Author : EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category : KDP NOVELS
taƙarasa magana har da su murguɗa baki.
AB bai sanda ya fashe da dariya ba da kyar ya tsagaita dariyar tasa, yana wani shafa gashin kansa still da murmushi akan fuskarsa "Aydah troublemaker wannan Allah, ya isa naki har da ni ciki saboda nima na kalleta kin ga kuwa Allah ya isa ɗin har da ni aciki.
Kukan shagwaɓa tasa masa tana faɗin "ni bada kai nake ba saboda ni na ankarar da kai tsyuwarta a bayanka na kuma yafe maka kallon da ka yi mata amma ita kan ban yafe mata ba, muguwar kawai wacce batada kunya.
Yadda ta takarkare tana ta faɗa ya yi masifar bashi dariya sai dariya yake abinsa can da yaga rigimar ta Aydah ba mai ƙarewa bace ya ce "Bara na koma ɗakina don ba zan iya da wannan rigimar taki ba.
"Eh! Gwara ka koma ɗin daman ai Yayanmu ba yawon bude ido ka zo ba. Ba dole bane sai ka zauna bakin ruwa.
AB bai fahimci Aydah kishi ne ke dawainiya da ita ba shi ya zaci shirmenta ne ya motsa tun da shi a wurinsa duk abunda za ta yi, a matsayin childness yake daukarsa dole ya koma ɗakinsa suka cigaba da firarsu sai saka shi nishaɗi take da ka ji sautin dariyarsa to tare da Aydah yake, tuni Aydah ta manta da wata Mami sai da aka fara kiran sallar magarib suka rabu sai dai bai faɗa mata gobe zai dawo ba.
*MASARAUTAR KUDU*
Duk yadda Fulani babba ke ba wa mai martaba kariya sai da Fulani karama ta fakaice idanunta ta aiwatar da aikin boka, kwana biyu a tsakani ciwon na mai martaba ya ƙara tsanani hakan ya kara tayawar masaurata da iyalinsa hankali. A daren ranar ba wanda ya zaci mai martaba zai kai safe ba. Ita kanta mai babban ɗaki duk juriyarta a wannan karo da ta je duba shi sai ta zubda masa da hawaye.
Cike da ƙasaita Kilishi take sauraren bayani da hadimi kallamu ke mata dangane da yanda ciwon mai martaba ya tashi, sai wani murmushi take tana jinjina kai Kallamu shine amintaccen bawanta duk wani information na masaurata shi ke zuwa mata dashi sai dai wani abin mamaki akwai ranar da ya nadin maganganu Ciroma da Galadima a gidan gonar Ciroma har ya yi gina ya binne wayar wacce har yau ɗinan bai kawowa wayar ba Kilishi asalima ya ɓoye wannan sirri ɗin. Shi kadai yasan manufarsa na ɓoye wannan sirri.
"Kallamu inason duk wani shige da ficen Ciroma ya kasance akan idonka inason sani duk wani motsinsa, ita kanta Fulani karama ban yarda da ita ba saboda haka ita ma ka samin ido akanta sosai.
"An gama Ranki shi dade duk abunda kika ce shi haka za a yi Allah ya ƙara miki lafiya.
"Tashi ka tafi gobe da safe ka sami jakadiya zan bata sako ta ba ka.
"Godiya nake uwar sarkin gobe sikari ba ki yi farin banza ba
Da hannun tai mishi alama ya miƙe da sauri ya fice.
Sosai Ciroma da Galadima ke farin ciki da yadda jikin mai martaba ya yi tsanani, da wannan daman Ciroma ya fara bin uwayen fada da 'yan majalisar sarki yana kamun ƙafa ba kunya balle tsoron Allah sa'ili da ya je wurin waziri duk da cikin hikima da azanci ya yi masa magana hakan bai hana waziri fahimtar inda kurman allonsa ya dosa ba cike da gundarin mamaki waziri yake kallonsa kafin ya bashi amsa "Ikon Allah! Lallai Ciroma bakada imani ban kara tabbatar da 'yan ubanci mugun abu bane ba sai yau ɗan uwanka yana kwance akan gadon asibiti cikin matsanancin hali, ba ma fatar kake ya sami lafiya ba Allah ya tashe kafaɗarsa cikin iyalinsa da al'ummar da yake mullka kai sarautar sa a gabanka. To bari ka ji Ciroma koda ta Allah ta kasance da mai martaba ba za ka taɓa hawa karagar mulkin kudu ba gwara tun wuri ka kauda idanunka akanta. Kada ka bari shaɗaniyar zuciyarka ta yaudare ka, ta jefa ka mahalaka. Tashi ka bace muna da gani shashasha kawai, mai zuciyar kafirai farko.
Jiki a sabule Ciroma ya baro gidan waziri amman da kudirin duk da ranar da ya cimma burinsa na zama sarki sai waziri yagane kuskurensa na faɗa masa magana.
*AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT*
Misali ƙarfen 3:22pm jirgin da AB ya biyo daga Lagos zuwa Kano ya yi landing Abdulkarim ya kira ya zo ya yi picking dinsa, suna tafe suna fira "Ak gidan Daddy za mu fara zuwa dan na yiwa Baby Aydah alkawarin da zarar na dawo zan zo na dauke ta kasan ba wani dadin zaman can gidan take ji ba, Sadiya takura mata take yi.
Tun sanda ya fara magana Abdulkarim yake satar kallonsa sai kuma ya ce "Ni na rasa wane irin jahilci ne ke dawainiya da Sadiya? Banda daƙiƙanci me Aydah ta yi mata meye laifinta da za ta ta uzira mata? Amman ba laifinta bane duk wannan sanyi hali ne naka AB ya jawowa Aydah.
"Ak bansan me zan yi mata ba in fact Sadiya ƙanwa ta ce duk yanda ta zama matsayinta ba zai taɓa canzawa ba a wurina.
"Mtss! Ai ka ji matsalarka duk sanda aka yi magana za ka ce ƙanwarka ce shiyasa take amfani da sanyi halinka tana yi yadda tagama dama.
Har suka iso AB bai ƙara cewa komai ba. A babban parlor suka tarar da Mami da su Siyama yau lectures ɗin safe suka yi shiyasa dukkan su suna gida, Aydah kuma tana ɗakinta a ƙunshe da ta fito parlor ta zauna Mami ta kore ta dole ta koma ɗakin, ta cigaba da karanta novel ɗinta. Ita daman ta fi sabawa da zaman ɗaki fiye da parlor shiyasa ko kaɗan bata damu ba. Siyama ta dinga murnar ganinsa ita ma Sadiya fara'a take yi ta kasa ɓoye farin cikinta.
#love story2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo
Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[1/3, 3:53 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye
050.
Gaisuwa da suka yiwa Mami da kyar ta amsa shi ma a dage Siyama ta tashi ta je kitchen ta hado masa abinci har ya kammala ci abinci bai ga Aydah ba sai kawai ya wuce ɓangarensa na da ya yi wanka, yana dawowa daga sallar la'asar ya kira Siyama ya ce ta kira masa Aydah ta zo su tafi. Mami dake kitchen ta fito a fusace Sadiya na biye da ita, Sadiya ta jingina jikinta ga bangon kitchen ta harɗe hannayenta a ƙirji sai da Mami ta fara jefa masa mugun kallo kamin ta ce "Abba ba inda Aydah za ta je ta dawo kenan ina jiran ka kawo min takardar sakin 'yata mai goyon bayanka baya gari saboda haka Aydah ta dawo kenan.
Mamaki ne ya lulluɓe AB ya kasa furta uffan Siyama ta fadawa Aydah sakon AB ta zubura ta shiga tattara kayanta da ta yi amfani dasu ta mayar cikin akwatinta, ta fito Siyama sai faman kallonta take yi tana murmushi suna saukowa ƙasa suka yi turus sakamakon yadda Mami ke ta fadar bakaken maganganu akan Abba.
"Da alama ka fara taɓa jikin Aydah zuwa gaba ma za ka iya wuce haka har ni Aydah za ta duba ta cemin duk abunda za ka yi mata ba haramu bane yaushe Aydah tasan da hakan idan har ba kaine ka fara ɗora ta a hanya ba. Tun da na fahimci ɗan iska ne kai ba zan bari ka lalatawa 'yata rayuwa ba kai ko kunya ba ka ji da girman kana lalluɓar yarinya ƙarama.
Wata irin kunya ce ta lulluɓe shi a maimakon maganganu Mami su farantawa Sadiya rai sai ta ji wani mugun haushi cikin fusata ta ce "Mami ki daina gani laifin yayanmu laifi na wannan little brat ne ita ke shige masa.
"Don me ba za ta shige masa ba yaya Sadiya ko kin manta su ɗin miji da mata ne ko akwai wani nafsi da ya yi hani mata ta shigewa mijinta.
Siyama ta faɗa cikin fushi don ba ƙaramin haushi Sadiya da Mami suka bata ba.
"Ya isa Siyama!
AB ya faɗa kamin ya mayar da ganinsa wurin Aydah ya tambaye ta gaskiyar abunda Mami ta faɗa girgiza kai Aydah ta yi idanunta har sun cicciko da hawaye "Yayanmu tun zuwana gidanan ko downstairs parlor ban sauko ba ko gaida Mami nayi bata amsawa, yaya Sadiya kuma ta bini da zagi to yaushe naga Mami balle na faɗa mata wannan maganar ba ni ban ma fahimci me kuke nufi ba.
Ta ƙarashe magana tana sharar hawaye da bayan hannunta.
Sosai ran Mami ya ƙara ɓaci ban taɓa tsammani Aydah ta iya tsara magana irin wannan ba.
"Aydah ni nake miki karya?"
Aydah ta girgiza kai alamar a'ah!
"To shi kenan bara na kira Huwaila ai a gabanta aka yi Huwaila zo nan!
Mami ta faɗa cikin daga murya Huwaila ta fito daga kitchen da sauri ta rakuɓe jikin bango saboda duk abunda ke faruwa akan kunneta cikin tsawa Mami ta tambaye ta Huwaila ta girgiza kai muryata yana rawa ta ce "Ki gafarce ni Mami ni kan ban ji sanda Aydah ta faɗi haka ba Allah na tuba dukka Aydah guda nawa ce da za ta faɗin manyan zantuka irin waɗannan.
Wani kalan ajiyar zuciya Aydah ta yi har cikin zuciyarta ta ji dadin yanda Huwaila ta kare ta.
"La'illaha illallahu muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam! Huwaila daman ke munafuka ce bansani ba ina zaune dake da zuciya guda za ki karyata ni koda karya nake yi Huwaila na zaci za ki rufan asiri to bari ki ji yau zamanki ya ƙare a gidanan yanzu nan za ki bar min gidana munafuka algunguma.
Huwaila ta zube guiwayoyinta ƙasa tana kuka tana rokon Mami ta yi hakuri amman Mami sai rantsuwa take yi sai ta bar mata gida, Sadiya ta fizgo hannun Huwaila har sai da ta miƙe tsaye ta tusa ƙeyarta gaba zuwa ɗakin da ya kasance nata a gidan.
AB ya kalli Mami "Mami dan Allah ki yi haƙuri kada ki kore Huwaila kada ki yi mata hukunci da laifin da ba nata ba.
"Mtss! Mami ta ja tsaki tare da watsa masa mugun kallo ta haura haura bene a fusace tana ji kamar zuciyarta za ta kama da wuta, wata kila dole sai ta bi hanyar da Hajiya Zeena take so ɗora ta akai kamin ta raba wannan ɗan iska yaron da Aydah.
Sadiya ba ta bar Huwaila ba sai ta haɗa kayanta kaf sannan suka dawo parlor, kallonta kurum AB yake yi yana jin tsanarta tana bin jini jikinsa ya yi ƙwafa ya juya domin idan ya ce zai cigaba da tsayuwa a wurin komai zai iya faruwa, Siyama ta kama hannun Aydah ta ce da Huwaila "zo mu tafi Huwaila wani hani ga bawa baiwa ce don an kore ki daga aiki a gidanan ba shi yake nufi kwanaki ki a duniya sun ƙare ba.
Suka fice Sadiya ta bi su da tsaki tana durawa musu ashariya, a parking lot suka tarar da AB ya shigo motarsa Siyama ta buɗewa Aydah front seat ta shiga kana ta dawo ta buɗewa Huwaila backseat ta ce ta shiga sannan ta miƙa mata akwatin Aydah. Ta dawo saitin da AB yake ta ce "Yayanmu ka cigaba da haƙuri da kake yi Allah yana tare da masu hakuri wata rana sai labari, ga Huwaila nan nasan kuna bukatar ta a gidanku.
Har suka isa gida ba wanda ya yi magana AB ya nunawa Huwaila ɗakin da za ta zauna ta shigar da kayanta fuskar nan tasa a haɗe ya ce Aydah ita ma ta ɗauki akwatinta ta wuce ɗakinta shi kuma ya wuce nasa bai sauko ƙasa ba sai da aka yi kiran sallar magarib bai baro masallaci ba sai da aka yi sallar isha daga nan ya wuce restaurant ya siyo musu abinci. Parlor ya ajiye takeaway ɗin ya haura sama kaitsaye ɗakin Aydah ya nufa har zuwa lokaci fuskarsa babu walwala ko kaɗan ya tura kofar ɗakin nata, tana kwance akan gado ƙarar buɗe ƙofar yasa ta juyowa cikin sauri idanunta suka faɗa cikin nasa yanda taga fuskarsa a murtuƙe sai da gabanta ya faɗi.
"Abinci yana parlor ki taso ki ci amman ki tabbatar kin yi wanka kin canza waɗannan kayan na jikinki.
Aydah ta ya mutsa fuska tamkar za ta
fashe da kuka take kallonsa, yi ya yi kamar bai ga abun da take shirin yi ba ya fice abinsa. Jikin Aydah ya yi sanyi don ta gama fahimtar fushi ne yake yi ta tashi ta shiga bathroom ta yi wanka kaman yadda ya umarce ta, ta shirya cikin doguwar rigar bacci ta sauka mata har ƙasa, ta ɗan shafa turare ta fice tun kamin ta karasa saukowa ta hango shi zaune yana waya, ta nemi kujera ta zauna da hannunsa ya yi mata nuni da ledoji takeaway ɗin dake kan centre table, ta ɗauki pack guda da spoon ɗin dake ciki ta shiga sai da ya gama waya batareda ya kalleta ba ya ce daita idan ta kammala ta ɗauki guda ɗaya ta kaiwa Huwaila, tana gamawa ta dauka ta kai mata ganin yau bai bata fuska ba sai kawai ta komawarta ɗakinta. Bata tsaya a parlor sunyi kallo kaman yadda suka saba ba ita yau tsoronshi ma take ji gwada tayi nesa-nesa dashi.
Washegari Huwaila tana kammala sallar asuba ta shiga gyaran gida ko'ina ya yi fess, da duba kitchen babu foodstuffs da nufinta ta yiwa masu gidan break fast dole ta koma ɗakinta ta kwanta ba don tana jin bacci ba. Aydah tana kammala shirinta na school ta fito bayanta goye da bagpack ɗinta, ta zauna a parlor tana jiran AB ya sauko ya kaita school bata fi five minutes da zama ba sai gashi ya sauko kaman dai jiya fuskarsa a haɗe.
"Ina kwana Yayanmu!
"Lafiya ƙalau tashi mu tafi.
Ta tashi jikinta a sanyayye tana mamakin wannan canzawa da ya yi mata, sai da ya tsaya a restaurant tayi break fast shi kuma ya yi musu takeaway shi da Huwaila sannan ya sauke ta school ya kawo three thousand as usual ya bata, bayan ya dawo ya yi wanka ya shirya cikin blue suit da white colour long sleeve shirt, ya saka necktie white ya yi matuƙar kyau a parlor ya tarar da Huwaila tana ƙara goge centre table ɗin da ke girke a tsakiyar parlorn, ya nuna mata abincinta kana ya ce zai aiko da direban Kamfani ya kawo foodstuffs sai ta yi musu girki. Huwaila ta amsa cikin girmamawa tare da yi masa fatar adawo lafiya. Bayan tafiyarsa ne ta haura sama ta shiga ɗakinsa ta gyara masa tsaf ta wanke bathroom tare da saka turaren wuta ɗakin ya gauraye da ƙamshi ta rufo ƙofar ta nufi na Aydah shi ma ta gyara shi ta wanke banɗaki da panties ɗin Aydah guda biyu da tarar a cikin laundry basket. Tana gamawa da ɗakin Aydah ta dawo downstairs parlor ta zauna.
*MASARAUTAR KUDU*
A yau Masarautar Kudu ta tashi da mummunan labari na mutuwar sarki Mahmood, ba ƙaramin tashin hankali iyalansa da jama'ar gari suka shiga ba Fulani babba ta yi kuka har ta gode Allah ita kuma dramar queen Fulani ƙarama har da suman ƙarya lokacin dasa mutuwar mai martaba ta riske Ciroma a lokacin yana parlornsa tare da iyalinsa suna taking breakfast Galadima ya kirasa a waya ya faɗa masa daddaɗan albishir, tsabar farin ciki mantawa ya yi da yana gaban Uwargidansa Maryama da 'ya'yansa wanda basu san takamaiman abun da ya aikata ba sai gashi tsanani farin cikinsa da ya kasa boyuwa ya miƙe tsaye yana hamdallah har dasu sujjudi shukur hakan yasa yana gafda
fallasa sirrinsa. Mamaki ne ya lulluɓe Maryama har ta gaza haƙuri ta furta "Ciroma wani abun farin ciki ne ya same mu?"
Ya ɗago daga sujjadar da ya yi yana wani tattara babbar rigarsa sai yaƙar haƙora yake yi "wallahi kuwa Maryama mai martaba dai wa'adi ya cika burina na zama sarkin kudu zai cika. Kai Al-hamdullilah Allah abin godiya boka mai Gundulelliya aikinka ya yi kyau dole nai maka babban tukuici.
Zazzaro idanuwa Maryama ta yi cikin kaɗuwa ta furta "Innalillahi wa'inna illahim raji'um! Ciroma daman kana da sa hannun a ciwon mai martaba? Anya kuwa Ciroma kana so ka gama da duniya lafiya? Meyasa kai Kwata-kwata babu tsoron Allah a zuciyarka? Wallahi Ciroma ka yi asara amman ba laifinka bane har da zugar wannan tsinanniyar matar taka Umaima kin zama annoba kin zama silar jefa rayuwar mijina halaka Allah ba zai barki ba Umaima.
Ciroma ya yi sakwarkwatai ya rasa me zance da zai kare kansa, maganar zarar bunu idan ta fito bata komuwa balle ya maidata, sai rarraba idanuwa yake yi na rashin gaskiya muraran. Umaima ce ta zuburo daman ita ba gudun abun kunya take yi ba.
"A'ah! Ya haka malama za ki kirani da tsinanniya? Don kawai na taimaki mijina domin ya cimma burinsa, in dai akan taimakon mijina ne ki kirani da abun da ya fi tsananniya ba abun da ya dame ni Allah na tuba me tsinuwarki za tayi me. Ko kuma ko kina so ko bakya so sai Ciroma ya zama sarkin kudu sai dai bakin ciki ya kar ki.
"Ke dallah ya isa haka! Maryama sa'arki ce da za ki dinga faɗa mata magana banaso kama hanya ki tafi ɓangarenki banaso fitina.
Ciroma ya yi magana a tsawace har wani zarewa Umaima idanunsa yake yi, dole ta fice ranta yana mata tuƙuƙi duk da Umaima bata yi mamaki yadda ya daka mata tsawa ba bakon abu bane a wurinta, daman can haka yake mata akan Maryama ta rasa wane irin tsoronta yake ji tasan Maryama bata bin malaman tsinbo balle bokaye hasali ma shahararriyar malamar addini ce da babu na biyun ta acikin da wajen masarautar kudu. Kuma riƙaƙƙiyar 'yar Ahalil sunnah ce. Sai dai Umaima ta danganta hakan da tsanani son Maryama da Ciroma ke yi yadda yake so ko Kilishi da ta