin da Aydah bata samu ba kenan har lokacin islamiyya yayi yana dawo masallaci ya dauketa da mota ya aje ta islamiyya duk ranta a ɓace yake.haka yaja motarsa ya barta tana famar kumbure-kumbure.
Har ya daukota daga islamiyya ran nan nata a ɓace yake shima sanin Huwaila na gidan kuma ba karamin dadi yaji ba da tazo gidan yasan Aydah bazata yi kewa ba yana sauketa ya juya kan motarsa kai tsaye wurin Abdulkarim ya wuce."Aure nakeso nayi Abdulkarim !"Ya fadi kalmar batareda ya kalli Abdulkarim ba da ya buɗe baki yana kallonsa da mamaki."aure kamar yaya ban fahimceka ba.?"mahaifin Rumaisa ya samu ganawa dani ya bani hakuri akan laifin da yayi min a baya."haka ya kara bani damar auren Rumaisa a karo na biyu sai dai ban san tayar da zan yiwa Daddy bayani ba."da kurciyarka za ka aje mata har biyu meke damunka Meya shiga kanka."duk ka manta irin mummunan wulakancin da mahaifin yarinyar nan yayi ma a ranar daurin aurenka.!"ai ina tunanin daga ranar bazaka kara kallon 'yarsa ba ashe ba haka bane AB
Abdulkarim ya faɗa da wani yanayi a Muryarsa yana ganin hoton sadda abun ya faru acikin kwanyar kansa,Yaya zan yi Abdulkarim ina son Rumaisa da dukkan zuciya da ruhi a baya nayi yunkurin rabuwa da ita na har abada,sai dai tausayin ta da nake ji na kasa duk irin soyayyar da ta nuna min a baya kuma bata da laifi ko kaɗan duk mahaifinta ne."ban baka shawara ka tun kari Daddy da wannan zancen ba ,ana barin halal dan kunya ka tuna yadda Daddy ya tsaya maka akan komai na rayuwarka."ita kuma wacce kake aure a gida isarka ne ba tayi ko yaya?"lokaci ɗaya Yanayin AB ya canja,jin inda Abdulkarim ya bullo masa, "sau nawa zan faɗa maka babu wannan maganar a tsakanina da Aydah lokacin sakinta na zuwa lokacin da tazo min da wanda take so ta aura. murmushi Abdulkarim yayi bai kara cewa komai ba sai murmushin da yake yi har kullum AB ba zai daina basa mamaki ba ga gaskiya kiri-kiri yana gani Amman sai ya take,da dare Abba ya yanke shawarar ya kira Daddy ya faɗa masa tunda baya gari sai dai yana dialling lambar Daddy yayi saurin katsewa idan ya tuna maganganun Abdulkarim sai yaji akwai kamshin gaskiya a maganganunsa ,to kuma yana bukatar Rumaisa cikin rayuwarsa acikin gidansa na aure ko dan ya kauda zargin da Mami keyi masa akan Aydah ,ya kamata yayi aure sai dai bai san taya zai fara tunkarar Daddy da maganar ba."
Cikin kwana biyu Mami tayi bala'in saka damuwar Aydah aranta musanman da ta ƙaryata a gaban Abba Bashir ta fahimci idan bata tashi tsaye ba Aydah neman take tafi karfinta duk akan Abba Bashir,da safe karfe goma tunda Daddy baya gari ta dauki motarta tayi gidan kawarta Hajiya zeenah ,Mami bata tsaya kofar gidan kowa da motarta ba sai kofar gidan Alhaji Sanusi ƙanin Daddy,nan tayi horn maigadi ya leko ta karamar kofa ya shaida motar ta Mami dan tana yawan zuwa gidan buɗe mata kofar gate yayi yana daga mata hannu alamar gaisuwa. A hankali ta shiga danna door bell,bata jima ba aka zo aka buɗe mai aiki ta gaisheta tayi mata iso cikin parlor, tace Bara ta karasa bangaren Hajiya zeenah ta kirata daga kai kurum mami tayi saboda damuwar dake kwance a kasan zucuyarta ,ba'a jimaba Hajiya zeena ta fito sanye cikin kayan bacci riga da wando masu kauri kana ganin fuskarta da take a yamutse kasan bata dade da tashi bacci ba,har cikin parlor ta karaso ta zauna da mamaki take kallon Mami,ko jia munyi waya baki cemin zaki zo ba Hajiya mariya."Hajiya zeenah ta faɗa tana kallonta,da raunin murya Mami ke faɗin."bana cikin hankalina zeenah bana cikin natsuwata ina gafda rasa tunani na zuciyata tana iya bugawa lokaci ɗaya,inhar Abba ya kusanci Aydah."Mami ta faɗa da wani irin yanayi a muryarta wani murmushin gefen baki Hajiya zeenah tayi tana faɗin."mu karasa kiyi break fast idan kin samu natsuwar da nake bukata sai muyi magana."da sauri Mami ta shiga girgiza kai tana faɗin."taya kike tunanin zan iya haɗe wani abinci cikin kwanakin nan ai abinci baya zama acikina zeenah mu karasa dakinki muyi magana cikin sirri."har bedroom din hajia Zeena suka shige suka zauna akan makeken gadonta Mami ta cire mayafin kanta , Zeena na yanke shawarar kawai zaki kaini wurin malaminki na yadda da maganarki sai ta wannan kaɗai zan samu Abba,ya rabu da ya'ta na har abada ke ko Sadiyar da nakeso ya aura na haramta mata aurensa ki tashi mu tafi wurin malamanki raba auren nan shine kwanciyar hankalina Zeenatu
lamarin Aydah ya gigita Ni zautukkanta sun dauremin kai kwanakin nan ko baccin kirki bana samu wallahi saboda damuwa."yanzu kika dawo hanya Hajiya Mariya ai yanzu ai daina zama a ga ikon Allah in har kina da kuɗi babu wata matsala da zata sakaki a gaba,bari na watsa ruwa nayi karin kumallo kin san fa ba'a cikin garin Kano yake ba a gaya yake ,zaki iya janmu da mota mu tafi ko mu tafi da driver na."kin san bazan iya dogon driving ba saboda ciwon baya,muje dai da driver zaifi sauki.
Hajiya Zeena ta gyada kai alamar gamsuwa ta shige toilet minti goma sha biyar ta gama karin kumallo ta shirya cikin atamfar super da mayafinta,suka fito cikin shirin zuwa garin (gaya)itada Mami,suna hanya kiran daddy ya shigo a Wayarta sai da gabanta yayi wata irin dokawa.dan bata faɗa masa zata fita ba,cike da karfin hali ta daga wayarsa bayan sun gaisa yake tambayarta bata gidane ?"yana jin karar abun hawa.?"da ido Hajiya Zeena ke kwatantawa Mami yadda zata fadawa daddy,naje gidan Safeena ne bata dan jin dadi Amman ba dadewa zanyi ba."kayi hakuri na manta ban faɗa maka ba, Daddy yayi mata addu'ar Allah ya bata lafiya haka yayiwa Mami alƙawarin idan ya samu lokaci zai kirata.da haka suka aje wayar
Da sauri Mami ta kira Aunty Safeena a waya tace idan Daddy ya kirata ya tambayeta ya jiki."ta faɗa masa taji sauki,dan tafita bata faɗa masa ba tace tana gidanta bata jin dadi. Safeena tace Insha Yaya,Allah ya tsare hanya."Mami ta amsa da Ameen tana sauke wayar,Hajiya Zeenah ta cigaba da zuzuta maganin malamin da zasuje wurinsa tace cikin minti goma idan har maganin ya fara aiki Abba, zai iya sakin Aydah,shiru Mami kawai tayi tafi Hajiya Zeena son auren nan ya tarwatse kowa ma ya huta.tafia suke Amman bata ganin ma driver na taka motar yadda takeso dan har magana tayi masa akan ya kara gudun motar,
da suka isa garin gaya har kofar gidan malam (dogo)motarsu ta tsaya ,suna fita daga motar Hajiya Zeenah ta karasa wurin driver ta ciro kudi a bag dinta ta kirga dubu goma ta soka masa a hannu,tace uzairu ka shiga gari ka ɗan shana da mungama zan kiraka."baki har kunne uzairu ya karbe kuɗin sa yayi reverse yabar cikin lungun dakyar mota ke shigowa kafin ka shigo da mota duka sai gabobin jikinka sunyi ciwo.mutum ɗaya suka samu yana dubawa Hajiya zeena tayi hamdala tana faɗin."Yau munzo a sa'a Kinga babu wani layi, kusan rabin awa da zuwa su suka samu ganin malamin ,nan Hajiya Zeenah ta gabatar da Mami a gaban malam dogo da kuma bukatar da ta kawosu wurinsa ,Aran Mami tace lallai kam kaci sunanka malam dogo irin wannan tsayi haka.Ya kalli Mami sa'annan ya soke kai yayi rubutu a kasa sai da ya kusa shafe wasu dakikai a haka kafin ya dago idonsa cikin na Mami yake faɗin."me kike so ayi masa?"kawai malam ina son ya sakar min ya'ta shi kawai nake bukata."malam dogo ya gyada kai ya kara soke kansa kasa yana cigaba da shafa kasa,ya dago ya kalli Mami yana faɗin."zamu fara saka masa tsanarta kafin mu saka ya saketa dan yaron nan da yarinyarki wani al'amari ne mai girma a tsakaninsu da ba'a bani ikon ganin ko menene ba, bazai iya rabuwa da ita cikin sauki ba yana yawan addu'a sosai sai dai zamu saka masa muguwar tsanarta aransa daga nan sai musan abunyi ,tau ayi haka Malam."Mami ta faɗa a gaggauce,
Malam dogo ya haɗe hannuwansa wuri ɗaya ya runtse ido yana karanto kalmomin tsafi sai ga bakar laya ta bayyana a hannunsa ya mikawa Mami jiki na rawa Mami ta karba,
Kusan yadda kukayi a sakata a inda yake kwanciyya ina nufin makwancinsa idan yau aka sakata aiki zai fara a yau.da sauri Mami ta turata cikin handbag cikin zumudi Mami,ke faɗin "malam nawa ne kudin aikin."Naira dubu dari biyar!"sai da Mami ta ɗan girgiza da kudin,ta kalli Zeenah da sauri tana faɗin."ba'a yi masa transfer na hannuna basu kai haka ba."nawa ne a wurinki dubu dari uku."tau zan ara maki sai kiyi min transfer anan wurin suka haɗawa malam dogo naira dubu ɗari biyar , suka yi masa sallama a mota Mami ta kalli hajia Zeenah cikin saukar da murya take faɗin."Tayaya xanyi wannan aikin zeena ?"kin san ko cikin mafarki bazan ba aidah ba nace ta saka ."na lura sadiya tanada wayau sosai da ita kawai zamu yi amfani wannan karon Mami tana kyaftawa Hajiya zeena ido alamar tana son taji karin bayani ,nan Hajiya Zeenah ta saka bakinta daidai kunne mami. Wani murmushi Mami ta saki da haka suka shiga garin Kano cikin farin ciki Hajiya Zeenah ta yiwa driver umurni kawai su wuce gidan Alhaji Bashir.






#Love story2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.
[1/4, 5:11 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels




054.




Banda zufa babu abun da take haɗawa tana dafe da cikinta tana bin ɗakin da kallo duk a tsorace take,mafarki ne !mafarki ne!"sai kuma ta fashe da kuka tana kiran sunan Abba da sauri ta lallubi wayarta ta kunna hasken fitilarta hannu ta kai ta kunna maballan fitilah da sauri ta sauka daga kan bed ta nufi kofa ta cire key, kai tsaye master bedroom ɗin Abba ta nufa ta rika buga masa ƙofa tana waiwayen bayanta,cikin bacci yaji ana buga masa ƙofa na fitar hankali da kyar ya buɗe idanunsa da mamaki jin muryar Aydah yayi tana faman ƙwalla masa kira bai san meyasa yake jin muryarta wani iri ba acikin kunnuwansa muryarta yake ji kamar ana doka masa wani abu acikin kwanyar kansa da gaske baya son jin wannan muryar da sauri ya dafe kansa jin ta cigaba da kiran sunansa kamar kansa zai fita da gangar jikinsa haka yake ji dakyar ya sauka kan bed ya nufi ƙofar ya cire key tana ganinsa ta faɗa jikinsa ta ƙanƙamesa babu inda baya rawa ajikinta jin yayi tamkar an zuba masa tafasasshen ruwan zafi ajikinsa jin Aydah ajikinsa ya fisgota yana kallon fuskarta a tsawace yake faɗin ."menene baki da hankali ne ya faɗa yana turata da karfi bai damu da inda zata fadi ba ya dafe kansa yana kallonta da fusassatun idanunsa bai san meyesa kallon fuskarta kurum yana saukar masa da wani irin ɓacin rai,cikin kuka Aydah tana ƙoƙarin kamo hannunsa tana faɗin."Yayanmu mafarki mafarki nayi."ta faɗa tana jan numfashi "saboda kinyi mafarki shine zaki rika bugamin ƙofa da daren nan are You crazy.?"ya faɗa sounding more angry ,tana ƙoƙarin shigowa ɗakin nasa ya daka mata wata irin razananniyar tsawa.keeeeee!"da mamaki take kallon yayan nata tamkar bashi ba dafe kansa yayi jin yana wani juya masa idan ya cigaba da ganin fuskarta komai zai iya faruwa dashi maida kofar yayi ya rufe batareda ya kara magana ba,yana jin yadda Aydah take kiran sunansa tana basa haƙuri
wani irin tsanarta yake ji na zagaye ruhinsa duka.ta daɗe tana buga masa ƙofa ganin yayan nata yaƙi buɗewa yasa ta sauka ƙasa tana bugawa Huwaila kofa,cikin bacci Huwaila taji bugun ƙofa a firgice ta tashi cikin muryar tsoro take tambayar "waye? Muryar Aydah taji tana kuka
A tsorace ta nufi ƙofar ta buɗe mata faɗawa cikin ɗakin Aydah tayi tamkar wacce aka jeho gaban Huwaila yayi mummunan bugawa da sauri Huwaila ta mayar da key,ta nufi Aydah ta rungume Huwaila tamkar zata shige cikin jikinta ga baki ɗaya. Sunfi minti goma a haka sai saukar ajiyar zuciya Aydah ke saki ajikin Huwaila sai lokacin wani tunani ya zowa Huwaila kodai Aydah daga wurin Abba ta gudu yau yana so ya karɓi hakkinsa ne taƙi basa haɗin kai?"dan irin yadda ta firgice lokaci ɗaya, "Aydah ki natsu ki faɗamin menene ina kuma yaya Abba?"yana ɗakinsa Aunty Huwaila tsoro nake ji mafarki nayi kibarni na kwanta dake,
shiru Huwaila tayi can kuma kama hannun Aydah zuwa ga gadonta jikin Aydah yana rawa ta hau gadon ta kwanta tare da dunƙule jikinta wurin ɗaya, Huwaila ta zauna kusa da ita tana shafa kanta tana tofa mata duk addu'ar da tazo bakinta nan take bacci mai nauyi ya dauke Aydah,sai da Huwaila ta tabbatar da tayi bacci ta samu ta kwanta gefenta acan ƙasan ran Huwaila damuwa ce tayi mata yawa tana tausayin yaya Abba,da Aydah musamman Aydah Mami taki karbar ƙaddarar Aydah da hannu bibbiyu shiyasa har yanzu babu wani jin dadi da kwanciyyar hankali a wurin Aydah,ta rasa Mami wace irin uwa ce wacce son kanta yayi mata yawa."tana yiwa Aydah addu'a rayuwa mai sassauci da sauki a dukkan lamuranta,da haka ita ma bacci mai nauyi ya dauketa
dukansu yau sun makara yau AB ko kallon room ɗin Aydah bai yi ba ya rasa meyasa ya kasa yin haka har ya dawo masallaci ya

39 / 80