Author : EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category : KDP NOVELS
Siyam ki dawo min da matata idan ba haka ba sai nayi mummunan saɓa maki. Da haka ya sauke wayar sai huci yake tamkar wani mayunwacin zaki mai jin yunwa, hannu yasa cikin sumar kansa yana ta hargitsawa, toilet ya shige yana sakarwa kansa ruwa akai,baya son tuna wannan yanayin shida Aydah ya hana zuciyarsa hutawa daga bugawa tun a mota Aydah taga yanayin Siyama ya canja dan bata nan lokacin da tayi wayar ta shiga toilet.
Yaya Siyam baki biya Dani siyan ice cream din ba kuma fa kinyi alkawari.
"Ki kira mijinki sai ya siyo maki ni gida zan wuce yammah tayi ,rai a ɓace Aydah ke faɗin "babu kyau saba alkawari yaya Siyam."ita dai Siyama banza tayi wa aidah a motar suna ƙarasawa gidan AB tayi parking motarta a bakin gate batareda tayi horn ba mai gadi ya bude,da mamaki Aydah ke faɗin."kin fasa kwana anan ɗin "sai wani lokaci Siyam ta faɗa rai a haɗe,haushi ya kama aidah ta fice daga motar ta nufi get.tunda ta doshi cikin compound ta hangi motar AB taji hanjin cikinta na yamutsewa,tamkar tayi kuka take faɗin "shine yaya siyam tasan yayanmu ya dawo ne shiyasa taki shiga,kasa bi ta cikin gidan tayi zagayawa tayi ta cikin balcony kofar kitchen tana ta addu'a Allah yasa babu key ajikin kofar tana rika handling kofar ta Murda tana turawa taji ya bude wata irin ajiyar zuciya ta sauke dai dai me wanda tayi ido biyu dashi yasa gabanta yayi mummunan bugawa ya harɗe hannunsa akan kirjinsa yana bin ta da wani irin kallon da tunda tayi wayau bai taɓa yimata kalarsa ba jin take tamkar ta juya,hawaye taji suna cika idonta lokaci ɗaya jikinta ya shiga kadawa duk takun da yake yana zuwa gabanta da yadda kalar bugun zuciyarta ke canjawa sai da ya karaso har inda take yana haɗe filin da yayi saura a tsakaninsu ga bango Aydah ta nanne tana tattare jikinta wuri ɗaya,kallon yadda jikinta ke kadawa yake ta rufe idonta hawaye na forming akan fuskarta, fuskarta kawai yake bi da kallo tamkar mai son gano wani abu acikin fuskartata har ya tsayar da idanunsa akan bakinta wani irin bugawa zuciyarsa keyi pink din janbakin da ta shafa yaji yana wani irin jansa tamkar an jona masa wutar lantarki yadda jikin nasa ke kadawa yadda zuciyarsa ke umartarsa akan yayi abunda gangar jikinsa ke so lokaci ɗaya taji an wani rike kafadarta kara ta saki tana buɗe idonta a tsorace cikin rawar murya da banbaki take faɗin ."dan Allah Yayanmu kayi hakuri tarefa da yaya Siyam muka fita kuma na kira wayarka baka dauka ba ta karasa cikin kalar shawagabar da ta kusa rikita sauran lissafin dake cikin kansa
Jada baya ya shigayi murya a shake yake faɗin "ta kawo masa bakin tea yanzu.juyawa yayi ya fice daga kitchen din.kunkuni ta shigayi aranta tana faɗin "na zata Rumaisa zaka kira ta kaima."ta faɗa rai a ɓace tamkar yana ganinta dakin Huwaila ta shige tana tambayarta bakin tea yayanta huwaila sai tambayarta take ina siyama din."a gajarce take faɗin."ta wuce juyawa tayi ta tafi cikin dinning area ta haɗa masa bakin tea ta dauki wainar kwai acikin plate ta nufi sama.tana shiga cikin parlor nasa tayi wani kicin-kicin da fuska sai bin parlor take da kallo har lokaci Abba na zaune cikin parlor ya dafe kansa da duka hannu biyu daga shi sai tree quarter da shirt marar nauyi,ƙarasawa tayi ta ɗora masa akan side table hankalinta duk yana kan window side din hoton yayanta da Rumaisa ashe bata aza cup tea din daidai ba jin kawai tayi ya dawo mata a kafa wani irin kalar ihu ta saki tana zama a kasa tana rike kafarta tamkar wacce aka yanka."a gigice AB ya karaso wurin yana rika kafar wani irin kuka ta fashe dashi ga kukan ruwan zafin data kona kafa dashi gana kuma kan me Rumaisa zata wani kafa hotonsu a parlor yayanta."kukan da take yaketa har gitsa sa har yana kasa controlling din fushinsa ya wani daka mata tsawa yana fiddo mata da manyyan fararen idanunsa yana faɗin."tayi masa shiru.
Tsit tayi tana haɗe kukan sakin kafar yayi ya miqe tsaye ya nufi master bedroom dinsa bai jima ba ya fito da cream a hannunsa dukawa yayi ya shiga shafa mata saboda takaici jin take kamar ta fisge kafar har ya gama hawaye basu daina zubar mata ba daman yana sakin kafar tayi kokarin mikewa tsaye ganin bata son tafia yasan ta fiye raki ba Tareda wani tunani ba taji ya dauketa dukanta ya fice daga parlor kai tsaye ɗakinta ya nufa daita har kan gadonta ya kaita ya aje,ya juya batareda yace mata komai ba ya fice daga dakin daman yana fita ta kifa kanta a pillow ta fashe da wani irin kuka mai sosa rai.tayi kukanta ta gaji a haka tayi bacci sai bayan sallar magarib jin shirun yayi yawa yasa huwaila ta taho sama.kai tsaye dakin aidah ta buɗe,ganin tayi har lokacin tana bacci dakyar huwaila ta tasheta ganin yadda idonta ya rine lokaci ɗaya Tasan kuka tayi sai dai bata tambayi dalilin kukanta ba tace mata har angama sallah.
An kusa fara series ɗinki."(unfortunately love)daman aidah tana kalla a zeeword kullum.ita yau yadda take jin zuciyarta a cunkushe bata ma da karfin yin wani kallo.huwaila na barin dakin itama ta nufi toilet...
#JEEDDAH ALIYU
#ASMY B ALIYU
#KURMAN ALLO
Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[1/12, 3:42 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye
067.
Bayan Aydah ta fito daga wanka ta shimfida praymat tayi sallar magarib tana sallamewa ta sunne kanta tsakanin cinyoyinta ita ba kuka take yi ba amma gara ma ace kukan ne take yi a irin raɗaɗi da ƙunci da take ji a zuciyarta. A duk sanda ta tuna da cewa saura kwanaki uku Rumaisa ta shigo gidanan a matsayin matar yaya Abba sai ta ji wani abu ya dunƙule mata a ƙahon zuciya. Tana nan zaune tana tufka da warwara har aka yi kiran sallar isha ta tashi ta gabatar da sallah, jikinta a mugun mace ta nufi closet ɗinta ta ciro riga da wando na bacci ta saka kana ta sauka ƙasa motsin Huwaila ta ji a kitchen shiyasa kanta tsaye ta wuce kitchen ɗin "sannu da aiki aunty Huwaila fruits salad ake haɗa mana?"
"Uhm! Yayanmu ne ya umarce ni da na haɗa masa.
"To nima a haɗa ni zan sha.
Ƙarasawa tayi kusa da Huwaila ta tayata yanka fruits ɗin tare suka yi komai bayan sun kammala Huwaila ta zubawa AB nasa acikin matsakaici bowl 🥣 tare da spoon ta miƙawa Aydah ta ce ta je ta kai mishi a ɗan tsorace Aydah ta ja baya tana faɗin "Ki rufa min asiri aunty Huwaila ɗazu ma da naje kai masa black tea na je aje masa bisa tsautsayi na ɓarar masa ya zuba min a ƙafana yanzu haka wurin yana min zafi. Banaso naje kuma na sake maimata kuskure da nayi ɗazu.
Murmushi Huwaila ta yi tare da maida bowl ɗin kan kitchen island ya riƙo hannayen Aydah, tayi ƙasa da murya "Haba Auta ya kike yi abu kamar marar wayau yanzu idan ba ki dinga shisshige masa so kike sai wacce kodaddiyar ta zo ta mamaye shi?"
Cikin sauri Aydah ta shiga girgiza kanta kamin cikin shagwaɓaɓbiyar muryarta ta furta "Wallahi aunty Huwaila da ina da dama ko ɗan yatsan yayana ba zan bari ta taɓa ba ballantana har ta kai ga mamayarsa.
"To idan haka ne kuwa yi maza ɗauki bowl ɗinan ki kai masa yadda kike zuba wannan ƙamshin na tabbata sai Yayanmu ya kusa zaucewa.
"Kai aunty Huwaila!!
Aydah ta faɗa cikin shagwaɓa.
"Yoo ai gaskiya na faɗa ban da ma namiji da shege gane-gane wanda keda yarinya ɗanya latsaf me zai yi da kodaddiyar mace irin Rumaisa sai ɗan banza fari kamar zabiya.
"Ba ma nata ne kaɗai ba tana haɗawa da na kanti.
Aydah ta faɗa tana cuno baki, Huwaila dai ta gama fahimtar mutuniyar ta, ta kishi ne ke cinta.
Aydah ta ɗauki bowl ta nufi Parlorn AB, tana tura ƙofa yana zaune akan three seater da remote a hannunsa da sallama ta shigo ya amsa tare da yada ganinsa akanta, ya kasa ɗauke idanunsa akanta yayin da Ƙamshin turaren ta ya cika ƙofufin hancinsa, Aydah ta nufi side table ta ajiye tana faɗin "barka da hutawa Yayanmu sai ƙyali angwaci kake yi.
Zaro idanuwa AB yana kallon ɗan mitsitsi bakinta da ya furta masa wannan magana daga bisani kuma ya galla mata harara "Baby yaushe raini ya shiga tsakanina dake da za ki faɗamin magana irin wannan ko ni sa'anki ne?"
Aydah tasa dariya ta tako tare da zaunawa kan centre table dake gabansa "Kai Yayanmu daga faɗar gaskiya to Allah ya ba ka haƙuri amman duk wanda yaganka dole zai faɗi kwatankwacin abun da na faɗa.
"Kowa zai iya faɗa amma ban dake saboda ni ba abokin wasar ki bane.
"Babu wani nan Yayanmu kawai dai ni ka tsaneni shiyasa ka faɗi haka da adane wani ko wata yace dani akwai ranar da za ta zo yayana ya tsaneni ya nuna min zazzafar kiyayya duka ƙaunar da yake min za ta rikiɗe zuwa kiyayya, ba zan yarda ba asalima da akwai takobi a hannuna ko a kusa dani sai na fille kan ko waye ya faɗi hakan idan kuma wuka ce a hannuna ba abun da zai hanani gimtse masa harshe. Yayanmu ban gino akan soyayyar uwa da uba ba kamar yadda na gino akan soyayyarka, duk da na taso a gaban iyayena amman bansan daɗi ƙaunarsu ba, kamar yanda nasan daɗin taka. Shin Yayanmu ka raine ni a bisa so da ƙaunarka don kawai wata rana ka juya baya?"
Yadda Aydah take magana cikin rauni da kariyar zuciya ga hawaye kwance akan kamatunta dole duk rashin imanin mutum ta bashi tausayi koda ɗan ƙanƙani ne,balle irin AB da Allah ya zuba masa tausayin mata da ƙanana yara sosai kalaman Aydah suka yi tasiri a jikinsa shi kansa yana yawan tambayar kansa da kansa meyasa yake jin tsanar Aydah wanda can farkon aurensu baya jin hakan akanta rana ɗaya ya waye gari cikin wannan sabon al'amari akanta, wanda da za a rutsa shi ba zai iya faɗin dalili da yasa ya tsane ta ba.
Hannunsa ya kai jikin centre table ɗin da take zaune ya matso dashi gafda shi sosai gaban Aydah ya faɗi yanda taga ya matso da table ɗin izuwa gabansa ya haɗe tazarar dake tsakaninsu, ya saki table ɗin ya kama dukkan hannuwanta ya matse cikin tafin hannunsa duk da yana jin wannan al'amari da yake ji a duk sanda kusanci irin wannan ya shiga tsakaninsu amman ya danne zuciyarsa har ya shiga kwararo addu'a a ƙasan zuciyar tasa, abin mamaki sai ya ji wannan abun yana fita a hankali tamkar dai wuri da ya yi kura ana kade shi da tsintsiya "Ki yi haƙuri dani Baby Aydah nima a can kasan zuciyata bana jin daɗi yadda nake treating ɗinki ban kuma san me ya hau kaina ba da nake miki hakan, amman ki tayani da addu'a Allah ya sassauta min koma mene ne ya kuma dawo mana da kyakkyawar alaƙarmu ta tun asali. In shaa Allah ba zan sake bari shaidan ya yi wasa da zuciyata akanki my Baby.
Wani irin daɗi ne ya lulluɓe Aydah wanda batasan lokaci da ta miƙe da sauri ta faɗa jikinsa ta zagaye hannayenta a gadon bayansa, tana karawa kukanta sauti "Nagode Yayanmu, kalaman bakina ba za su ishe ni ba wurin bayyana maka irin farin ciki da ka haifar min, kawai dai zan yi maka addu'a Allah ya rufa maka asiri fil dunniya wal akhar Allah ya tsare min gabanka da bayanka Ubangiji ya haskaka zuciyarka da farin ciki marar adadi.
Tsanani daɗin addu'arta yasa shi matse ta gam akan ƙirjinsa yana bubbuga bayanta,tare da wata sabuwar ƙaunarta da tasha banban da wacce ya gina zuciyarsa akai.
"Amin thumma Amin! Kuma duk abun nan da kika roka min my little Baby Allahu ya ba mu su a tare.
"Amin! Yayanmu mai kirki.
Aydah ta faɗa da raguwar hawaye a idanunta, AB ya ciro ta daga jikinsa ta sake ƙanƙame shi "Bari nasha fruits salad ɗina Baby kin ga ɗazu kin ɓarar min da tea ban sha ba kuma yunwa nake ji.
"Uhm! Yayanmu dan Allah ka barni na ji ɗumin jikinka kaɗan na manta when last da na samun irin hakan.
Murmushi mai sauti ne ya subuce wa AB ya cire ta, ta ƙarfi sannan ya ja karan hancinta "baby yaushe kika koyi karya naga ko ɗazu da kaina na dauke ki, na kaiki ɗakinki za ki ce kin daina jin ɗumin jikina.
"Yayanmu wannan daukar ta dole ce saboda na kona ƙafana.
Sai lokaci ya tuna da zance konuwar ta, ta da azama ya kama ƙafarta yana dubawa ba abun da ya same kafar hamdallah ya yi tare da ɗaukar bowl ɗin fruits salad ɗinsa, sai ga AB idan ya yi one spoon ya ɗiba ya saka wa Aydah a baki tare suka shanye fruits salad ɗin tass! Sai da Aydah ta fara gyangyadi sa'annan AB ya rako ta ɗakinta, ta kwanta bai baro ɗakin nata ba sai da yaga baccinta ya yi nauyi ya tofe ta da addu'a ya sumbace forehead da lips ɗinta kana ya kashe mata wuta ya fice. A hotel ɗin da Sadiya ta kama sai da tasha sha kayan mayenta yi tatul sai da ta sha baccinta sannan ta nufo gida koda ta dawo babu kowa a main parlor da sauri ta wuce ɗakinta tana zuwa ta zube kan gado ta shiga baccinta na asara sai dab da magarib tashi shima Mami ce ta tashe ta, bayan tayi wanka da salolin da ake bin ta sai lokaci ta tuna da abun da malam ya bata ya ce ta nemi murhun gargajiya ta jefa laya acikin idan ta kama da wuta sai ta ciro ta,ta ajiye a ƙasa ta dinga ambatar sunan Rumaisa har sai laya ɗin ya cinye ya zama toka, babbar damuwarta inda za ta sami murhun gargajiya saboda Mami dai gas take aiki Kwata-kwata gidan Babu murhu idan kaga an yi amfani dashi sai ga sallar layya, sai lokacin Sadiya ta shiga damuwa ta rasa yanda za ta yi gaba ɗaya kanta ya kwance ta rasa mafita, ta ɗauki wayarta ta kira Sarah ta faɗa mata halin da ake ciki kai tsaye Sarah ta ce ta je kawai ta kona kan gas ai wuta duk wuta ce "Sarah kina gani idan na kona kan gas kina gani babu matsala aikina ba zai lalace ba?"
"Ba abun da zai faru ƙawata ki jaraba kawai shima malam dan babu gas a gidansa ne ya shiyasa ya yi amfani da abun da yake da amma miye banbanci murhu da gas naga dai dukkun su wuta ne.
"Haka ne ƙawata.
"To jeki ki aiwatar da aikinki Please karki sake kirana bacci nake yi ko yanzu da ba don ke bace wallahi ba zan ɗaga ba.
Kafin Sadiya ta bata amsa har ta kashe wayarta sai da dare ya raba tsakiya Sadiya ta fito ta shiga kitchen ta kunna gas ta ɗora laya akai da ya kama da wuta ta kashe gas ta ciro shi ta jefar kan tiles ɗin kitchen, ta shiga kiran sunan Rumaisa har sai da layar ta zama toka Sadiya ta fice abinta da sassafe da mai aikinsu ta shigo taga toka a tsakiyar kitchen tasaka tsintsiya da parker ta kwashe shi tass ta zuba a bin.
Aydah tana tashi tayi wanka da sallah kana ta shirya cikin school uniform ɗinta, agurguje ta wuce school saboda tayi latti gashi yau za su kammala exams.
*MASARAUTAR KUDU*
Galadima ya dubi Ciroma da daurarriyar fuska yanayi kallo da kaɗai yake aikawa Ciroma ya isa ya bayyanar da irin matsanancin fushi da yake ciki "Ciroma kasani bari fa bari fa ba shegiya bace da ubanta idan ka nemi raina min hankali to kuwa za ka haɗu da fushina.
Wani makirin murmushi Ciroma ya yi yana shafar geminsa"kai dai Galadima ka cika gaggawa kuma gaggawa aikin shaidan ce komai na duniya a hankali ake bin sa matukar ana so ayi nasara akansa Aliyu da kake gani ba kamar gama gari saura mutane bane. Cire shi daga sarautar sabon birnin kudu ba abu mai sauki bane da kunnenka, ka ji abin da boka mai Gundulelliya ya faɗa akansa idan har baso kake yi allura ta tono galma ba ka bari mu bi wannan al'amari daki-daki.
"Mtss! Ciroma karka mayar dani wani sabon yankar rake mana. Meyasa shi bokan naka ba zai bi hanyar da yabi ka cimma burinka nima na cimma nawa?"
"Wallahi Galadima kana da matsala bayani nake maka amma sai yi kake yi tamkar ba ka fahimci me nake nufi ba. Idan har muna so mu yi nasara akan Aliyu dole mu nemo wani da za mu bata shi a idanuwan al'umma abun da zai yi tarnishing image ɗinsa wanda hakan zai sa manyan fada su tsige shi da kansu ita fa siyasa 'yar zabo ce.
"To naji amma kai a ganinka me za mu yi amfani dashi da za mu goga masa bakin fanti wanda zai sa har ya rasa kujerar mulkin sabon birnin kudu?"
Shiru Ciroma ya yi tare da zurfafa tunaninsa can ya sauke ƙarfaffiyar ajiyar zuciya kamin ya ce "Dole ka yi haƙuri Galadima sai bayan an naɗa ni sarkin kudu sannan ne abubuwa za su kankama daga nan burinka zai cika.
Wani mugun kallo Galadima ya watsawa Ciroma "Amman gaskiya Ciroma ka raina min da hankali shi ko ka manta tare za a yi naɗin ku kai da Aliyu?"
"Ban manta ba Galadima dalilin hakan yasa nace ka ɗan dakata idan har ban cika maka burinka ba na zama sarkin sabon birnin kudu na yarda ka fallasa sirrina.
Murmushi kurum Galadima ya yi mugu shi yasan makwancin mugu.
*ALHAJI BELLO MADAWAKI MANSION*
Yau ce ranar da ta