Author : EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category : KDP NOVELS
yawa ya sake kwatar da muryarsa, ya ce "Na haɗa ka da girman Allah Aliyu ka buɗe baki ka yi magana ka tuna girman wannan al'amari idan ba ka yi magana ba, fada za ta yanke maka hukunci marar daɗi. Ina ji a jikina Aliyu ba ka aikata wannan al'amari ba dole da akwai wani kurman allo da kai kaɗai kasan da wanzuwar sa.
Karo na farko da Aliyu na Uku ya ɗago ya bi mutane dake zazzaune a faɗa da idanunsa, kafin ya sauke numfashi ciki maganarsa mai cike da zallan izza ya ce "Ina mai ba wa fada haƙuri da sauran jama'a tabbas wannan video ɗin babu ƙarya ni ne a ciki.
Nan da nan fada ta hartsune da surutu mutane sai sallati da tafa hannuwa suke yi, sai da sarkin fada ya tsawata musu sa'annan suka yi shiru, waziri ya kalli Aliyu na Uku ya ce "Kai muke saurare ranka shidade ko iya abun da za ka ce kenan.
"Shuɗadden al'amari ne da ya faru tun lokacin da na je karatu a London, anan na haɗu da ita a wancan lokaci tana amsa sunaye guda biyu domin iyayenta suna bin mabanbanta addinai, mahaifinta ya kasance musulmi ne ɗan ƙasar Qatar shi yana kiranta da Maysun, mahaifiyarta kuma 'yar asalin Rasha ce Christan ce shi yasa take kiranta da Elissa. Koda muka yi aure tana matsayin christan.
Sake harsunewa fada ta yi da surutu, kowa da kalar abun da yake fada. Hakan yasa Aliyu na Uku ya dakata da basu labari ya ja bakinsa ya tsuke.
Ga baki ɗaya mutane dake fada mamaki ne ya lulluɓe su an ɗauki lokaci kamin sun yi shiru in da Aliyu na uku ya cigaba da basu labarin yadda soyayyarsa da Maysun ta fara har izuwa aurensa tare da ɗa da suka haifa har ɓatansa da irin fafutukar nemansa da suke yi, domin ya sami wata majiya mai doshe wanda suke zargin ɗansu yana wurinsa yana zaune a garin Katsina.
#JEEDDAH ALIYU
#ASMY B ALIYU
#KURMAN ALLO.
[2/6, 1:54 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye
098.
Bayan ya gama basu labari fada ta yi shiru yayin da baƙin ciki ya lulluɓe Ciroma ji yake yi kamar ya haɗiye zuciya, ga takaicin Waziri da ya gama cika sa duk shi ne ya rugaza masa plan da so ya yi da zarar Aliyu ya amsa kiran fada ba zai tsaya sauraren wani banzan labarinsa ba zai sa a tube masa rawaninsa ya cikawa Galadima alkawarin da ya ɗaukar masa amma wannan ɗan bagidajiya waziri ya lalata masa komai. Amma duk da haka zai nuna shi yake da ƙarfin iko a masaurata yana wani muzurai ya ɗago ya ƙarewa fada kallo, kana ya kara ɗaure fuska tamau ya murza zoben tsafi da boka mai Gundulelliya ya mallaka masa a duk sanda yake so ya aiwatar da wani zalunci wanda babu wanda ya isa ya musa masa yake amfani dashi da zarar ya murzarsa shi kenan magana ta kare. Cikin kakkausar murya ya ce "wannan labarin naka Aliyu duk wani mai cikakken hankali ba zai yarda dashi ba, idan har da gaske kun yi aure da ita dadiron taka ka faɗa mana ina shaidunka, da waliyain ka,ko kana nufi haka sidam kun ka yi aure har da haifar ɗan shege.
Wani irin ɗagowa Aliyu na uku ya yi kiran ɗansa da suna shege da Ciroma ya yi ya taɓa sa matuƙa, nan da nan idanunsa suka fara canza colour. Tsanani ɓacin rai yasa ya yi shiru ya kasa bashi amsa, daman abun da Ciroma ke so kenan ya harzuƙa sa saboda yasan Aliyu akwai zuciya da zafin kai.
"Ka ba mu amsa Aliyu idan kuma ƙaryayyakin naka sun ƙare sai mu sani.
Nan ma Aliyu bai tanka sa ba sai ajiyar zuciya yake saukewa tare da furza da zazzafar iska daga bakinsa, waziri ne ya taso da gun zamansa ya koma kusa da Aliyu ya sassauta murya ya ce "Kada ka bari fushinka ya zama makamin da za a cutar da kai Aliyu, ka tuna girma da martabar da wannan masauratar take da babban abun takaici ne ace yau an kore ka daga cikinta. Ka tuna halin da mahaifiyarka take ciki da irin abun da zai iya faruwa da ita idan ta farfaɗo ta sami mummunan labarin korar ku daga masaurata.
Runtse idanuwa Aliyu na Uku ya yi shi kadai yasan irin zogi da raɗaɗin da yake ji ciki da wajen zuciyarsa, amman da ya tuna da mai babban ɗaki ya tuna da irin yadda ta dauki gidan sarauta tamkar rai da numfashinta tabbas idan aka kore su za ta iya haɗiye zuciya ta mutu. Tunawa da haka da ya yi yasa ya ɗan sassauta fushinsa ya ce "Allah ne kaɗai shaida ta, sai kuma church ɗin da aka ɗaura mana aure, domin gudun faruwar hakan yasa muka yi marriage certificate idan fada tana bukata zan iya gabatar mata da certificate ɗin tare da waɗansu daga cikin pictures da muka ɗauka a ranar daurin auren mu.
"Wadannan ba za su taɓa zama gamsasshiyar hujja a garemu Aliyu, ka kawo mana shaidu na mutane da suka ga lokacin da kuka yi aure, tsawon shekaru talatin har da doriya ba wasa ba. Idan har ba ka da shaidun gani da ido kasani za mu hukunta ka, kamar yadda yake acikin kundin tsarin mulkin masauratar Kudu.
"Ina da shaidun gani da ido ahalin yanzu bansan inda suke ba, sune mutane da yarona Muhammad Azhar yake hannunsu ina rokon fada da tabani dama zan nemo Bashir da mai ɗakinsa Maryama a wancan lokaci a gaban idonsu aure ya wakana tsananina da Maysun, zan kuma kawo Maysun fada ku ji ta bakinta.
Aliyu na uku ya ƙarasa magana yana ƙoƙarin danne zuciyarsa don ji yake kamar ya gaggayawa Ciroma baƙaƙen maganganu sai kuma ya tuna da matsayin Ciroma a yanzu. Ciroma ya ƙara daure fuska, alamar zai zantar da hukunci da yake da burin zantarwa da Aliyu na Uku.
"ina son kasani Aliyu mu ba jahilai bane muna da ilimin addini da na zamani kuma Allah ya yi mana basirar fahimtar gane gaskiya da karya. Kasani ka ci mutuncin masaurata ka zubarwa da ahalin wannan gidan daraja sabida haka ba za mu bar haka ba dole sai mun hukunta ka domin ya zama izzana ga 'yan baya. Na tabbata da mahaifin mu na raye ba zai kyaleka ba a bisa wannan mummunan zunubi da ka aikata. Don haka mu ma da shi muke koyi ba za mu lamunta ba jini wannan alhali ya je yana aikata fasikanci a fili har mutane suna dauka ana yaɗawa akan kafafen sada zumunta, lallai kasani ba za mu kyale ka ba Aliyu Ina sarkin fada?
"Gani Allah ya ƙara ma lafiya.
"Ka tube mana rawani da ke kan Aliyu na Uku daga yau mun cire shi daga karagar sa ta mulki daga yanzu shi ba sarkin sabon birnin kudu bane. Kuma ya tattara shi da ahalinsa dukka su fice daga masarauta ba ma bukatarsa kuma yasani daga yau mun cire shi daga zuri'ar mai martaba sarki Usman na Uku. Hatta da mahaifiyarsa dake kwance akan gadon asibiti ba ma bukatarta acikin masaurata.
Nan take sarkin fada ya tube rawani Aliyu na uku, magatakarda ya rubuta takardar korar Aliyu sarki Hashim Ciroma ya buga hatimin masaurata akai.
"Akwai wanda yake da ja akan hukuncina?"
Ciroma ya faɗa yana zare ido fada ta yi shiru kowa ya kasa koda kwakkwaran motsi, hatta da waziri dake kare Aliyu na Uku ya kasa magana sai sadda kansa ƙasa da ya yi yana jin baƙin ciki akan abun da aka yi wa Aliyu zuciyar Aliyu tana farfasa ya karɓi takardar ya fice daga fada Magaji ƙaramin ne ya biyo shi a baya "Yaya ka yi haƙuri kowanne bawa da kalar tasa ƙaddara idan muka yi haƙuri komai zai wuce babbar damuwata yaya Gimbiya domin ita mutum ce mai zafin gaske marar karɓar uzuri dole ka toshe kunnuwanka domin Allah ne kaɗai yasan adadin maganganu da za ka ji daga bakinta.
"Karka damu magaji ƙarami nasani na aikata laifi mai girma amman duk da girman laifina a tsaye a dubi lamarina da idon basira na faɗi hujjojina da dalilai da yasa na yi aure batare da sanin alhalina ba, na kuma ɓoye hakan tsawon wasu shekaru haka sidam ba zan boye wannan al'amari mai girman gaske.
"Haka ne yaya ni dama jikina ya bani da dole akwai dalilinka na yi hakan.
Aliyu bai ƙara cewa komai ba ya cigaba da tafiya kamin ya isa ɓangaren sa ya sami kira daga ɓangaren mai babban ɗaki dole ya juya ya nufi can koda ya iso parlornta 'yan uwansa su biyar da suke uwa ɗaya uba ɗaya sun yi zaune zugu-zugun ƙanwarsa Hauwa da yaya Gimbiya sun sha kuka har idanuwansu sun kumbure, babban ƙasƙanci ne ga jinin sarauta ya waye gari an kore sa daga masaurata musamman Aliyu idan ya kasance ya aikata fasikanci. Jikinsa ya yi bala'in sanyi ya nemi wuri ya zauna yaya Gimbiya ta taso a mugun fusace ta yi kansa ta rufe shi da duka tana dukansa tana kuka tare da fadar maganganu marasa daɗi "Ka cuce mu Aliyu ka dasa mana baƙin ciki da har mu kwanta dama ba zai fita daga zukatanmu ba. Ka ja mana abun kunya da tozarci a zuri'ar mu, kasani ba za mu taɓa yafe maka ba.
Abdallah na Uku ne ya taso ya kama yaya Gimbiya ya maida ta wurin zamanta, daman Abdallah kusan halinsa ɗaya da marigayi Mahmood na Uku, halin dattaku da haƙuri da matuƙar wahala su biyu nan su yi fushi haka zalika mubashir wanda suke kira da magaji ƙarami, kasancewar shi ne ƙarami daga cikin 'ya'ya Usman na uku shiyasa ake kiransa da magaji ƙarami, sai kuma Gimbiya Hauwa wacce daga Aliyu na Uku sai ita. Ita ma Hauwa tana da sanyi hali sosai bata da hayaniya sai dai akwai ta da izza da taƙama, kusan halin mai babban ɗaki ta dauko.
"Dan Allah ya isa haka yaya Gimbiya wasu matsaloli ba a iya magance su acikin fushi, kamata ya yi ki tsaya mu ji ta bakinsa.
Abdallah na uku ya faɗa yana kallon cikin idanuwan yaya Gimbiya, wacce sai huci take yi tare da jin tsanar Aliyu.
"Babu buƙatar hakan Abdallah, tun da har ya zabi ya ci mutuncin mu ya tozarta mu, ya sani muma bama buƙatarsa daga cikinmu daga mun cire ka daga cikin yayan da mahaifiyar mu ta haifa, daga yanzu mu huɗu ne.
Aliyu ya ɗago ransa a ɓace yake kallon yaya Gimbiya kafin ya miƙe tsaye, idanunsa sun yi jajir "Daman can ban tsammaci sassauci ko tausayawa daga gare ki ba yaya Gimbiya, ga kowanne irin al'amari kanki kawai kika sani bakisan ki yi waninki uzuri ba, idan har barin cikinku shi zai sa ku rage jin raɗaɗi da zafin ɓata muku suna da nayi to albishirinku zan yi nesa daku har izuwa lokacin da gaskiya za ta yi halinta a wannan lokaci ku ne za ku nemi ni da kanku. Domin nasan wannan hukuncin da Ciroma ya yanke min kaitsaye akwai maƙarƙashiya acikinsa tare da munakisa, dole da akwai wata boyayyar manufa da yake so ya cimma. Zan koma Lagos ku yi haƙuri a bisa ɓata muku suna da nayi.
Yana karashe magana ya juya "Abbu mu ma za mu bika mu koma tare Lagos ɗin.
Zaheed ya faɗa cikin sanyi murya a rikice Fulani babba ta ɗago tare da daka masa tsawa "Ku koma ina? Ai ku da sake zama dashi hayatan-hayatan ko su kike yi ya ɗora ku a bakar hanyar da yake kai. Kashin kaji da ya shafa muku ya isa haka.
Daidai kofar fita Aliyu na uku ya tsaya cak! cikin kaɗuwa ya juyo yana kallon Fulani babba, bai taɓa tsammani fitar irin wannan maganganu daga bakinta ba duba da yadda take mace mai kawaici da kauda kai, ashe akwai ranar da za ta zo duk masoyansa su koma makiyansa. Ya juya da sauri ya fice, tafe yake yana haɗa hanya don har wani dishi-dishi yake gani.
Aliyu yana ficewa yaya Gimbiya tasa aka haɗa kayan sawar mai babban ɗaki tare da waɗansu muhimman abubuwanta, suka bar cikin masaurata daga nan suka wuce Abuja da ita.
Aliyu yana shiga ɓangarensa ya tarar da Safiya ta gama hada kayan sawarta da na yaranta dukka a manyan trolleys hatta da na Anaal ta haɗa bata bar ko ɗaya ba. Duk da tun zuwan Aliyu bata ga Anaal tare dashi ba taga twins amman babu Anaal acikinsu tashin hankali da take ciki ya hanata tambayar twins ina take.
Yana shigowa tambaya ta farko da ta fara masa "Ina Anaal?"
Yadda tai masa tambaya da daurarriyar fuska yasa jikinsa ya ƙara yi wani irin cikin sanyi murya ya ce "Tana Kano.
"Na kira wayarta bata shiga idan akwai wani layi ka gayamata idan tana bukatar gani na ta same ni a Bauchi.
"Bauchi? Safiya me za ki je yi a Bauchi? A tunanina za ki bini Lagos.
"A'ah! Bauchi zan koma gaban iyayena gara mu ba wa junanmu space Aliyu wata kila ta hakan za mu iya gane muhimmancin junanmu.
"Kina nufi kema za ki guje ni Safiya kema kina min kallon fasiki?"
"Ba ko ɗaya kawai dai ina gani lokaci ya yi da kowanne mu ke buƙatar hutu.
"Karki min haka Safiya Dan Allah karki guje ni adaidai lokacin da kowa yake guduna, ina tsananin buƙatarki kusa dani.
"Kada ka cilasta min Aliyu zuciyata ba za ta iya jurewa ba,ka tuna da adadin baƙin ciki da na dinga shanye wa akanka a wannan karon ka zo min da babban al'amari da nake bukatar nisanta kaina daga gare ka koda na ɗan wani takaitaccen lokaci ne Dan Allah ka bani wannan damar, ita kadai nake buƙata gareka.
"Safiya Dan Allah!
"Ya isa Aliyu kada ka cigaba da rokona saboda na rika na yanke hukunci, zan tafi.
Tana karasa magana ta juya idanunta na fidda zafafan hawaye, da sauri ya riƙo hannunta tana juyowa ya rungumeta sosai, cikin rauni murya mai cike da ban tausayi ya ce "Kamin ki tafi ki barni na ji ɗumin jikinki Safiya bansani ba ko shi ne abu na ƙarshe da zai sake kasancewa tsakanina dake, in fact ina buƙatar kafaɗar da zan ɗora kaina na yi kuka kuma a tausaya min har a rarrashini ina da yaƙini ke kaɗai ce za ki yi min wannan.
Kukan da Safiya take dannewa ne ya subuce mata ga baki ɗaya, tsananin tausayin mijinta ya lulluɓeta har batasan sanda ta ƙanƙame shi tana bubbuga gadon bayansa, wani irin jan numfashi Aliyu ke yi idanunsa sun ri ga da sun soye jaruntarsa ba za ta barsa ya zubda hawaye ba. Amma yana jin wani irin tuƙuƙi a kasan zuciyarsa. Sun ɗauki lokaci rungume da juna kamin ta janye jininta daga nasa ta juya da sauri ta nufi ɗakin yaranta Amal da Amatullah tarar dasu zaune sun yi zugu-zugun kowacce taci kuka wanda har zuwa lokaci basu daina yin sa.
"Ku taso mu tafi.
Ta faɗa cikin muryarta mai ɗauke da kuka, su Amal suna fitowa suka ga Aliyu da gudu suka rungumesa, tare da ƙarawa kukansu sauti.
"Ku yi haƙuri my little princesses Barbie Abbu bai kyauta muku ba ya zama silar zubda hawayenku.
"Ka daina faɗar haka Abbu dukkan mu, mun sani sharri aka yi maka kuma in shaa Allahu duk wanda yake da sa hannu wurin bata maka suna Allah ya tona masa asiri.
Amal ta faɗa tana shasshakar kuka.
Murmushi kurum Aliyu ya yi tare da sumbatar forehead ɗinsu, ya ce "Za ku tafi Bauchi tare da umminku idan komai ya daidaita zan zo gare ku, ku kula da umminku.
Safiya da kasa jure cigaba da jin kalaman Aliyu ta juya da sauri ta fice daga parlorn idan ta cigaba da tsayuwa zai iya karya mata da zuciya ta fasa tafiya, alhali tana gani tafiyarta ita ce zai basa damar fahimtar amfaninta cikin rayuwarsa. Ta hakan ne kaɗai za ta san matsayinta a wurinsa. Har parking lot ya rakasu yana tsaye har motarsa ta fice daga masarauta, sai da ya daina hange su kana ya juya jiri na dibar sa, sai lokacin ya ji wasu ruwa masu zafi sun sauka a kumatunsa a tsorace ya kai hannunsa ya shafi kumatun nasa, hawaye ya gani a tafin hannunsa. Da saurinsa ya koma ɓangarensa yana jin tsoron ya haɗu da wani yaga hawayen idonsa garesa wannan babbar kasawa ce. Cike da jarunta da ya ara ya yafa kansa ya harhada muhimman abubuwansa, ya yi parking ɗinsu a trolley biyu. Direbansa ya umarta da ya kaisa Airport har ya isa airport yana gwada kiran layunka Anaal, still dai a kashe. Misali ƙarfe 4:00pm jirgin da zai shiga ya ɗaga zuwa Lagos.
Amintacciyar jakadiyar Kilishi ce ta zo mata daddaɗan labari na korar alhalin mai babban ɗaki da Ciroma ya yi a maimakon ta ga farin ciki akan fuskar Kilishi sai taga saɓanin tunaninta, domin kuwa wata kalar zabura Kilishi ta yi, jikinta ya ɗauki rawa tana kakkarwa "Lallai ki sani Jakadiya Ciroma ya tafka babban kuskure wanda ba shi kaɗai ba har mu ɗinan sai ya shafa shiyasa tun farko na hane sa da hawa karagar mulkin kudu amma yaƙi ji, to tun da yaƙi ji lallai baya ƙi gani ba, a wannan karon bana tunani bokansa zai iya cetonsa daga wutar dashi ya kunnowa kansa ita.
"Ban fahimci wannan kurman allo naki ba ranki shidade shin ko za ki iya warware min zare da abawa?"
"Lokaci ne zai warware miki hakan jakadiya sai dai ina miki albishir da komai ya lalace ki tuna da maganar da jiya malam na kan tudu ya faɗa.
A rikice Jakadiya ta faɗi zaune daga durƙuso da take idanunta suka firfito waje "Na shiga uku uwargijiyata yanzu mene ne mafita?"
"Bana tunanin muna da wata mafita Jakadiya kawai dai yanzu ki yi kokari ɗan abun da ya rage mana ki fito dashi, gara ayi mutuwar kasko.
*ALH BELLO MADAWAKI MANSION*
Daga Daddy sai yaransa suka zo gidan su Rumaisa Mami kasa biyo su ta yi, saboda tsananin kunyar abun da ta aikata take ji. Kyakkyawar tarba Ammi ta yi musu cikin sa'a suka tarar da mahaifin Rumaisa yana gida a mutunce suka gaisa da Daddy, kana Daddy ya faɗa musu makasudin zuwansa.
"Babu komai Alhaji daman can wasiyyar da Rumaisah ta bari kenan