Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   43 / 80

126K to 129K   out of 237.2K words

ga doctor wata kila sai an ƙara yi miki waɗansu allurai.
Wani kalan zare idanuwa Aydah ta yi tana girgiza kanta "wallahi na ji sauki sosai Yayanmu ba sai an min wasu allurai ba.
Girgiza kai kawai ya yi ya juya tare da nufar ƙofar fita daman wannan tsayuwar da ya yi a tare da ita jiki yake tamkar ana hura masa wuta ne a jikinsa, daurewa kawai yake yi Aydah ta bishi da kallo tana jin wata irin ƙaunar yayan nata ta musamman tana bin zuciyarta. Tun daga sanda Aydah tasan zance auren AB da Rumaisa ta bi ta tsangwami kanta da yawan tunani duk ta bi ta kare kamar kuɗin guzuri daman ga jikin nata sai a hankali.
Ta bangaren Sadiya ita ma kamar za ta yi hauka takanas ta shirya ta je har office ɗin AB ta same shi tana mishi kuka tagumi kurum ya yi tare da zuba mata ido sai da tayi kukanta mai isarta ta share hawayenta "Yanzu yayanmu duk irin ƙaunar da nake maka kana nufi za ta, tashi a banza ne?
"To miye amfaninta ne Sadiya? Sanin kanki ne koda ban aure Aydah ba Sadiya da matuƙar wahala mu sake kasancewar a karkashin inuwar aure.
"Wai me kake nufi ne yayanmu soyayyar tawa ce bata gamsar da kai ba ko ban kai matsayin da zaka soni ba?"
"Ba ko ɗaya kawai dai ita zuciya ba a mata dole tun farko zuciyata da wacce take so Rumaisa ita kadai ce mace da na tsara rayuwata da ita daga kanta bana tunani zuciyata za ta iya karbar wata mace.
"Wallahi-azim Abba ba ka isa ba ko sama da ƙasa za su haɗe sai na mallake ka walau ta saukaƙkiyar hanya ko kuma akasin ta daga Rumaisa har wannan kwaila sai na fincike su ta karfin tsiya daga rayuwarka, don ni kaɗai Halimatus-Sadiya aka halicci ka idan har ba za ka zama nawa ni kaɗai ba na rantse da Ubangiji sammai bakwai ba wata 'ya mace da zan bari ta rabe ka, cikin sauki wannan alƙawarina ne.
Sadiya ta faɗa a mugun fusace tana mai miƙewa tsaye tana dukan desk ɗinsa, shi ma Abban miƙewa ya yi saboda ta fara kai shi makura, ga baki ɗaya ta bi ta gallazawa rayuwarsa haka take kiran wayarsa dare da rana sam ba ruwanta da duba lokaci, ta zarar abin ya motsa mata numbernsa kawai za tayi dialling wani lokaci yana tsakiyar bacci kiranta ne zai tada shi wasu lokuta yana aiki, shi bai taɓa gani mace marar class da kamun kai irin Sadiya Bashir ba, har mamaki yake yi uwa ɗaya uba ɗaya ne ya basu tarbiyya a wasu lokuta kuma sai ya yi mata uzuri a dalili fahimtar da ya yi tana tu'anmali da miyagun kwayoyi wanda yake gani har da taimakon su wajen yaye mata kunyarta, ta 'ya mace. "Sadiya tashi maza ki fice min daga office na fahimci kwayoyi da kike sha sun fara taɓa miki ƙwaƙwalwa.
"Yes! Abba ina sha kwayoyi, kasani sonka da ƙaunarka sune silar jefa ni cikin wannan mummunan hali, idai akanka ne yayanmu bana ji bana gani na shirya tsaf na ƙara jefa kaina acikin hali da yafi shan kwayoyi da nake yi muni wallahi ko rai zan iya dauka akanka.
Tsaye kawai AB ya yi yana kallon Sadiya yadda take ta faɗa munana maganganu, bai yi mamaki ba saboda shi ya dauketa ne ya jefa a layin marasa cikakken hankali.
"Idan kin fasa ɗaukar rai akaina Sadiya Allah ya tsine miki, so nake ki ɗauki rai ɗin shashasha banza mahaukaciyar wofi dakikakiya, 'yar ƙwaya kawai wacce batasan inda yake mata ciwo ba.
"Ni, ni yaya Abba ni Sadiya kake jifa da wannan muggan maganganu?"
"Ke ɗin har wata tsiya ce da ba za a jefa ki da muggan maganganu ba? Ke bari ki ji ki daina gani ina daga miki ƙafa ina lallaɓaki ki ɗauke ni just for granted, duk lokacin da kika sha ƙwayar ki ta birkita miki tunani ki zo ki baza min hauka, to daga yau ba zan sake lamunta da wannan iskanci ba wuce ga hanya nan ki fita min daga office.
Wani zazzafan numfashi Sadiya ta sauke hawaye masu zafin gaske suna silalo mata akan kumatunta, sai da ta ƙare masa kallo from head to toe kamin ta wani girgiza kai hawaye suna watse akan fuskarta "Kada ka yi tunani waɗannan maganganu naka za su yi tasiri akaina na haƙura da kai wallahi ko dar ban ji ba asalima sun daɗa ƙara min kwarin gwiwa, sai na sake zama matarka Yayanmu a karo na biyu ko kana so ko baka so we'll surely get back together saboda zallan ƙiyayya da kake min sai ka tanadin wuƙa da za ka dabamin ko ka yanka ni a daren farkon mu kamar dai yadda nai maka a wancan karo.






#JEEDDAH ALIYU
#ASMY B ALIYU
#KURMAN ALLO






Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[1/7, 10:18 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye


059.


(MASARAUTAR KUDU)


Abu kamar wasa masu iya magana suka ce ƙaramar magana ta zama babba, domin kuwa ta tabbata Ciroma shi ne zaɓaɓɓen sabon sarkin kudu, lokaci da wannan magana ta kai kunnen Kilishi yanke jiki tayi ta faɗi ta riga ta ƙwallafa ranta, akan Ahmadu ne zai zama sabon sarki duk wani burinta akan Ahmadu yake, sai gashi Ciroma ya yi mata shigar sauri lokacin da wannan labarin ya riske mai babban ɗaki ko kaɗan hakan bai mata daɗi ba domin ita ma burinta ace Aliyu ne zai hau karagar mulkin kudu shi kansa Aliyu yaso ace Ahmadu ne ya zama sarki ba Ciroma ba. A dalilin mugun halin Ciroma da ya gama sani da wahala ya yiwa talakawa adalci. Sai dai ba yadda suka iya saboda manyan fada ne suka zaɓe shi. Aliyu na Uku bai baro masarauta ba har sai da aka saka date ɗin nadin su a wannan karo bai nuna ƙin amincewarsa ba, fahimtar da ya yi burin mahaifiyarsa kenan na gani ya karɓi sarauta. Koda ya koma Lagos kwana sa uku a ya wuce Germany akan wani business trip.
KIM'S AUTOMOBILE INDUSTRY LAGOS
Anaal zaune a office ɗinta hannunta riƙe da wayarta picture ɗin AB take kallo batasan yaushe zuciyarta ta kamu da matsananciyar soyayyarsa ba, tana ji a yanzu ya zama wani bangare na jikinta, soyayyarsa tayi mata wani kalan kamu da ba za ta iya haƙura dashi ba. Shi ne namiji na farko da zuciyarta ta fara so gashi bai masan tana yi ba iyakacinsa da ita abun da ya shafi business ɗinsu duk da tana da masaniyar bai daɗe da yin aure ba, sai take gani shi ɗin mijin mace huɗu ne za ta iya samun gurbi a zuciyarsa. Number ɗinsa ta yi dialling tana dab da tsinkewa ya yi picking muryarsa kaɗai da Anaal ta ji a dodon kunnenta sai da ta saki ƙarfaffiyar ajiyar zuciya ta ji wata irin natsuwa tana saukar mata cikin taushin muryarsa yai mata sallama, sai dai wani irin zullumi na rashin sani me za ta ce dashi ya lulluɓe ta "Hello mss Anaal kina ji na kuwa?
Da sauri Anaal ta katse kiran tana danne sautin da zuciyarta yake, tana sauke wahalallen numfashi a tunaninta AB zai kirata sai daga sabanin tunanin nata, don kuwa bai kira ta ɗin ba ga zuciyarta sai azalzalarta da son sake jin muryarsa tayi nisa a tunaninsa har bata ji sanda Zaheed ya turo ƙofar office ɗin nata ya shigo yana gani yadda ta kurawa wayarta ido cikin sanɗa ya qaraso gabda ita ya fizge wayar hakan yasa ta zubura ta miƙe tsaye Zaheed ya tintsire da dariya yana mai kai idanunsa akan screen ɗin wayarta, picture ɗin wanda yaga tana kallo yasa shi ɗagowa da sauri ya yada ganinsa akanta cikin sauri ta kauda fuska "Sis kar dai ki cemin you're in love with this guy?"
Kasa bashi amsa Anaal tayi sai kawai ta nufi ɗaya daga cikin cushion ɗin dake cikin office ɗin nata, ta zauna tare da tallaɓe kumatunta da hannayenta biyu. Zaheed ya tako ya zauna kusa da ita sai da ya kare mata kallo kamin ya sake maimaita mata tambayarsa da farko "I don't know.
"Ban gane ba kisani ba me hakan yake nufi Anaal?"
"Zaheed koda ina sonshi ba wani amfani acikin soyayyar da nake masa gara kawai nayi kokari yakice shi daga raina.
"Hey! Don't say that idan har da gaske kina sonshi you have to fight for his love, ba abun da kika rasa na cikakkiyar mace firstly you're an educated both boko da ilimin addini Allah ya wadata ki dasu also you're a very beautiful girl kowanne namiji yana da burin mallakar mace irinki saboda haka kada ki tsaya wasa just fight to get his love.
"Ba za ka gane ba Zaheed he's married yana da mata ko wata ɗaya bai yi ba da aure.
"So what don yana da aure kin manta da Addini ya hore masa da ya aure mace har guda huɗu?"
"Ban manta ba Zaheed sai dai bansan nayi abun da zai taɓa kima da darajata, ta 'ya mace.
"Anaal ni kaina ba zan so ki yi abun da zai taɓa mutuncinki ba amman zan so ki sami namiji da kike so, dan ki faɗamasa kina sonshi ba zunubi bane dan Allah kada ki cuce kanki.
"Okay! Na ji zan yi tunani akai idan naga dacewar na gayamasa zan faɗamasa ɗin.
"Shi kenan ki yi tunani mai kyau kada ki kwari kanki ki dawo daga baya kina danasani.
Murmushi kurum Anaal tayi tare da amsar wayarta daga hannunsa.
***********
Wata kalar tsawa AB ya dakawa Sadiya har ga Allah haƙuri sa ya fara karewa ta fara kai shi makura, cikin kakkausar murya ya ce da ita "Sadiya wannan shi ne kashedi na dake na ƙarshe idan ba ki ficemin daga office ba wallahil-azim zan yi miki wulaƙanci da ba a taɓa yi miki kwatakwacinsa ba.
"Zan fita Yayanmu ba wai dan kace za ka wulakanta ni ba kawai dai zan fita ne a bisa ra'ayin kaina, duk masifa da wulaƙanci da za ka yi ba zai dame ni ba ballantana ya hana min cimma burina akanka.
Tana ƙarasa magana ta dauki handbag ɗinta a fusace ta fice ta buɗe kofa tare da rufu ta da ƙarfi, AB ya ɗauki telephone ya kira secretary ɗinsa Skyler ya bata umarnin daga yanzu ko Sadiya ta zo karta sake ta barta ta shigo masa office.
Sadiya tana baro office ɗin AB tayo gidansu Rumaisa har cikin compound ɗin gidan tayi parking motarta ta kashe motar tare da fitowa ta nufi entrance ɗin gidan kanta tsaye ta tura ƙofar main parlor mai aikin gidan ta fara cin karo da ita cikin zuciyarta tana bugawa da kalli mai aikin tare da tambayarta mutane gidan "Ammi ta fita sai in aunty Rumaisa za a kira miki.
Kyakkyawar ajiyar zuciya Sadiya tayi tare da faɗin a kira mata Rumaisa ɗin daman gunta ta zo, 'yar aiki har ta fara haura mattakalar bene Sadiya ta dakatar da ita ta hanyar faɗin ta nuna mata ɗakin nata kawai ta same ta acan, a tunani mai aiki Sadiya tana ɗaya daga cikin ƙawayen Rumaisa ne saboda kusan kullum sai ƙawayen nata sun zo suna tayata shirye-shiryen bikinta da ya karato don haka bata kawo komai aranta ba ta wuce gaba Sadiya ta bi ta a baya suna zuwa daidai ƙofar shiga ɗakin Sadiya ta dakatar da ita "Komawarki bakin aikinki zan ƙarasa da kaina.
Batareda da mai aikin tace komai ba ta juya abinta, kai tsaye Sadiya ta tura ƙofar ta shiga ba ko neman izni balle sallama daidai Rumaisa ta fito daga wanka tana daure da ƙaramin towel wanda iyakancinsa cinyoyinta, hannunta riƙe da hand towel tana goge gefen wuyanta, jin an turo ƙofar ɗakinta batareda da an yi knocking ba yasata yada ganinta akan ƙofar wacce ta gani ta shigo ce ta haifar mata da faduwa gaba "Sadiya!!
Ta kira sunanta da madaukakin mamaki shimfiɗe akan fuskarta.
Cike da izza da zallan izgilanci Sadiya ta tako ta iso gaban Rumaisa ta tsaya ta shiga kare mata kallo from head to toe, sai kuma ta ja dogon tsaki "Sadiya lafiya za ka fadomin ɗaki babu neman izinina tsabar wulaƙanci da rainin wayau ki dube ni sama da ƙasa ki ka min tsaki kanki ɗaya kuwa kodai kin fara shaye-shaye ne?"
Cikin tafarfasar zuciya Sadiya ta jefa idanunta cikin ƙwayar idon Rumaisa, ranta yana mata ƙuna wato kowa ma ya gama sani tana tu'ammali da miyagun kwayoyi wato yanzu kowa ya buɗe bakinsa zai mata magana sai ya gorata mata saboda haka ta ji ranta na ɓaci zuciyata ta harzuƙa "Zuwa nayi na kashe miki gargaɗi da kakkausar murya Rumaisa kada soyayyar yayanmu ta rufe miki ido ki kasa gane irin masifar da kike kokarin jefa kanki. Rumaisa kisani bakin rijiya fa ba wurin wasan makaho bane mijina yafi karfin kucakar mace irinki kada ki sake ki aure mijina idan har kika bari ƙaddarar aure ta shiga tsakaninku na rantse wanda rayuwata take hannunsa sai na gana miki azaba sai na mayar da rayuwarki abin kwatancce. Abba nawa ne ni kaɗai duk 'yar da ta kuskura ta rabe shi sai na datse mata farin cikinta sai na mayar da duniyarta baƙa wulik!
Rumaisa ta ɗage girar ido tare da rungume hannuwanta a ƙirjinta, tana kallon bakin Sadiya yadda take da irin wannan ƙarfin hali na shigowa cikin gidansu, kuma har cikin ɗakinta sannan kuma tana mata gargadi ta rabuda AB wanda dukka kwanaki ƙalilan ya rage musu, su mallaki juna ta hanyar aure lallai kuwa Sadiya bata da hankali cikakkiyar mahaukaciya ce in ma banda hauka ita da AB yake auren ƙanwarta uwa ɗaya uba ɗaya meye gamin ta da zuwa yi mata kashedi akansa sai dai Aydah ita da take matarsa ba dai ita ba da ta gama zama tarihi acikin rayuwarsa. Sai kawai abin yabawa Rumaisa dariya ta saukar da hannayenta daga ƙirjinta tayi flagging da hand towel ɗin dake riƙe da hannun nata, ta yiwa Sadiya kaskantatcen kallo "Ke wama kike da suna?oh Sadiya ko ke har kin isa ki shigo mana gida ki karanta min bayan littafi sannan kuma ki yi tunani karatun naki zai girgiza ni?" Idan haka yaudararriyar zuciyarki ta gayamiki Sadiya tayi kuskure, Abba Bashir ya yi miki nisan da har ki kwanta dama ba za ki taba samun sa ai abin da ba ki sani ba Sadiya opportunity comes once kin ri ga da ki yi wasa da damarki Abba Bashir ya subuce miki, yadda kika bar nonon uwarki haka zalika kika bar Abba.
Wani irin zazzafan numfashi Sadiya take saukewa Rumaisa tana dasa aya tayi kukan kure ta cafke wuyanta, nan take suka kaure da ƙazamin dambe ɗan towel ɗin jikin Rumaisa ya zame ya faɗi ƙasa hakan ne ya bawa Sadiya damar cafkar boobs ɗin Rumaisa ta ja su da bala'in ƙarfi tamkar dai yadda ake jan hanjin akuya wani kalan ihu Rumaisa ta ƙwalla ji take tamkar ana zare mata rai Sadiya bata sakar mata boobs ɗin nata ba sai ƙara murɗe su take yi, a haka ta ja ta zuwa ga dressing mirror ta buga kanta ga mirror ɗin nan take ya tarwatse jini ya yi inda yake so yayin da numfashin Rumaisa ya tsaya cak! Sadiya ta sake ta ta zube ƙasa hakan bai sa Sadiya ta kyaleta bin ta tayi ta haye ruwan cikinta tayi ta dukanta ga Rumaisa yashe tsirara haihuwar uwarta, buri da fatan Sadiya Rumaisa ta mutu, cikin sauri ta fito daga ɗakin har ta sauko downstairs parlor ta fice bata haɗu da mai aiki ba. Zuciyata ba ko dar balle alamar tsorata ta ja motarta maigadi ya buɗe mata gate ta fice abinta. Daga gidansu Rumaisa tayo gida kai tsaye ɗakin Mami ta wuce ta tarar da Mami tsaye a jikin wardrobe ɗinta tana shirya kayanta da aka kawo daga wurin wanki, zubewa tayi akan gadon Mami tana wani sauke numfashi ɗaɗɗaya da gaske ba za ta lamunci ta rasa AB ba domin kuwa ya zama mata tamkar rayuwata ne tana sonsa kwatankwacin Irin so da komai za ta iya aikatawa dan kawai ta same shi wannan abun da ta yiwa Rumaisa somin taɓi ne wanda tanadarwa da Aydah sai yafi na Rumaisa madawaki muni sai ta fincike su da ƙarfin tsiya daga rayuwar Abba Bashir, guntun tsaki Mami ta ja tare da rufe wardrobe ɗin ta ƙaraso gefen Sadiya ta zauna "ke lafiya kika shigo min kina wannan irin sauke numfashi tamkar wacce ta yi tseren gudun gasar Olympic ta zo ta ɗaya?"
Sadiya bata iya furta uffan ba jin maganganu Mami take yi suna amsa kuwa acikin kwayar kanta, ta runtse idanuwanta da karfi har Mami na iya gani yanda ƙirjinta ke bugawa fat fat "Sadiya ki yi min magana mana ko bakida lafiya ne na kira doctor ya zo ya duba ki ko kuma ki tashi mu tafi asibiti.
Still Sadiya bata ce komai ba hakan ya hasala Mami ta rufe ta da faɗa, cikin mugun yanayi Sadiya ta buɗe idanunta da suka yi jajur ta kalle Mami dasu kamin cikin rawar murya ta furta "Mami ina sonsa ina azabar sonsa idan har zan rasa shi to kuwa babu wata 'ya mace da za ta same shi na kashe Rumaisa madawaki saura Aydah dukka su biyu ba zan barsu da rai ba.
"Innalillahi wa'inna illahim raji'um! Me kike faɗa ne Sadiya kisa fa na ji kin faɗa? Anya kuwa Sadiya ba ki shawo kwayar da tafi ƙarfin ƙwaƙwalwarki ba?" Aydah fa ƙanwarki ce ta jini kike faɗar za ki kasheta saboda wani ƙato ɗan shegiya wanda bai da cikakken asali.
"Mami ko daga sama Yayanmu ya fado ina sonsa a haka shi ne duniya ta kisa ita ce hanyar da kaɗai zai gamsar da Yayanmu irin matsanancin so da nake masa. Wawan duka Mami ta kai mata a

43 / 80